Showing 12001 words to 15000 words out of 25074 words
kwantar da ita
kan gado yacigaba, da aika mata da sa'konni, a ranar dai saida khaleed yasan Auta a matsayin
mace, aiko Auta tasha wahala ba kad'anba, shikuwa khaleed banda rarrashinta ba abinda
yake,yanata shimata albarka, sai gurin 'karfe d'aya da rabi bacci yayi awon gaba dasu Auta tana
jikin khaleed duk ta wani shagwa6e mashi.
Kiraye-kirayen sallar asubah ne ya tashesu daga baccin da suke, khaleed ne yafara tashi
yashiga toilet d'in dakinta yayi wanka, sannan itama ya ha'da mata ruwa me dumi da Kansa
yazo ya d'auketa yakaita toilet yayi mata wankan tsarki tare da gasa mata jikinta, sannan yasa
sabulu ya wanketa ya d'aura mata towel ya d'aukota, kan gado ya direta sannan ya d'auko mata
doguwar riga ta atamfa, simple ta sanya sannan suka gabatar da sallar asuba, bayan sun gama
suka koma kan gado suka kwanta.
Wani sabon bacci yayi awon gaba dasu me cike da nisha'di da tsantsar 'kaunar juna.
Zee Elkaseem
Mmn khady.
[10/16, 7:55 PM] +234 816 616 9254: [09/08 11:12 am] .:
*AUTAR HAJIYA*
®NWA
_ZEE MMN KHADY_
```Page````111-115```
✍ Ahaka Fadila tayi kwana biyu tana masu girki, kullum daurewa kawai khaleed keyi yana cin
abincin ba dan yana jin dad'insa ba, Auta ma daurewa kawai take dan ta lura da yanda shi
kanshi me gidan yake cin abincin yana 6ata rai kamar yana cin magani, amma beta6a bud'a
baki yace beyi dad'iba, saboda haka itama bata ta6a nuna kome ba.
6anagaren Fadila kuwa tayi mamakin yanda khaleed ke daurewa yana cin abincinta, wanda ko
ita kanta data girka shi bata jin dad'insa.
Da misalin 'karfe shidda na yamma Auta ta shiga kitchen ta d'ora girki, kasancewar yau Fadila
ta cika kwanakinta biyu.
Cikin tsari da tsafta da 'kwarewar girki Auta take aiwatar da girkinta, jalouf din shinkafa da
makaroni ta dafa, Wanda yaji kayan lambu da kayan kamshi, da kayan d'and'ano na girki, hanta
zallah tayi girkin dashi maimakon tasanya nama, cikin 'kan'kanin lokaci 'kamshin girkinta ya
gauraye gidan.
Fadila na d'akinta taji k'amshin girkin Auta ya daki hancinta, take ta had'iyi wayu, dan tasan yau
zasu debi girki,
```{Kaji fadila iyayen kwadayi ansan aci da dad'i amma ba'asan a girka da dad'i ba }```
Haka Auta tagama girkinta ta kammala kome ta jera kan dining table, gefe kuma ga kunun ayar
data had'a Wanda yaji dabino da kwakwa tun a gurin markad'en ayar, sannan ta zuba mashi
sugar dai-dai kima saboda bataso yayi za'ki da yawa, ga kamahin flavor mai d'andanon ayaba,
sai 'kan'kara data jefa ciki lokaci guda jug d'in yayi ra6a.
Da misalin karfe takwas da rabi suka hallara kan dining domin cin abinci, Auta ce ta zuba ma
kowa ta ajiye gabanshi, lokaci guda suka d'ebi abincin suka kai bakinsu, Fadila taji dad'in
abincin har cikin kwanyarta, khaleed kuwa lumshe ido yayi, yana taunar abincin cikin nishad'i ya
kalli Auta yace " Zainab amma bayan kinyi candy kin shiga makarantar koyon girki koh?, Auta ta
tuntsure da dariya tare dasa hannunta ta tallabo bayanshi, tace "bari ayima waigi kada ka fad'i
daga kujerar, shima dariyar yayi yace "Allah kuwa da gaske tambayar ki nake, indai ba
makarantar koyon girkiba yaushe mace zata iya tsara abinci haka wanda ko hotel baze kama
'kafarsaba, lokaci guda ta rage dariyar datake tare da gyara zama tace "wannan makarantar
Hajiya ce, domin itace ta dage gurin ganin na iya girki kala daban-daban, tin daga na zamani
har zuwa na gargajiaya, cike dajin dadi da nishad'i khaleed yakara kai abincin bakinsa, yace
"Amma gaskiya Hajiya ta kyauta mana Allah saka mata da Alajannah Firdausi, Auta tace
Ameen ya rabbi.
Fadila kuwa wani irin kishi ne ya tokare mata zuciya, lokaci guda taji bata iya cin abincin duk da
dad'insa datake ji haka tabarsa.
Bayan sun kammala cin abincin, Auta ta zuba masu kunun ayar suka sha, nan ma saida
khaleed yayi wani santin, Auta kuwa dayayi saita tareshi tace bari ayimashi waigi.
Fadila kuwa Auta tagama 'kuleta wani irin haushinta takeji,
Auta kuwa ta lura da yanda Fadila ta 6ata ranta saboda haka, ranar dad'i har cikin ranta,
basu wani dad'e suna fira ba Auta ta nuna tana jin bacci, haka suka tashi suka nufi d'aki tare
dayima Fadila saida safe, itama d'akinta tanufa tana shiga ta fad'a kan gado ta fashe da kuka,
cikin ranta tana ganin laifin momynta da bata koya mata girkiba, kodayake itama Momyn tata ba
dakanta takeyiba masu ayki ne kemata koda kuwa dahuwar ruwan zafine.
Haka tacigaba da tunani kala-kala, daga 'karshe bacci 6arawo yayi gaba da ita.
Zee Elkaseem
Mmn khady
[09/08 1:02 pm] .:
*AUTAR HAJIYA*
®NWA
_ZEE MMN KHADY_
```page``` 116-120
✍ washe gari da safe Auta ta had'a break fast, nan suka zauna sukaci kamar yanda suka
saba, bayan sun kammala khaleed ya tashi tare da d'aukar makullin motarsa, yace "nizan wuce
gurin aiki saina dawo, Fadila tace Allah kiyaye hanya ya kuma bada sa'a yace "Ameen, sannan
ya kalli Auta yace "zan tafi amma zan dawo da wuri, inaso kiyi mani girki me dad'i wanda zesa
kunnena ya tsinke, wani tattausan murmushi tayi mashi tace "zan yi maka girki me dad'i, amma
ba wanda ze tsinka kunnenka ba, sai dai Wanda zesa kayi santi wanda yafi Wanda kayi jiya,
yace to shikenan nizan tafi, ita ta d'aukar Mashi jakarsa tarakashi har bakin mota saida taga
tafiyarshi tana daga mashi hannu harya fice daga gidan sannan takoma zuciyarta cike da farin
ciki.
Fadila tariga ta gama 'kulewa da yanda koda yaushe khaleed ke yabon girkin Auta, amma ita
idan girkintane yanaci yana 6ata rai kamar mecin magani, amma ita bata ganin laifin kowa sai
na momynta dan itace bata koya mata girkiba, gashi Auta har magana take gayamata a
kaikaice, wai makarantar Hajiya ta koyi girki," Hmm tayi kwafa sannan ta wuce d'akinta.
Da misalin 'karfe daya da rabi na rana Auta tagama had'a kome ta jera kan dining, 'kamshin
girkinta yagama buge ko'ina na gidan kamar yanda ta saba.
Dambun shinkafa ne tayi me rai da lafiya, Wanda yaji kayan lambu, Kara's da kabeji da
sauransu, ga kamshin kori, nama ta yanka gutsi-gutsi ta zuba gurin yin dambun ta yanda zeyi
wuya mutum yayi cokali guda batare daya ci da naman ba, gefe Kuma zo6o ne tahad'a Wanda
shima yayi dadi sosai yaji flavor me 'kamshin Abarba yayi sanyi dan jug d'in har ra6a yake.
Bayan ta kammala wannan d'akinta tanufa ta she'ka wanka, bayan tagama gyara ko'ina na
gidan da kuma kitchen d'inta, ta turare gidan da turaren wuta, abin dai gwanin birgewa.
```{ kaini su Auta an iya kwanare da sa kishiya taji haushi}```
Da karfe biyu khaleed ya dawo gidan, bayan Auta tarakashi d'akinsa yayi wanka, ya canja kaya,
wata 'karamar riga ce yasanya sai wando three quarter, sannan suka hallara su duka kan
dining, Auta cike da nishad'i da jin dad'i ta zuba ma kowa a plate tare da sanya cokali, sannan
ta tsiyayama kowa zo6o a cup d'in glass ta ajiye gabanshi, sannan itama ta zauna, khaleed cike
dajin dad'i ya d'ebi abincin yakai bakinsa, tare da lumshe ido.
```Yasalam ya furta tare da saurin furzar da abincin dake bakinsa```
Lokacin itama Fadila ta kai abincin bakinta dan jin meke faruwa, da sauri ta zuddo abincin tare
da saurin d'aukar ruwa tasha, dan kuwa wani irin mugun gishiri ne yayi yawa cikin abincin, dan
komin dauriyar mutum baze iya cin saba.
Cikin tsananin rud'ewa Auta ta ebi abincin taci dan taji meye yasa khaleed zubar da abincin
data 6ata lokaci gurin girka Mashi dan ya yaba, wani irin zau taji abakinta
*Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un* tashiga furtawa, aranta tace yaushe nayi wannan aikin haka,
yaushe na zabga gishiri cikin abincina har ya wuce misali.
Khaleed kuwa kasa magana yayi, dan yasan ko be fad'aba suduka sun san kome kenan, baya
bu'katar a can-cana maganar.
Kitchen d'in Auta yanufa ya d'ebo cake cikin plate dan kuwa yunwar jinta yake sosai, dan har
gidan abokinsa Ahmad yaje akayimasa tayin abinci ya'ki ci dan yasan Auta zata yimashi special
coaking .
Zama yayi ya fara cin cake d'in sannan ya d'auko zo6on da Auta ta zuba mashi a cup yakai
bakinsa, da sauri ya cire cup d'in daga bakinshi dan jin wani sabon d'and'ano a zo6on wanda
beyi tinanin jinsa acikiba, lokaci guda ya maida kallonshi ga Auta wanda mamaki yahanata
motsawa daga inda take, Khaleed yagama 'kulewa da Al'amarin Auta, saboda haka batare dayace kome ba yatashi
ya wuce d'akinsa,
Cikin tsananin mamaki Auta ta d'auki cup d'in ta kur6i zo6on gishiri taji zau Wanda har ya
zarce za'kin sugar, kalmar *innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un* kawai take furtawa,
Binshi tayi d'akinsa kwance ta iskeshi kan gado ranshi yayi matu'kar 6aci, nan tashiga
rarraahinshi tana bashi ha'kuri tare da nuna mashi wallahi batada masaniya akan wannan
gishirin da yayi yawa cikin abinci barantana kuma cikin zo6o.
Fadila kuwa koda taga shigewarsu d'aki wata irin shu'umar dariya tayi tace ~```Hmm Auta dani
kike magana```~
Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 7:55 PM] +234 816 616 9254: [06/08 10:33 pm] .: [06/08 9:42 pm] .:
*AUTAR HAJIYA*
®NWA
_ZEE MMN KHADY_
*_Page_* 101-105
✍ A firgice Fadila ta farka daga baccin datakeyi da niyyar zuwa falo dan kada khaleed ya
dawo ya wuce d'akin Auta bata saniba.
Innalillahiwa'ainna,ilaihirraji'un tafad'a tare da saurin le'kewa ta windon d'akinta dan tabbatar ma
idonta abinda ta gani gaskiya ne,
Hasken ranar daya haske idonta shine ya tabbatar mata da cewa tabbas ba mafarki takeba,
safiya tayi, da sauri ta fita zuwa d'akin khaleed dan taga nan ya kwana ko kuwa, tana zuwa ta
tura 'kofar d'akin tashiga taga ba kowa aciki, kuma babu Alamar mutum ya kwana aciki.
Take wani irin kishi ya turni'keta, "shikenan abinda ta kwana ukku tahana idonta bacci
sabodashi yariga ya afku, jitayi 'kafafunta sun kasa d'aukarta, batasan lokacin data sulale
'kasan d'akinba kan tiles tayi zaman dirshan tana zubar da wasu zafafan hawaye, a zuciyarta
take cewa:
*_(Shikenan khaleed ka cuceni ka gama sanyawa yarinyar nan ta rainani, shikenan khaleed ka
fito fili ka nuna kafi son Auta a kaina, )_*
Shiru tayi na kimanin minti goma tana tunani, tana sa'ke-sa'ke a zuciyarta, zuwa can sai tayi
wani shu'umin murmushi, tace
*~Hmm Auta idan Kin san wata baki san wata ba "Hmm dani kike magana~*
: Tashi tayi daga zaman takaicin datake, tanufi d'akinta tafad'a toilet tayi wanka sannan ta d'auro
Alwala ta kabbara sallah lokacin har karfe bakwai da minti sha shidda na safiya, bayan ta idar
da sallar ta wuce gaban dressing mirror ta 6ata lokaci gurin gyara fuskarta, sannan ta sharce
gashinta wanda koda yaushe yake a 'kone, ta d'aure shi tsakiyar kai, bayan tagama wannan
wadrop tanufa wasu Riga da siket na atamfa ta d'auko d'inkin zamani ta sanya ajikinta, kayan
sun matu'kar zama ajikinta, dan ba 'karamin kyau sukayimata ba, sannan ta d'auko manyan
turarrukanta masu dad'in 'kamshi ta feshi jikinta dasu, bayan humra data rin'ka mungulawa
ajikinta.
Lokaci guda kuwa 'kamshinta ya mamaye dakin,
Tana cikin d'aura d'an kwali ne khaleed yashigo d'akin da sallama, sanye yake cikin farar
shadda d'inkin zamani, bayan ta amsa sallamar ta juyo ta kalleshi, tayi mashi wani tattausan
murmushi tace "Barka da fitowa my man, wani irin dad'i yaji ya ratsashi har cikin zuciyarsa, dan
yayi tunanin Fadila zata tada hankalinta ne idan gari ya waye ta tabbatar da d'akin Auta ya
kwana, shima wani murmushi ya sakar mata, har cikin ranshi yaji dad'in yanda ta tarbeshi, ga
kwalliyarta ta masifar yimata kyau, lokaci guda yaji ta matu'kar burgeshi, take kuma yaji wani
sabon sonta ya shiga zuciyarshi.
Ahankali ya 'karaso inda take yayi mata wata kya'ky'kyawar runguma, sannan yabata kiss a
kumatu yace "Gud morning my special wife, har cikin ranta taji dad'in kalamansa, itama ta
mayar masa da nata sakon kiss d'in a lips, tace "morning my man.
Auta kuwa koda ta tashi kitchen tafad'a dan had'a musu break fast,
Cikin k'ank'anin lokaci tagama had'a kome na break ta jera kan dining table, sannan takoma
d'akinta ta fad'a toilet ta she'ka wanka, bayan tafito ta tsaya gaban dressing mirror tayi simple
make-up sannan ta nufi Wadrope ta d'auko wasu English wear riga da siket, siket d'in farine har
'kasa, amma ya kameta daga sama, sannan k'asan ya bada fad'i, jikinsa akwai kwaliyya flowers
da copee zare, sai rigar copee colour, tasha ado da duwatsu daga gabanta, rigar batada hannu,
sai wani siriri kamar na bes, bayan tasanya kayan sun matu'kar yimata kyau, wani 'karamin farin
gyale ta d'auko tayi rolling din kanta, sai ta ida fitowa balarabiya sak.
Zee Elkaseem
Mmn khady
[06/08 11:42 pm] .: [06/08 11:10 pm] .:
*AUTAR HAJIYA*
®NWA
_ZEE MMN KHADY_
*_Page_* 106-110
✍ Zaune suke kan dining suna break, kowanensu ci yake yana jin dad'in abin, dan kuwa Auta
ba daga baya ba gurin iya girki, ita kanta Fadila ta jinjina ma Auta a zuciyarta, dan ko a hotel
abinci baze wuce wannan dad'i ba.
Bayan sun gama ne khaleed yafara magana "Amma gaskiya naji dad'in yanda kuka dawo
yanzu, kungane wannan rigimar ba abinyi bace, saboda haka inaso inyi amfani da wannan
dama inyimaku nasiha akan dan Allah ku had'e kawunanku ku zauna lafiya, ba cuta ba cutarwa,
domin zamanku lafiya shine kwanciyar hankalina.
Sannan ya kalli Fadila, yace "kinga Fadila jiya na kwana d'akin Auta, to gobema zan kwana
d'akinta kinga kwana biyu kenan, daga lokacin kuma zan dawo d'akinki inyi kwana biyu.
Suduka sunyi shiru suna saurarensa, kowace da abinda take kitsawa a ranta.
Auta tace "to wane lokaci kake ganin ya dace ari'ka kar6ar aykin? Khleed yace "Ku yakamata
ku fidda, sai lokacin Fadila tayi magana tace kamar da 'karfe biyar da rabi na yamma, ta kallesu
tace hakan yayi koh,? Khaleed yace "yayi.
Haka dai suka d'an ta6a fira, wacce yawancinta tsakanin khaleed ne da Fadila, dan Auta ita
haushi ke hanata magana, dan ita kome Fadila zatayi bala'in haushi yake bata, wani irin mugun
kishin khaleed ne ke kamata duk lokacin dataga yana kula Fadila.
A haka aka cikama Auta kwananta d'aya batare da wani tashin hankali ba, dan Fadila ta hakura,
kuma kullum girkin Autar takeci, dan kuwa tare suke cin abinci su duka,
••••••••••••••••••••••••••••••••••••
Yau yakama ranar da Fadila ta kar6i kwana, saboda haka itace tayi masu abincin dare,
Ta had'a kome ta jera kan dining, da misalin 'karfe takwas na dare suka zauna cin abinci,
Fadilar da kanta ta zuba ma Auta bayan ta zuba ma khaleed ta tura mashi gabanshi.
Auta cike da jin haushi ta debi abincin takai bakinta, bata San lokacin da tasaki wani tattausan
murmushi ba dan jin testing d'in abincin, a zuciyarta tace
" ~_Salmanu!...... kada inga salame idan haka take_~"
Dan jin abincin tayi ba wani testing ko kad'an, aiko take wani irin farin ciki ya mamaye zuciyarta,
data tuno cikin kwana biyunan yanda khaleed ke buga santi idan yana cin abincinta, koda
yaushe yana yaba mata kan iya girki.
Khaleed kuwa koda ya d'ebi cokali d'aya yakai bakinsa, yaji abin ba'a magana, daurewa yayi ya
had'iye na bakinsa, haka dai ya daure yaci gaba da ci, itama Auta dataga haka saita ri'ka
tutturawa tanaci tana jin dad'i aranta, ita kanta Fadilar daurewa kawai take tanaci dan tasan ba
yanda za'ayi tayi girki kuma ta'ki ci' sai afara zargin kota tasarma rashin gaskiyane, amma ko ita
kanta tasan abincin beyi dad'iba, saboda haka ta dage tayita d'ibar girki.
Bayan sun kammala sun d'an ta6a fira har kusan 'karfe sha d'aya da rabi Auta nata jan khaleed
da surutu dan kada su tafi su kwanta, shikuwa ya biye mata dan bemasan lokaci yayi nisa haka
ba.
Saida Fadila tagaji, ga bacci tanaji, tanata hamma sannan ta kalli khaleed tace "my man bacci
nakeji kazo muje kaga dare yayi har sha d'aya, sai lokacin ya duba agogon wayarsa yaga k'arfe
sha d'aya da minti arba'in da tara, saboda haka khaleed yatashi sukayima Auta sallama suka
wuce d'aki.
Itama nata d'akin tanufa, ta cire kayan jikinta ta sanya wata doguwar riga ta bacci ta haye gado
da niyyar yin bacci, amma ina kasawa tayi lokacin data tuno yanzufa khaleed yana d'akin wata
ba itaba, kuma ze nuna mata soyayya irin yanda ya nuna mata.
Zunbur tayi ta tashi kamar wacce aka tsikara, takama zagayen d'akin zuciyarta nata tafarfasa,
falo ta dawo ta zauna ta sa hunnu biyu ta buga uban tagumi, zuwa can taga zaman beyi ta tashi
ta dinga safa da marwa tsakanin falo da d'akinta, daga 'karshe da takaicin ya ciyota batasan
lokacin data fashe da wani irin kuka ba, tafad'a kan gado tacigba dayi, har misalin 'karfe ukku da
rabi na dare Auta na aykin kuka, daga 'karshe dai bacci 6arawo