Showing 21001 words to 24000 words out of 25074 words

Chapter 8 - Autar Hajiya Book Compelet By Zeey Maman khady

20 Jul 2026

79

da mijina, menayimaki dazaki
saka mani da wannan,
Wani sanyi Auta taji cikin zuciyarta, dataga Fadila bata nemeta da fad'aba, danko da dafarko
tafara tinanin yanda zasu kwashe, amma sai taga Alamun Fadila na Neman sulhu ne.

Har cikin ranta taji tausayin Fadila, yakamata, dan ita dama tincan mutum ce mai matu'kar
tausayi.

Cikin sanyin murya Auta tafara magana, "ni dama ba da niyyar wani Abu nayiba, naga kin
shigone kamar zaki dakeni, nikuma kinga dole in nemarma kaina mafita.

Fadila tayi wata nannauyar ajiyar zuciya, cikin Zuciyarta tace
```{"Da kinsan abinda nazo dashi lokacin da baki sakamin da abinda kikayimaniba}```

"Koda kikaga na shigo ba da niyyar tashin hakali Nazo ba, nazo ne kawai muyi magana.

Auta tace "To ayni bansaniba, da saikiyimin sallama kafin ki shigo, tunda naga kin shigo ba
sallama sai inyi tunanin ba arzi'ki yakawokiba,
"Amma kiyi hakuri, tafad'a tare da juyar da fuskarta gefe, tana wani turo baki.

Fadila ta 'kara zama tare da matsowa kusa da Auta, Auta tad'an matsa, dan ita har yanzu da
d'an sauran tsoro tattare da ita, gani take fadila nada wata manufa cikin zuciyarta

Fadila tace "Amma miye yasa kike 6atamin duk wani abu dana dafa, a gidannan?

Auta ta turo baki tace "to ay ke kikafara, dan rannan da kaina na kamaki, kina zubamin gishiri a
binci, kawai kyaleki nayi a lokacin, idan bazaki manta ranar danayi sakwara da miyar agushi.

Fadila tayi murmushin takaici, mai cike da nadamar abinda ta aikata tun farko,

*_(Dama ance farau batada zafi sai ramau)_*

"To yanzu dai nazo neman sulhu, yakamata mubar duk wannan abun damukeyi, kinga
bekamata ace mun zauna muna yima kanmu abunda be daceba.

Auta tace "ni dama ban d'auki abun da zafi ba, kawai dai kinsan hausawa sunce _*"Ramuwar
gayya tafi gayya zafi*_
Amma kome ya wuce Allah shige mana gaba, Fadila ta Amsa da "Ameen.


*```To you my namesy Autar Hajiay```*

_ina mi'ka gaisuwa ga masoya a duk inda kuke_

~kibiyo *Zee Mmn khady* akwai sauran labari~

Zee Elkaseem
Mmn khady.
[10/16, 7:55 PM] +234 816 616 9254:

*AUTAR HAJIYA*




®NWA



_ZEE MMN KHADY_


```page``` 171-175





✍ koda Hajiya ta farfad'o daga dogon suman datayi, doctor ya'kara dubata ya tabbatar da
lafiyarta, sannan yace za'a iya tafiya da ita, amma ari'ka kula da kiyaye abinda ze jefata cikin
tashin hankali.

Daga asibitin gidan khaleed aka wuce da ita kai tsaye, dan an riga an wuce da gawar a can.

Cikin likaffaninsu ta iskesu, hankalinta yayi matu'kar tashi, ta fashe da wani sabon kuka, tana
cewa.
*shikenan zainab kin tafi kin barni bayan kinsan banida wani d'a ko d'iya sai ke, Allah kai ka bani
zainab kuma kai ka kwace abinka badan baka sonta ba, ya Allah ka ji'kan zainab ka kai haske
cikin kabarinta*

Haka tacigaba da kuka tanayima Auta addu'a nan mutane aka shiga rarrashinta ana kwantar
mata da hankali.


A asibiti kuma momyn khaleed da momyn Fadila sunacan suna jiran abasu dama su shiga su
duba me jego da babynta,
sai bayan magrib aka basu izinin Shiga,
Haka suka shiga jikinsu ba 'kwari ko kad'an,

Zaune take kan gado, ga baby gefenta, kuka take kamar zata fitar da ranta, idanunta sun
kumbura fuskarta tayi ja, tayi face-face da hawaye, jin motsin shigowar mutane yasa ta d'ago da
fuskarta wadda ruwan hawaye yagama wankewa, takai dubanta garesu.

Momyn fadila itace gaba, tana zumud'in ganin fadila da babynta,
```Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un```
Ta faurta lokacin da idanunta suka sauka kan Auta, Zaune kan gado ga babynta kusa da ita.
Momyn khaleed ce ta dafe, 'kirji Alamar mamaki tace
*"Auta dama ba ke bace aka cemana kin mutu ba*
.Auta ta fashe da wani sabon kuka, tana cewa, Momy fadila.....fadila.... ce tatafi ta barni, wani
sabon kuka ya kwace mata.

Momyn fadila najin haka tanemi numfashinta ta rasa, nan tafa'di sumammiya, Momyn khaleed
tarud'e da ganin yanda 'yar'uwarta ta suma,
Da sauri ta ebo ruwa ta yayafa mata, nan ta farfad'o,

Zaunar da ita Momyn khaleed tayi tana rarrashinta, tana gaya mata, irin Rahamar da Wanda
yamutu gurin haihuwa yake samu, tace "kawai yanzu Addu'a Fadila take nema garemu ba kuka
ba.

Wani sabon kuka Momyn Fadila ta fashe dashi, dan rarrashinma da akemata jitake kamar ana
zuba mata garwashin wuta cikin zuciyarta, shiru suka d'anyi nawasu yan mintittika, bakajin
kome sai sheshshekar kukan Auta, Momyn khaleed ta maida hankalinta kan Auta tana
rarraahinta, sai jin fad'uwar Momyn Fadila tayi, A hanzarce tajuyo gareta, tarin'ka jijjigata tana kiran sunanta, amma ina ba maganar lumfashi
tattare da ita, cikin tsananin rud'ewa momyn khaleed tafita tana Neman taimako, wasu leburori
ne mata suka taimaka mata, suka d'ora momyn Fadila kan gadon da ake tura marassa lafiya
aka nufi Emergency da ita, nan fa lokitoci suka taru anata Abu d'aya amma numfashi ko
Alamarsa babu jikin momym Fadila, amma kuma da an Auna sai aga zuciyarta na bugawa
Alamar akwai rai tattare da ita.

Oxygen aka sanya mata *(Abin jawo numfashi)*
Sai lokacin Momyn khaleed ta buga waya ta sanar da daddyn fadila halin da ake ciki, aiko cikin
tsananin rud'ewa ya iso asibitin, dan shima yayi tinanin Auta ce ta rasu amma yanzu ance
Fadila ce
d'iyarshi wacce yakeso, wasu guntayen hawaye suka zubo daga idonshi, yasa hannu ya goge.

Sai 'karfe hud'u na asuba Momyn Fadila ta farafad'o, da misalin 'karfe takwas doctor yabata
sallama dan ganin jikin nata da sau'ki sosai.

Lokacin kuma aka sallami Auta, bayan likitan ya tabbatar da lafiyarta data babynta.

'Karfe tara dai-dai suka isa gida, lokacin an fito da gawar Fadila data babynta,

Aiko da gudu Auta ta fito daga motar, tana goye da babynta, yayinda momyn khaleed ke goye
da 'diyar da fadila ta bari.

Bata ko kalli yawan mutanen dake gurinba tabi tacikinsu ta isa gaban makarar ta ri'ke tana cewa
```Wayyo sister fadila kada ki tafi ki barni, fadila ki dawo mu zauna mucigaba da gina
rayuwarmu yanda muka tsara.... Fadila kin manta munce zamu rike yaranmu mu had'a
kawunansu su tashi tsin-tsiya mad'aurinki daya, wayyo sister fadila ki dawo garemu....``` haka
tayita surutai tana kuka, nan aka kakkamata ana bata ha'kuri aka shige da ita cikin gida,

Hajiya tana cikin gida tanajin hayaniya daga waje, sai kunnuwanta suka ri'ka jiyo mata kamar
muryar Autar ta, amma saita share tacigaba da istigifari tana nemar ma Auta rahamar ubangiji,
dan tariga tasan Auta ta mutu kuma Wanda yamutu baya dawowa.

Da sauri ta taso dan ganin anshigo da Auta tana kuka, wasu mata sun rirrekata,
Cike da mamaki ta isa gareta tace Auta dama bake bace kika mutu, bata bata amsaba sai wasu
zafafan hawaye dasuka 'kara ganagarowa daga idanunta.


Hajiya batasan lokacin data rugume Auta ba tana wani irin kuka me wuyar fassara, na farin
cikine kona ba'kin ciki.

Da misalin 'karfe sha d'aya yan kai gawa suka dawo, Allahu Akbar ankai Fadila makwancinta.

Lokacin Kuma akayi addu'a aka shafa, gidan yayi tsit bakajin kome sai sheshshekar kukan
mutane 'kasa-'kasa.








```Kulli nafsin za'ikatul maut, dukkan mai rai mamacine " fadila tarigamu
gidan gaskiya```





Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 7:56 PM] +234 816 616 9254: [15/08 9:39 am] .:

*AUTAR HAJIYA*




®NWA



_ZEE MMN KHADY_



```Page``` 161-165




✍ Alhmdulillahi dan kuwa yanzu ansamu jituwa tsakanin Fadila da Zainab ```{AutarHajiya}```
yanzu kowace tarage jin haushin 'yar'uwarta,
Saidai fa maganar girki idan fadila tayi, basu iya ci sai dai su d'an yafuta su tashi badan sun
'koshiba, Auta kuwa kalaluwan girki takeyimasu masu dad'in gaske.

Watarana Auta na zaune falo tana kallon wani tsohon Indian film mai suna *(Maharaja)* ta
maida hankalinta tsaf kan TV sai jitayi an rufe mata ido ta baya, takama lalube tana dariya,
takama hannun da aka rufemata fuska ta ri'ke tana dariya, tana cewa "dan Allah ko waye ayimin
afuwa kada ayi wani Abu a film dinnan ban ganiba,
Sakin fuskar tayi ta zagayo ta zauna kusada ita, tana dariya itama Auta dariyar take, takai
kallonta ga Fadila tace "Kai sister yanzu abinda kikayimin kin kyauta, kinja an wuce banga wani
wurinba, Fadila tayi dariya tace "to ay sai kiyo tariya, cike da nishad'ia Auta ta mi'ko mata
remote d'in tana dariya tace "kar6i tariyo min, dan tasan ba maganar tariya tunda ba kaset bane
ta sanya.
Fadila tayi dariya tace "ni ban iya wannan tariyar bakedai ki tariyo tinda kece meson kallon,
murmushi kawai Auta tayi tacigaba da kallonta.

Kusan Awa d'aya da yan mintoci Fadila na zaune tana taya Auta kallo, saida film d'in ya'kare
ana shirin sanyo wani, Auta takai dubanta kan agogon dake manne jikin bangon d'akin taga har
12 ta d'an gota.

Auta ta kalli fadila tace girki fa? Kinsan fa rana tayi baki d'ora mana ba, gaskiya ki tashi kada
kiyi mana horon yunwa, fadila tayi dariya tace wace ni in horaki da yunwa, kinaso me gidan ya

d'aga min yellow card kenan abani hutun sati biyu, Auta tayi dariya tace ayko baze fara ba,
kinsan kuwa irin son dayake maki, ai ko hutun kwana biyu baze iya bakiba baranatana sati biyu,
dariya sukayi su duka.

Bayan shiru ya ratsa na yan wasu mintittika Fadila takai dubanta ga Auta tace "Niko Auta me
zaihana murin'ka yin girki tare, ranar girkinki muyi tare nima idan nawa yazo muyi tare.

Auta tayi dariya, tariga tagama d'agowa da fadila, so kawai take tari'ka tayata dan itama tasamu
girkinta yayi armashi kamar nata.

Tare suka shiga kitchen suka fara girki, farar shinkafa suka dafa me had'e da makaroni, sannan
sukayi miya mai rai da lafiya, cikin 'kan'kanin lokaci suka gama suka jera kome kan dining
sannan suka gyara kitchen d'in tsaf sukayi moping, kafinnan kowace tawuce d'akinta ta sheka
wanka suka fito falo suka zauna zaman jiran me gidansu, sunyi kyau suduka shar dasu abin
gwanin ban sha'awa.

Khaleed ne yashigo gidan da sallama suduka suka tashi suka tarbeshi sunayimashi sannu da
zuwa, fadila ta kar6i jakar dake hannunsa ta wuce mashi da ita d'akinsa,

Saida yaba Auta lafiyayyen kiss sannan ya wuce d'akinsa, ya tarar har fadila tagama had'a
mashi ruwan wanka,

Wanka yashiga, bayan yafito ya sanya kananan kaya marassa nauyi, sannan suka fito suka
zauna kan dining, sunfara cin abinci gwanin ban sha'awa sunata fira suna dariya,.

khaleed ya kai dubansa ga Fadila yace waini fadila kodai kema kin Shiga makarntar koyon
girkine bansaniba,? Auta tayi saurin tashi ta d'auko filo daga cikin filon kujerun daka zagaye a
falon ta mi'koma Fadila tana dariya tace "kar6i sister yimasa waigi kada yafadi ace mune muka
kadashi, suduka suka sanya dariya hada kyalkyatawa,
Fadila tad'an tsagaita da dariyar datake tace "bawata makaranta nashiga ba illah makarantar
sister d'ita gata zaune kusa dakai, ta nuna Auta.

Cike da jin dadi, khaleed yad'aga hannunsa sama, yace "Allah nagodema daka bani mata
nagari masu sona masu 'kaunata masu son kasancewata cikin farin ciki koda yaushe, ya
kallesu su duka yace Allah yayi maku Albarka suduka suka amsa da "Ameen.

Ranar dai haka suka wuni cikin nushad'i da annushuwa, dan ranar khaleed be fita ko'inaba,
saboda jin dad'in zaman gidan dayayi.

*************************
*_BAYAN WATA TAKWAS_*

Ahankali take takawa zuwa d'ankin Auta saboda nauyin da cikinta yayimata, tura kyauren d'akin
tayi sannan ta shiga da sallama, Auta dake kwance kan kujera 3seater itama da 'katon cikinta,
idanunta rufe kamar me bacci, jin shigowar Fadila yasa ta bud'esu takai dubanta gareta, sannan
takai dubanta ga cikin Fadila, har cikin ranta take tausayama Fadila yanda take fama da ciki,
dan tinda tasamu cukin take ta rashin lafiya, yau zazza6i, gobe ciwon kai, ga kuma rashin 'karfin
jiki, babban abin ban tausayin shine tinda Fadila tasamu ciki bata iya cin abincin kirki, ga wani
irinkumburi datayi, danma koda yaushe khaleed na kula da lafiyarsu itada Auta.

Duk da itama Auta tana d'an ta6a rashin lafiyar jefi-jefi, amma idan ka kalli fadila sai kace Auta
ba ciwo take ba.

Tare suka fito falo suka zauna suna firar duniya, duk rabin firar tasu ta yanda zasu tsara
rayuwarsu ne nan gaba, da yanda zasu had'a kan 'ya'yansu sutashi kansu a had'e.









Zee Elkaseem
Mmn khady
[15/08 11:11 am] .:

*AUTAR HAJIYA*




®NWA



_ZEE MMN KHADY_


```Page``` 166-170

✍ Yau Fadila ta tashi da matsanancin ciwon mara da ciwon baya, ga 'kugunta da takeji kamar
ze 6are saboda azabar ciwo,
Daga khaleed har Auta sun rud'e sun rasa inda zasusa Kansu, cikin tsananin rud'ewa khaleed
yakira Momynsa yasanar da ita halin da fadila take ciki, nan ta umarceshi da sutafi asibiti
gatanan zuwa asbitin, tare da taimakon Auta aka kai Fadila mota sai asibiti,

An wuce da ita labour room, nurses sun taru kanta anata faman amma, har 'karfe 3 na rana
bata haihuba, lokacin Momyn Fadeela ta iso asibitin cike da tashin hankali, nan ta iske Momyn
khaleed sai kai komo take cikin asibitin, kallo d'aya zakayimata ka gane tana cikin tsananin
damuwa, khaleed kuwa tagumi yayi yarasa me kemasa dad'i.
Lokacin wayarsa tayi ringing, hannu yasa ya dauka, sunan Auta yagani yana yawo kan screen
d'in wayar, da Sauri ya d'auka ya kara a kunneshi, muryar dayaji Auta tana magana da itace ta
d'aga mashi hankali, cikin tsananin ciwo take maganar _"kha....khaleed kazo ka taimakeni zan
mutu_...... Dai-dai lokacin wayar ta su6uce Daga hannunta, cikin tsananin rud'ewa khaleed yasanar da
momynsa abinda ke faruwa, tare suka tafi gidan, da sauri suka shiga bayan sun ajiye motarsu
inda yadace.

Bedroom suka isketa cikin jini male-male, ba Alamar numfashi tattare da ita, Cikin tsananin
rud'ewa suka d'auketa suka nufi asibiti, khaleed kuwa banda kyarma ba abinda yakeyi, dan ko
tu'kin yinsa kawai yakeyi, amma besan inda kansa yakeba, da taimakon Allah suka isa asibitin,
labour room itama aka wuce da ita.
Nan fa likitoci suka taru akanta, amma abin sai du'a,i
Wasa-wasa har karfe shidda na yamma basuji wani dadd'an kabari ba, lokacin kuma Hajiyar
Auta ta dad'e da zowa asibitin, zazzaune suke sunyi jugum-jugum Kowa Allah-Allah yake yaji
ance d'anshi ya haihu, yayinda khaleed ke cikin matsanancin tashin hankali.

Can gurin 'karfe shida da rabi dictor yafito daga d'akin duk yahad'a gumi, duk illahirin jikinshi ya
6aci da jini, suna ganin fitowarshi sukayimashi caaa, suna tambayarshi "Yaya dai doctor sun
haihu kuwa, wata nannauyar ajiyar zuciya likitan yayi sannan yace "ina mijinsu yake?, khaleed
yace "gani, biyoni office, Momyn khaleed tace dan Allah doctor kayi mamu bayani anan Kowa
yaji halin da suke ciki, ko hankalinmu ya kwanta, nan da kake gani muduka iyayensune, ba wani
abu ka fad'i kawai.

Doctor ya share wani gumi daya tsatstsafo mai a goshi, yace " ina farin cikin sanar daku cewa
su duka sun haihu, Fadila ta haifi yara biyu mace da namiji, sai kuma Zainab ta haif d'a namiji.

Lokaci guda fuskokinsu suka washe cikin farin ciki suka fara yima Allah godiya,
Sai lokacin likitan yacigaba da magana "amma inaso Ku Sani Allah shi ke badawa kuma
shine me kar6ewa a duk lokacin dayaso,
saboda haka ina me ba'kin cikin sanar daku d'a namijin da aka Haifa ya rasu, kafin daga bisani

itama uwarsa tabishi, Allah yafiku sonsu, saboda haka kuyi hakuri addu'a kawai zakuyi masu sai
Ku d'auki gawar kuje gida ku shiryasu dan kada akaisu matuary,

```Innalillahiwa'inna,ilaihirrajiun```
Suka furta lokaci guda suka shiga matsanancin tashin hankali, khaleed kuwa jiyayi 'kafafunsa
bazasu iya d'aukarsaba zaman dirahan yayi yana zuabar da hawaye, yana cewa "shikenan
Zainab kin tafi kiin barni ina zan saka raina, yakama 'kafafun momynshi yari'ke gam yana cewa
Momy kicema Auta kada ta mutu ta barni, sosai Momy ta taasayama d'anta ganin yanda yake
aurutai marassa kan gado, itama hawayenne suka gangaro kan kumatunta.

Hajiya kau tinda likitan yafad'i rasuwar taji kanta yayimata wani Jim, tana tsaye dafe da kai,
kawai sai jinta sukayi 'kasa ta fad'i sumammiya.

Da sauri sukayi kanta, suna salati, nanfa aka shiga wani sabon tashin hankali, dan Hajiya an
yayyafa mata ruwa amma ba Alamar numfashi tatare da ita.

Nan aka d'auketa Emergency aka nufa da ita, likitoci ne suka taru dan ganin an ceto rayuwarta,
akalla ankai awa biyu kafin asamu numfashinta yafara dawowa.


Nan aka sanar da Baban Auta da baban khaleed abinda ke faruwa asibitin,
lokaci guda suka iso hadda mahaifin fadila, nan aka d'auki gawar jaririn data mahaifiyarshi
aka nufi gida dasu, tin daren a kayi masu wanka, aka shiryasu, sukayi kwanan keso.





``` Allahu Akbar, kulli nafsin za'ikatul maut" dukkan me rai
mamacine```





Zee Elkaseem
Mmn khady
[10/16, 7:56 PM] +234 816 616 9254: [15/08 8:13 pm] .:

*AUTAR HAJIYA*



®NWA



_ZEE MMN KHADY_


```Page```176-180



✍ Bayan kwana bakwai da rasuwar Fadila, kuma ranar aka rad'ama yaran suna, d'an gurin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login