Showing 27001 words to 30000 words out of 79986 words

Chapter 10 - Ban Saketa Ba Compelet Billyn Abdull

01 Aug 2026

806

matseni ajikinsa, daga nana yahaďe bakina danasa, ayaudai nabada
gudummawa, dan sosai nataimaka masa yasamu farinciki wajen sumbata, wadda inada
tabbacin yasamu ďin kuma.
Saida yayansa yakirashi awaya sanan yazare bakinsa daga nawa akasalace, baiyi
maganaba ya ďauki jakarsa yasa akafaďa yana ďagamin hannu, nikam nai k'asa dakai saboda
hawayen dasuka cikamin ido.
Banyimasa rakiyaba gudun karnaje gaban mutane ina kuka, saikawai nakoma đakina
nakwanta ina kukana.

_*11:56 am*_
Har k'arfe shaďaya dawani abu ban tashiba, nayi kuka harna gaji, nikaina bansan dalilin
kukan nawaba, saboda bayau doctor yata6a tafiya yabarniba, amma nafijin zafin tayau da
kewarsa, zuwa shabiyu saura na hak'ura natashi domin gyara ďaki, ina cikin kakka6e gado
naga takarda tafaďo. Harna ajeta saman durowar gado dazaton doctor ne ya manta da ita, saikuma zuciyata
takasa nutsuwa na ďauka nabuďe.
_"Inna lillahi wa'inna ilaihirra raji'un"_, kawai nake ammbata, jikina sai rawa yake.
Adaidai wanan lokacin deexerh tashigo ďakin...............



_*kuyi hak'uri dajina shiru, wlhy abubuwane suka min yawa, amma insha ALLAHU bayan biki
zaku cigaba da samun book ďin yanda yakamata masoyana, ina alfahari daku sosai*._
*luv u oll*







_*((S))..........2017*_
_*luv u oll my fan's*_
_*Battery low*_
[8/6, 6:01 PM] mrs bilkisu: *________________________________*
*BAN SAKETA BA!*
*________________________________*
*NA*
*BILKEESA IBRAHEEM*
_*{bilyn Abdul}*_
*________________________________*
https://mrsbilkisa.blogspot.com

_sadaukarwa_ *ya Abdul {city phone's}*




*MIYAKAMATA NAYI?.*
_'yar uwa! ďan uwa!, yakamata dani dake da kai mutaru mu mutunta juna, k'yautata
mu'amularku da jama'a 'yan uwanku, walau musulmai ko ba musulmaiba_
_karku zama masu girman kai, saboda wata ďaukaka ta duniya, babu wanda yafi wani gurin
ALLAH sai wanda ya k'yautata ibadarsa, to ashe nidake da kai duk bamuda tabbas, domin duk
k'ok'arin ibadarka wani yafika, ballema yanzu damuka lalace, muka shagala aduniya da kayan
cikinta._ _saika samu mutum yahaďa shekara ďaya bai karanta *alkur'ani* ba, baya sallah akan lokaci,
baya neman ilimi akan addininsa, baya tunawa da *ubangijinsa* sai masifa ta rikesa sanan ya
ce, "ALLAH ne ya ďora masa, humm kaji ďan adam sarkin butulci da izgilanci, duk sanda alkairi
yasamesa saiya ďauka wayonsa da iyawarsace tabasa, wanan kuskurene da jahilci._ _mudaure murunga neman _ilimi akan addini, bawai aboko_ kawaiba, _saikaga mutim
yanata_ _fafa shi yanada digiri ko_ _difloma_ _ko yana karatu a jami'a kaza, amma_ _wlhy idan
zaka tsaresa bazai iya_ _kawo maka alwala cikakkiyaba,_ _bare azo ga sallar kanta, amma_
_turanci da iya salo abakinsa ko_ _mista k'yarank'yan yashafa_ _masa lafiya, larabcikan sai
ace_ _aiba yarena bane._
_to hajiyata alhajina shi turanci yarenkine?, hasalima turancin namak'iyankine, afannin addini
al'ada jinsi, dan bature bazai ta6a k'aunar musulmiba kuma bak'in mutum, larabci kam abin
al'faharinkine tunda koba komai *Annabinmu* yafito daga wanan tsatsonne._
_Inaga lokaci yayi dazaki gane ka gane na gane cewa da mutunci ake gano mutunci, da ilimi
ake gano gyara, to *miya kamata nayi?* na nemi ilimi na addini bawai boko kawaiba._
*ALLAH yasa muga ne.*




*~page.......15~*

..................da sauri deexerh ta rik'eni nafaďo hannunta dan tuni numfashina ya tsaya,
k'arar da deexerh ta kwallace ta jawo hankalin jama'ar gidan harda yaya dadyn su deexerh.
Da gudu suka iso 6angarenmu suna tambayar lafiya??, ganina akwance yabasu tabbacin
nice babu lafiya ba deexerh ba, aunty ce tafara cewa akira doctor, amma yaya yahana, wani
abokinsa aka kira, kafin ya iso yaya yazare takardar daya gani ahannuna, tuni zufa ta wanke

masa dukkan sassan jikinsa, sai k'ara maimaita karanta takardar yake kamar wanda akabama
hadda.
Ya maimaitata yafi ak'irga, tuni kuwa ya haddace komai dake cikin takardar, mama tana lura
da halin dayake ciki, zuwan doctor ne yahanata tambayarsa.
Dr Auwal yadubani tareda mak'alamin k'arin ruwa, ya ce, "insha ALLAHU zuwa anjima zan
tashi normal, yanzuma wani abune ya firgitani na suma, amma na farfaďo.
Godiya sukai masa sanan yatafi.
Dama tuni yaya yabar wajen, yana 6angaren mama, acan mama tasamesa zaune akujera
kamar gunki, idonsa cike da kwallah, zuwan mama yasa yatashi sosai, yasa gefen rigarsa ya
share kwallar data gangaro masa kaďan agefen ido.
Jiki asanyaye mama ta zauna dan tabbas tasan ba lafiyaba, yaya yanada k'ok'arin 6oye
damuwa komai tsananinta, amma yanzu hakan ya gagara, cikin sark'ewar murya mama ta ce,
"Mansur miya faru ne?.
Yaya yaja ajiyar zuciya, muryarsa naďan rawa ya ce, "mama Isma'il ya saki iman!!.
Cikin wani irin yanayi mama take kallonsa, ta ce, "ban ganeba Mansur mikakeson
faďamini?.
Takardar hannunsa yamik'a mata, ta kar6a takaranta.....
*ni Isma'il Muh'd basheer!. Nasaki matata saudat sulaiman saki uku!!. Idan tasamu miji tayi
aure.*
Tuni gumi ya wanke jikin mama, bata buk'atar k'arin bayani danhaka tayi tagumi kamar
yanda yaya yayi.
Yayane yay k'arfin halin faďin mama amma yaronnan ya cucemu, yanzu dan ALLAH dawane
ido zamu kalli iyayen yarinyarnan?, ni abindama yake bani mamaki shine miya haďasu dahar
zai mata saki har uku?, miya hau kan yaronnan haka?, kuma wlhy mama rubutunsane barema
ya musa mana. Mama taja ajiyar zuciya toni Mansur ai komaima ya kwace mini, bansan yanda zan kira
wanan abinba kuma.
Haka mama da yaya sukaita tattaunawa, kuma wani abun mamaki sunkira wayar doctor
arufe, mama ta ce, "tunda yasan miya aikata ai dole yakashe waya, kabarsa kawai.
Nikam ina ďaki ina barci, aunty da deexerh da Raihan suna 6angarena, saidai basusan
abinda yake faruwaba, dan deexerh ma bata karanta takardarba tunda tana zuwa ina suma.
Haka akaita tafiya har zuwa yamma dana farka, mama dakanta ta taimaka mini nayi wanka,
aka bani abinci naci kaďan har zuwa sanan kuka nake rurus.

*bayan kwana uku*
Yau tsawon kwana uku kenan angaza samun number doctor kwata2, nikuma namatsa
zanje gida, dan yakama iyayena su san halin da'ake ciki, mama da yaya basaso natafi, hakama
deexerh da marwan, amma yaza'ayi da k'addarar ALLAH, ganin namatsa yasa mama da yaya
suka kaini har gida. Bak'aramin ruďani gwaggo tashigaba itada Abbah dajin abinda yafaru, dan su yaya basu
6oye musu komaiba, suka ďora dabasu hak'uri.
Abbah ya ce, "babu komai haka ALLAH ya k'addara aii, bayan ďan tattaunawa dabawa juna
baki su yaya suka tafi aka barni agida.

Tunda nadawo gida banida wata walwala, kulum cikin kuka nake, ga rashin lafiya data tasoni
gaba, dandanan nayi bak'i na rame kamar baniba, lokacin da labari yakai kunanen aunty salma
da ya majeed ransu ya 6aci matuk'a, ya majeed ya ce, "bazai k'yaleba saiya ďauki mataki akan
doctor, da k'yar abbah da gwaggo suka shawo kansa ya hak'ura. Ganin yanda na k'untata kaina agidan yasa ya majeed rok'on abbah yabari nakoma wajensu
k'ila zanfi samun sakewa, abbah baiyi musuba dan dama farin cikina yakeso, aranar muka
tattara muka koma.
Acanma haka nayita rashin lafiya wadda tasa dole suka kaini asibiti, tofa wata sabuwa,
bayan gwaje2 da likita yayi ya tabbatar mana inada ciki na sati uku, tun agurin nasa kuka sai
anzubar dashi, amma ya majeed ya hana.
Ranar nayi kuka harna godema ubangijina, duk wanda yaganni saiya tausaya mini.
Muna dawowa gida ya majeed yasanarma su abba halin da'ake ciki, aranar kuma aka
sanarma gidansu doctor, mama da yaya sunyi matuk'ar murna da wanan abin farinciki, dan cikin
zai zama sanadin cigaban zumincin mu.
Har tsawon wata ďaya babu labarin doctor kota waya bare kuma ayi maganar dawowa.
Nikam inanan a6oye inata k'ok'arin zubar da ciki, duk abinda naji ance yana zubar da ciki
saina sha a6oye, amma abanza wai man kaza, dan ciki ko gezau, saidai nasha azabar ciwon
cikina.
Ahaka aka akai wata biyu da sati ďaya.
Awata ranar alhamis doctor yazo kano, saidai kuma yatarar da sabon tashin hankali, dan
kowa ya ďauke masa wuta agidansu.
Kowa ya tambaya iman sai suyi masa banza harsu marwan da deexerh.
Hankanlinsa yatashi matuk'a, inda yaga sunk'i bashi wata amsa ta gamsarwa sai kawai ya
tsare deexerh da marwan da bulala.
Tsoro yakamasu sosai dan ganin yanda yaburkice musu ďinnan zasu iya shan duka abanza,
aiko suka sanar dashi komai, atake jikinsa yay sanyi, yanufi wajen mama hankali tashe.
Agabanta yashiga rantsuwar wlhy *BAN SAKETA BA!* mama, na rantse da ALLAH k'arya
takemini.
Mama tayi masa banza, wuni guda yana magiya da rok'o amma kowa yak'i saurarensa,
dayaga nan babu ci saiya nufi gidanmu, to gara nan abbah yayi masa nasiha da nuna masa
muhimmancin yarda da k'addara.
Shidai doctor bashida wata magana sai *ban saketa ba*, tun suna kallon abun amatsayin
wasa harya fara zarta tunaninsu, dan doctor neman zare musu yakeyi, awani daren litinin sai a
asibiti ya kwana.
Wasa2 dai al'amira sun fara tsauri, doctor baisan waye akansaba, kuma indai idonsa biyu
bashida magana saita *ban saketa ba*, wannan yasa hankalinsu yayansa yafara tashi suka fara
tausayinsa kuma, dan abin yafara wuce makiďi da rawa.

Ahaka cikina yashiga wata biyar, nima kaina nazama mara lafiyar, kulum daga tunani sai
kuka, duk sanda na kalli cikina sainayi kuka, har banason tuna inada ciki, duk halin da doctor
yake ciki labari yana zuwa mini, dansu aunty salma suna zuwa ganinsa hakama su gwaggo.
Jikin doctor yay tsanani dole aka maidashi k'asar indiya, dan ciwon zuciya yana neman
aikashi lahira, kowa yana tausaya masa.

Ban ta6a zuwa ganinsaba saidai kusan tare muke jinyar dan kullum zuciyata tana damuwa
da halin dayake ciki.
Karna jaku da nisa, haka cikina harya cika wata tara, zuwa sanan jikin doctor da sauk'i
amma ba'a dawo dashi 9ja ba yana indiya abinsa.
Awani dare juma'a na farka da nak'uda, cikin hanzari muka nufi asibiti, tun anasaran zan
haihu acikin awa biyu har likitocin suka fidda rai, dan har washe garin ranar haihuwa shiru sai
bak'ar azabar danake sha.
Har k'arfe sha biyun rana haihuwa shiru, zuwa sannan k'arfina yagama k'arewa, ko ďaga
hannuna bana iyawa bare kuma nayi wani nishi, ganin halin danake ciki aka yanke shawarar
yimini aiki.
Babu musu su abbah suka yarda, dadyn su deexerh yasa hannu a maimakon doctor, aka
shiga dani ďakin tiyata.
Ancuromin yaro namiji k'ato mai kama da babansa kamar an tsaga kara, lallai yau naga
farinciki wajen dangin doctor danawa dangin, kowa kamar yacinye yaron haka yakeji, haka nima
kowa yana tausaya mini da addu'ar samun lafiya.
Duk wata hidima yayansa yayita, kuma shima ansanar dashi na haihu, yayi farinciki kuma
yasha kuka, dan ranar saida ciwonsa yak'ara tashi, likitoci sunata faďa akan adaina gaya masa
komai daya danganci 6acin rai.
Ina gadon asibiti har tsawon sati uku, dan haka ba'ayi taron sunaba, andai raďama yaro suna
*Musayyeef*, to iman ALLAH yaraya mana musayeef, amin.
Bayan sati uku aka sallamemu, amma wannan karon gidanmu aka dawo dani, dan ina
buk'atar kulawar gwaggona, haka nacigaba da rainon musayeef wanda kulum kallonsa
yanasani tunawa da ubansa, dan kamarsu tayi yawa matuk'a, kullum mama tana k'ok'arin
kwantar da hankalina, ahankali yauda gobe harna dake, komai yafara zama tarihi na maida
hankalina akan rainon musayeef.
Musayeef yanada wata ďaya da kwanaki aduniya aka dawo da doctor gida, danya samu
sauk'i sosai, shima yawan addu'ar da aka dage ana masa yasa yadake yanzu, kwanansa uku
da dawowa yayansa yarakosa yaga musayeef, jiyayi kamar yamaida musayeef acikinsa, yana
matuk'ar k'aunar ďansa gudan jininsa, dak'yar yayansa ya lalla6ashi suka tafi. Yayi yayi yaganni amma nak'i amincewa, dole yahak'ura suka tafi wani abu na sukar
zuciyarsa.
Daya koma gida saida aka haďa da lalashi, dan yanzu ba'aso yana tada hankalinsa.

Haka naci gaba da rainon musayeef nida gwaggo harya shiga shekara ďaya, asanane kuma ya
majeed yabada shawarar nazana s,s,c,e ďina nakoma karatu, abbah ya yarda da shawararsa,
dan haka nayi Exam, cikin amincin ubangiji nasamu result mai k'yau, dan haka ba'asamu
matsalaba wajen nema mini makaranta. ALLAH yacidani samun nan (A B U zariya), samun makarantar yasa na yaye musayeef na
maida hankalina akan karatuna.
Shima doctor yakoma aikinsa yabarma ubangiji komai, amma lokaci2 yana zuwa duba
musayeef, hakama yaya da mama da aunty.
To yanzudai ansaka musayeef makaranta kuma yayansa ne da wanan aikin, idan anyi hutu
yana zuwa gidansu hakama weekend ana kaisa yayi kwana biyu.

Tunda nabaro gidan bansake haďuwa da doctor ba, bamma k'ara zuwa gidanba, idan yazo
ganin musayeef kuwa bana yadda muhaďu, zadai akai masa ďansa, kuma susha hirarsu da
gwaggo, ammani yagagara ganina, garama lokacin da maman su deexerh zata koma gidan
naso zuwa amma ALLAH bai k'addaraba. Xoxo ta ce, "oh maman su deexerh takoma??.
Eh yaya ya maidata yanzu hakama tana gab da haihuwa deexerh tace min.
ALLAH sarki kai natayata murna wlhy, musamman ma su deexerh dan babu abinda yafi
karayu da 'ya'yanka daďi.
Wlhy hakane xoxo Reefat tafaďa.
Iman ta ce, "to wanan shine sirrin dana daďe ina 6oye muku.
"To miyasa kike yawan waige2? cewar Reefat.

Iman tayi murmushi, wato tunda nazo makarantarnan lokuta da dama nakanji turaren doctor ya
yawaita awaje, wanan shine ke sakani yawan kuka da waige2, kuma kunga ranar nagansa,
wanan yatabbar mini dashi ďinne saidai yana 6oyema ganina.
Tabbas labarin iman ya girgiza k'awayenta Reefat da miss xoxo, kuma sunyi alk'awarin
taimaka mata har agano gsky, dan suma basu yarda cewa doctor ya saketaba, sunaji ajikinsu
*bai saketaba*, amma basu sanar da ita zasuyi komaiba.
Saidai sun tanmbayeta yanzu ina deexerh?.
Deexerh tana nan, tana karatu a jami'ar abuja yanzun.
"Kuna waya?".
Eh muna waya sosai da ita, kuma aii kunsan haka, saidai sanan bakusan wacece itabane.
Hakane suka faďa, xoxo ta ce, "yakamata mukaima deexerh ziyara.
Iman tazaro ido ziyara kuma?, tanafa makaranta nece, eh aii makarantar zamuje, amma sai
weekend, tunda bawani nisa bane tsakanin zariya da abuja.
Shiru iman tayi dan batasan amsar daya kamata tabasuba, Reefat ta ce, "iman kinyi shiru.
Ajiyar zuciya iman tayi, bashiru nayiba Reefat kawai ganin abun nake abaibai.
Babu wani baibai, deexerh sa'ar muce, kuma tana k'aunarki aii yakamata zumincinku
yacigaba karya yanke.
Xoxo ai zumincinmu bai yankeba tunda muna gaisawa, kuma idan ina kano tana zuwa aii
mugaisa, tana zuwa ta ďauki musayeef.
Eh dukda haka, yakamata mukai mata ziyara.
To shikenan saimu duba ranar daya dace saimuje kenan.
Okey ALLAH yakaimu.

Ammafa iman kinsamu akwali, wlhy da duk zatonmu gwaggo ta haifi musayeef.
Dariya iman tayi ta ce, "tokuyi hak'uri.
Suma suka dara tareda faďin yayuce, munyimi uzuri.................

_*((S)).........2017*_
_*luv u oll my fan's*_
_*battery low*_
[8/6, 6:01 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!_*




*_NA Bilyn Abdul_*



_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*




_*sak'on barka da sallah*_
_dolene nafara isar da sak'on barka da sallah ga masoyana aduk ida suke, kafin na
tsunduma alabari_
_Nasan bazan iya jere sunanku dukaba, saboda yawa, wasuma bansansuba, amma dukda
haka zan kawo sunayen kad'an daga cikinku insha ALLAHU._

*gaisuwa gareku*
*_Aysha Manshat, Reefat yahya, hafsat (miss xoxo), Ayusher muh'd, Abba Gana, Sajna,
Maman Shaheed, Maryam 'yar mama, cwtjiddah, feedo, saffiya galadanci, billy galadanci,
Lemcy, Maman useey, my Ikilee, deexerh, hudallah, zarah ms, Feedausi, Maman 'yan biyu,
Zainab Zanfara, Teema, Maryam Nijar, salma Nijar, sa'adatu sa'ad, hafsy, Aysha umar
Abubakar, shamsiyya muh'd, umayma, fa'iza, Xee Salees, Fatee, Xee babe, ummy, Maman
aneesat, Maman yasmeen ,muneerat,nanerh, khadeejarh, beauty angel, bby hanan, Aysha
umar, d'an mom, ikram saje, kairat safyan, sadiya baby, mimin mom, Luby, Afra'ce, maigadon
zinaree, sumayya waziri, Aysha mai'tama, Maman Affan, momyn sultan, momyn Aysha,
ummulkairi, Mrs muh'd, Mrs Amman, Asma'u taura, ikileema Zaria, Maman Mubarak, Ruky,
Ash-Nur, Mrs uwaisu, matar Safwan, ummy ta kano, Rashida madaki, Mrs isma'il._*
_bari nadasa aya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0