Showing 3001 words to 6000 words out of 79986 words

Chapter 2 - Ban Saketa Ba Compelet Billyn Abdull

01 Aug 2026

800

da mama
zasu yarda, yakamata fa ace kayi aure tuni, kosaika zama tunzurun zurun ne?.
Dr Isma'il yay dariya, kana min wula'kanci wlhy majeed kaima naga duka shekararka nawa da
auren?, su yaya kuwa banida matsala dasu, abinda nakeso suma shi suke so, kaidai katayani
da addu'ar neman za6in ALLAH kawai.
Shikenan ALLAH yaza6a mana abinda yafi alkairi.
Amin Dr Isma'il yafa�a.

Da dai ya majeed ya fahimci Dr Isma'il da gsk yakeyi, saiya shige masa gaba awajen Abbah.
Abbah yayima Dr Isma'il tambayoyi kamar yanda shari'a ta tsara, yako amsa masa yanda
yadace.
Saiya bashi izinin neman SO a wajena, nikam bammasan abinda ake cikiba, dan lokacin da
nadawo gida mun koma makaranta.
Kai kutashi muyi sallah �aya ta wuce, kuma ALLAH yunwa nakeji, Xoxo ta harareta ALLAH
iman kin iya wula 'kanci saida labarin yafara �aukar da�i zaki 'kir'kiroma mutane wani jin yunwa,
inama laifin muyi sallar??.
Iman tayi dariya sorry dear karki damu aii idan tunbi ya �auka labarin saiyafi da�i ko??.
Reefat ta ce, "ALLAH ni ko yunwarma banaji, burina kawai naji 'karshen labarinnan, karku
damu aii muna gamawa zan cigaba.
To gsky saidai asiyo abincin ko asake cin indomi dan in ba hakaba girki zai 6ata mana lokaci,
gsky ne Xoxo kunga kuyi sallar tunda ni an hutar dani, kafin ku idar naje na samo mana abinda
zamuci ko bai yiba??.
Sukace yayi.
Bayan sun gama cin abinci iman ta ce, "saitayi wanka sanan, saida tagama ja musu rai sanan
taci gaba.

Dr Isma'il yakasa sanar dani sirrin zuciyarsa saboda yana min kallon 'karamar yarinya, dan gsky
asanan ban wuce sha biyar ba.
Ahaka wata yazagayo al'adata tazo nasha wahala sosai, su gwaggo suka rasa yanda zasuyi
dani, na daure na ce, "sukira aunty Salma.
Babu 6ata lokaci aunty Salma tazo muka tafi asibiti wajen Dr Isma'il, shiyya dubani yamin
allura ya�an kwantar dani na yini �aya.

Daga nanfa ciwon mara yazamemin jiki, har fargaba nake wata yazo, hakama gwaggo tana
tausaya mini sosai.
Ana haka Dr Isma'il yazo ma Abbah da zancen zai shiga soja, dan dama burinsa kenan tun
yana yaro, amma saboda yayansa yanason yazama likita ya ha'kura yayi karatun likita, to yanzu
damace tazo masa, shine yakeson yayi amfani da ita.
Abbah ya ce, "ALLAH sarki, ai haka akeso Isma'il mutum duk inda yake yazama mai biyayya
ga nagaba dashi, saiyaga yazama abinda baiyi zatoba arayuwa, dan masu iya magana nacewa
dana gaba ake gane zurfin ruwa, to inamaka fatan Al'kairi arayuwar ka, domin kai yaron kirkine,
ALLAH yabada abinda akaje nema, kuma ayo nasara. Amin Abbah nagode da addu'arka gareni ALLAH yasaka da al'kairi, babu damuwa abba
yafa�a, kaga bari naturo maka iman �in kuyi sallama ko??.
Cikin jin kunya Dr Isma'il ya ce, "Abbah dama ka 'kyaleta.
Abbah ya ce, "sabodami Isma'il?, ba sallama zakuyiba?, Dr Isma'l ya�an sosa gefen wuyansa
saboda jin kunya ya ce, "Abbah karka damu, iman tayi 'karamane yanzu, inason saita gama
koda secondary ne, saina fahimtar da ita nufina akanta, amma yanzu za'a raba mata hankali
gida biyu. Abbah yay dariya to shikenan Isma'il ALLAH yay maka albarka, yakuma bada sa'a akan
abinda akaje nema.
Dr Isma'il ya ce, "Amin Abbah ngd da 'kaunarka gareni.
Abbah ya ce, "karka damu aii kai yaron arzi'kine wanda ya cancanci a 'kaunacesa fiyema da
haka..
Daga nandai sukayi sallama, Dr Isma'il yatafi training �in soja na wata shidda..
Nikam ban saniba, nagadai bana ganin yana zuwa wajen Abbah yanzu kamar yanda yakeyi
da, ban ta6a yun kurin tambayar waniba, dan babu wata ala'ka tsakanina dashi banda ta mara
lafiya da likita, haka nacigaba da shan wahala duk 'karshen wata, dukda wani likita yana dubani
a asibitin su Dr Isma'il, amma bai iya shawo matsalata kamar Dr Isma'il.
Awata Asabar datayi dai2 da dawowar Dr Isma'il kano, dan ayanzu yazama soja, ALLAH yacika
masa burinsa, yazama likitan sojoji, gashi likita gashi babban Soja.
Aranar natashi da matsanancin ciwon mara wanda zan iya cemuku tamkar yafi na kullum ma
dan har suma nake, gaba �aya hankalin iyayena yatashi, ankira likitan dake taimaka min
yaymin allurar amma abanza dan babu abinda ya canja agareni, har zuwa 'karfe hu�u na
yamma, saidai yalafa yadawo. Awanan lokacin tuni Dr Isma'il yana gida yana hutawa, amma sai barcin ya gagari idanunsa,
dan tunda yashigo kano gabansa ke fa�uwa zuciyarsa tanata kwa�aita masa son ganina, dan
ba 'karamin kewata yayiba acikin shekara �ayar nan..
Zumbur yami'ke yacanja kayansa zuwa shadda mai 'kyau �inkin zamani, dan Dr Isma'il
yanada 'kyau babu laifi, yafito falo yana �aura agogo, auntynsa matar yayansa ta ce, "a'a
angona sai ina kuma??.
Dr Isma'il yay dariya angon iman dai, kekam ga angonki nan akusada ke, ya nuna yayansa
dake zaune yana masu dariya.
Ta ce, "wacece iman kuma??.
Dr Isma'il yay murmushi karki damu zaki santa kwanan nan, yanzuma sauri nakeyi amma

kibini bashi idan na dawo zan sanar dake iman, yafice yana fa�in yaya aunty saina dawo, yanaji
tana kwala masa kira amma bai sauraretaba, motar yayansa ya �auka yafice danshi bashida
mota sai mashin, yayansa kuma baya masa shamaki da nasa motocin.
Yayansa ya tuntsure da dariya nikam kina bani mamaki keda Isma'il ke yanzu har kin yarda
da zancensa ne??.
To ya bazan yardaba tunda bai ta6a kawo mana makamanciyar wanan maganarba.
Ito hakane ALLAH yasa da gsk yakeyi.

Dr Isma'il kuwa kaitsaye gidanmu yanufo, yay parking a kofar gida, yana tsaye gaban motar
saiga deeni yadawo daga aika.
Dr Isma'il ya ce, "zomana abokina, babu musu deeni ya'karasa garesa, ya gaishesa.
Dr Isma'il ya ce, "dan ALLAH shiga gidanan kamin sallama damai gidan.
Deeni ya ce, "wai Abbah??.
Eh shinake nufi, ko kaima �an gidanne ?, dan naga kana kama da Iman.
Ya ce, "lah ina kasan aunty iman??, Dr Isma'il ya ce, "anan gidan, to aii yanzuma itace batada
lafiya dan har suma takeyi, aru�e Dr Isma'il ya ce, "suma kuma??, deeni ya ce, "eh suma, to
yanzun Abbah na nan?, eh yana ciki, jeka ce masa Isma'il ne yazo gunsa.
Deeni yazo ya sanar da Abbah, Abbah yanajin Dr Isma'il ne da hanxari yafito, bayan sun
gaisa Dr isma'il ya ce, "yanzu wani yaro yake sanar dani Iman babu kafiya?.
Eh hakane Isma'il.
Sun shigo gidan, sanda suka shigo inata mur'kususu ajikin gwaggo dan har wani shi�ewa
nake saboda azabar ciwo, gwaggo sai kuka take.
Dr Isma'il yakalli Abbah aru�e Abbah idan bazaka damuba na �auketa muje asibiti mana.
Abbah ya ce, "babu wata matsala Isma'il......aibai bari Abbah ya 'karasa fa�aba ya sunkuceni
yay waje, amota yasakani Abbah yakaraso da hanzari yashige muka tafi asibiti, acanma
�aukata yayi, �aki guda aka waremini nika�ai, ya shiga bani kulawa ta musamman, cikin 'yan
mintina ya shawo kan matsalata harna samu barci................�🏻






💕💚💕







Page~4⃣

..........Washe gari nadawo dai2 ina kwance agado gwaggo tana zaune akusa dani, aunty Salma
kuma tana tsaye tana waya, Dr Isma'il yaturo 'kofa yashigo da sallama, rissinawa yayi ya gaida
gwaggo, gwaggo tami'ke tafita dan tanajin kunyar sirikin nata, itama aunty Salma saitayi waje,
Dr Isma'il yajawo kujerar da gwaggo ta tashi ya zauna kusadani ya tsuramin idanu Iman ya jikin
naki?.
Cikin jin kunya na ce, "da sau'ki.
yanzun babu inda yake miki ciwo?.
na ce, "babu, ya ce, "Alhmdllh.
Ince dai kinci abinci ko?, na�an kalleshi ta gefen ido na ce, "a'a na koshi, ya ce, "mikikaci da
har kika 'koshi?, na ce, "nasha tee �azu.
Yay murmushi kice na shirya nemo maganin cin abinci matata batason cin abinci, da sauri na
kalleshi, ya kannemin ido �aya tareda �aga gira, hannu nasa na rufe fuskata saboda kunya, ya
ce, "inson mace mai kunya ashe ALLAH zai bani, na kuma cusa kaina cikin cinyoyina.
Yay dariya sanan ya �auki filet, kulan da aunty salma tazo dashi ya bu�e, ya ce, "iman lallai
ke 'yar gatace, wannan irin farfesu haka, nidai kaina na tsakiyar cinyoyina nakasa �agowa
saboda kunyar maganganunsa.
Ya zuba farfesun yace nazo naci nasha magani.
Na �ago kaina cikin jin kunya na ce, "kawo to, ya ce, "waneni da barin gimbiya cin abinci da
kanta, aii da hannuna zan baki, na ce, "A'a ngd zanci da kaina, ya ce, "nikuma ban yardaba,
haka dole na hakura yabani da kansa, saidai cikin matu'kar jin kunya nake kar6a, shikam sai
dariya yake mini. Aranar aka sallameni muka koma gida..
Kunaga kutashi muyi sallar la'asar sanan saimu cigaba.
Bayan sun idar da sallar la'asar iman ta �ora labari.

Iman tabi Reefat da Xoxo da kallo tareda jan numfashi, wato 'yan uwa bayan kwana �aya da
sallamata Dr Isma'il yazo gidanmu, an masa tarba ta mutunci, dan su gwaggo suna son Dr
Isma'il sosai.
Bayan sun gama gaisawa Dr Isma'il ya ce, "Abbah dama nazone nayi muku bayani akan
ciwon iman.
Abbah ya ce, "ina saurarenka Isma'il.
Dr Isma'il yay 'kasa da kai sanan ya ce, "wato Abbah na�anyi bincikene akan ciwon iman,
saina gano ta hanya �ayane kawai zata iya rabuwa da ciwon, hanyar kuma itace......saikuma
yayi shiru, Abba ya ce, "inajinka Isma'il karkaji komai ka sanar dani, Dr Isma'il ya 'kara kasa da
kai dan maganar tayi masa nauyi abaki, amma ya daure ya ce, "hanyar itace aii mata aure, ta
wanan hanyar kawai nake ganin za'a samu mafita.
Abbah yay murmushi to aii Isma'il inadai hakane banida damuwa tunda lafiyarta muke
bu'kata, inaga indai har iyayenka sun amince saisu turo, inyaso saita cigaba da karatun a
�akinta, dan haka nabaka dama kaje kayi shawara da nagabatanka, nima zanyi da gwaggonsu
dakuma 'yan uwana. Dr Isma'il ya ce, "to ngd ALLAH ya 'kara girma.
Abbah ya ce, "amin, yami'ke yana fa�in bari na turo maka maman tawa.

Bayan Abbah yashigo ya ce, "naje falon ba'ki ana jirana, na ce, "to, hijjabi nasaka na nufi
falon, yana zaune akujera mai zaman mutum �aya, yana cikin farar shadda �inkin boda amma
babu hula akansa, yayi min 'kyau sosai, dan Dr Isma'il farine 'kyakykyawa, yanada suma mai
'kyau wadda take shan gyara, bayida saje saidai wani �an gemu na gayu daya ajiye, wanda
ya'kawata 'kyawun fuskarsa, dogone sosai yanada 'yar kiba daidai misali, akwaishi da yawan
fara'a, dan a yanda nakula kamar ba miskili bane.
Da sallama na shigo 'kamshin turarensa ya bigi hancina, inason kamshin turaren tun sanda
aka fara kaini asibitinsa, ya�anja gilas �insa ka�an zuwa 'kasan ido, yakuramin idanunsa
matsakaita girma, na zauna saman carpet, yay saurin fa�in a'a ban yardaba tashi ki hau kujera,
cikin jin kunya na ce, "nanma ya isa. To shikenan nima bari na sauka kasan tunda nan kikeson mu zauna, ganin zai zauna kasa
nayi saurin hawa saman kujerar, ya tuntsure da dariya to shikenan gimbiya, nidai kaina yana
'kasa na gaisheshi, ya amsa cikin fara'a, sanan ya ce, "ya jikinki??.
Na ce, "aii ni na warke.
Ya ce, "zakidai warke in sha ALLAHU nan gaba ka�an.
Murmushi kawai nayi batareda nayi maganaba.

Ya gyara zamansa sosai, tareda 'kara daidaita nutsuwarsa, yay�an gyaran murya alamar
maganar dazaiyi tanada muhimmanci.
Ya ce, "imaniii nasan kin sanni tunba yanzuba, tun sanda aka fara kaiki asibiti a matsayin
patient �ina??, na �aga kai alamar hakane, ya jin jina kai, to tun aranar naji kin kwanta min arai,
nakamu da sonki na gsky, dalilin dayasa na sanar da majeed abinda ke raina kenan, shine ya
shige mini gaba zuwa wajen abbah, banyi kasa aguywa ba wajen sanar da abbah sirrin
zuciyata.
Alhmdllh Abbah ya fahimceni yakuma kar6eni amatsayin siriki, tunkuma a wancan lokacin ya
mallaka minke, yakuma bani damar neman so awajenki.
Alokacin nayi wani nazari akanki, dan na lura ke yarinyace karama, wanan dalilin yasa na ce,
"abarki sainan gaba, dama na sanar dasune kamar yanda addinina ya koyar dani, to saikuma
wani uzuri yatasomin alokacin, natafi training �in soja saboda tuni inason zama soja, saidai
yayana yafison nazama likita, ina girmama bukatarsa dan haka nacika masa burinsa nazama
likita, tonima sai ALLAH yacika min nawa burin nasamu damar zama soja ayanzu.
Ranar dana iso kano saina tarar bakida lafiya, danayi bincike akan ciwonki saina gano nine
maganinsa, dan haka nazo yaunayima abbah bayanin komai.
Ya gyara zamansa to yanzudai zancen danake miki abbah yabani izinin turo iyayena su
nemamin aurenki, shiyyasa nakeson jin tabakiki dan kar asoya mai amanta da albasa iman kina
SONA kuwa???, nayi miki??, karki 6oyemin sirrin zuciyarki kinji..
Gsky naji kunyar zancensa dan haka na 6oye fuskata da tafin hannuna, Dr Isma'il yazare
gilas �insa karkimin haka Saudat!!, ki daure kisanar dani kina SONA???.
cikin jin kunya na�aga kaina alamar eh.
Yasaki murmushinsa mai 'kayatarwa ya ce, "Alhmdllh, iman nagode da soyayyarki gareni,
ALLAH yabarmu tare har abada, yakuma ka�e duk wata fitina dazata wanzu a tsakaninmu,
ala66ana na ce, "amin ya rabbi.
Ya kalli agogon hannunsa idan bazaki damuba zan sanar dake koni wanene dan naga

munada sauran lokaci.
Na ce, "babu damuwa.
Lemo ya �auka ya tsiyaya acikin kofi, yasha ka�an sanan ya ajiye, ya �auki gilas �insa
yasaka, gilas �in yana matu'kar kara masa 'kyau sosai.

♡☆♡

Nidai sunan Isma'il Muh'd Basheer, mu biyu iyayenmu suka haifa, yayana Mansur saini auta,
mu 'yan asalin garin sakoto ne, aikine yakawo mahaifinmu kano, mamata kuma 'yar tarabace
Jalingo kenan, bafulatanace ta asali, dan harta bar duniya hausarta bata fita sosai, tuni
mahaifinmu ALLAH yay masa rasuwa saka makon ha�arin mota dayayi daga kano zuwa
sokoto, sanan ina wata 6 a duniya, Rasuwarsa ta girgiza maman mu dan haka takamu da ciwon
zucuya itama babu da�ewa tabi bayansa, inada wata 10 sanan aduniya, 'kanuwar maman
muce tacigaba da ri'konmu, itama tana aure anan kano dawani abokin Abbanmu.
Sun nuna mana gata sosai wanda har muka manta da maraicin dake kanmu, dansu basu
ta6a haihuwaba, sun taimaka mana munyi karatu mai zurfi, ina shekarar 'karshe a secondary
ALLAH yayma uncle rasuwa, akabar mama da �awauniyarmu, karatunmu tarbiyyarmu, cinmu
shanmu, saidai abinda 'yan uwa suka taimaka mata. Natashi mutum mai yawan laulayi na ciyo, ina yawan yin rashin lafiya akai2, idan ina cikin
wanan halin mama takan ru�e itada yayana, hakadai rayuwa tacigaba da garawa har yayana ya
kammala digiri �insa, bai tsaya neman aikiba ya tsunduma kasuwanci, nikuma sanan na
kammala sacondary, kullum burina bai wuce nazama sojaba, amma awajen yayana da mama
ba haka bane, burinsu nazama cikakken likita, dan haka burinsu ya danne nawa, nadage
nazama likita domin na faranta musu, yayana yayi aure tuni, yanzu haka yanada yara biyu,
Marwan da Hadeeza, (deexerh) saidai sun rabu da maman yaran, yanzu yana auren wata mata
mai suna Ramla, agida �aya muke zaune muduka, yayi mana gini kowa da 6angarensa
saikuma na mama agefe, wannan shine tarihina a ta'kaice, ALLAH yasa kin gamsu.
Murmushi nayi ina satar kallonsa, na gamsu sosai, kuma tarihinka ya 'kayatar dani, ALLAH
yajikansu mama ya yafe musu, yabamu hakurin rashinsu, ameen doctor yafa�a yanamai jin
da�in addu'ata.
Ya kalli agogon hannunsa sanan ya mi'ke iman bari na wuce ko, magriba tana gabatowa.
Na ce, "to aii bakaci komaiba sai lemo, yayi murmushinsa mai 'kyawun gani, karki damu
kasancewa dake kawai ya wadatar dani, na ce, "to na gode, na�an rakoshi bakin 'kofar falon
ina fa�in ka gaidamin dasu deexerh da marwan, saida yajuyo ya kalleni sanan ya ce, "zasuji
insha ALLAHU. bayan fitarsa daga gidan na lumshe idona ina murmushi da maida nannauyan numfashi,
babu 'karya nima inason doctor Isma'il, domin kuwa ya cancanci asoshi, mutumne mai kwarjini
a ayuka da kuma dangan taka, ga yawan fara'a, uwa uba 'kyawawan halaye, amma baza'a
kirasa mutum mai tsananin 'kyauba, saidai tsaka tsaki. Lalai na more da samun miji nagari, kamshinsa kawai ya wadatar dani burin kasancewa
dashi har abada, saidai ina ba'kin cikin katsewar karatuna, dukda nanda wata shekarar zan
kammala, amma ina bukatar rabuwa da wananan azababben ciwon dakansani tagumi tunkan
kamawar wata, ALLAH dai yaza6a mana abinda yafi alkairi.

Kwala kiran sallar limance tasakani fitowa daga falon nanufi cikin gida..............�🏻


Kuyi ha'kuri dani, wlhy ina busy�🏻�









Luv u oll my fan's
(S)......2017
battery low🔋�👌🏻
[8/6, 5:59 PM] mrs bilkisu: ________________________________

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0