Showing 15001 words to 18000 words out of 79986 words
_muhaďu agaba domin jin yanda yakamata ki tsara_ *Duniyarki 'yar uwata*_domin keda
*zuri'arki*ku amfana_ *a lahirarku*
*ALLAH yasa mugane*.
~page.......~1⃣0⃣.
*............*da sallam nashiga falon babu kowa alamun *doctor* yana cikin _bedroom_
kenan.
Dukda inajin kunya wannan bai hanani nufar ďakinba, nashiga da _sallama_.
Yana tsaye atsakiyar ďakin yana k'ok'arin cire kayansa, yajuyo ahankali yana kallona, nikam
nayi k'asa da kai saboda kunyarsa danakeji.
Yasaki _murmushi_ mai k'yatarwa, ahankali ya ce, " *my iman* k'araso mana.
Nak'ara k'asa da kai saboda kunya, na ce, "bari naje falo idan kagama saina dawo, wlhy
bammasan kana shirin wanka bane.
Takowa yayi cikin takun k'asaita har inda nake tsaye.
Nikam jinake tamkar na zura da gudu, amma babu dama.......kusantowarsa gareni tasa na
ďago da sauri muka haďa ido.
Nai saurin maida kaina k'asa.
Baice min komaiba sai kama hannuna dayayi muka k'arasa cikin ďakin sosai.
Ya zaunar dani abakin gado sanan yacigaba da cire kayansa.
Araina na ce, "waishi doctor baisan inajin kunyarsa bane?.
Ina nan zaune harya gama cire kayansa, ya k'araso yazauna kusa dani dagashi sai gajeren
wando.
Yaďan rungumoni jikinsa yana magana ahankali tamkar mai raďa ko baisan tada yaro mai
barci.
_farin cikina abar alfaharina, har yanzu kunyar tawa bata k'arebane?_.
Maimakon nabashi amsar tambayarsa sainace kadawo lafiya?.
Yakama hannuna danake wasa dashi yaďan matsa, naďago da sauri ina kallonsa dan naji
zafi.
*Ya ďaga min gira*
Miyasa baki bani amsar tambayataba??, saikika sakko taki tambayar??.
Nayi murmushi wanda yakeso yaga nakasance akoda yaushe inayi, amma ina niďin
_muskilancina_ bazai barniba.
To kayi hak'uri nafaďa atak'aice.
To nahak'ura *saudat* nasameku lafiya?.
Lafiya k'alau.
Ya aiki?.
Aiki *Alhmdllh* saidai kewarki da begenki sunta addabata musamman alokacin barci.
Ban bashi amsabama yanzu.
Ganin haka yasa yasake matseni sosai ajikinsa, saikuma nafara masa rawar jiki, nakan bashi
mamaki idan yaga nashiga wani hali alokacin daya haďani da jikinsa, amma saiya basar.
Yamik'e tareda mik'ar dani tsaye, zomuje ki haďamin ruwan wanka.
Bayan gama haďa masa ruwan wanka na ce, "nagama.
Kafin ya ce, "wani abu nafice.
Rakani yayi da wani shu'umin kallo, ala66ansa yafurta iman kinkusa zuwa hannu aii, kunyar
nan tana cutata dayawa.
Bayin yashiga yayi wanka yafito, dashirin kwanciya yafito amma sai yaga lokaci yatafi
kasancewar yau _juma'a_ shirin masallaci yayi cikin jar shadda sai maik'o takeyi.
Ya murza bak'ar hula da bak'in agogo, turarensa na kullum ya fesa, tunkafin yafito
k'amshinsa yayo gaba.
Na tsurama k'ofar ďakinsa idanu, yayinda yafito aisai naga tamkar ba *Dr Isma'il* ďinaba, yayi
kyau harya gaji.
Sosai na dasa masa idanuna ko k'yaftawa banayi.
Jinai anhuremin ido".
Na sauke nannauyar ajiyar zuciya, tareda cusa kaina cikin cinyoyi saboda kunyar yakamani ina
kallonsa.
Kusadani yazauna yana dariya da faďin ďago abinki ki kalli _mijinki_ matana, niďin nakine ke
kaďai.
Ina nakasa ďagowa saboda ba k'aramar kunya najiba wlhy.
Da kansa yaďagoni yakuma rik'e fuskar tawa tamau atafin hanunsa yanda bazan iya
kwacewaba.
Rintse idona nayi dan bazan juri haďa ido dashiba, shikam yadasamin mayun idanunsa
tamkar yau yafara ganina.
Yakai tsawon minti biyar yana kallona.
Ban fargaba naji bakinsa cikin nawa, cikin kwarewa yake sumbatata, ban hanashiba domin
nima inajin daďin hakan dayakemin, *kunsandai SO yanda yake, yakansa ka aikata abinda
bakayi niyyaba*
_dan so yahaďu da so, sai ahaďu asoye tare_
Munkai tsawon minti ashirin ahaka, doctor yana abuďaya, saida yayi mai isarsa sanan
yazare bakinsa ahankali yana maida numfashi, fuskarsa cike da *annuri na musamman*.
Yaji daďin yanda yau natayashi abinda yakeso.
Saidai ni kaina nayik'asa ina fidda nawa numfashin ahankali.
Wata sassanyar dariya yasaki akunnena, cikin sigar *Salon so* ya ce, "lallai my iman kin fara
haddace karatun aure.........
Bai k'arasaba marwan yashigo shima cikin shirin masallaci, doctor ya hararesa koma kayi
sallama.
Marwan ya narke murya *ALLAH* Uncle nayi bakujibane kawai.
Banason k'arya".
*ALLAH* kuwa marwan yaske faďa kamar zaiyi kuka.
Na ce, "yayi sallamafa.
Ya maido da kallonsa gareni, kinji kenan?.
Kai naďaga batareda nayi maganaba.
Yay k'asa da murya, kece kika rikitani har nakasaji nakasa gani, *INASONKI DAYAWA
SAUDAT*.
ajiyar zuciya nasauke ahankali, yayinda shikuma yamik'e yana kama hannun Marwan.
My boy ya akayi?".
Marwan ya ce, "daddy ne yadawo shine na ce, "bari na sanar dakai.
Okey my son muje.
Saida suka kai k'ofa sanan yajuyo ya ce, "idan kinjishiru munwuce masallaci.
Kaina ak'asa na ce, " *ALLAH* yatsare, yadawo daku lafiya.
Amin mungide yafaďa yana fita.
Dr da Marwan suka nufi 6angaren yaya, da sallama suka shiga.
Yayansa yana zaune shima cikin shirin masallaci da alama su yake jirama.
Yamik'e da sauri tareda warema doctor hannu, alamar yazo.
Aiko da sauri yak'arasa yashige, suka rungume juna da faďin kewar dasukayi na nisantar
ruhinsu.
Yaya ya ďago kan doctor suka haďa ido suna sakarma juna murmushi, autan mama *soja*
kuma *likita*, katafi kabarmu da kewarka ko??.
Kuyi hak'uri yaya wlhy nima nayi kewarku, duk son danake nazama *soja* yanzu sainaji yafita
kaina.
Yayansa ya nunasa yana dariya anya kuwa zan yarda dakai Isma'il??.
Dr yayi dariya, wlhy gsky nake faďama yaya.
Rungumesa yayansa yaskeyi saboda jin daďin maganarsa.
Aunty ta balla musu harara batareda sun ganiba, azuciyarta ta ce, "naga *rai da mutum,*
k'arewar 'yan uwantaka.
Amma afili saita ce, "zakuyi missing ďin sallaffa Abban deexerh, dan ďaya harta kusa.
Da sauri suka saki juna suna kallon agogo.
Tak'araso tana salo ta fesama yaya turare tareda ďora masa hularsa akai.
Ya ce, "ngd gimbiyata.
Murmushi tayi masa, sanan tajuyo ga doctor zata fesa masa turaren, amma saiya kauce da
sauri, yana faďin a'a wanda matata tasamin ya wadatar.
Dariya yaya yamusu ya ce, " *ALLAH* yashiryaka Isma'il, kazama mara kunya dai.
Fita doctor yayi yana dariya.
Gaff sukai karo da mutum abakin k'ofa.
Yaďago da niyyar masifa amma saiyayi shiru dan ganin wadda sukai karon.
Suduka sun k'urama juna ido cikin wani yanayi wanda bakowane zai iya fassarawaba,
Bawata bace illah *Raihan* k'anwar aunty Sadiya, matar yayansa.
Shine yafara janye nasa idon akasalance, itako Kallonsa take tamkar zata cinyeshi ďanye.
Yadaure ya ce, "Raihan kece a kanon mu yau??.
Tasaki dariya cikin salo ta ce, "eh wlhy *yaa Isma'il*.
Ya ce, "sannunki dazuwa to, yafaďa yana k'ok'arin kar6ar k'aton akwatin hannunta, wanda
yanuna da shirin dogon zama tazo garin na kano.
Taďan janye tana faďin haba yaa Isma'il aiiba girmanka bane.....
Kafin yabata amsa yayansa yafito yana faďin kaidawa auta.......?
Maganarsa ta kakare dan ganin Raihan tsaye da kaya nik'i2, wata 'yar fara'a yasaki maikama
da yak'e, a'a Raihan kece tafe??.
Ta ce, "eh yaya, ina yini.
Bai amsaba ya ce, "shiga ciki mana.
Suka kauce suna bata hanya.
Taja akwatinta da jaka k'eeyyyy zuwa ciki.
Wani ihun murna auntyn tasaki saboda ganin k'anwarta, doctor da yayansa suka fice kowa
yana sak'a mai fisheshi azuciya.
Nikam koda yafita saina mik'e nanufi ďaki domin fesa wanka, dan inason fara amfani da
shawarwarin da deexerh take bani yau da kullum, akan narage kunya wajen kula da mijina, inba
hakaba wata zata samu k'ofar dazata shigo rayuwarmu.
Na yarda da batun deexerh musamman data bani na karanta wani *Novel na bilyn Abdul*
mai suna *RASHIN SANI* naga yanda *Nazeefa ta ruďa ya Mus'aff* dayake mata kallon 'yar
k'auye ada, har yana gudun aurenta, amma da aunty khadija ta gyarata yadawo yaganta saiya
haukace akan *RASHIN SANI*. to barema ni nawa mijin yana sona.
Nikam son danakema doctor aii bana fatan haka koda amafarkine, dan haka daga yau na
zage damtsen yimasa abubuwa na ban mamaki.
Karnayi saken da *sopy ta akan Abdul* a littafin *NI DA AMINIYATA* har fareeda ta samu
damar kwace matashi, kodayake tasamu *uncle G* wanda yafi Abdul komai.
Saidaifa ina hangen matsala kasancewar tun shekaranjiya marata take ciwo kaďan2, ina
daurewane kawai saboda batamin ciwo kamar da.
Haka na daure ina cije baki ina kwalliya tamkar dole.
Na tsara kwalliya tagani da faďa, nasan kowa yaganni saiya sake kallo kodan k'yawun danayi
na musamaman.
Nidai doguwace sosai kamar yanda kuka sani, dan tsawona yasa har 'yar rankwafawa nayi
kaďan, banida k'iba gsky dan kamar ahureni haka nake, bazance inada tsananin k'yauba amma
*Alhmdllh* muna tsaka tsaki, inada ďan haskena iya gwargwado dan ba'a kirani faraba, idan ina
kusada masu ra'ayin babu _chocolate colour_ aduniya, to dole akirani bak'a kuwa, _(dan wasu
sunce kala biyu suka sani aduniya daga bak'i sai fari)_.
Hancina kam ba dogo bane, saidai nace gajere, ga idanuna atsaka tsaki suba manyaba
bakuma k'ananaba, ďan gashina daidai wadaida masha ALLAHU.
wanan itace surata ni saudat amusalce, kunga kuwa niba mai mugun k'yau bace tafaďa da
nunawa, irinmuma ba'a sakamu gaban mota ace za'a farty.
Wata uwar harara *xoxo* tamata, ta ce, "iman aii dai godema ALLAH, duk wanda ya ce,
"bakida k'yau saidai _hasidin iza hasada_ wanda yakali sama ya ce, "akarkace take".
Reefat ta tuntsire da dariya, gskyar kine my xoxo.
Bagashi ta haukata mana *Dr Isma'il* ba.
Gaba ďaya suka shek'e da dariya suna tafawa.
*(na ce, "kai 'yammatan nan suna burgeni ni bilyn Abdul)lolí ½í±Œí ¼í¿»* ...............✍í ¼í¿»
*((S))........2017*
*luv u oll my fan's*
*Battery low*
[8/6, 6:00 PM] mrs bilkisu: *________________________________*
*BAN SAKETA BA!!!*
*________________________________*
*NA*
*BILKEESA IBRAHEEM*
*{bilyn Abdul}*
*_________________________________*
https://mrsbilkisa.blogspot.com
_sadaukarwa_ *~ya Abdul (city phone's)*
*MIYAKAMA NAYI???.*
_ba matane kawai suka shagala a *duniyaba* harda abokan jinsinsu wato *maza*_
*maza* _ma sun shagala a *duniya* wlhy, zakaga babban mutum magidanci mai tarin *zuri'a*
amma yana wasa da ibada, saboda uzurin office kona kasuwa._
_wani akan kunnensa liman zai kwala kiran sallah, amma saiyace bari yagama sallamar
*customers* sannan, wani kuma idan a office ne saiya kawo uzurin k'are takardun dake
gabansa_
_Haba ďan uwa duk abinda kakenema yana wajenfa wanda aka kiraka domin bauta masa,
magidanta sunada matuk'ar sakaci awajen yawan nafilfili na dare da azumin nafila, saboda
hujarsu tacewa sunje nema sun gaji_.
_A'a ďan uwa gyara sai ALLAH ya gyara maka, gyara kodan iyalinka suyi koyi dakai,
amatsayinka na uba, miji, shugaba._
_Abinda mukayi da shi 'ya'yanmu zasuyi koyi, su tsira mu tsira, aranarda aikinmune kawai
garkuwarmu!!!!!!!._
*ALLAH yasa muga ne.*
~page........1⃣1⃣~
................bayan sun idar da sallah suka sake zama.
Iman ta ďora labari."
Bayan nagama tsara kwalliya na baďe 6angarena dawani sabon k'amshin, dan nasan
mijina ma'abocin son k'amshine, gida yaďauki haramin k'amshi tamkar gidan saida turare.
Duk wanan aikin cikin dauriya da jarumta nakeyinshi, ina zama saiga deexerh tashigo da
sallama, hannunta ďauke da filet.
Naďago ina amsa mata tareda tsokana, ďiyar uncle mi'aka samomanane?.
Kusadani tazauna tana dariya, abinda kike matuk'ar so nasamo, ammafa saidai ayi cinikinsa.
Da sauri na ce, "indai har abinda nakeson ne, to mikikeso nabaki??, taďan langa6e kai
alamar tunani, saikuma taďago tana faďaďa murmushinta, ba kuďi nakesoba, sonake ki lalla6a
min uncle yasa dady yakaimu wajen mom ďinmu gobe idan ALLAH yakaimu mu wuni acan.
Tabani tausayi matuk'a, amma gudun karna karya mata zuciya sainayi murmushin k'arfin hali,
na ce, "insha ALLAHU dee.....ďin uncle zanyi wanan k'ok'arin.
Ta faďaďa murmushinta tareda faďin ngd sosai auntyna k'awata, mamana, kuma ta biyu,
shiyyasa akulum nake k'ara sonki, zuwanki gidannan yasa muka k'ara rage maraicin rashin uwa
akusa, dukda k'ok'arin mama na son sharemana hawaye itada uncle, ta k'are magana da matso
kwalla. Hannu nasa ina goge mata hawayen, badan karna k'ara tada mata hankaliba dana
tambayeta dalilin barin mom nasu gidannan, amma saikawai nacigaba da lallashinta.
Bayan wasu 'yan mintina ta lafa da kuka ta bani filet ďin dake rufe, cikin zaro ido na ce, "lah
dee.... ina kika samo fara??.
Tayi 'yar dariya, wlhy a school na siyo miki saboda nasan kina sonta sosai.
Rungumeta nayi ina murna damata godiya harda addu'ar fatan alkairi arayuwa..........da sauri
muka juyo danjin k'arar buďe k'ofa da matuk'ar k'arfi.
Cikin sanyin jiki muke kallonta, sa6anin ita datake kallonmu cikin tsana da tsangwama, ta
ta6e baki tana yatsina, bazanyi mamakiba domin yanzu mace da macema haďuwa suke su sa6i
ALLAH.
afirgice muke kallonta danjin ficinta mai matuk'ar muni da firgici.
Deexerh ce ta iya daurewa tafurta wani abu, ta mik'e tana kallon matar baban nata cikin
tsana, ''k *Sadiya!!!* kishiga hankalinki wlhy, muba shaiďanu bane bare ki jinginamu da wanan
fasik'ancin, kuma tabbas daga yau munta haďaki da ALLAH kenan acikin sallolinmu harsai ya
saka mana, kuma zakiga fasik'ai insha ALLAHU a zuri'arku, _tsumma mak'ullin cuta kawai_
*ALLAH zaimana maganinki komai daren daďewa* deexerh nagama faďa tafice daga falon
tanufi 6angaren mama tana kuka. Nikam aii mutuwar tsaye nayi ga marata ta k'ulle tamau, itama auntyn tana tsaye tamkar
gunkin da aka dasa awaje ďaya, ta maido da kallonta gareni zuwa sanan nafara shiga
mawuyacin hali..... dan 6acin ran maganarta yasa marata tayi wata muguwar wakitawa, kafin
tayi wani yunk'uri nafaďo k'asa ina murk'ususu, adai dai kuma wanan lokacin doctor yashigo
falon.
Da gudu yak'araso gareni yana kiran _iman! Iman!!_ ina nayi nisa cikin ciwo, arikice
yaďagoni jikinsa yana girgizawa saiga su mama da deexerh sun shigo.
Mama tak'araso arikece tana tambayar lafiya??, tanayi tana kallon aunty sadiya dan deexerh
taje ta sanar mata abinda aunty taimana.
Aunty ta ce, "wlhy mama bansan miya sametaba, nima naga kawai ta faďi tana rik'e
ciki........doctor yakatse musu zancen da faďin karku damu mama nasan matsalarta, rik'eta ina
zuwa.
Mama ta kar6eni doctor kuma yafice domin nemo allura.
Tunda yatafi nake murkususu ajikin mama dakiran sunan gwaggo, dakuma duk addu'ar
datazo bakina.
deexerh sai kuka take azatonta abinda auntyn tayi manane yakawo ciwon, lokacin da soctor
yadawo har suma nake dan azaba, tareda yayansa suka shigo.
Mama ta rik'eni yay min allurar, zuwa wani lokaci sainayi sakwat alamar ciwon ya gudu,
harma barci yafara ďibata.
Mama ta ce, "isma'il ďaukrta kakaita ďaki.
Kamar jaririya haka ya ďaukeni yakai saman gado yadire, yana mai k'ara jin tausayina da
tuhumar kansa akan sakaki, dan yasan shine maganin matsalata amma yakasa min maganin
tunda wuri, saboda shagalal dayayi akan wata yawuce banyiba.
Rashin lafiyata ta hana tada maganar da aunty tayi mana.
Har dare ina barcina ba'a tadaniba.
Dak'yar suka lalla6a doctor ya