Showing 39001 words to 42000 words out of 79986 words

Chapter 14 - Ban Saketa Ba Compelet Billyn Abdull

01 Aug 2026

805

iman, fisge
wayar yayi ya yanke kiran, 'yammata saifa kin saurareni.
To tunda ana dole basai muganiba.
Dariya yayi sosai, zan kar6i number ki wajen khadija zan gaya miki satar dakikamin, sanan
kijira zuwan rundunar sojoji gidanku kar6ar madadin satar dakikamin..
Daidainan deexerh ta k'araso, yamik'a mata wayarta tareda fad'in sai kinjini, kud'i yad'akko
yabama deexerh, khadija ga wanan kibama bak'uwarmu tahau mota.
Deexerh ta rissina ta kar6a tana fad'in to uncle angode.
Xoxo kan gaba tayi bata tanka musuba.
Hannu yasaka a aljihu yana binsu da kallo har suka 6ace sanan Yakoma cikin asibitin yana
murmushi masifar Xoxo.
Dr Isma'il ya kallesa kai abokina duk kawani rud'e wlhy.
Dariya Dr Nabeel yayi, badoleba abokina soyayya aii ba k'arya bace.
Hakane Dr Isma'il yafad'a yana murmushi.

Deexerh ta ce, " aunty hafsat Kodai Kodai keda uncle Nabeel ne?.
Kodai2 me Xoxo tafad'a tana zaro ido😳.
Dariya deexerh tayi, naga kamar sonki yakeyine?.
Tab rufani ki sayani, ko d'aya tafad'a tana tare adaidaita sahu, saida tashiga sanan Deexerh
tasaka mata kud'in da Dr Nabeel yabata a jaka, toga k'yautarki.
Tab nifa bazan kar6aba ki maida masa kayansa.
Habadai ai ba'a maida hannun k'yauta baya, ngd sosai kigaidamin mutan gidan.
To zasuji mai adaidaita yaja suka wuce deexerh na d'aga mata hannu.

Iman kuwa tunda suka bar asibitin tazama wata shiru2, koda suka koma gidama d'aki tashige
tayi shiru, sallah kaiwai ketashinta, wajen k'arfe 6 taji wayarta tad'anyi wringing, d'auka tayi
taduba, saitaga Xoxo, tayi murmushi 'yammata ni kikema flashing?.
Komawa tayi takwanta, ganin xoxo bata sake kiraba yasa ta tashi, d'ari biyu ta d'auka tafice.
Deeni na zaune afalo yana cin abinci tabasa, deeni idan ka gama Dan ALLAH d'an siyo min
kati.
To aunty, Dan ALLAH Nima d'an bani d'ari, inada d'ari nacika nasiyo katin, data nakeson saya.
Hararasa iman tayi, kai Dama kud'inka aii a sayen data zasu k'are, ALLAH ya shiryeka.
Amin aunty, nidai idan zaki bani aii babu matsala.
Fita tayi bata tanka masaba, babu dad'ewa tadawo da d'ari biyu ahannu tabashi.
Kai my aunty ngd, shiyyasa wlhy nake k'ara sonki.
Iman tayi murmushi kawai takoma d'aki ta kwanta.
Babu dad'ewa yakawo mata katin tasaka.
Saida tafara gwada Number Reefat, har yanzudai bata Shiga, afili ta ce, "ALLAH yasadai lafiya.
Xoxo takira bugu d'aya ta amsa, suka gaisa cike da kewar juna, Xoxo ta ce, " ai d'azu naso
na kiraki nace miki INA wajen mijinki, saikuma aka samu matsala.
Aii flashing d'inki Dana ganine ma yasa nakira da fushi nakeyi dake.
Ohh my sis.... Kiyi hak'uri, wlhy zanzo gobe idan ALLAH ya kaimu insha ALLAHU, wani

abunema yahana in zuwa jiya da yau.
To shikenan na hak'ura, kinsan bana iya fushi dake, ALLAH ya kawoki lfy.
Amindai,
Wai Yaya kema har yau bakya samun Reefat?.
"Wlhy bana samu, ni harma nafara tunanin ko lafiya?, wlhy Nina haka, to ALLAH yajishemu
alkairi.
" Ameen dai".
Sukai sallama kowa ya kashe wayar.

_Bayan kwana hud'u_
Jikin Dr Isma'il yayi sauk'i sosai harma an sallamesa yau.
Iman dai bata sake zuwa dubashiba, bakuma takira wayarsaba, gwaggo da Abbah sunje har
sau uku, hakama su aunty salma sun sake zuwa, Xoxo ma tak'ara zuwa.
To Dr Isama'il ALLAH yak'ara sauk'i.

*_WATA SABUWA_*
Gidan su Dr isma'il yau cike yake da mutane, dangin mahaifinsu ne sukazo dubashi, ciki
kuma harda baban su aunty sadiya, bayan anci ansha aka zauna ana hira.
Acikin hirarne kawu Falalu yake fad'in sufa dawata magana sukazo, mama ta ce, "to falalu
muna saurarenka.
Kawu falalu yagyara zama yana kallon mama, ya ce, " maganace akan Sama'il, lokaci yayi
daya kamata yayi aure, wanan zaman dayakeyi bazai haifar da d'a mai idoba, tunda kowa
yasandai ba'a komawa saki uku, to Dan haka yama fidda rai akan matarsa, saidai idan darabon
zama nan gaba zasu zauna. Hakane mama tafad'a fuskarta babu walwala, Dan tasan Dama ba alkairine yakawosuba.
Kawu falalu yacigaba, to yanzu dai mun yanke shawara Nida Lurwanu da Maharazu, da
Karima akan zamu k'ara k'ulla zuminci, mudai nida maharazu da Karima bamuda yara mata, sai
Lurwanu, Dan haka muka Yanke shawarar aurama Sama'ila Zakiyya,(Raihan).
Gaban Dr Isma'il ne yafad'i da Sauri yad'ago yana kallon kawu falalu.
Kawu falalu yacigaba da fad'in, to yanzudai maganar damuke muku, ni na biya sadaki an
d'aura auren tun a can, shinema dalilin dayasa kukaga mun taho da Raihan, gata nan
munkawota suzauna lafiya, ga 'yar uwarta nan intayi ba daidaiba zata ringa tsawatar matane,
kumadai saiku kula, intayi ba daidaiba a gyara mata Dan kunsan yarinyace karama sai hak'uri. Tunda yafara maganar falon yakarayin tsit, bakajin motsin kowa, sai aunty da Raihan Dasuke
murmushi.
Yaya ya bud'e baki zaiyi magana mama ta girgiza masa kai alamar yayi shiru.
Shirun kuwa yayi amma idanunsa sun cika da kwallah, tu da mahaifinsu suka bar duniya,
dangin mahaifinsu suka watsar dasu, basa kulawa dasu ko kad'an, basa zuwa Inda suke, har
saida sukaga sun girma sun zama wani Abu, shine akazo aka k'ak'aba masa auren sadiya,
zuwan sadiya baifi da wata ukuba uwar 'ya'yansa tabar gidan mamansu deexerh. To gashi kuma yanzu an mannama Isma'il Raihan, bayan abaya mahaifiyarta ta CE, "bata
yarda Isma'il ya auri Raihanba baza'a tara mata 'ya 'ya agida d'ayaba........
Maganar mama ta takatse masa tunani.

Shikenan falalu, mun amshi k'yautarku ALLAH yasanya alkairi, saidaifa kunyi kuskure Dan
yakamata kafin kuyi Auren kukiramu asanar damu Dan aji tabakin Isma'il d'in, amma yanzu ya
wuce saidai Atari gaba kawai.
Baban su raihan ya katse mata zancen da fad'in, Maryama kinsandai munada iko da Sama'ila
muma ko?, Dan duk duniya bashida iyayen dasuka wuce mu, ko Neman auren zashi wani waje
dolene mune wakilansa, to tunda abin yazama na gida kuwa aikinga koya sani ko bai saniba,
koya yarda kobai yardaba dolene yakar6i 'yar uwarsa yarik'e da hannu biyu, kuma naga dama
suduka suna son juna daga sama'ilan har Raihan d'in, kawai abaya ALLAH ya rubuta bazata
zama matarsa bane.
Kaga Lurwanu nifa babu abinda nace maka, Dan haka maganarnan bata 6acin rai bace,
aurene kun d'aura kuma nace mun kar6a, to saime?, duk wata maganarma kun Isa bata tasoba,
Inda bama ku isanba aii wlhy babu mai aurama yarona aure batareda yardarsaba.
Sunsan halin mama sarai Dan haka suka Shiga bata hak'uri da magana mai dad'i, anandai ka
masu Dr Isma'il nasiha shida raihan.

Deexerh taji zafin wanan had'in ammafa tawani 6angaren taji dad'i, Dan idan bata mantaba
aranda suka Gana da bilyn Abdul tace musu inama Raihan ta Auri Uncle, da komai saiyafi
saurin fitowa fili.
Wanan yasa bataji haushiba sosai.

Saidai ana gamawa da uncle d'inta aka dawo kanta.
Kawu Maharazu ya ce, "kema hadiza mun Baki nan da wata Biyar Kodai ki fito da mijin aure
kokuma muhad'aki aure da Kamilu na wajena.
Ido deexerh ta zaro ta ce, " kawu Kamilufa kace?.
Eh shifa nace, Dan haka saikiyi gaggawa..... Dr Isma'il ne ya katse masa zancen da fad'in a'a
kawu nanfa ba huruminku baneba, domin khadija jikace agareku, mune iyayen khadija mu
Muke da damar aurar da ita lokacin da mukaso, ayanzu kuma karatu takeyi, sainan da wata
Tara zata kammala, saikuma ta kammala sanan zamuyi mata maganar aure, mudai damuke
'ya'yan d'an uwanku, Duk abinda kukaga dama kuyi damu, saboda darajar kun kasance jinin
mahaifinmu na kusa.....
Sama'ila mukake gayama haka Dan ubanka, to ai ko Mahammadu dayanada rai bazai
fad'amin hakaba akan zuri'arsa......
Mama ta katseshi, Maharazu gskya fa Isma'il yafad'a bakuda hurumin za6ama hadiza miji,
sudai dasuke 'ya'yanku zaku iya amma banda su hadiza jikoki.
Ehh lallai maryama aii dama duk wata wuta kece kike kunnata tsakaninmu da yarannan, kece
kikasaka basa ganin darajarmu, wanan mugun halin naki yasa Karima ta CE, "bazata
biyomuba.
'Mama tayi wata 'yar dariya, Maharazu kenan, aiini duk abinda zakuce dangane da yarannan
banida Matsala daku'.
Kundai San inada iko dasu, todan haka maganarma ina 6ataku agunsu aii daga baya kenan,
Dan tuni sukasan matsayin su agunku.
Haka aikata cacar Baki, daga bayadai Yaya yashiga tsakani aka sulhunta.
Washe gari su kawu lurwanu suka koma.............

_to masu karatu koya Iman zataji wanan labari?,._
_Yaya zaman Raihan da Dr Isma'il zai kasance?._
_shin auren Raihan zai kawo mafita dangane da matsalarsu Dr Isma'il da Iman, kamar yanda
Bilyn Abdul tafad'ama su deexerh?._
*humm kubiyoni danjin yanda zata kasance*




*luv u oll my fan's*
*(((S)).....2017*
[8/6, 6:01 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!._*





*NA Bilyn Abdul*




_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*

https://mrsbilkisa.blogspot.com




*miya kamata nayi?*
_babu nakasashshe sai kasashshe, babu maraya sai rago._
_Karka zauna kadogara dawani, kadage kidake munemi nakammmu, addini yana ingantuwa
idan masuyinsa suna cikin natsuwar wadata, ba tarin dukiya bane wadata, wadar zuci itace
wada, komin k'ank'antar abinka ka rungumeshi kasaka masa albarka, kahangi na k'asa dakai,
kada ka hangin nasama dakai, kagodema ALLAH dakad'an d'in daya Baka, duk Wanda yakasa
Gode kad'an koya samu mai yawa bazai godeba._
_Duk Wanda yagaza godema ALLAH to kuwa zai godema azabarsa._
*ALLAH yasa Mugabe*

*(Page 21)*
Ya Majeed nagaba, hannunsa rik'e da affan, aunty salma tana bayansa, iman CE
ak'arshe, tafiya take tamkar wadda kwai ya fashewa aciki.
Saida suka shigo cikin asibitin sosai sanan ya Majeed yad'auki wayarsa yayikira, assalamu
alaikum.
Eh gamu mun iso, okey.
Juyowa yayi yace kumuje nama gane d'akin.
Ak'ofar wani d'akin suka tsaya ya Majeed ya kwankwasa, sanan yatura da sallama suka
Shiga, d'akin cike yake da mutane, aunty salma da iman suka shigo, sannu dazuwa aketa
musu, itadai iman kanta yana k'asa bata kalli kowaba.
Jitai an rik'e hannunta da Sauri tad'ago danson ganin waye, deexerh tayi dariya my aunty
nabaki tsoro ko sorry.
Ido iman tazaro sai yanzu ta fahimci Wanda sukazo gani..... Deexerh ta k'atsemata tunani da
fad'in kai auntyna naji dad'in zuwanki wlhy, murmushin yak'e tayi suka k'arasa, su aunty sunata
gaisawa da mutane datanbayar mai jiki.
Iman ma ta daure ta ce, "INA yininku, yamai jiki?.
Gabad'aya aka amsa, Dr Isma'il dake a jingine da fillo, 'yan biyu sun sakashi tsakkiya, yasaki
wata wawuyar ajiyar zuciya saboda ganin Iman.
Gaba d'aya d'akin aka maida kallo gareshi, ganin wadda yake kallo yasa suka dawo da
kallonsu kanta, babu Wanda yagane Iman da farko, saboda ta lull6e fuskarta da gyale.
Mama ta ce, " hadiza wacece wanan?.
Dariya deexerh tayi, lallai mama kindai k'ara tsufa wlhy, to aunty Iman CE, ta janye galen
iman.
Mama ta mik'e da sauri ta Isa Inda suke, hannun iman takama tana mai jin dad'in ganinta,
iman 6oye mana kanki kikeyi?.
Cike da kunya iman ta rusina tana gaida mama, mama ta rungumeta haba iman duk kin
manta damu, Yaya da mom deexerh sai murmushin sukeyi, amma aunty tuni nasaka mata
alamar tambaya, Dan afirgicema take kallon iman d'in.
Mama takama hannun iman taje ta zaunar, harga ALLAH tana tsananin k'aunar iman domin
yarinyar kirkice, k'addarace kawai tarabasu Dan basuda yanda zasuyi.
Iman ta rissina tana gaidasu Yaya, cike da fara'a suka amsa, Yaya ya ce, "iman kin manta
damu ko?.
A'a Yaya wlhy karatune.
Da k'yau, yanzu kina level nawa?.
"Ina level 3, iman ta amsa kanta ak'asa.
Lallai Iman kun zama manyan 'yan boko, murmushin tayi batareda tace komaiba.
Ya Majeed ya ce, "zadai su zama nagaba kad'an, aii sun d'akko hanya Majeed Yaya yafad'a
yana dariya.
Iman tad'an kalli Dr Isma'il ta ce, " INA yini, ya jiki?.
Dr Isma'il dake zaune ya dasa mata idanu ko k'yaftawa bayayi, ya sauke ajiyar zuciya
ahankali ya ce, "da sauk'i ykk?.

Shiru tayi bata amsaba, deexerh dake gefe sai zabga murmushin take, jitake inama har
yanzu Iman tana tareda Uncle d'inta.
" gsky lokaci yayi dazata taka rawar gani wajen binciko gskyar Al'amaree, amma zata nemi
Xoxo akan shawarar dasukayi ranar na nema *bilyn Abdul*, ance tashahara wajen irin wanan
aikin, akwaita da naci wajen nemo rahoto, insha ALLAHU zasu nemeta kuma ko nawa takeso
zasu biyata taimusu aiki, itadai Uncle d'inta yasamu farinciki. Marwan da Musayeef suka shigo d'akin da sallama, Dama basanan an aikesune.
Yana hango mamansa yasaki hannun marwan ya cilla da gudu ya rungume iman, aunty maa
yaushe kikazo?.
Kansa ta shafa tana murmushi, yanzu nazo Musayeef.
Aunty maa kinzo ganin dadyna bashida lafiya?, kai tad'aga masa kawai, Yakuma fad'in danfa
bakizo kin koya masa game bane ranar, yake rashin lafiya ko daddy?.
Kai Dr Isma'il ya d'aga masa alamar eh.
Yadawo da kallonsa kan iman, ni babu ruwana dake, yafad'a yana ja da baya tareda turo
Baki.
Mutuwar zaune iman tayi, a zuciyarta ta ce, "kajimin yaro zai d'aureni azaune.
Yaya ya ce, " a'a my son aii ba'a 6atawa da uwa, zonaji miya faru?.
Wajen daddynsu deexerh yanufa, Iman Addu'a take ALLAH yasa kada yafad'a tasan shegen
surutun Musayeef. Wayonsa ya girmi shekarunsa.
Yaya ya CE, "miya faru kaida aunty maa d'in kake fushi da ita.
Dady ba ita bace, nasa daddyna yakiramin ita na ce, " tazo takoyama daddyna game, ta ce,
"zatazo amma tak'i zuwa.
To kayi hak'uri ai yanzu gata Tazo zata koya masa Kaje Ku shirya. Musayeef ya kalli iman,
aunty maa wai zaki koyama dadyna game d'in?.
Ganin yanda Dr Isma'il ya tsareta da idanu yasa ta gyad'a kai alamar eh, tsallen murna
yafarayi.
Yanufi dadynsa, hannun yasa ya d'auki d'aya daga cikin wayoyinsa dake gefensa yakaima
Iman, to gashi zoki koya masa, idan mun koma gida sai muringa yi nida shi.
Iman ta ce, ''kaga yanzu bashida Lafiya kabari saiya warke sainazo har gida na koya masa.
Ehumm ehumm!, Musayeef yafad'a yana nok'e kafad'a da kya6e fuska😞.
Iman tayi banza dashi Dan taga rigimarsa bamai k'arewa bace, yakware Baki zaiyi kuka.
Da sauri mom d'in su deexerh ta ce, " kaga ishirunka yarona zata koya masa, jeka bata wayar.
Jin anfad'i haka yasashi saurin kallon Iman, ta had'e fuska tana harararsa, yaja da baya yana
hawaye.
Dr Isma'il dake kallonsu saidai babu magana, sabida baya iyawa sosai, ahankali ya ce, "pls
My live ki kar6a..
Dukda ahankali yayi maganar duk sunji abinda yace, aunty tana siririn tsaki Wanda basu
jitaba.
Hannun iman tamik'ama Musayeef ya d'ora mata wayar daddynsa ahannunta, yana dariya ga
hawaye afuska.
Aunty Salma ta ce, " hum su Musayeef rigima.
Hannun Iman ya hau ja yana fad'in ki tashi to kinji aunty maa, kinji!.
Mama ta CE, "ohni maigida kabi ka hanamin d'iya zaman lfya, kabarta ta huta Dan ALLAH.

shidai kira yake kitashi kinji aunty maa.
Marwan yay dariya, aunty Iman idanfa baki koya game d'innanba yau kinga takanki wlhy,
garama kawai ki koya.
Murmushi iman tayi ta ce, " Dan ALLAH marwan ka d'aukeshi kufita ALLAH dukya isheni.
Harararta Dr Isma'il yayi, yakamo hannun Musayeef, ahakali yake magana, kaga Musayeef
zokaji wata magana, deexerh ta d'auki Musayeef tad'ora kangado Kusada Dr Isma'il, akunne
yafad'a masa maganar tuni Musayeef ya washe Baki yana Murna, yakalli iman yay mata gwalo
ummmeeh �bazamu da aunty maa ba kuma. Gaba d'aya d'akin akasaka dariya, banda iman da Dr Isma'il dasuke murmushi.
Aunty tamik'e zatafita itama batayi dariyarba, Yaya ya ce, "INA zaki? Zan siyo kati ne tafad'a
tana tafiya.
Yanzu nan ga Marwan ga Khadija bazaki bama wani yasiyo mikiba sai kinje da kanki?.
Na hutar dasu tafad'a tana ida fita girgiza kai Yaya yayi Dan halin sadiya yafara isarsa,
kwata2 bayajin dad'in zama da ita, sauk'inma ba ita kad'ai gareshiba aii datuni shima ciwon
zuciyar ya kamashi.
Deexerh tafaki idon kowa ta fice,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0