Showing 18001 words to 21000 words out of 79986 words
halarci wajen cin abincin, sai asanan mama da deexerh da
marwan suka san da zuwan Raihan, basu canja da komaiba suka k'ar6eta kamar yanda suka
saba, dan sunsan laifin yayartane, _(laifin wani kuwa aii baya shafar wani)_.
Sai bayan isha'i na farka, lokacin doctor yatafi masallaci shida yayansa da marwan,
deexerh ta taimaka min na gyara jikina tsaf kamar komai bai faruba, sanan muka nufi wajen
mama.
Tana falo zaune muka shigo, tabini da kallon mamaki 'yar nan wanan ciwo naki tamkar iska?.
Nayi dariya tareda risinawa ina gaisheta, ta ce, "yajikin??.
Da sauk'i mama aii yakuma tafi.
To ALLAH yak'ara sauk'i ya kiyaye gaba, na ce, "amin mama, anan ne mama take bani hak'uri
akan abinda yafaru ďazu, takuma rok'eni karna gayama mijina.
Babu komai mama insha ALLAHU bazai jiba, kumani wlhy harma na manta.
Yauwa ďiyar kwarai ALLAH yayi miku albarka kunji, nida dee....mukace amin.
Muna nan zaune muna 'yar hira saiga marwan yashigo, mukai masa sannu da masallaci ya ce,
"yauwa auntys, yajiki aunty??, da sauk'i marwan aina warke........kafin yabani amsa Raihan
tashigo falon, muka amsa mata sallamar datayi, nidai sai binta nake da kallon mamaki dan
bansantaba, saidai suna kama da aunty kam. Ta zauna tana min sannu da jiki, cikin sanyin jiki na amsa mata, deexerh ta ce, "k'anwar aunty
ce, ďazu tazo.
Na ce, "ayya sannu da zuwa".
Ta amsa da yauwa kema sannunki.
Doctor yashigo shima yana faďin dama kinan nan iman??, eh ina nan babu daďewa muka
shigo nida dee...., okey yafaďa yana zama kusadani, ya ce, "yajikin naki??, Alhmdllh nafaďa
kaina ak'asa saboda kunya.
Mama ta ce, "auta kundawo?.
Eh wlhy mama mundawo.
Ta ce, "sannunku."
Yauwa mama.
Sau wajen huďu ina kama Raihan da doctor suna kallon juna, shi idan ya kalleta yakan
janye idonsa amma ita ko gezau bare kunyar mama.
Zuciyata tashiga nazarinsu, dan suna kallon junane cikin rashin gsky da alalomin tambaya??.
abinda na kula bani kaďai nagane hakanba, harsu mama suna kallonsu, kallo ďaya nayima
mama kuma nagano alamar 6acin rai afuskarta, da ga k'arshema sainaga kawai ta tashi tabar
falon.
Lokacin maga tamkar alamun tsoro sun bayyana afuskar doctor, akasalance yakama
hannuna mukabar falon muma, tareda faďin saida safenku.
Koda muka koma 6angarenmu ban tanbayesa wacece Raihanba?, zama kawai nayi saman
kujera, shima yazauna yana shafa kaina my iman sannu kinji, wlhy lokaci k'an k'ani kinsha
wahala.
Ban cemasa komai ba, dan wasu abubuwa suna yawo akaina, ganin bazan tanka masaba
yasashi mik'ewa yashiga ďakinsa.
Babu daďewa yafito sanye da gajeren wando da bes, yazauna k'asan kafet ya ce, "nakawo
masa kayan marmari yasha.
Akasalance namik'e zuwa kicin yayinda shikuma yabini da kallo mai cike da tunani iri2.
Nakawo masa yankakkun kayan itatuwa na ajiye.
ya ce, "sannunki.
na ce, "yauwa.
Harna juya zan koma ya ce, "zo mana, babu musu nadawo, ya nunamin kusadashi, nanma ban
musaba na zauna.
Ya ďako abarba zuwa bakina, amma saina girgiza kai na ce, "nak'oshi.
Yaďan rage fara'a, idan na amince kin k'oshin ko??, yafaďa yana 'yar hararata.
ban ta6a ganin fuskarsa a haďeba sai yau, dan haka na buďe baki yasaka mini, haka yayta
bani shima yana sha har muka k'oshi.
Daganan falon muka zauna saidai yau babu hira, idan na kalli doctor ma sainaga bashida
walwala, dahaka har goma tayi mukaije muka kwanta konace na kwanta.
Dan harna fara barci sanan naji motsin shigowar doctor ďakina.
Ban motsaba bare yagane na farka, ya hawo gadon ya kwanta saidai amamakina yau bai
rungumeniba tamkar yanda yasaba, abin yabani mamaki amma saina danganta hakan da
gajiyar tafiya dakuma fashin sallah danakeyi.
Wasa2 har wajen k'arfe ďayan dare doctor bai runtsaba, nima ko barcin ya ďaukeni saina
farka saboda yawan motsin da yakeyi, yanzu tunanina yatashi daga zargin farko, yakoma akan
Raihan k'anwar aunty.
Tabbas akwai abinda bansaniba, akwai wata alak'a tsakaninta da doctor da Raihan.
_" wai wacece *Raihan* ne???._
Mutum ďayace zata bani amsar tambayata, wato _*deexerh!!!!.*_.
Sai gabannin asuba barci ya ďaukemu, wanan yasa muka makara sallar asuba.
Ban koma barciba nafice wajen aunty kamar yanda nafara kwanan nan dan yanzu dani ake
girkin gidan.
Shikam doctor barci yakoma.
Haka mukayi aikinnan nida ita bamaima ďan uwansa magana dama haka mukeyi dan babu
shak'uwa tsakanina da ita.
K'arfe bakwai na safe muka gama haďa break 'yan aiki suka kwasa zuwa 6angaren mama,
mukuma kowa yanufi ďakinsa.
Koda naje ban kwantaba saikawai na hau gyaran 6angarena dukda bawani datti bane, tunda
nakula doctor baya ra'ayin masu aiki nima saina daina sakasu gyaran wajena, nazage inayi da
kaina.
Bayan nagama nayi wanka nashirya tsaf cikin rigar material doguwa, ina fesa turare doctor
yatashi.
Yadaďe datashi ban saniba, idonsa na kaina duk motsin danayi saiďan murmushi yake yana
lumshe idanu, tacikin madubi nagansa tsaye abayana sanye cikin pink ďin kayan barci.
Najuyo ina faďin lah katashi?.
Murmushi yayimin ya ce, "badoleba tunda gimbiyata tatashi bata tadaniba.
Kaina ak'asa ina wasa da zoben hannuna na ce, "kayi hak'uri to dan ALLAH, naga bakayi
barci ishashshe bane jiya.
Maimakon yabani amsar tambayata ta k'arshe, saiya ďauki ta farko yay sharhi akai.
hannuna yakama yana murzawa karki damu na hak'ura, aike bak'ya laifi awajena my iman,
kinrigaya kin mallake zuciyar Isma'il daduk wani aikinsa.
Huumm to shikenan ngd, yakamata kayi wanka ko?.
Nafaďa ina zare hannuna daya rik'e.
Bai iya amsaminba saidai bina da kallo dayayi harna fice, aďakinsa na haďa masa
ruwan wanka, sanan nadawo shikuma yatafi.
☆
A falon mama duk mun hallara muna break, yauma tamkar jiya haka doctor da Raihan suke
satar kallon juna, zuwa can kuma saina farga da taka k'afar doctor da Raihan takeyi ta
k'ark'ashin tebir, shikuma yana janyewa.
Abisa tsautsayi ta taka k'afata saboda nike kusada doctor, na kalleta muka haďa ido sosai,
saitayi k'asa da kai cikin jin kunya.
Dahakadai muka kammala break, yayansa ya ce, "yazo su tafi kasuwa..
Sallama sukai mana suka tafi, muka rakasu da ALLLAH ya kiyaye hanya..
_*miss xoxo da Reefat*_ sukace tofa kaji wata sabu kuma??, iman kin k'ara sakamu
atunanifa.
Shin wacece Raihan!!.?
_*iman*_ tasaki murmushin basarwa, karku damu 'yan uwana, zuwa gobe zakusan wacece
Raihan, ammafa kar tazame muku matsala, dan ita ba matsala baceba.
To ALLAH yasa hakan, suka faďa kowa yana kwanciya................✍í ¼í¿»
_*luv u oll my fan's*_
_*((S)).........2017*_
_*battery low*_
[8/6, 6:00 PM] mrs bilkisu: *________________________________*
*BAN SAKETA BA!!!.*
*________________________________*
*NA*
*BILKEESA IBRAHEEM*
*{bilyn Abdul}*
*________________________________*
https://mrsbilkisa.blogspot.com
_sadaukarwa_ *~ya Abdul {city phone's}*
*MIYAKAMATA NAYI??,*
_Komai ka rasa zaka iya samun wanda ya fishi, Amma banda kwanakin rayuwarka,
idan sun tafi sun tafi kenan, Domin haka karka 6ata rayuwar ka wajen abinda bazai amfane ka
ba, yi kokari wajan yin abinda zai amfaneka duniya da lahira...""_
_kyautata ibadarka domin danmu bautama ALLAH ya halicemu, idan baka iyaba ko
kanada k'arancin ilimi nemi malami ya koya maka, ba'a ibada da jahilci, "ubangiji baya kar6ar
ibadar jahili._
_muguji salwantar da yininmu da kwananmu akan duniya da abinda ke cikinta, domin lokacin
ďan adam mai tsadane, asarar second ďaya ga mumini daidai take da asarar shekara dubu._
_Mizai hana mutsara lokacinmu domin ammafanarsa a ranar data dace_.
```Karka bari duniyarka taringa tafiya tamkar cin abinci, dakaci saikayi kashi, kaga kuwa sara
kenan```.
_gyara yau da gobenka domin amfanar jibinka_
*ALLAH yasa mugane.*
_*wannan page ďin nakune 'yan group ďina, ina alfahari daku sosai, ina k'aunarku har bansan
iya adadiba, ALLAH yabarmu tare, kuďin nadabbane agareni, luv u wujiga wujiga, lolí ½í±Œí ¼í¿».*_
~*Page.......12*~
..................Bayan tafiyarsu kowa yakama gabansa, deexerh da Raihan suka fita raka
mama wani guri, aunty ma takama gabanta, nikam saina tashi nashiga gyara 6angaren mama
wanda ayanzu nice nake gyarwa na hana masu aiki yi.
Bayan na kammala na koma 6angarena, wanka na sakeyi dan 12 ta wuce, yau banajin
kwalliya dan haka nashafa fauda kawai da abinda ya sauwak'a, bak'ar doguwar riga nasaka
nayi k'yau sosai saboda k'ibar dana ďan k'ara, ga fatata ta murje gwanin sha'awa.
Falo nadawo na kwanta saman doguwar kujera tareda lumshe idanunana ina tunanin
karatuna, inason na koma makaranta na k'arasa karatuna.
K'amshi yacikamin hancina, na buďe idanu ahankali, doctor nagani tsaye akaina yana min
murmushi.
Na mik'e da sauri ina faďin sannu dazuwa, ince dai lafiya??, ya ce, "saiba lafiya mai gida yake
dawowa gidansa?."
Na ce, "a'a, na kar6i ledar hannunsa dayake mik'omin, ya ce, "rakene nagani ahanya shine
nasiyo miki ban saniba kozaki sha?.
Murmushi nayi na ce, "ina sha mana".
Na ajiye ledan saman tebir nanufi kicin, ruwa nakawo masa yasha, ya ajiye kofin yana faďin
ngd sosai _gimbiya_, nikam duk kunya ta isheni dan haganin mayataccen kallon dayake bina
dashi.
Kamar daga sama mukaga an banko k'ofa, gaba ďaya muka maida kallonmu wajen, aunty
sadiya ce, ta ce, "lallai Isma'il dawowa kayi da wuri haka, lafiya kuwa??.
Ya daure ya ce, "lafiya lau aunty nazo ganin k'anwarkine.
Ta ta6e baki yo har yanzu batada lafiyar??.
Yaďan rage fara'a ta warke ina kwaďayin gani k'yak'yk'yawar fuskartane kawai.....nikam gaba
nayi zuwa kicin domin haďo mada abin motsa baki.
Batace komaiba tanemi guri ta zauna, ta jawo ledan raken gabanta mikuma aka kawo mana
ne??, baice mata komaiba dan al'amuranta sun fara bashi haushi, nashigo falon da sallama,
shikaďai ya amsa mini, naje gabansa na ajiye filet đin kayan marmari.
Ya ce, "ngd babyna".
Nayi ďan murmushi kawai sanan nakoma kujerar nesa dashi na zauna.
Ya kalleni taso kisha mana?, na ce, "a'a duk nakane......kafin yayi magana aunty ta ce, "nida
ba'amin tayiba bari nazo nasha, kan kujerar dayake zaune tadawo ta zauna kusadashi daf,
taďauki cokali tahausha.
Ya ce, "a'a aunty mu mun isa muk'i yimiki tayi yafaďa yana matsawa, dayake doguwar
kujerace.
Nikam nayi gum dan mamaki take bani idan tana wani 'yan kamancin, ya kalleni iman yadai?,
ďan murmushin k'arfin hali nayi na ce, "babu komai.
Itakam ko kallo ban ishetaba sai danna abinta take.
Ya mik'e bari naje na watsa ruwa dan duk nagaji, na ce, "afito lafiya.
Ya nufo inda nake ya kama hannuna yana faďin aikece zakimin wankan, baibi takan auntyba
muka nufi ďakin yana faďin aunty muna zuwa.
Wata uwar harara tarakomu da ita wadda nikaďai nagani, taja tsaki tatashi tafita, azuciyata na
ce, " *kishin banza*.
Miss xoxo ta ce, " *kishin banza kam* tunda ba miji kuka haďaba, wai dama ana samun irin
haka??.
Reefat ta ce, "sosaima, wannan shi ake kira kishin sauri, wlhy wasu irin wanan kishin yakesa
suraba zumincin family ďin mazansu, akwai mata dayawa dake kishin banza kamar haka, kiga
matar k'ani ta tsani matar wa, matarwa tana kishi da matar k'ani, tamkar mijinsu ďaya.
Miss xoxo da iman sukace to ALLAH ya shiryamu
*(ni bilyn Abdul na ce, "wanan asarar lokacine, yakamata mata kugane badan kishi aka
haliccemuba bare ki 6ata lokacinki awajen kishin, garama ki nutsu kisan inda yake miki k'aik'ayi
ki sosa, baki k'are akan kishin banza mara amfaniba, ALLAH yaganar damu)*
Reefat tamik'e taje tayo fitsari tadawo, drinks ta ďakko musu tazubo cincin afilet ta ajiye
musu dan labarin sai anayi ana jik'a makoshi.
_(nima bilyn Abdul ina gefe danawa na katsire ina korawa dan inji daďin kwaso muku rahoto
*lol*)_
Miss xoxo ta ce, "sis....jamije mana."
Iman ta haďiye lemon dake bakinta, taci gaba.
Bayan mun shiga ďaki ya zaunar dani bakin gado shima ya zauna kusadani, naďan takure
jikina dan bako yaushe nakeso yata6aniba.
Hannuna yakamo ya damk'e anasa yamatso kusadani sosai, yana faďin abinda bak'ya son,
dan tuni nakula bakison na ra6u jikinki bansan miyasaba?.
Na duk'ar dakai k'asa, ya ce, "faďamin kobaki sonane??, na girgiza kai alamar a'a, ya ce, "to
minene dalili?.
Ahankali nađago kai ina kallonsa, ganin ya tsura min idonsa yasa nayi saurin maida kaina
k'asa, na ce, "dama umma ta ce, "mana karmu yarda namiji yarik'e hannunmu, inkuwa ba
hakaba zamu samu ciki.
Bai san sanda ya tuntsure da dariyaba harda kwanciya akan gado, nikam nasaki baki ina
kallonsa, dan ba k'aramin k'yau dariyar taimasaba, inason sa sosai, harma bansan yanda zan
musalta ba.
Jinayi an huremin idanu, naja wata ajiyar zuciya mai k'arfi, yay murmushinsa mai k'ayatarwa,
sannan yagyara zamansa ya ce, "saudat!....yakira sunan dawata irin murya mai cike da kasala.
Na ce, "na'am".
Ya ce, "aii gwaggo tafaďa miki hakane danki kare mutuncinki ga wanda ba mijinkiba, nikuma
mijinkine yafaďa tareda nuna kansa, aii ni yanzu ko rik'e hannun naki nayi kika samu ciki babu
matsala, su gwaggoma murna zasuyi da samun jika.
K'asa nak'arayi dakai, shikuma yarungumoni sosai zuwa kikinsa yana faďin inasonki dayawa
iman, ya ďago ya mannamin summba akumatu mai shiga jiki da 6argo.
Nikam sai k'ara sinne kaina nake ajikinsa ina k'ara shak'ar daddaďan k'amshin turarensa.
Jin anturo k'ofa ko sallama babu yasa yaďago kai da sauri yana kallonta, nima namik'e zaune
sosai inaďan janye jikina daga nasa.
Lafiya kuwa?, doctor yafaďa yana kallonta.
Ta juya idanunta dasuke manya sosai nazo kiran iman ne mu ďora abinci.
Ya ce, "to tana zuwa, ta kalleshi yanda yawaniyi kicin2n da rai, tasan halinsa sarai idan
ransa ya6aci dan haka tayi waje tana kun kuni.
Na kallesa ya haďe rai sosai kamar bashine yagama dariyaba yanzu, tsaki yayi sanan
yamik'e yana faďin kwanannan zanyi maganin 'yar isakar matannan wlhy, nidai bance komaiba,
yashige bayi.
Nimadai abin mamaki yake bani dukda k'arancin shekaruna, kuma gidanmu bantaso naga
kishiyaba, bare nasan yanda ake kishi, saidai nakanji ana faďar kishi kishi.
To amma su waďancan ai mijinsu ďaya, nikuma ba mijinmu ďayaba, to kenan wanan kishin
banzane takeyi??.
Maganar mama naji tana faďin ina iman ďin takene?, namik'e da sauri na nufo falon ina faďin
mama ganinan kundawo??.
Ta ce, "eh nadawo su nabarasu acan.
Na ce, "sannu dazuwa."
Ta ce, "yauwa sannunki kema"
Makullin 6angarenta naďauka muka tafi, nabuďe muka shiga, ruwa maisanyi naďako
nabata tasha, ta ce, "ALLAH yayimiki albarka.
Na ce, "amin mama".
Doctor yafito daga bayi yaga bana nan, sai zuciyarsa tak'ara tunzura, wato yarinyarnan tafiya
tayi wajen girkin tabarni saboda kiranta yafini ko??, yaja dogon tsaki yafice, ďakinsa yanufa
yashiga wanka, yafito yay shirinsa cikin k'ananun kaya, yayi k'yau sosai.
Yadawo falon yazauna, yana kallo yana shan raken daya siyo.
Yaji shirun yayi yawa dan haka yamik'e yanufi 6angaren mama yagani idan tadawo.
Da sallama yashigo ganin inama mama matsar k'afa sai yayi turus.
Mama ta kallesa a'a auta kadawo?, ince dai lafiya?.
Ya ce, "lafiya lau mama nadai dawone kawai, zaman kasuwarnan saisu yaya surutun yayi
yawa, har kaina yafara juyawa shiyyasa nagudo.
Yazauna yana hararata.
Mama ta ce, "mitayi maka kake harararta ne?.
Da sauri ya ce, "babu komai mama, yana magana yana sosa gefen wuyansa.
Nayi k'asa dakai ina murmushi danya bani dariya