Showing 45001 words to 48000 words out of 79986 words

Chapter 16 - Ban Saketa Ba Compelet Billyn Abdull

01 Aug 2026

803


bak'yaso wlhy.
Shiru iman tayi.
Saida yakalli musayeef sanan yadawo da kallonsa gunta.
Ya janye hannun rigarta yana kallon k'unshin cike da sha'awa, sumbatar hannun yayi, iman
tayi saurin janye hannunta tana k'ara d'aure fuska.
Murmushi yayi, kai my life mai k'unshinanfa ta iya wlhy, kinganki kuwa, inga k'afar?, yafad'a
yana duk'awa zai lek'a k'afarta.
Da Sauri tajanye k'afarta ta tura k'ark'ashin kujera.
Yad'ago yana kallonta, Indai bazaki bani naganiba tofa zamu kwana a motarnan.
Baki ta murgud'a MASA.
Bata ankaraba taji bakinsa akan NATA.
Fisge2 tafarayi amma takasa kwatar kanta, tsotsar le6enta yake da harshenta tamkar zai
ciresu, duk iya k'ok'arinta nata kwace takasa, Dan haka tahak'ura saida yayi mai isarsa sanan
yasaketa yana sauke numfashi.
Itakuma tafara hawaye.
Ya ce, "nunamin konayi abinda yafi haka wlhy...... Kafin yak'arasa ta d'ago k'afarta.
Murmushi yayi yajanye rigar yana kallo, yayinda ita kuma tarintse idanu tana hawaye.
Shikam sai shafa k'afarta yakeyi, daga bayama saiya d'auki wayarsa yad'au k'afar ta da
hannunta photo, tanajinsa tai masa banza.
Xoxo kam tanacan sunshiga gidan makwafciyarsu Zara kar6o abu awajenta.
Saida yagaji dankansa sanan ya ajiye kafar, fuskantarta yayi sosai.

My life magana nakeso muyi.
Bana buk'ata tafad'a idonta arufe.
Saboda mi bak'ya buk'ata muyi?.
Haka kawai.
A'a akwai dalili dai.
Banida wani dalili nikam.
Aii duk abinda kikaga d'an Adam yayi akwai dalili.
Toni banidashi, tafad'a cike da k'osawa.
Tom shikenan tunda bak'yaso ambar maganar, yanzu yaushene tafiyar taku?.
" jibi Idan ALLAH yakaimu".
Hummm dabamu had'ubama saidai naji alabari ko?.
Bud'e ido tayi tana kallonsa batareda tace uffanba, ita aganinita mizaisa tasanar dashi......
Yakatse mata tunani dafad'in koba hakaba.
Tad'an yatsine fuska, ai baizama dole saika saniba danbamuda wata alak'a.
'Yar dariya yayi tareda fad'in "ko?."
Kanta tsaye ta gyad'a MASA kai.
Yad'an cije le6ensa, Ashe kuwa zan hana tafiyarnan wlhy.
Da Sauri ta ware ido tana kallonsa.
Ya ta6e baki, ya ce, kallonfa?.
Kauda idonta tayi tace mizan kalla anan.
K'yau mana yafad'a cike da murmushi.
Ta ce, "Ashe";.
Asheme?.
Shiru tayi babu amsa.
Zanbarkine kawai kije Dan ALLAH amma badan halinkiba, kuma kema idan kin dawo kifara
shirin komawa naki gidan.
Wata 'yar dariya tayi mai Nuna alamun ka ta6u, tamurd'a k'ofar zata fita.
Yasake damk'e hannunta, INA zuwa kuma?.
Batareda tajuyoba ta ce, " Dan ALLA kabarni inada abubuwa masu muhimmanci agabana.
Nima aii hakantake.
Batace komaiba.

Nifa zan wuce tafad'a kanta yana kallon waje, Nima aii ba kwana zanyiba anan, kaika sani
tafad'a azuciyarta.
Ya ce, ''gobe idan ALLAH yakaimu zan shigo, kuma Nima inada zuwa d'aurin aure Adamawa
nida Nabeel jibi. Dan haka kubari mutafi tare.
Nikam bazan hau mortar kowaba.
Humm karki hau mana, nidai nagama magana, ki had'oma musayeef wasu kayan Dan dashi
zanje.
Bata tankaba tabud'e tafice, daidainan xoxo tafito.
Shima Dr Isma'il yafito, hannunsa rik'e da ledoji guda biyu babba da k'arama.
Xoxo yabama k'aramar sanan yamik'ama iman babbar.
Kallo d'aya tayi musu shida ledar ta kauda kai, nifa bana buk'ata, baki ya ta6e tareda ajiyewa

kusada k'afarta, idan kingadama ki yarda yafad'a yana nufar mota.
Xoxo tak'ara masa godiya, harya tada motar ya ce, "af na manta hafsat!.
Xoxo ta ce, " na'am tareda zuwa jikin mortar talek'a kanta.
Jibi dayaushe zaku tafi?.
Tunda sassafe.
Okey kujirani, dannima zanje Adamawa d'aurin Auren wani d'an uwan Nabeel, saimu tafi tare.
To shikenen mungode sosai fa, ALLAH yak'ara lfy.
Ameen saikunjini.

Bayan tafiyarsa Xoxo takali iman datayi gaba tabar ledar a Inda Dr Isma'il ya ajiye.
Dauka kawai tayi suka Shiga gidansu Xoxo..

Afalo suka iske umman su Xoxo, fuskarta cike da fara'a ta ce, "kun dawo?.
Eh wlhy Umma munyi sauri ko?.
A gsky kunyi Sauri.
Kunshin suka Shiga Nuna mata, itakuma tana yabawa.
Ta ce, " kunsamu adaidaita dawuri kenan d'azu?.
Inafa Umma, wlhy sai daddyn Musayeef ne yakaimu, muna tsaye munata jira harmun fara
gajiya saigashi shida musayeef zasuje aski, aiko shiya kaimu Yakoma ya d'akkomu.
ALLAH sarki bawan ALLAH, ALLAH yasaka MASA da alkairi, amindai Umma, kingama
abinda ya saya mana.
Xoxo tamik'ama Umma ledanta, Umma tabud'e ledan saiga doguwar Riga mai d'anbanzan
k'yau, da takalma, harda turare guda biyu, da kayan kwalliya.
Kai amma kin code wlhy, wanan bawa akwai kirki, ALLAH dai yagyara wanan lamari iman ki
koma d'akinki ki rungumi d'anki kema.
Ameen Xoxo tafad'a tana dariya, iman kuma tayi k'asa da kai tanajin kunyar zancen Umma,
amma dukda haka saida ta ce, "ameen azuciyarta, Dan itama tana fatan faruwan hakan, tana
bala'in son Dr Isma'il sosai.
Xoxo tamik'ama Umma ledan iman, kinga NATA itama wai bataso.
Umma ta ce, " kai habadai, itama fad'a take kawai, Umma ta ce, "jeki ajiye mata zata bud'a
anjima, murya kasa2 ta ce, " Umma kibud'a kigani mana.
Dariya Xoxo takwashe dashi, kai iman akwai gulmar tsiya, anason daddyn musayeef ana
kaiwa kasuwa, keda kikace bak'yaso.
Hararata IMAN tayi, ita kuma Umma tabud'e ledar.
Itama dogayen rigunane guda uku masu azabar k'yau, sai hijjabai Biyar manya, sai takalma
biyu da kayan kwalliya.
Umma ta ce, "ALLAH yasaka da alkairi, kukai d'aki Ku ajiye ga break d'inku can.
To Umma Xoxo tafad'a tana mik'ewa.

Anan gidan iman tawuni, Dan saida sukaje suka wanke kai sanan ta tafi gida da ledar kayanta,
dakuma wasu turarurruka masu k'amshi da umman Xoxo tabata, *(so kunsandai kanuri sun
had'u a wajen turare😉, Xoxo kuma kanuri ce�)*

Shikam Doctor daga nan gida ya wuce dasu, yana faka motarsa a harabar gidansu ya d'auki
musayeef dake barci akan kafad'a.
Da sallama yashiga 6angarensa, aunty da Raihan dake kuskus suka d'ago da Sauri suna
kallonsa.
Baice komaiba yak'arasa cikin falon, aunty tamik'e tana MASA sannu da zuwa, Raihan kuma
tazo zata kar6i musayeef amma saiyace tabarsa.
Baijira amsartaba yawuce d'akinsa, Wanda yanda yabarsa da datti haka yazo ya sameshi.
Dan tsaki yayi, ya kwantar da musayeef saman kujera sanan yazo yafita.
Yanzu raihan CE kawai afalon aunty ta tafi, baice mata komaiba yasake fita
Babu dad'ewa saigashi tareda deexerh, suka wuce Raihan zaune tana kallo.
Dakinsa yakira deexerh ta gyara Masa Dan haka yak'ara fita danufin d'akko kaya amota.
Da Sauri Raihan tasha gabansa, yaa Isma'il wai Dan ALLAH miye haka?
Wani kallo ya watsa mata ya ce, " a ina kenan?.
Dukda atsorace take tadaure ta ce, "kashigo muna maka sannu Baka amsaba, sanan Nazo
kar6ar musayeef ka hana, yanzu kuma naga kaje ka kira khadija mizata maka?.
K'ara had'e fuska yayi, ya ce, " zata gyaramin d'akine ko akwai wata Matsala?.
"A'a."
Tafad'a a sanyaye.
Ra6awa yayi ta gefenta yafice, babu dad'ewa yadawo d'auke da Leda, yanzu Raihan tabar
falon tashiga d'akinta, tana Shiga waya ta d'auka takira aunty, aunty ki kwantar da hankalinki ba
maganar damukayi yajiba Ashe, abin nasane ya motsa. Ajiyar zuciya aunty ta sauke ta ce, "kai
harnaji dad'i wlhy, da nakasa zaune nakasa tsaye sai zagaye d'aki nake. To hankalinki ya
kwanta yanzu Raihan tafad'a tana dariya.

Babu dad'ewa deexerh tagama gyara d'akin, tamaida musayeef kan gado, tasaka MASA turare
d'akin yad'au kamshi sanan tafito tasamesa afalo kwance, uncle nagama.
Tashi yayi zaune yauwa deexerh sannu da k'ok'ari, bari naje na watsa ruwa, nazo mu gaisa
da mama.
To saikazo tafad'a tana fita.
Tashi yayi yashiga yay wanka yafito tsaf abinsa sai 6angaren mama.

Iman tana zaune ad'aki kayan da Dr yasiya mata take dubawa, kayan sun mata k'yau sosai Dan
haka ta shiryasu cikin kayan zuwa adamawa, kad'an2 saitayi murmushi ta shafa le6enta, idan
tatuna summbar da Dr yay mata saitaji wani farinciki na ratsata, dahakadai barci ya saceta.


*9:39pm*
Dr Isma'il zaune abakin gado, yajingina Kansa da fuskar gado, k'afarsa d'aya ak'asa d'aya
lankwashe akan gado, musayeef yatada kai da ta lankwashen yana barci, hannunsa d'aya yana
shafa kan musayeef d'ayan kuwa yana rik'e da waya yana dannawa, sai faman murmushi
yakeyi Dan k'unshin iman yake kallo, harda fuskarta wadda batasan ya d'aukaba. Raihan dake tsaye abakin k'ofa tana kallonsa ta ta6e baki. Cikin d'akin ta k'arasa sosai, taje
kusadashi tazauna, d'agowa yayi yana kallonta sanye take cikin rigar barci fara tas, wadda ta

tsaya iya cinyarta, ta d'ora 'yar saman data kai mata had k'asa, tasaki igiyoyin rigar batareda ta
d'aureba wanan yasa ake kallon k'irjinta daya cika rigar FAM danba bra.
Kauda Kansa yayi daga kallonta yace lfy?.
d'an farin tayi ta ce, "saibabu lafiya ake Shiga turakar miji?.
Baice mata komaba yafara gyarama musayeef kwanciya sosai, ta kwanto da kanta ajikinsa
muryarta anarke ta ce, " haba my one wai haka ake aure?.
Cike da mamaki yake kallonta, ya ce, "to ya akeyi?.
Tayi far da idanunta aii kaima kasani, ta turo Baki gaba, jiya na hak'ura na kwana nikad'ai
yaukam bazan iyaba gsky.
Shidai kallonta kawai yakeyi, yadaure ya ce, " to ya kikeso ayi?.
Murmushi tayi tana shafa k'irjinsa Dan rigar baccinsa mai bud'ad'd'en k'irjice, yauwa my one
sonake mukwana tare.
Ajiyar zuciya ya sauke tareda janye hannunta daga k'irjinsa Dan abinda take MASA yafara
tasiri akansa.
Gyara kwanciyarta tayi sosai ajikinsa, tana k'ara Zame rigarta ta sama komai NATA na
bayyana, kauda idonsa yayi daya fara canja launi zuwa jaa.
Ganin haka yasa Raihan tadawo da fuskarsa Inda take, ta marairaice fuska Baka yarda
mukwana tareba ko?.
Yanda tayi maganar saita bashi tausayi kumashi ba dutse bane yana buk'atar abokiyar
hallittarsa, yana daurewane kawai, amma ganin shigar dake jikin Raihan dukta sauya MASA
tunani, ga wani fitinannen turare data shafa, Wanda dukya motsa MASA sha'awa.
Kallon fuskarta yayi harta fara hawayen kissa, hannu yasa yana share mata hawayen,
akasalance ya ce, "naji ZAMU kwana tare bar kuka.
Ta turo Baki gaba tana yunk'urin tashi, a'a nikam banaso, aii hak'k'inane akanka, idanka
tauyeni ALLAH bazai barkaba tamik'e zata fice.
Da sauri yarik'e hannunta Yakuma dawo da ita jikinsa, shikenan naji yihak'uri to.
Yanda yake shafa kan ta saitayi luf ajikinsa, ahankali takai hannu itama tana shafa k'irjinsa,
ajiyar zuciya ya sauke yalumshe idanunsa tareda jingina kansa da gado.
Daga haka ta fara yimasa abubuwa na d'aukar hankali, Wanda duk aunty CE ta koya matasu,
Dan acewar aunty saita maida kanta Mara kunya sanan zata samu Dr ahannu, aiiko taga
shawarar aunty tayi tasiri sosai, Dan gashi cikin sauk'i ta d'akko hangar samunsa.
Baisan sanda yafara maida mata murtaniba, saida sukayi nisa sosai sanan yad'an janye
jikinsa da k'yar yana kallon musayeef daketa barci abinsa, itama Inda yake kallo ta kalla,
muryarta can k'asa ta ce, "lfy?.
Muryarsa a sark'e ya ce, tashi muje d'ankinki kinga nan akwai musayeef.
Ta ce, " shida yake barcinsa.
Kai ya girgiza mata yana fad'in bazai yuwuba idan ya farkafa?.
Tad'an ta6e Baki to idan muka tafi cand'in yafarka yay kukafa?.
Mik'ewa yayi yana lilli6e musayeef karki damu aii nan zandawo na kwana.
Banza tayi masa, aranta ta ce, "Idan na barkaba, tanayi yana Hararar musayeef dabaisan
tanayiba.
Bayan ya lullu6esa Yakama hannunta suka fita zuwa d'akinta.............

😡 *_"nidai masu karatu bazan bisuba kuyi hak'uri INA taya iman kishi"_*🙄







*luv u oll my fan's*
*(((S))).........2017*
[8/6, 6:02 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!._*






*_NA Bilyn Abdul_*



_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*


https://mrsbilkisa.blongspot.com



*miya kamata nayi?.*
_karka zama mashayi._
_Shaye shaye na 6ata rayuwar maiyinsa, ga d'unmin Zunibi awajen ALLAH Yana hana sallah
akan lokaci, baya barinka kayi k'yak'yk'yawan tunani arayuwarka bare harka banbance fari da
bak'i, bazai barka ka karanta alkur'ani mai girmaba balle harkasan yi da hani, bazai bari ka
girmama nagaba da kaiba Dan kana ganin kowa daidai tsawonka, zaka iya ganin akuya atiti
katsugunna ka gaisheta, zaka iya kashe mutum domin Baka tareda tunaninka, zaka zaka zaka
zaka dayawa 'yan uwa._
_Dan ALLAH kubari shaye shaye ba wayewa baceba, abin damuwar yanzu harda mata,
haba 'yar uwa keda kike amsa sunan uwa miya kaiki Aikata wanan aiki._
_Wanan duk yana d'aya daga cikin aikin shaid'an shugaban hassada ga aikin alkairi, kullum
burinsa yaganka a wutar jahannama._
*ya ALLAH ka kiyashemu shigarta*
*ALLAH yasa Mugane*

*(Page 26)*
Humm lallai yau su Dr Isma'il ansha amarci shida amaryarsa Raihan, saidaifa tabbas ya
yarda mata suna suka Tara.
Yana kwance akan gadon Raihan idanunsa alumshe tamkar Yana barci, Raihan dake tsaye
Kansa ta dasa masa idanu, daga wanka tafito Dan d'aure take da guntun tawul iya cinya, wani
irin farincikine yake ratsata wai yau itace ta kwana gadon d'aya da yaa Isma'il, lallai tayarda
soyayyama iya wace, yaa Isma'il dabbane afagen iya soyayya. Ahankali yabud'e idanunsa akanta, kallo d'aya yaymata ya kauda kai, imance tafad'o masa
arai, yatuna ranar Daren farkonsu ko ido bata iya d'agawa ta kalleshi bare tamasa kallon tsaf,
haryay rayuwarsa suka rabu da iman baita6a ganin tazo ta tsaya gabansa da guntun tawul ba,
ko wanka tashiga, yashigo d'akinta Indai har tasan Yana ciki to bazata fitoba kuwa, amma jibi
ita wanan tawanizo ta tsaya masa getsetse agaba tamkar wata matar k'auye, koma irin 'yar
kunyarnan babu........ Jiyay tana shafa bayansa, siririn tsaki Yaja sanan yajuyo.
Haba my one katashi mana kallifa lokaci kagani, kar aita jurammu awajen break.
Tashi yay zaune batareda tayi maganaba, ya ziro k'afafunsa k'asa ya sakko, hanyar fita
yanufa, ta ce, ''my one!.
Bai juyoba amma ya tsaya.
Ince anan zakayi wankan?.
Kai ya girgiza mata, sanan yace zanje nayima musayeef wanka, baijira amsartaba yafice.
Itama da harara tarakashi, d'an rainin hankali, da daddare kagama yima mutane sambatu
yanzu kuma kazo kana mazurai Mtsoowwww taja wani wawan tsaki.

Shikam Yana shiga d'akinsa yaga babu musayeef da sauri yanufi bathroom nanma bata nan,
ya ilahi INA yaronnan yanufa be?.
Da sauri yasaka jallabiya yafito, 6angaran mama yanufa, saiya Tarar da musayeef suna
game awaya shida Marwan, harna anyi masa wanka tsaf.
Ajiyar zuciya ya sauke adaidainan deexerh tafito daga d'aki, ta ce, ''lah uncle lfy?.
Musayeef yanuna mata, waya kawoshi nan?.
Sai asanan Marwan da musayeef sukasan yashigo, musayeef yazo yarungume daddynsa.
Deexerh ta ce, "ni na d'akkoshi jiya da daddare, naje na sanar dakai zan koma makaranta yau,
Dan ana nemanmu da gaggawa saina Tarar musayeef yanata kuka ad'aki shi kad'ai.
Nazata kana bathroom amma nakai awa d'aya ina jiranka shiru, babuma alamar motsin ruwa
shine na d'akkoshi kawai muka taho nan.
Ayya sorry my Darling, yafad'a Yana shafar fuskar musayeef.
Deexerh kam da marwan kallon juna sukayi, deexerh ta harari Dr amma bai ganiba, fita yayi
da musayeef ahannu.
Marwan ya ce, "kinjifa aii bai bada amsaba saboda bashida gsky.
Humm kabari kawai, aii dama dannaji zaice Yana inane?, tunda nagabaci 6angarensufa
nakejin kukan musayeef amma babu Wanda yanemeshi acikinsu, sai yanzu zaiwani zoma
mutane arikice, nasandai Yana d'akin Raihan.

Mtsowwww!! Wlhy Uncle yafara bani haushi.......... Mama takatse musu zancen, kai kunci
k'aniyarku, shida matarsa bazaije d'akintaba.
Gaba deexerh tayi tana k'unk'unai, marwan kuma yace mama aiiba hanashi mukayiba.

Sai bayan kamar Minti talatin suka fito cikin kwalliya, lokacin kowa ya hallara a dani, suma
kad'ai ake jira, bayan gaishe gaishe suka zauna aka farayin breakfast, Raihan sai wani yatsine2
takeyi, Dr yana kallonta ya watsar da banza.

Bayan sun gama break deexerh ta ce, " uncle nifa yau zan koma makaranta.
Tofa wanan tafiya babu shiri, humm toyazamuyi karatun kenan aii.
Shikenan babu damuwa, ALLAH yakaimu, Nima gobe zanje Adamawa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0