Showing 66001 words to 69000 words out of 79986 words
nifa bana son
wankan.
Dr yarik'eshi yana murmushi, haba big boy rashin wankafa k'azantane, ko kanaso aringa
cemaka k'azami.
A'a daddy.
Yauwa to jeka amaka wankan.
Nidai daddy saina fara cin abinci za'amin wankan.
Dr yad'ago yana kallon imam, aunty maa Dan ALLAH amana hak'uri muci abincin munajin
yuwafa sosai.
Itama fuska ta marairaice Dan ALLAH karka biye masa, kallifa kayan jikinsa, ni bammasan
inda yaje yay wannan dattinba.
d'aukar musayeef yayi yana fad'in mudai mun tafi saikin taho.
Rakasu da ido iman kawai tayi, yazatayi da uba da d'an.
Wanka itama tashiga, bayan tafito ganin lokacin sallar la'asar yayi tayo alwala, kayanta da Dr
yad'ebo daga d'akinta yasaka a durowarsa taduba tad'akko zani da hijjab.
Tana cikin yin sallah, tayi raka'a ta farko tana ta biyu Dr yashigo d'akin tamkar anjehoshi,
tsayawa yayi cak yana kallonta tamkar yau ya fara ganinta.
Ya ce, "hummm dama manya suna k'arya?.
Iman dai sallarta takeyi, saima yanzu ta tuna da shirinta, saurin kauda tunanin tayi tacigaba
da sallah anutse.
Dr yafito daga bayi da Alama alwala ya d'auro, ya fice yana wata 'Yar dariya wadda iman
batasan fassarartaba.
Koda ta idar da sallar duk jikinta yayi sanyi, tamanta wlhy har tayi saken da Dr yakamata,
tagama shafa mai tayi 'Yar kwalliya, sanan tanufi 6angaren mama Dan taci abinci.
Musayeef yana ganinta yagudu cinyar mama, iman ta ce, " haba yaro zan kamakane aii.
Mama da deexerh sukayi dariya, mama ta ce, "mi mai gidana yayine?.
Mama wankafa zanma yaron nan shine yabiyo daddynsa suka fito wai yunwa yakeji,
maimakon yaci abincin yadawo namasa wankan shine Yakama wata tashar.
Mama ta shafa kan musayeef asheni mijin nawa k'azamine ban saniba.
Deexerh ta ce, " a'a mama yanzu zamu cakire abinmu, musayeef zomuje ni nayimaka kaji.
Babu musu yabi deexerh.
•+•+•+•+•+•+•+•
Iman zaune abakin gado tanama musayeef shirin barci, Dr yafito daga bayi da'alama wanka
yayi.
Musayeef ya ce, "daddy zaka koyamin game d'in d'azu?.
Dr ya d'aga masa kai, zan koya maka amma ba yauba yaro.
Um'um musayeef yafad'a a shagwa6e, nidai daddy yanzun.
Lallai yaro ka d'obo da zafi, yau baranar koyon game bace ba, Dan inada babban game
adaren yau.
Iman ta kalleshi cike da rashin fahimta, shima ita yake Kalo, yad'aga mata gira, ta kauda kai
tana girgizawa.
Musayeef dake danna wayar daddynsa shi adole game yake nema, yatako inda Dr yake
yabashi wayar, daddy gashi kamomin.
Kaga jeka bama mamanka ta kamomaka nikam mai nake shafawa.
Musayeef yajuya wajen Iman shikuma Dr yacigaba da shirinsa.
Tana kamomasa game ya haye gadon yanayin abinsa.
Dr ya kalli Iman my life bazakiyi shirin barci bane?.
A'a ba yanzuba.
Sai yaushe?.
Sai anjima yanzu banajin barci.
Yawani kafeta da idanu, saikuma yayi murmushi aidama yau ba ranar barcinki bane, kedai
tashi kiyi wanka kawai, danma saboda oga na k'yaleki datuni kin tsinci kanki cikin ruwan wanka.
Murmushi Iman tayi, tajuya tana kallon musayeef dayayi busy akan waya, ta ce, ni
barinmuku d'akinma zanyi.
Baice komaiba yamik'e yay shiri cikin kayan barci.
Tana zaune yafice saigashi da fresh milk akofi, itadai kallonsa kawai takeyi.
Yazauna Kusada musayeef, my dear son tashi kasha madara.
Musayeef yathi zaune ya haye cinyar daddynsa.
Da Kansa yabashi madarar, yana gama sha yazame yay barci.
Cikin mamaki Iman take kallon Dr, yad'aga mata gira yana gyarama musayeef kwanciya.
Doctor wai mikabama yaron nan?.
Bai bata amsaba saida ya lilli6e musayeef da bargo, sanan yanufota, cak yad'auketa yanufi
bayi, tafara zille2.
Bata ankaraba tajita acikin ruwa.
Wani d'an kukan ta6ara tasakar masa, yay dariya Saita burgeshi, dakansa yay mata wanka
tanata rufe ido har aka gama, yanad'o kayarsa atawul.
Ta ce, "pls kasaukeni Dr yaron nanfa zai iya farkawa.
Hhhhh kwantar da hankalinki, Indai musayeef ne saikuma gobe idan ALLAH ya kaimu.
Cike da alamar tambaya ta kalleshi.
Yayi murmushi, dainamin tuhuma da ido, maganin barci nabasa kawai.
Ido Iman tazaro saboda mi?.
Saboda yau babu sauk'i, daddynsa da momynsa zasu angwance.
Kafin ta ce, " wani Abu ya had'e bakinsu waje d'aya.
Cikeda salo yake mata abubuwa, lallai tayarda mijinta yayi missing nata, komai a yunwace
yake matashi, dukda tana cike da tsoro haka tadake ta hak'ura.
Yayinda akafara nisa sainajawo 'yammatan k'afafuna nayo wajeí ½íº¶í ¼í¿»â€�.
************************
Bari mu waywayi su Raihan.
Tunda suka bar gidan basu nufi tashaba, gidan wata k'awar aunty sukaje.
Cike da mamaki take kallonsu, tofa Sadiya yana ganku rik'im2 dakaya?, incedai lfy?.
Inafa lfy Zubaida, kedai muje daga ciki.
Afalon zubaida suka zube, takawo musu abinci sukaci, dama yunwa sukeji.
Bayan sunci sunsha suka mik'e k'afa suna bama zubaida labarin komai.
Zubaida tarik'e Baki lallaima sadiya ya akayi kukayi sakaki haka, yo ALLAH na tuba
bakuyima 'yan iska mai kankat.
Aunty ta CE, "kamar ya mai kankat?.
Wata dariyar mugaye zubaida tasaki, tagyara zama tashiga fanfasu sosai.
Zancen natadai bai yuce zuwa wajen malam da boka ba.
Sunkuma hau sun zauna daram, gobe asubar fari awani k'auye zata musu.
(Ni bilyn Abdul na ce " ajuridai zuwa rafi).
Wacece zubaida ne?.
Zubaida dai 'Yar sokoto CE, kuma k'awar aunty CE tun a sokoto, adaliln aunty ma tayi aure
kano, Dan awajen bikin anuty tayi gamo da mijin dasuke tare yanzu.
Ko kad'an bayajin dad'in zama da ita, Dan zubaida halinsu d'aya da aunty jirgi d'ayane
yad'ebosu.
Saboda bala'inta yaraba musu gida itada matarsa uwargidansa kenan.
Itadai ta haihu Dan yaranta biyu duk mata.
To yanzudai gashi tayima su Aunty hanyar malamai to kozasu dace, saimun bisu asannu
sanan zamu tabbatar.......
*luv u oll my fan's*
*(((S)))............2017*
[8/6, 6:03 PM] mrs bilkisu: *_BAN SAKETA BA!!_*
*_NA Bilyn Abdul_*
_sadaukarwa_ *ya Abdul (city phone's)*
https://mrsbilkisa.blogspot.com
*_wanan page nakune Basma er Lele & Zarah bukar, ALLAH yak'ara basira da hikima, bilyn
Abdul namuku fatan alkairi arayuwa_*
*```(Zuma saidai wuta)*```
Acigaba da gashi zarahí ¾í´ .
*(page 39 & 40)*
Asubar fari zakara yabama su aunty sa'a.
Ba k'aramar tafiya sukayiba har dawaki, adawakinma wani k'auye suka shiga cikin ruk'uk'in
daji.
Aunty tatsaya tana maida numfashi saboda gajiya, Dan yanzu dak'afa suke da6awa saboda
hanyar batada k'yau, babu kuma d'an mashind'in dazai yarda yashiga dajin, itama zuby bazata
yardaba.
Kai Zuby wai har yau bamuzoba ne?.
'Yar dariya zuby tayi, tareda dafa kafad'ar aunty, haba sadiya biyan buk'ata aii yafi dogon buri,
ki daure aii munkusa, duk Wanda ya iya jure zama da mak'iyi, aii zaijure zuwan ranar d'aukar
fansa kuwa.
Hakane aunty tafad'a tana murmushin mugunta.
Tafiya suka cigaba dayi, itadai Raihan binsu kawai takeyi cikeda fargaba da fad'uwar gaban.
Zuby ta ce, "banga laifinkuba dominku 'yan hutune, mazanku sun tsaya muku daga mota sai
gida, muko ALLAH natuba yaku bayi wake ta tamu, idan tafiya zata tashi daga nan har birnin
lantsandan zamu iya kai kammu da k'afa.
Kafin aunty ta ce, " wani abu sun iso wajen wani k'aton dutsi, zuby ta kallesu nanfa zamu hau.
Raihan ta gwalalo ido cike da mamaki tana kallon zuby, aunty zuby yanzu nan mutum ke
zaune akan dutennan?.
Kwaraikuwa zuby tafad'a.
Aunty dai batace komaiba, saidai tana mamakin zuby sosai, tasan ta sanadinta zuby tasan
kano, hartai aure aciki, amma yanzu tafita sanin birnin kano da kewaye, Inda tasani ita ko
azance bata saniba.
Maganar Raihan ta katse tunanin aunty, aunty zuby to yanzu ta INA zamu hau?.
Wata matattakala zuby ta nuna musu, wadda babu shakka kayi kuskuren takawa tuni zakayo
k'asa ka rugurguje visa k'ananun duwatsin wajen.
Ajiyar zuciya suka sauke suduka, cike da fargaba suka fara tattaki ga matakalar, saida suka
kai k'arshe cike da jindad'i, abisa tsautsayi k'afar Raihan ta goce, takwala wata k'ara Dan
tsorata, jitayi anyi sama da ita akan dutsen, sassanyar ajiyar zuciya ta sauke yayinda taga ta
tsira, saidai tana bud'e ido tashiga wata sabuwar fargaban. Zaratan samari tagani majiya k'arfi, wad'anda da mutuwa na tsoron mutum idan tagansu
guduwa zatayi.
Aunty ma binsu take d'aya bayan d'aya, sunkai adadin goma k'artan, saikuma wani
wargajejen mutum fari tas azaune, Wanda bana tsammamin yasan kalma d'aya tak daga yaren
Hausa.
Aunty da Raihan suka kalli zuby wadda ita hankalinta akwance take babu alamar fargaba ko
tsoron atareda ita..... Mamakinsu bai k'aruba saida sukaga zuby tak'arasa wajen wargajejen
mutum nan mai kamada tankin ruwa ta gurfana tamkar zata MASA sujada.
Ya sarkina dodo yataya maka.
Daya daga cikin zaratan k'artan nan ya ce, "sarki ya amsa miki jinin dodo.
Aunty da Raihan suka zaro ido, tuni jikin su yafara rawa.
Zuby ta kuma gurfanawa agaban k'aton muminnan ta ce, " ya sarki ga alk'awari na cika kamar
yanda nayi, nakawo k'awata ga dodo harma da k'arin k'anwarta idan dodo yana buk'ata.
d'aya daga cikin k'artin Yakuma amsawa, dodo da sarki sun jinjina miki tareda babban yabo,
kin kuma tashi daga jinin dodo kin koma baiwar dodo, daga yau kema kinzama d'aya daga cikin
'Yar kungiya.
Hhhhhhhhhhhhhhhhhhh!!!!!!!. Wargajejen k'aton nan ya tuntsure da dariya, wadda duk kanin
dajin ke amsawa, dutsen dasuke kai kuwa har girgiza yakeyi.
(Na ce, hummm, dabadan dariyar da k'aton nan yayiba saika d'auka gunkine aka dasa awajen
wlhy.)
Aunty da Raihan tuni sun fara sakin fitsari awando, jikake tsulululu..., wani garjejen k'aton
yazo yadamk'i gashinsu, tuni jikin su yak'ara tsananta rawa, summa rasa hawayen kuka.
Sunaji suna gani aka aske musu gashi, akayi musu zindir, wanka akayi musu da ruwan jini
Dana magani, sanan akabama zuby su takai cikin wani k'aton tanki......
Aunty da Raihan suka fashe da kuka, bakin aunty na rawa ta ce, "Haba zuby yanzu nan
muzakiyima haka........ Hannu zuby tad'aga mata kinga dakata kunama mai haihuwar d'an sharri
yimin shiru.
Rama cuta ga macucu ibadane.
Zuby nikam azatona banta6a cutar dakeba.
Wani kallon banza zuby tabi aunty dashi, saikuma ta kwashe da dariya tana zagayasu,
sukuma suna binta da kallo, sady baby! Idan maye yaci yamanta uwar d'a bazata mantaba.
Tare muka tashi dake tun muna k'anana, amma ayayin dakika samu damar auren mai kud'i
saika manta dani atsarin rayuwarki.
Ban 6oye mikiba tunkan aurenki nace inason k'anin mijinki isma'il, kikayimin alk'awarin kota
yaya zakisa ya aureni amma daga baya sainaji shiru wai malam yaci shirwa.
Wani abun mamakima saiga labarin yazo gareni zai auri k'anwarki, haka nashiga nafita NASA
mamarku ta ce, bata yarda da auren isma'il da k'anwarki ba.
Bayanan ban gajiyaba nakuma tada miki zancen inason isma'il, amma saikikayi burus da
batuna.
Babu yanda zanyi dole na hak'ura na auri murtala badan INA sonsaba, na aureshi visa
tursasawar babana.
Kinsani sadiya kinsan halina kokad'an banida tsoron arayuwata, kuma bana Barin bashin
gaba.
Wanan yasa nafara tunanin INA zan samu kud'i Dan nawuce da ajinki.
Ina cikin wanan tunanin ranar na hau WhatsApp saiga wani group anturo ana gargad'ar kada
mutane sushiga na 'yan mafiyane.
Take kaina yakawo wuta Dan Dama kud'i nake burin yi toga hanyar mai sauk'i, tuni nake gaya
miki na afka group d'in nan zuciya ta adake, Ashe mutane da gsk sukeyi group d'in na 'yan
mafiyane, babu wani 6ata lokaci na afka cikinsu, saidai bazaka zama cikakken d'an cikinsuba
saika sadaukar da d'aya daga cikin masoyanka. Bazan iya bada Mamana ballantana baba, ko 'ya'yana, hakama murtala dukda banason da
bazan iya bada jinin saba saboda mutumin kirmine, ko kad'an bankawo araina zan kawokiba
kema, Dan burina saina zama mai k'azamin kud'i sanan na nuna miki wutsiyar rak'umi tayi nesa
da k'asa. Saidai kuma labarin ya canja alokacin da'akace idan bankawo wani nawaba za'abama dodo
jinina, tuni kaina yakawomin haske akanki, saidai bansan a INA zan damk'ekiba.
Kwatsam saigaku jiya kumzo gareni cikin sauk'i, Dan haka nayi matuk'ar farinciki, ayanzudai
taku tak'are Dan na cika umarnin dodo da sarki, kuma nazama cikakkiyar 'Yar kungiya, zanyi
kud'i na Shana.
Ta kuma kewayasu tana dariya, sady baby yau wai INA babban gidan da ake mana raini
akansa, INA motar hawan da ake hura mana hanci, INA mijin da ake mana salo, duk babu, saki
uku gakuma mutuwa dake jiranku.
Hhhhhhhhhhh, kin fad'a tarkona sady baby, kin fad'a tarkon zuby, Zuma ga zak'i ga harbi.
Kuka sosai aunty da Raihan sukeyi, suna rok'on zuby tayi hak'uri k'artan badasu, wlhy komai
take buk'ata zasuyi mata.
Bata sauraresuba ta iza k'eyarsu cikin kwantaina da mutane dayawa ke cikin, tsirara duk jikin
su wani iri babu k'yawun gani, su tsoroma suke basu, Dan haka suka raku6e waje d'aya suna
rabzar kuka.
(Nace duniya makaranta, Wanda baizobama jiransa takeyi).
Kowa yagina Ramin mugunta........
****************************
Iman da Dr kam ansha soyayya, daren nan zir a angwaci suka cinyeshi, iman ta murzu, Dan
Daren jiya Sabon Daren farko Yakoma musu.
Wanan karan dai babu kuka amma yasha shagwa6a da ta6arar iman, da k'yar suka tashi
sukayi sallar asubar, suka sake bud'e sabon babin barci.
Sai shabiyu dawani Abu suka tashi, alokacin tuni musayeef ya tashi yay tafiyarsa 6angaren
su yaya.
Imam ta tashi da k'yar, fuskar Dr ta tsurama idanu, barcinsa yake amma tamkar yana
murmushi, fuskarnan fayau sai hasken angwaci yakeyi, talumshe idanu tasake bud'ewa akansa,
tana k'aunar Dr harma batasan iya adadin k'aunar datake masaba, tana fata ALLAH ya sa babu
wata k'addara dazata sake raba rayuwarsu anan gaba. Ahankali tamik'e tanufi bayi danyin wanka, Dan jikinta sai ciwo yakeyi wlhy.
Ruwa mai zafi ta had'a ta gasa ko INA najikinta hartaji d'an k'arfi.
Tafito d'aure da tawul tana goge jikinta da k'arami, Dr dake kwance yatsura mata idanu jiyake
tamkar ya had'iyeta saboda so, tunda yake baita6a tunanin yaso wani Abu bayan iyayensa da
mama da ya'yaba bayan IMAN, yanajinta sosai azuciyarsa, fatansa ALLAH ya tsawaita
rayuwarsu suci amfanin juna. Iman dabatasan yanayiba ta k'arasa jikin madubi tayi kwalliya mai sauk'i, durowa tanufa,
tad'akko wata dakakkiyar shadda zani dariga, ta d'aura zanin, tana k'ok'arin saika riga suka
had'a ido da Dr da idonsa yake tsaye kam a k'irjinta ko k'yaftawa bayayi, da sauri tasaka rigar
tana fad'in daddy katashi?. Bai amsataba baikuma daina kallontaba, d'ankwalin kayan tad'auka tak'araso Inda yake
tareda rankwafowa ta hura MASA iska a idonsa.
Ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya.
Ta ce, ''kallonfa?, aii saika karemin muni Dr.
Murmushi yayi tareda ziro k'afafunsa k'asa, yakafeta da idanunsa yana fad'in, aii kozan
shekara dubu INA kallonki bazanga muninkiba.
A'a daddyn musayeef banda zigadai.
Tasowa yayi yarungumeta tabaya, yad'ora Kansa saman kafad'arta suna kallon juna
tamadubi, ahankali ya CE da gsk nakeyi Ni'imatullah.
Cike da mamaki take kallonsa ta ce, "wanan sunanfa daga ina?.
Saitin kunnenta yamatsar da bakinsa ahankali yarad'a mata maganar danima banjiba masu
karatu.
Ta zaro ido waje saikuma tasa hannu tarufe fuska tana fad'in nidai babu ruwana kaje kayi
wankanka.
Dariya yayi yana k'ara matseta ajikinsa, nikam da ruwana harda d'an tsaki tsaki.
Dariya tayi, nidai kaje wanka Kasan musayeef zai iya shigowa d'akinnan akowane lokaci.
Da sauri yakalli gadon, o, wai yana INA?.
Hummm sai yanzu kalura baya nan?.
ALLAH nazata