Showing 36001 words to 39000 words out of 43330 words
mik'asu cikin saurin likitoci ban
k'ara bi ta Kansu ba domin ba b'arayi na bane , bayan yan kwanaki sai aka kirani ake sanar dani
cewar mutanen nan duk 'yan uwansu sun gansu amma banda mutum biyu dan d'ayan ma bai
farfad'oba likitoce nata aiki akanshi shikam d'ayan ya farka , tunda naji hakan na garzayo nazo
asibitin , abunda na gani ba k'aramin rud'ani nashiga ba amma na dake duk dan kar agane ,
fuskar Abdallah iri d'ayace da fuskar d'ana Abdallah da yarasu shekara bakwai kenan da ace
yana Raye to tabbas za'a kirasu da identical twince wannan dalilin ne yasa naji ina son taimaka
masa"
Tunda ga nan Dr Ahmad ya cigaba da bada labari har yau da suke tare .
Malam yayi ajiyar zuciya yace "lallai Allah mai girma wato Abdallah Allah bainifi zakayi ilimi har
ka zama wani abuba sai da basirarka ta gushi lallai Allah mai girma ne , Alhaji babu abunda
zamu ce maka sai dai mu bika da godiya gami da fatan alkhairi Allah yasaka maka da mafificin
alkhairi , Allah ya jik'an Abdallah"
Nan dai Malam yayita kwararo addu'oi suna amsawa da Amin,
Daganan Dr Ahmad ya buk'aci yasan wane ne Abdallah , tiryan tiryan Malam ya runk'a bashi
labarin tundaga haihuwar Abdallah har zuwa ranar da suka rabu dashi da sunan zuwa kano
saro kaya , maikaratu idan ya had'a da labarin Dr zai bashi cikkaken taruhin Abdallah,
Ko da Malam ya gama bada labari gaba d'ayan su kowa da hawaye a idonshi musamman ma
Saifullah da baitab'a tsamanin Abdallah zaiyi irin wannan rayuwar ba tsantsar tausayin
abokinshi ne ya kamashi matuk'a .
Shikam Abdallah kuka yake kamar yaro dan sai yau duk abubuwan da yake gani suka fayyace
mishi gaba d'aya ya rasa bakin magana sai hawaye dayake ta faman yi .
Ummi kuwa abad'aya farinciki ne ya mamaye mata zuciyarta Rana ji kamar taje ta rungume
mijinta dan murna da jin dad'i .
Duk dauriyar da Mama taso yi amma hakan ya gagara sai hawaye ya sub'uce mata .
Umar , Saifullah tare da Aminullah su kaita rarrashin Abdallah
*gareku readers shin me kuke tunanin dai Kasan ce bayan nan ? Shin Dr zai bar Abdallah
hakanan duk da cewar ya taka muhimmiyar rawa a rayuwar shi ? Shin ya alak'arshi da Ummi
zata kasance , maiye makomar soyayyar Saifullah ga Ummi? Wannan da ma sauran wasu
tambayoyi suna cikin page na gaba*
Taku ce Maman Muhammad
@08165728746
[1/24, 4:46 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*
*MRS NN ONEí ½í²‹*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*Wannan page d'in na sadaukar da shi ga dukkanin masoya labarin bawan Allah , tare da duk
mai suna Zainab*
*Fatan alkhairi*❤
*Edited by Mum Mussadiq*
3⃣9⃣
Bayan natsuwa gami da gamsuwa ta ratsa zukatan su sannan Malam ya maida hankalinshi kan
Abdallah yace " to Abdallah yanzun ka gane ko kai waye ko ?"
Sai da ya ajiye wata nan nauyar ajiyar zuciya sannan yace "na gane Malam"
Murmushi Malam yayi sannan yace " to wace ce waccen?" Ya nuna Mama
Kallonta yayi tana ta sharar k'walla yaja gwuiwoyin shi ya tafi kusa da ita tare da rik'e hannuwan
ta yana fad'in " Ki yafe min Mamana na saki kuka insha Allah ba zaki k'ara kuka ba daga yau"
Dafa kanshi tayi tana Sosa gashin kanshi da ya kwanta yayi luf tamkar D'an India tama kasa
magana tsabar farinciki ,
Dr Ahmad yayi gyaran murya yace " Allah ne k'addara zumunci tsakanin mu shiya sa bai bani
ikon Neman danginka ba tunda farko kuma zumuncin mu ba zai tsaya anan ba "
Rarrafawa ya sake yi yakoma gaban Dr Ahmad yana mai share k'walla yace " thank you soo
much Dad bansan da bakin da zan godemaka ba hak'ika kai wani haske ne acikin rayuwata, ka
bani ilimin da ina rayuwar zahiri banyishi ba sai gashi na samu alokacin da iyayena da dangi na
suka cire tsammani da rayuwata, nagode Allah ya saka maka da mafificin alkhairi Allah ya jik'an
d'an uwana Abdallah yayi mishi Rahama"
Duka suka amsa da "Amin"
Kusa da Umar ya koma tare da rik'e hannun shi yace "ina cikin kewar d'an uwana wani lokacin
nakanji zuciyata tayi min baki Ashe rashin abokin arzik'i ine irin ka"
Murmushi kawai Umar yayi
Dai dai kusa da Aminullah ya koma ya saiti kunnanshi yace " thanks for taking care of my wife I
really appreciate you are indeed a real hero"
Aminullah yace " you deserve it"
Banza yayi da Saifullah kamar bai ganshi ba , Ashe shikuma abin ya bashi haushi sai ya mik'e
afusace zai bar gurin , cikin sauri Abdallah ya rik'o hannunshi " where do you think you're
going? ka kwantar da hankalinka ba sai na ambace ka ba you're always and ever in my heart"
Nan duk suka kwashe da dariya haka sukayita hira har lokacin azahar yayi ,
Awaje haka mutane keta tururuwar zuwa ganin D'an gayu Abdallah wasu ma sai sun tab'a shi
sunji .
Mama kuwa haka mak'ota suka ta zuwa mata barka da taya murnar dawowar tilon d'anta cikin
lafiya da aminci
Bayan tafiyar su massalaci sai ga yara daga gidan su ummi d'aya Leda ce ahanunshi bak'a
d'ayan kuma d'irkeken zakara ne anyanka shi an fige sukace gashi inji Malam , nan da nan
suka fara aikin su ,
K'arfe 2:30 suka dawo massalaci , suko su Ummi har sun gama dafa jalof d'in shinkafa da wake
ga naman k'aza k'amshi sai tashi yake , su jera kan tabarma .
Bayan sun ci abinci sun k'oshi Dr Ahmad yace musu dama yau yake San komawa kano ,
Abdallah yaso ya bishi amma k'emadagas Dr yak'i yace ya zauna sai ya huta agida sunaji suna
gani yayi musu sallama yatafi bayan ya yima Mama da Malam alkhair
Nan fa suka zauna shida abokanshi suna ta hira Mama na gefe yana kallon D'an nata zuciyarta
k'all.
Ummi kuwa duk haushi ne da takaici ya cikata wato yasan da zaman kowa amma banda ita?
lallai ma meyake nufi ? badai jiran banza tayi ba?
Haka taita jero tambayoyi har Hafsa tazo ta sameta Cikin tsokana ta fara magana "Amarya
angon naki ya dawo madadin na ganki cikin fara'a amma naga sai cin magani kike "
Wani kallon shatara shatakwas ta aika mata dashi , tsabar takaici ma ta rasa me zata ce.
Abdallah , Saifullah , Aminullah, tare da Umar suna tare har k'arfe Tara sannan Aminullah yayi
hamma gami da salati yace "jama'a Bakujin bacci ne?"
"Subhanallah" cewar Saifullah yayin da ya kalli agogon hannun shi
Mik'e wa sukayi dukan su Mama na d'aki ta jiyosu ta lek'o cikin barkwanci tace " Amintacce
inace pillows kawai zan mik'o muku".
Dariya kawai sukayi sai da suka rakasu har bakin mota sannan suka Shiga suka tada ita suka
tafi , yarage daga Abdallah sai Umar .
Abdallah yace" kaima badai guduwar zakayi ba ko?"
Kallon shi yayi da idanuwanshi da sukayi fici-fici saboda tsabar bacci yace " jiyafa saboda
tsabar k'osawa da nayi inganka Sam nakasa yin bacci"
Dariyar mugunta Abdallah yayi sannan yace " ayyah abokina "
Umar tsaki yaja ya k'ara gaba yana cewa" ajedai a rungumi pillow" gaba ya abinshi
Shikam dariya kawai yake yi ahaka ya Shiga gida .
Ummi kuwa tunda magrib tayi ta fara kwasan kayan da zata buk'ata adare ta maidasu d'akin
Hafsa dan chan take so taje ta kwana .
Dai dai k'ofar d'aki taci karo dashi shikuma zai Shigo cikin hanzari ta fad'a d'akin Ummi kamar
an wurgo ta , shikam abin ma dariya ya bashi d'akin ya nufa direct , yana ta k'are mai kallo
komai nanan yadda yake da ba tarkace jakar kayanshi da Aminullah ya kawo mai ya tuna dashi
fita yayi ya nufi d'akin Mama wadda har ta fara bacci a hankali ya d'auki jakar tare da sakayo
mata k'ofa Kasan cewar yanayin sanyi ne , komawa yayi d'akin ya rage kayan jikinshi , sannan
ya fito ya tunjumi ruwa arijiya ya nufi bayi ,
*kuyi hak'uri da wannan readers ina fama da ciwon kai*í ¾í´¦♀í ½í¹�
[1/26, 4:53 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*
*MRS NN ONEí ½í²‹*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
Page 4⃣0⃣
Sai da ya watsa ruwan ajikinshi yaji wani sanyi yana ratsa shi , haka nan dai ya k'arasa
wankanshi ya fito sai rawar sanyi yake yana Shiga d'akin ya fara Neman bargo chan gefen
katifa yaga bargon Wanda da alama an ajeshine aka manta ba'a d'auka ba , aiko ba shiri ya
d'auki bargon ya lullub'e har kai wanda duk da hakan bai hanashi jin sanyin da yake ji ba
Wanda k'afafuwan shi da hannayen shi sukayi sanyi tarara sai wani kyarma yake.
A d'akin Hafsa kuwa Ummi keta k'orafi sai Hafsa taje ta d'auko mata bargon ta , ita kuma Hafsa
tace bazata ba .
Da dai taga da gaske Hafsa take kuma ga dare yana dad'a yi ga sanyi yana k'ara sauka hakan
ya sata fita ba shiri dan sanyi ya gama ratsata.
Da sallama ta Shiga d'akin idon ta duk ya rufe bargon ta kawai take hange bata lura da
Abdallah dake ta rawar sanyi ba ta kai hannu tafara yaye bargon , bata Ankara ba taji an
janyota an wurga ta cikin bargon tare da k'udundune ta , tafa ihu kenan taji an toshe mata baki ,
cikin muryarshi dake rawa yace
"Shhh ba abinda zan miki d'umin jikinki kawai nake so"
Ruk'on da yayi mata ya sata kasa k'wacewa a hannun shi , tana ji tana gani ya runk'a murza
duk wata gab'a da keda d'umi ajikin ta Ummi tun tana 'yan k'ana nan kukan ta har ta daina
domin ta fara jin dad'in abin , dukkan su basu San iya lokacin da suka d'auka awanan yanayin
ba ita dai Ummi taji Abdallah shiru ne sai wata sassanyar ajiyar zuciya da yake hakan ya tabbar
mata da cewar yayi bacci .
D'agowa tayi ta kalleshi yana ta sharar baccin shi azuciyar ta tace " kai maza kunyarsu ragagga
ce " kayanta ta d'auka tasa sannan ta koma ta kwanta ajikinshi ta k'ank'ameshi tamkar zata
farka taga bashi.
Tofa masoya ansha bacci Abdallah ne ya fara farkawa yaga da kyakyawar fuskar abar
k'aunarshi ya fara tozali murmushi yayi ya furta a hankali " you are always beautiful my Queen"
ahankali ya zameta ajikin shi ya mik'e sai alokacin ya lura da yadda gari yayi tangaras , dafe
kanshi yayi yana fad'in "ya subhanallah"
Cikin hanzari ya zura jallabiya ya fita bokiti ya d'auka ya nufi kitchen dai dai lokacin Hafsa ta
d'aga tukunyar ruwan zafi zata shek'a ma kama ya ce
"Ke! Ke! Tsaya"
tsaf ta gane me yake nufi dan ta d'ago ta kalleshi amma sai ta k'ara seta tukunyar da bakin
bokitin
Cikin kirne fuska yace " ina mai tabbatar miki kika juye ruwan nan duk zafin shi sai kin shanye
shi"
Yadda yayi maganar ya bata tsoro shiyasa ta aje tukunyar , aje bokin yayi yace" zubamin" ta
d'auki tukunyar ta zuba ruwan rabi , ahasale yace " wai ke kinraina nine ko to duka zaki juye "
Sai alokacin tayi magana " to kokon fa?"
"Ki dafa wani ruwan dallah ni juyemin "
Ahaka tana k'unk'unai ta juye ruwan ba don ranta yaso ba .
Wani bokitin ya d'auka ya raba ruwan zafin biyu duka ya tafi rijiya ya surka su sannan ya aje
bokiti d'aya a k'ofar d'aki ya tafi da d'aya bayi .
Hafsa ko baki ta saki kamar wawiya azuciyar ta tace "idan baka mutu ba baka gama ganin abun
mamaki ba " hakanan ta sake d'aura wani ruwan kokon.
Ummi kuwa tunda ya fita ba dad'e wa ta farka kunya ce ta hanata motsi Sam tana zaune har
Abdallah ya fito wanka tana jin motsinshi tayi sauri taja bargon tafe har fuskarta da sallama ya
shigo tana ji bata amsa ba
A hankali ya fara magana " Ummi kije ga ruwa can a k'ofar d'aki kiyi wanka 8 ta kusa "
Zumb'ura baki tayi ta yaye bargon ko kallon inda yake bata yiba, yadda ta d'aga labulen ta lek'a
ba k'aramar dariya ta bashi ba aciki yake dariyar .
Tunda ta lek'a ta hango ba Mama a tsakar gidan sai Hafsa da ke shara yasa ta fita ta d'au
bokitin , me Hafsa zatayi inba dariya ba .
Lokacin da tagama wankan Mama ta fito tsakar gidan Ummi tana tsaye a bayan k'ofar bayin ta
na lek'e ita ala dole sai Mama ta Shiga d'aki zata fito .
Kamar ance Mama ta kalli k'ofar bayin ta hango Ummi a tsaye ta d'aura hannu akai , murmushi
Mama tayi ta mik'e ta Shiga d'aki Ummi na ganin haka ko tsayawa d'aukan bokitin batayi ba
fella d'akin Hafsa .Hafsa ko sai shak'ar dariya take abinta .
Ummi na Shiga ta chanja kaya ta tada kabarar sallah.
Abdallah kuwa tunda ya jira Ummi bata shigo ba nan ya mik'e ya fito ba kowa a tsakar gidan
hakan yasa kai tsaye d'akin Mama ya nufa ya sameta tana ta gyaran 'yar tsohuwar drower
kayanta cike da tausayin mahaifiyar tashi ya gaisheta ta amsa mai fuska a sake , d'akin ya
d'anyi shiru sai Mama ta katse shirun da cewa " abincin Ku nanan a k'ofar kitchen " to kawai
yace ya mik'e dan gaskiya yana jin yunwa , yana bud'e kwanon yayi arba da d'umamen tuwon
masara miyar busashen kub'ewa " oh my GOD" abinda ya fad'i kenan ya rufe kwanon ya fita
machine ya hau yaje wani restaurant yaci abinci sannan ya kira number Umar ya tambayeshi
yana ina , Umar yace" yana gida yanzun zai wuce kasuwa"
"Kajira ni ganinan zuwa " ya kashe wayar
Ko da yakoma gida yayi karo da motar Saifullah a k'ofar gidan su k'arasawa yayi ya gaida
Malam da keta fama da almajirai , sannan ya bar gurin ya Shiga gida still bai ga Saifullah ba ,
nan ya kira wayarshi ringing biyu ya d'aga bayan sallama Abdallah yace
"Aboki ya naga motarka ban ganka ba?"
Dariya Saifullah yayi yace " gatanan aro na baka kafin kasiya taka amma ka sani idan ka tashi
mayar min sabuwa zaka siyan mun"
Abdallah ma dariya yayi sannan yace " to waya gaya maka ina San kwancen wasu "
Haka dai sukayi ta barkwanci daga k'arshe Saifullah ya ce mai "key d'in motar yana bayan k'ofa
a sagale a zaure "
Da haka sukayi sallama irin tasu ta abokai.
Fita ya sake yi dan so yake yaje ya siyo kayan abinci dan gaskiya ba zai iya cimar nan tasu ba
ya saba da irin cimar turawa í ½í¸¨
A b'angaren Ummi kuwa Sam tak'i fitowa saboda kunya sai da Hafsa ta kaimata abinci , sannan
ta ce mata ta shirya suna da lecture anjuma , wannan dalilin ne ya fata mik'e wa daga inda take
ta fara shiri , ahankali take fitowa sai da tazo dai dai k'ofar d'akin ta sukayi clashing da Mama ta
fito band'aki , akunyace ya gaisheta Mama ta amsa sannan ta wuce ita kuma ta wuceta d'auko
abunda take buk'ata ta fito ,
Lokacin da suka je makaranta suka samu lecturer yace bazai Shiga ba sai 4 kowa yana ta Allah
wadaran halinshi , kowa ya fita ya kama sabgogin gaban shi ,
Hafsa kuwa Aminullah ta kira ya Zo shima suka zauna suka dasa shiriritar su , ita kuwa Ummi
tsaninta dasu ido , ana haka suka tsinkayi muryar Saifullah yana cewa "to na mamajo"
Aminullah na had'a ido dashi ya d'aure fuska dan yasan yanzun zaizo ya takura mai
Zama yayi kusa da k'aninshi sannan ya ce ma Ummi" Madam d'in mu ina wuni?"
Akunyace ta amsa da taso ace ita ta fara gaisheshi , Hafsa ta gaidashi a dak'ile shima a
dak'ilen ya amsa mata , juyawa yayi ya kalli Ummi yace
"Wai wannan k'anwarki ce "
Ummi tambayar ya bata dariya amma sai ta kalli Hafsa taga yadda ta d'aure fuska itama sai ta
tsare gidanta tace "eh k'anwa tace "
Hafsa dan takaici kamar tayi kuka .
Sai kuma ya sake jefo mata wata tambayar " k'anwarki ta jini ko kuwa"
Tsaki Hafsa Hafsa tayi ta tashi tabar gurin , Aminullah me zaiyi inba dariya ba
Ummi tace "ah ah k'anwar yata Abdallah ne shima kuma y'ar wan Mama ne"
"That's great ina jin nan zan maida shek'ata"
Da sauri Aminuallah ya juyo yace " what do you