Showing 39001 words to 42000 words out of 43330 words

Chapter 14 - Bawan Allah Book Compelet Maman Muhammad

01 Aug 2026

450

mean?"

"Abinda kunannan ka yaji "

" to da sakel inji Fulani , wai kai yayan nan duk abunda nace ina so sai ka yi k'ok'arin rabani
dashi " ya ko had'e rai ya juyar da fuskarshi gefe


Saifullah gyara zamanshi yayi yace " mekake nufi ?"


" ina nufin ina son Hafsa haka sanda ina tsak'a da son Ummi ka fara k'ok'arin rabani da ita
wannan kam bazan barma ita ba I have already win her heart , go and find your own"

Ummi kam rufe fuskarta tayi ta runk'a shek'a dariya abinta....



Follow me readers*

*Maman Muhammad d'inku ce*�
[1/27, 9:12 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*


*MRS NN ONE💋*



® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ �ųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com


*Nafi khan Nd k'awalli wannan page d'in nakune zamuga Wanda za'a yi ma gwalo kwando
kwando*😜😜

*Amma fa kar ace nayi nayi son kai ehe*😉

*ina gefe ina cin daria*�🤭

*edited by husnah beauty love you sis*😉

*page* 4⃣1⃣



Wani bak'in ciki ne ya tokare Saifullah amma sai ya dake ya ce " zo muje D'an k'anina musa
contains kar Madam tayi mana dariya"


Nok'e kafad'a Aminullah yayi yace "nak'i wayon "

"Haba my little bro my best friend ever "

Da k'yar ya lallab'eshi suka matsa gefe kad'an .


Ita dai Ummi tana gefe tana cin dariya


Can sai taji Aminullah ya na cewa " asshhh da zafi fa " ko da ta juya ta kalleso sai taga suna ta
dariya har da rungumar juna , nan suka canja salon hirar tasu .

Sai da sukayi sallar la'asar sannan suka Shiga lectures .



Ba su duka Shiga gida ba sai k'arfe 7:30 , ga wahala ga yunwa agurguje sukayi sallah sannan
kowa ta mik'e awurin don jiran sallar isha Ummi kuwa wani wahalallen bacci ne yayi awon gaba
da ita Hafsa da taga tayi bacci saita fita ta tafi d'akin Mama , tana d'akin Abdallah ya shigo yana
shigowa bayan sun gaisa yace ma Hafsa
"Ke kira min Ummi"

"Tayi bacci "

"Baccin gaske ko baccin k'arya ?"

"Wallahi tayi bacci tun d'azun "

"Go and call her for me my Friend!"

Sumi sumi ta mik'e ta fita , Ummi na bacci taji ana jijjigata ana kiran sunan ta , tana bud'e ido
taga Hafsa ce taja wani wawan tsaki ,

Hafsa abun ya bata haushi tace "oh ga marainiyar wayaunki ko , to bani ke kiran Ki mijin Ki ke
kiranki "


Cikin muryar bacci tace "baki ce mai ina bacci bane ?"


"Na gaya miki Malama Ki tashi kije kafin ya gaya wa mutane a matse yake dan naga yana gab"


"Bafa inda zanje idan kinga na tashi awajen nan to Tara tayi "


Baki a sake Hafsa tace " eyyeh haka kika ce , ni 'yar sak'oce , kar ya huce a kaina "


Hafsa ta fita taje d'akin Mama baya nan sai ta tafi d'akin su sallama tayi ak'ofar d'akin sai da ya
amsa sannan yace "ya akayi kuma ?"


Kai tsaye tace " tace ba zata zo ba"


Shiru yayi sannan yace "tana da waya?"

"Eh"

"Bani number ta"

Nan da nan ta rattafo mishi numbers din sannan yace mata "jeki " ta tafi tana sauke wani
nannauyan ajiyan zuciya,.


Tana kwance taji wayarta na ringing da kamar ba zata d'auka ba sai da kiran ya kusa katsewa
sannan ta d'aga tare da sallama ,


Amsa sallamar kawai yayi sannan yace " kizo Ki sameni ad'aki ina jiranki minti biyar kawai na

baki" k'itt ya kashe wayar ,


Wata zuciyar tana cemata taje wata zuciyar tana cemata kije ya sake rik'e Ki irin na jiya Ki
kwashi abun kunya da safe shi ba ruwan shi🤷�♀

Can kuma dai me tatuna oho sai ta mik'e ta fita , tana zuwa bak'in k'ofar tayi ta jero sallama bai
amsa ba sai da ya mula ya mulmule sannan ya amsa be ce mata ta Shiga ba ita ma kuma bata
Shiga ba takai kusan minti biyar awajen sannan ya ce

"Idan baki gaji ba to kiyi ta tsayuwa " ba shiri ta banko labulen ta shigo ta nemi gefe ta rakub'e
kamar wata bak'uwa,


Juyawa yayi ya kalleta cikin tsare gidan shi yace mata " Ummi na lura Sam bakya murna da
dawowa ta "

Cikin sauri ta d'aga ido ta kalleshi kallo me tattare da alamar tambaya


Shima kallonta yayi yace "yes da kin damu dani da zaki nuna farin cikinki gareni amma dayake
ba damu wa da ni kikayi ba sai wa wasan b'oyo mukeyi "


Ita dai ta kasa magana Wanda tasan har ga Allah ko mahaifiyashi da wiya ta kaita zumud'in
ganin shi , tana cikin tunani taji muryar shi yana cewa " shikenan tunda ni ba bazaki iya magana
ba kije kawai "


Ba tare da tayi tunanin komai ba tayi waje abinta .


Abdallah kam bak'in ciki ne ya isheshi wato ma ba zata iya zama kusa dashi ba me take nufi ?
Irin wannan tunanin yayi tayi har dare ya raba sannan ya fita ya d'auro alwala .



Ummi kuwa d'akin Hafsa ta koma ta k'udun dune cikin hijab d'in ta tana ta kuka azuciyarta tana
fad'in " ina ma ace zan iya fad'a maka sirrin zuciyata , ina ma ace zan iya fad'a ma irin kewarka
da nayi ina ma ace zan iya fad'a maka irin farin cikin da nashiga lokacin da ka bayyana agareni
amma bazan iya ba dan duk sun wuce gaban kwatance sai dai a aikace mijina "
Irin wad'an nan kalaman tai ta fad'i cikin mayan shauk'in soyayya har Hafsa ta dawo daga d'akin

Mama ta same ta wajen tana kuka ,


A hankali Hafsa ta zauna gefen Ummi tace " Aunty Ummi lafiya ?, me ya faru?"


Kamar jira take dama akulata sai ta zauna ta dasa sabon kuka , da k'yar Hafsa ta lallesata
sannan ta sake tambayarta me ya faru cikin kuka take sanar da ita yadda sukayi da Abdallah .

Hafsa ko mai zatayi inba dariya ba Ummi kam had'e rai tayi tace " saboda wulak'anci kice na
gaya miki damuwata madadin Ki bani shawara sai tsaya kina yi min dariya ?"


Cikin dariya Hafsa tace " yo Aunty Ummi AI ke d'in ce sai a hankali"


"Da nayi me fa?"


Murmushi tayi tace "Aunty Ummi yaya Abdallah kulawar Ki yake nema kin kasa ganewa
yanzun haka ma k'ila ko D'an welcome kiss d'in nan baki mishi ba , au ko dayake bari nayi shiru
naga jiya kun kwana d'aki d'aya " ta k'arasa maganar tana dariyar mugunta .

Ummi kam abin ya k'uleta ta d'auki pillow ta makawa Hafsa tare da fad'in " wallahi baby bakiyi
ba"


Duk suka kwashe da dariya daganan Ummi ta mik'e ta d'auro alwalar sallar isha da batayi ba
sai da tayi sannan 'yan hanjinta suka fara Neman agaji , ba shiri ta nufi kitchen shinkafa da miya
ta tarar miyar taji soyayyen nama sai buga k'amshi take nan tazubo taci sannan ta koma ta
kwanta.



*DA SAFE*

Kamar yadda Umar yake yi yanzun kafin ya tafi kasuwa sai yazo sunsha hira da Abdallah
sannan ya wuce , yauma suna tsaka da fira sai Umar yace

"Aboki nima fa na kusa Shiga daga ciki "

Cikin sauri Abdallah yace " Allah mutumi na "

"Wallahi kuwa , yau saura sati biyu"


Had'e fuska Abdallah yayi sannan yace " amma gaskiya bana kyauta min ba sai yanzun kake
gaya min"


"Kayi hak'uri abokina na bari ka samu natsuwa ne sai muyi maganar "

Ajiyar zuciya yayi sannan yace " shikenan Allah ya Santa alkhairi , a ina ka samu matar?"


"A funtua 'yar k'anwar Mama ce"

"Hakan yayi kyau , to ya maganar kayan aure an had'a ?"

"Eh an gama komai "


"Masha Allah na tayaka murna sosai , a ina zaku zauna?"


"A nan d'aki na mana "

"To ai kaji matsalar guy haya zaka nema idan ba haka ba ina mai tabbatar maka ba zaka mori
amarcin ka ba"


Umar ya kalleshi ya kwashe da dariya yace "ahankali dai abokina yanzun kam dole mu zauna a
nan dan duk basira ta ta k'are Mama kanta bataso mu zauna wuri d'aya amma insha Allah ba
da jimawa ba zan nemi hayar"


"Tashi muje Umar "

"Ina zamu? nifa kasuwa zanje "

"Shikenan kaje amma kasani gobe ba inda zaka je "

"Allah ya kaimu"

Nan sukayi sallama
[2/6, 10:54 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*


*MRS NN ONE💋*



® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ �ųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com



*dedicated to you readers ina alfahari daku*


*BAwan Allah fans much luv dearies Allah ya barmu tare*�



Page4⃣2⃣



Su Abdallah anata shirye shiryen bikin Babban aboki , acikin kwana uku ya Samar ma Umar
gidan haya me dan sauk'in kud'i .



Alokacin da biki ya rage saura sati d'iya sai Mama ta kira Abdallah tana masa fad'a , ranar ba
kowa agidan su Ummi duk sun tafi makaranta ,


"Kai ma ai ya kamata ka d'auki taka matar kusan inda dare yayi muku "

Shiru yayi yana Sosa k'eya sannan yace "to Mama ina zamuje?"

"Kai ma hayar zaka nema kuje can Ku bani guri in sarara"



Sai da yad'anyi nazari sannan Yace " ni da Mama na bari ne idan na fara aiki na samu kud'i sai
in siyan mana wadataccen gida sai mu koma gaba d'aya"


"Eh tunanin ka yayi kyau amma dai yanzun kafin wannan lokacin ka nemam muku wani gurin da
zaku D'an zauna"


"Shikenan nan Mama bari a gama bikin Umar sai na fara Neman gidan"


"A'ah *BAWAN ALLAH* ni so samu ma Ku tare rana d'aya da abokin naka"


Kunya ce ta kamashi ya mik'e yana Sosa k'eya yace " to Mama sai anjima"

"Mu juma da yawa" ta fad'i tana murmushi .


Bayan ya dawo da daddare ya samu Malam ya fad'a masa yadda sukayi da Mama fatan alkhairi
ya bisu dashi Sannan suka k'ara tattaunawa daga nan ya rok'i alfarmar kar asanar da Ummi
komai har sai ta tare Malam dai murmushi kawai yayi,


Daga nan ya koma gida bayan yayi wanka yayi shirin baccin shi tsaf sannan ya kira Dr Ahmad
shima cikin jin kunya ya sanar masa , cike da jin dad'i da murna yayi masa fatan alkhairi
Sannan sukayi sallama,


Ajiyar zuciya Abdallah ya sauke sannan ya furta a fili "komai ya kusa zuwa k'arshe" murmushi
yayi tare da jero addu'oi sannan yayi bacci,



Washe gari da safe Umar yazo gidan dama sunyi da Abdallah zasu je funtua gidan Amaryar
Umar d'in, bayan sun gama shirya wa tsaf suka fito. Abdallah ya sha kwalliya kamar wani sabon
ango sai fara'a yake , Ummi dake zaune d'akin Hafsa tunda ta k'yallara ido ta ganshi sam ta

kasa kauda idonta ba dan k'yafta ido dole bane to da Ummi bata yiba tasan Abdallah
kyakkyawa ne amma bata tab'a ganin asalin kyanshi ba sai yau .


Shikam tunda ya juya suka had'a ido sau d'aya bai k'ara waiwayar inda take ba , ya nufi k'ofar
Mama , yana shirin yin sallama ita kuma tana fitowa, hakan yasa duk suka zauna a k'ofar d'akin
kan tsaftacecciyar tabarmar dake gurin ,

Bayan sun gaisa Mama tace "Umar ina zuwa haka wannan shiri kamar yaune za'a kawo mana
suruka "


Caraf Abdallah ya amshe da " wata surukar za'a je nemo miki"


Cike da mamaki Mama tace"wata suruka kuma AI ni na gama aurar da yarana maza sai dai na
jira suruki kuma"


Dariya Abdallah yayi sannan yace " to Mama suruka ta biyu za'aje ne mammiki" ya k'arishe
maganar yana langab'ar da kanshi tare da had'e hannunshi guri d'aya alamar pleading ,


Mama ta gane zolaya yake ji sai tai murmushi ta ce "Hakan yana da kyau AI Allah ya sanya
alkhairi "

Duk suka amsa da "amin"


Umar yace " Mama AI yarinyar ma k'awar Maryam ce "


"Masha Allah Abu yayi kyau" nan dai sukayi ta barkwancin su sannan suka fita .


Ummi kuwa tunda suka fara maganar take jin zuciyar ta kamar zata tarwatse , mekunanta ya
ke jiye mata ne ?tun kafin ta tare Abdallah zai mata kishiya ? , wani kuka ta fashe dashi , Hafsa
kam ya kwance a d'aki tana sharar baccin ta har Ummi taci kukanta ta gaji , har tayi shiru



Shikam Abdallah ko ajikin shi fita ma yayi harkarta duk da hakan bai mishi dad'i shirye shiryen
kawai yasa agaba

A b'angaren Dr Ahmad kuwa zuzurutun kud'i ya turama Abdallah yace su sha shagali shida
aminin shi


Abdallah kuwa wani gidan haya ya samu unguwar me kyau gashi babu hayaniya


Plat uku ne agidan da ya wadatu da manya manyan dakuna 2 bedrooms ne sai Babban parlor
mai tare da dining area gefe kuma kitchen ne da madai daicin store aciki balaifi gidan yana da
tsari mai kyau



Wajen Ummi Mama da ummanta gyara suke mata sosai da tambayi dalili duk amsa d'aya suka
bata suna so 'yarsu tafi ta kowa kyau , Babban abinda abinda ke damun ta kuwa shine yadda
Abdallah ya d'auke k'afa agidan sai ya kwana bai shigo ba bata San yana can ya k'ok'arin
karb'ar Amarya ba ,


Akwana a tashi ba wuya agurin mai rai yau ta kasance juma'a, Wanda gobe asabar za'a sha
shagalin biki,


Ummi na zaune ita da Hafsa ad'aki yayin da Mama tana tsakar gida tana Taryar bak'i daga
danginta zuwa dangin Baban Abdallah , wata daga cikin k'annen MAMAN Ummi tashigo d'akin
da sallama bayan sun amsa mata tace "Ummi yaya tace maza Ki tashi muje gidan su Habiba
mai kotso da k'unshi ayi miki"

Shiru tayi kamar bata jita ba da yake ba wani girman Ummin sosai tayi ba.


Hafsa tace" ummi dake fa ake magana ,"


Azuciye ta juyo dan bak'in ciki duk ya gama cikata tace " naji sai mene ? Ni ku k'yaleni da
kinibibin kU ba inda zanje"

Zuwaira k'anwar Umma taji haushi ta fita kai tsaye Mama ta sanar ma duk yadda sukayi da

Ummi , murmushi Mama tayi tace "muje gurin Ummin "


Ummi najin sallamar Mama sai ta hau kuka ita bazata ba da k'yar da sid'in goshi Mama ta
lallab'a ta ta tafi ,


Daren ranar kuka ta kwana yi sai ta d'aga waya zata kira Abdallah dan ta gaya mai irin dumbin
k'aunarshi da take yi sai kuma ta kasa domin zuciyar ke gargad'in ta muddin tayi hakan to zaiga
zak'ewar ta bare ma yanzun da yake rawar jiki za'a kawo mai sabuwar Amarya zai yi auren
soyayyah acewar Ummi fa kenan🤣 [2/7, 10:12 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*


*MRS NN ONE💋*



® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ �ųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com


_Assalamu_ _alaikum_ _readers anan Zan tsaya da littafin*bawan Allah*sakamakon wasu
dalilai ina fata zaku yi min uzuri�sai mun had'u a sabon novel dina mesuna RAYUWA TA ina
fatan shima zai nishad'antar damu ngd_


*GODIYA*

_Godiya ta musamman ga k'ungiyar REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS,like I said
b4"sisters we are the best ever so let's keep shining like a stars in the sky🌠🌠_📚�

*jinjina gareku readers*

*Bawan Allah fans bansan ta inda zan fara ba duk fad'in social media bani tamkarku ina yinku
irin sossai d'in nan Allah ya bar zumun ci*

*my bestie I miss you (Ummu Sadeeq)*

*Ameenert*

*Rahma Ismail*
*Sadiya illa*
*acceya*
*Maman hanan*
*Ummu adil*
*fareeda*
*nafi khan*
*matar me kake*
*sadeeya*
*MAMAN sa'a*
*Binta mala*
*aisha saleh idrees*

*Kai aradun Allah kuna da yawa ba zaku lissafu ba Kawai Kudai Ku sani kuna mak'ale
azuciyata*�🤸�♀


*miss husnah*no more hawan water yanzun agayama likita bawan Allah yazo k'arshe dan haka
ya ajiye ya ajiye makaman aikinsa agefe wannan ba fanni shi bane Maman Muhammad ce zata
yi aikin ta🤣


*Maman Mimi*
*MAMAN Abdul*
*ummul khairi Gj*
*ummul khairi Jibril*
*hussaina sanee*
*Rabi'atu paki*
Love you guys�



Kuyi hakuri readers idan nace zan lissafoku to kunfi k'arfin fige d'aya mai d'auke da read more
goma fatan kun gane

🤣🤣🤣🤣🤣🤣



🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚


Page 4⃣3⃣


Washe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0