Showing 18001 words to 21000 words out of 43330 words
,
Key yasa ya bud'e k'ofar d'akin sannan ya ba Abdallah izinin shiga , tun da Abdallah ya d'aga
kai bai sauke ba har sai da yaci tuntub'e da center table , shiko Dr murmushi kawai yake
sannan yace ,
"Nan d'akin ka ne akwai duk wani abun buk'ata aciki bari nasa akawo maka abinci"
Kai kawai ya gyad'a tare da zama acikin d'aya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun d'akin,
Tunani da yawa yake acikin ransa , wane ne shi?, waye kuma wannan mutumin? Waye
Abdallah , sunan da yafi d'aga masa hankali kenan idan ya tuna,
Yana nan zaune Dr ya shigo shi da wani matashi d'auke da tire a hannu ,
Cike da mamaki matashin ya tsaya yana kallon Abdallah , sai da Dr ya daka masa tsawa
sannan ya aje kayan abincin ya fita ,
Kusa dashi Dr ya ya zauna sannan ya dafa kafad'ar shi yace"Babana tashi muje na nuna maka
d'akin ka kayi wanka lokacin magrib yayi "
Jin maganar sallah ya sashi saurin mik'e wa , wata k'ofa ya bud'e suka kutsa , bedroom ne na
gani na fad'a tamkar a k'asar turai , duk kayan more rayuwa akwai gidan , directtoilet ya wuce
da shi ya nuna masa yadda zaiyi amfani da komai sannan ya kullo masa k'ofar ya fita,
Cikin tsoro Abdallah ke wanka har ya gama ya fito kayan da ya cire ne ajikin shi ganin wasu
kaya yayi an aje mai su akan bed nan ya cire na jikin shi ya sasu , k'ananan kaya ne sunyi
matuk'ar yi mishi kyau asalin kyanshi da talauci ya b'oye duk sun bayyana, masu karatu zanso
kuga *Bawan Allah*
Ko da ya fito pallor ba kowa , daga gefen kujera yata an shimfid'a mishi sallaya , nan ya hau ya
gabatar da sallah
*Waye DR AHMAD*
Dr Ahmad bakano ne ciki da bai awata k'aramar hukuma da ake cema Rano , *Ahmad
Abdallah* shine cikakken sunan shi su biyu ne awajen iyayen su shi da k'anwar shi *Fiddausi*
Alhaji Abdallah d'an kasuwa ne yana da rufin asirin shi dai dai na Alhajin k'auye, matar sa d'aya
ce *Maimuna* kuma ita ta Haifa masa yaran sa biyu da yake matuk'ar so da k'auna,
Tun asalin Ahmad mutum ne me son taimakon jama'a hakan ya sanyan ya sanar mawa
mahaifin shi yana son zama likita , mahaifin shi ya bashi kulawa ta musamman har ya kammala
karatun shi, nan mahaifin shi yayi mishi aure da wata 'yar abokin shi *RAMLA*
Bayan bikin shi da kimanin wata uku ya samu aiki a asibitin Aminu kano , bayan shekara d'aya
Ramla ta sunkuto d'anta namiji yaci suna *Abdallah* suna kiran shi da Abba,
Dr Ahmad ya samu nasarori masu d'imbin yawa ciki harda bud'e asibiti nashi mai zaman kanshi
wato private sai da Abdallah ya shekara goma sannan Ramla ta sake haifo wani namijin yaci
sunan Babanta *Abubakar*
Abdallah yana da shekara ashirin da bakwai ya gama karatun shi na law a k'asar England
saurayi ne ajin farko kamili, alokacin da ya dawo aka fara batun auran shi da wata yarinya
*Aisha* amma kuma cikin ikon Allah bikin shi saura wata d'aya ciwan ciki ya murd'e shi ya rasu ,
K'ololuwar tashin hankali Dr Ahmad da Hajiya Ramla sunshige shi amma da suka sa tawwakalli
sai suka hak'ura , ,
Masu karatu idan kuka ga *Abdallah Ahmad Abdallah* ba zaku banban tashi da *Abdallah
Abdallah* ba
Wannan ne mafarin taimakon da Dr Ahmad yake shirin yima Abdallah
[12/29/2017, 7:56 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*
*MRS NN ONEí ½í²‹*
*To readers ina Wanda ya shirya zuwa kano Neman bawan Allah Sadiya neman bawan wa
Allah Wanda rashinsa Sam baiyi mata d@d'i ba cikin sa'a ko ta samu abokan tafiya Maman sa'a
tace ba'a barta a baya ba dole su nema wa Ummi farincikin ta , aceeya kuwa cewa tayi jirgin ya
tsaya ajigawa ya d'auke , Amne kuwa da yake 'yar black stormach ce cewa ta ba inda za'a je
saboda man fuel yayi tsada , Aunty axland ma tace ba'a barta a baya ba*í ¾í´£í ¾í´£í ¾í´£
� *Gaisuwar fatan alkhair agareku masoya masu bibiyar littafin bawan Allah sakon ku na
fatan alkhairi yana isowa agarene nagode agaskiya bansan da bakin da zan gode muku ba
amma kusa ni har cikin raina inajin dad'in yadda kuka amshi wannan litttafin nagode sosai Allah
ya had'a fuskokin mu a aljannatul firdaus Amin ya Allah*â�¤â�¤â�¤. *one luv*í ½í¸˜
*Ameenart Nd fatima (MAMAN Sadeeq) wannan page d'in naku ne dama d'aukacin yan Bawan
Allah fans , I really like your comments�*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ �ųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
Page 21----22
Haka nan su Malam suka tattara suka koma Zaria ba tare Abdallah ba zuciyoyin su cike da
zullumin me zasu gaya ma mahaifiyar shi da kuma matar shi , ahaka suka sauka a tasha suka
hau napep , direct gidan su Umar suka wuce ,
Aiko Maman Umar na ganin shi sai kuka domin yadda ta Ganshi ba k'aramin firgita tayi ba nan
k'annen shi suka hau ihu " yaya Umar oyoyo !"
D'an autan su ne ya fita da gudu yaje gidan su Abdallah Ummi na alwalar la'asar Mama na kofar
d'aki Hafsa kuma tafito daga bayan gida ,
Yaron ya k'arasa kusa da Mama cikin zumud'i yake ce mata "Mama yaya Umar ya dawo "
Cikin zafin nama Ummi ta waigo tana kallon shi
Mama ko cewa tayi "da gaske ?!"
"Eh Mama amma ya dawo kanshi a d'aure da wani Abu"
AI nan Ummi ta yarda butar hannun da dama already akwai hijab ajikin ta AI sai ta nufi k'ofar
gida ,
"Ke Ummi ina zaki je ?" Mama ta fad'i yadda taga Ummi zata fita kamar zautacciya
"Ina zuwa Mama "kawai Ummi tace tasa kai
Hafsa da sai yanzun ta k'araso waje sai k'wala kira tayi "Aunty Ummi jira ni"
AI ina AUNTY Ummi gudu-gudu sauri-sauri ta runk'a had'a wa ,
*Kano*
Yau kwana bakwai kenan ana fama da Abdallah amma Sam be san ana yi ba gashi zuciyar shi
tana aiki amma kuma gangar jikin shi bata motsi , duk sun sare da al-amarin shi,
Yauma kamar kullum likitoci ne zaune awani k'awataccen office suna tattaunawa akan Abdallah
, wata nurse ta shigo cikin sauri ta fara gaya musu patient din room no 18 ya farka kamar jira
suke nan suka mik'e cikin sauri suka k'ara k'ofar d'akin ,
A zaune suka same shi akan gadon ya sakko da k'afafun shi k'asa , ya rik'e kanshi dake
tsananin Sara masa ,
Koda suka bud'e k'ofar suka shigo kallo kawai ya bisu dashi domin be tab'a ganin su ba ,
Doctor d'in nan ne da ya ce ya sanshi ya matsa kusa da shi ya fara magana
"Ni sunana Dr Ahmad , zan iya sanin naka sunan?"
Shiru yayi bece komai ba , Dr Ahmad ya sake cewa "ko zan iya sanin naka sunan?"
"Ban sani ba" ita ce amsar da ta fito daga bakin Abdallah
Dukkan su likitocin suka kalli junan su
Dr Ahmad ya sake jefa mashi wata tambayar "ya sunan garin ku?".
Girgiza kai yayi nan ma alamar be sani ba
Nan likitoci suka sake firgita wani likita ne ya ce mai "nan ina ne ?" K'are ma d'akin kallo yayi tas
sannan ya runtse idon shi gami da matse hannun shi kamar zai kai naushi
Dr Ahmad ne yace su k'yale shi ya huta , nan suka yi mai allurar barci ya koma
[12/30/2017, 10:59 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*
*MRS NN ONEí ½í²‹*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ �ųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
2⃣5⃣
*Cigaban labari*
A b'angaren Dr Ahmad kuwa be b'oye ma iyalin shi komai game da Abdallah ba ,
Hajiya Ramla tayi farin ciki sosai har ta k'osa safiya tayi taga me kama da d'anta,
*Zaria*
Yau kusan sati uku kenen ba labarin Abdallah hakan bai sauya akalar damuwa acikin zuciyoyin
dangin sa ba musamman ma mahaifiyar shi da matar shi ,
Ummi kuwa yanzun wani irin tsantsar son Abdallah ne ke damun ta gashi yayi mata nisa , Dan
yanzun gani take bayan iyayen ta babu Wanda take ma so da k'auna tare da mararin gani irin
Abdallah,
Malam kuwa ya duk'ufa addu'oi ba dare ba rana ,
Umar kuwa Alhamdulillah ya ji sauk'i sai dai damuwar rashin d'anuwan shi amininshi, shi kad'ai
ke tayar mai da hankali akoda yaushe
Hafsa ce keta fama da Ummi akan taci abinci " haba Aunty Ummi yanzun ke kullum sai an ta
fama da ke wajen cin abinci kamar k'aramar yarinya ?"
Ummi dai bata ce komai ba iya kacin k'walla da keta gudu a kan kumatunta ,
Hafsa ta sake cewa , " ayyah k'awata Dan Allah ciki kinga rabon Ki da abinci tun jiya da rana
gashi yanzun Kusan k'arfe uku"
Kallon Hafsa tayi tace "zanci amma sai in zaki bani a baki " ta k'arasa maganar cikin shagwab'a
"Naji duk wannan me sauk'i ne "
Nan Hafsa tayi ta ba Ummi abincin tana ci , haka Mama ta fito ta samesu duk sai suka bata
tausayi,
*Kanon Dabo*
Kamar yadda Dr Ahmad ya tsara acikin sati uku ya samar masu *Visa* shida D'an mak'ocin sa
kamar yadda yake fad'i , basu bar garin ba sai da yasan yadda yayi ya masamar ma Abdallah
takaddun makaranta sannan suka d'aga birnin *London*
Sosai Abdallah yayi k'auyanci Kasan cewar bai tab'a sanin wani Abu makamancin k'asar ba ,
A wani hotel suka sauka , bayan sun D'an huta sannan Dr ya nema masa Wanda zai runk'a
koya mai turanci
Ba da jimawa ba ya saman mai admission a London university , inda zai karanci medicine,
Sosai Abdallah ya maida hankali wurin karatun shi saboda bashida damuwar kowa acikin
k'wak'walwar shi,
Sai da Dr ya tabbar da Abdallah ba shida matsalar komai sai nan ya dawo Nigeria tare da barin
shin amanar shi awajen wani Bature
í ½í²Ÿí ½í²Ÿí ½í²Ÿí ½í²Ÿí ½í²Ÿí ½í²Ÿí ½í²Ÿ
Wasa-wasa dai yanzun wata takwas da b'atan Abdallah ko wanda yaga me kama da shi basu
gani ba,
Abun da yake k'ara d'aga ma Ummi da Mama hankali bai wuce duk in sunyi istikhara suna
samun natsuwa ba hakan ke nuna musu Abdallah yana cikin kwanciyar hankali, to amma yana
ina ne? Mai ya sa yayi nesa da su? Shin baya tunanin halin da zasu shiga ne? Wad'an nan
tambayoyi su suke ta yawo a k'ak'walen su amma kuma kaf babu mai amsa masu su,
Wata rana Mama tashir ya taje gidan su Ummi domin su tattauna da mahaifiyar ta akan
makomar auren Ummi da Abdallah,
Bayan sun gaggaisa tace " Dama nazo ne akan maganar wad'an nan yaran , kinga yanzun wata
takwas amma bawan Allah shiru , shine nace ko za'a raba auren Ummi idan ta samu wani mijin
tayi aure"
Maman Ummi tace " amma Maman Hafsa sai naga kamar yayi wuri afara wannan maganar
balle ma muna sa ran insha Allah ba da jimawa ba zai dawo"
Ajiyar zuciya Mama tayi sannan tace " to AI shikenan ni dama naga k'a'idar musulunci wata
shida ne shiya sa kuma da naga babu rabo a tsakanin su"
"Hakane Maman Hafsa my dai k'ara hak'uri"
Nan dai suka gama maganar su ta tafi ,
Ummi na kwance a d'aki tunani duk ya isheta Mama ta d'aga labulen d'akin ta shigo da sallama
amma Ummi Sam bata ma anayi ba ,
Sai da Mama ta dafa ta sannan ta waigo a firgice ta kalleta "yanzun Ummi ba zaki cire wannan
yawan tunanin a ranki ba ,? Shi wanda kike yi Dan shi d'in yana chan hankalin shi kwance
bema San kina yi ba , Dan Allah Ki rage tunanin nan kar ya haifar miki da wata matsalar kuma"
Cikin jin kunya Ummi tace "to Mama"
í ½í²Ÿí ½í²Ÿí ½í²Ÿí ½í²Ÿí ½í²Ÿí ½í²Ÿí ½í²Ÿ
*BAYAN SHEKARA D'AYA DA RABI*
*London*
Wa ni had'add'en guy ne na gani na fad'a zaune a cikin library yana karatu fuskarsa d'auke da
wani farin glass , kamar daga sama , yaji an ce mai
"Hi"
D'agowa yayi yakalli wanda yayi maganar shima matashi shi ne kyakyawa , "hi"kawai yace
masa ya maida hankalin shi zuwa littafin da yake dubawa
Matashin ya sake cewa " please can I have a sit?"
D'aga mishi kai kawai yayi , ,
Shi kuma wancan ya zauna yana murmushi, mik'amai hannu yayi yace " I'm saifullah from
Nigeria "
Sai alokacin mai karatun ya aje littafin tare da cire glass d'in idonshi sannan ya mik'a masa
hannu sai ya ce " Abdallah also from Nigeria"
*Nikam nace lallai ma lallai Ashe Abdallah ne gaskiya ya k'aro wulak'anci*
Cike da murmushi Saifullah ya ce "Ashe dai nasamu D'an uwa"
Murmushi kawai Abdallah ya mai ,
Saifullah irin mutanan nan ne masu shegen surutu ba irin su Abdallah ba miskilai,
Ba jimawa suka saba sosai har suka k'ulla abota
[1/1, 6:56 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*
*MRS NN ONEí ½í²‹*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ �ųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
2⃣6⃣
Mama ce zaune a tsakar gida ta zabga tagumi tana kallon Ummi da keta faman wanki , hak'ik'a
yarinyar tana matuk'ar bata tausayi tayi aure amma bata San miye auren ba balle ta tantance
dad'in shi , babu abinda ta tsinta a cikinshi sai wahala ita irin tata k'addarar auren kenan , can
kuma ta mik'e kamar an tsikare ta , ta zari Hijab d'inta da ke sagale jikin k'ofa sannan ta juya ta
ce ma Ummi "bari naje na dawo"
"To Mama adawo lafiya"
Mama na fita bata zame ko ina ba sai gidan su Ummi ta ci sa'a ta samu Malam yana nan bayan
sun gaggaisa ta fara fad'in abin da ya kawo ta ,
"Dama Malam Maganar Ummi ne ya kawo ni"
Malam yace "to Allah yasa dai ba laifi tayi ba"
"Ko kad'an Malam Ummi bata laifi , sai dai mune muke k'ok'arin yi mata laifi"
"Kamar yaya kenan?"
"Malam tunda kaga har yanzun Abdallah bai dawo ba kuma gashi shekara har ta gota Dan Allah
anema ma yarinyar nan sauk'i a raba ta da wannan auran"
Shiru Malam yayi sannan yayi ajiyar zuciya yace "maganar Ki gaskiya ne amma kafin mu yanke
hukunci ya kamata muji ta bakin Ummin , Dan haka idan kin koma Ki turo min ita "
"To shikenan Malam mungode Allah ya k'ara girma"
Nan suka k'ara tattaunawa akan maganar sannan Mama ta yi musu sallama ta tafi ,
Mama kuwa bayan sallar isha ta kira Ummi tace mata taje Malam yana Neman ta , sai da ta
D'an ji gaban ta ya fad'i amma kuma ta daure ta tafi ,
Kai tsaye cikin gidan su ta nufa bayan gaishe-gaishe suna D'an fira da k'anan ta a tsakar gida
sai ga Malam ya shigo , Maman Ummi ta shimfid'a mai tabar ma ya zauna suka gaisa sannan
ya k'ara da cewa " Ummi dama ba wani Abu bane yasa nakira Ki akan auran Ki ne da Abdallah
shin kin yarda a raba ko kuwa zaki iya hak'urin jiran shi?"
Tunda Malam ke magana hawaye suke ambaliya a fuskar Ummi , ta kasa magana ,
Malam ne ya sake magana "ina jinki Ummi baki ce komai ba "
Ummi ta fara magana muryar ta na rawa " Baba Dan Allah karku raba ku D'an k'ara mai lokaci
Dan Allah Baba"
Shiru Malam yayi domin ya fahimci 'yar tashi tana son mijin ta "shikenan Ummi mun k'ara mai
shekara d'aya idan be dawo ba ko ba da yardar Ki ba za'a warware auren nan"
"Baba na amince na gode"
"Shikenan Allah yayi miki albarka shi kuma Allah ya bayyanar mana dashi"
"Amin" Ummi tace sannan kuma tayi shiru
"To tashi Ki tafi dare nayi ko kuma akwai Wani Abu ne "
Shiru tayi kamar bazata ce komai ba sannan kuma ta fara magana bakinta na rawa "Baba dama
alfarma nake nema"
"Ki fad'eta ko menene indai bai sab'a ma addini na ba zanyi miki shi "
"Baba dama so nake Dan Allah ka barni