Showing 33001 words to 36000 words out of 43330 words
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
3⃣6⃣
Tun da ta runtuma bata tsaya ba mutane sai kallonta suke , duk iya k'ok'arin Aminullah ya tsaida
Ummi ya kasa , aiko yana ganin sun kai wurin wani kwararo da ba mutane ya figo hijab d'inta ta
dawo baya , kamar zata bangaje shi ,
Ganin yadda take kuka harda majina gashi sai wani tittirjewa take kamar sabuwar 'yar bori ya
sashi daka mata tsawa " ke Zainab!!"
K'ara firgita tayi zata sake gudu sai ya sassauta muryarshi yafara magana cikin sanyi " Ummi Ki
natsu mene ne ?, me ya faru ?, wani Abu aka miki,?"
Duk ya gama jero tambayoyin shi amma kawai da ido tabishi
Azuciyar ta ko fad'i take ina ma tana da halin amsa masa wad'an nan tambayoyi data amsa su
Shi kuma ganin shirun da tayi ga hawaye yana ta sintiri a fuskarta sai ya fara tunanin anya
Ummi kam kanta k'alau ? Bai sake cewa komai ba yaja hannun ta har gurin motar shi sannan
yace mata ta Shiga , tana Shiga ya rufe sannan ya zagaya shima ya Shiga , sannan ya tada
motar har a lokacin kuka take shak'a ,
Haka yayi ta tuk'i amma Sam zuciyarshi bata mishi dad'i saboda yadda yake jin kukan Ummi a
zuciyarshi kamar ana d'iga mishi tafasasshen ruwa.
Suna isa k'ofar gidan su ta hangame murfin motar ta fito ko tsayawa ta rufe batayi ba ta fad'a
gidan su Hafsa , shi dai Aminullah kanshi duk ya d'aure ya rasa gane meke damun Ummi ayyah
batada junnu, nan ya coge a k'ofar gidan.
Ummi kuwa tun da tasa kanta a zauren gidan ta fara k'wala ma Mama kira
Mama na d'aki abin da bata tab'a ji ba kenan afirgice ta fito tana "Ummi mene ne ?"
Amma ina zubewa tayi ta dasa sabon kuka , Mama duk ta kid'ime ,
Hafsa dake d'aki tana fama da kanta tafito ganin yadda Ummi ke kuka bilhak'i da gaskiya sai
jikin ta ya k'ara sanyi domin duk runanin ta wani mummunan abun ne ya faru .
Duk suka rud'e da tambayoyi amma Sam Ummi tak'i magana sai kuka , cikin k'unci Hafsa ta
koma d'aki ta d'auko hijab d'in ta ta fice , yanayin tashin hankalin da take ciki shi yasa bata lura
da Aminullah dake zaune kan dakali ya zabga uban tagumi ba , shima kuma bai kula ta ba .
Direct gidan su Ummi ta fad'a ba'afi minti biyar ba sai gashi sun fito tare da Malam.
Malam ya ga Aminullah zaune turus ya zabga tagumi , shi kanshi Malam d'in sai da gaban Shi
ya fad'i , cikin sanyi ya ce " Amintacce meke faruwa ne ?"
Aminullah ya kalli Malam cikin damuwa sannan ya labarta mishi sukkan abubuwan da suka faru
d'azun ,
Bai yi wata wata ba yace ma Aminullah zo muje , suna suga gidan Malam ya hau fad'a yana
tambayar ta me ya faru ? Ko tayi hauka ne duk ta tayar wa da mutane hankali,
Murya na rawa kamar ta mai koyon magana tace "Baba na...na..Ganshi"
"Wa kika gani?"
Zata k'ara wani kukan Malam ya yi jan ido yace takuma sai ya lallasa ta
Da k'yar tace " *ABDALLAH* "
Maman kam dab'as ta zauna a k'asa tayi zaman 'yan bori , tana tunanin to kodai mafarkin ta na
jiya ya zama gaskiya ne?
Hafsa ma sai da ta Zabura,
Aminullah gaba d'aya ya firgice domin bai gane inda zancen ya dosa ba .
Malam ma kanshi duk ya d'aure ya kalli Ummi da keta wik'i-wik'i da ido dan yanzun kukan ya
tsaya ya ce "Ummi kinsan me kike fad'a kuwa?".
With confidence ta d'aga kanta tare da fad'in "ku tambayi Aminullah AI shi ya kaini inda yake "
Nan fa kallo ya koma kan Amintacce wanda duk sun k'ara birkita shi , Malam ya kalli Aminullah
yace " Amintacce mene ne hak'ik'anin wannan zancen?"
Cikin muryar rud'u Aminullah yace "kamar yadda na gaya maka a waje , abokin yaya na ne bai
da lafiya shine yaya na yakirani na je na karb'i kaya na wuce mai dasu gida , shine na rok'i
Ummi ta raka ni lafiya lau muka shigo asibitin amma tunda muka Shiga d'akin duk ta birkice
kuma ni bata cemin komai ba shine na kwaso ta na dawo da ita"
Malam ya kalli Ummi cikin takaici zai magana tayi sauri ta ce "wallahi tallahi Baba naga yayan
Hafsa indan kuma baka yarda ba kuje dashi ka gani idan bashi ba wallahi na yarda daga yau na
zama bazawara" ta k'arike maganar da wani kuka me tsuma zuciyar me saurare.
Kowa awurin sai da ta bashi tausayi , Mama da k'ar ta tattaro natsuwar ta tace " Malam aje a
duba ko Allah yasa za'a dace"
"To"kawai yace ya fice Aminullah ya bi bayan shi , suna fita ya juyo ya kalli Aminullah yace " ka
tsaya muyi sallar magrib anan sai muje ka kaini" jiki a sanyaye yace "to"
Shikam Bawan Allah duk wainar da ake toyawa bai sani ba sharar baccin shi kawai yake yi
sabo allurar da aka mai
Saifullah kuwa tun da su Aminullah suka fita yabi bayan su amma cikin rashin sa'a ya sa bai
gansu ba , tun lokacin ya ke kiran wayar Aminullah amma bai d'aga ba hankalishi duk ya tashi
gashi shi kad'ai ne awajen Abdallah ballantana yabi bayan su .
Sai 7:30 sannan Dr Ahmad ya dawo ganin Saifullah cikin rud'ani yasa shi tambayar meke
damunshi amma ya rasa amsar da zai bashi kawai sai yace mai "ba komai "
Bayan minti goma Abdallah ya farka gami da mik'a da salati , duk suka yi mishi sannu jiki a
mace yakalli agogon da ke mak'ale a bangon d'akin zumbur ya mik'e ya fad'a toilet domin d'auro
alwala , shigarsa bayin kenan Aminullah ya bud'e k'ofar d'akin tare da sallama suka shigo da
Malam
Cike da girma-mawa suka gaggaisa Malam yayi musu ya mai jiki , Saifullah ya kalli Aminullah
domin Neman k'arin bayani suna had'a ido yayi sauri yuyar da kanshi ,
Murfin k'ofar bayin aka bud'in tun da Malam yayi arba da wannan fuskar gaban shi yayi
mummunan fad'uwa ya tabbatar da ba'a zaune yake ba da sai ya fad'i k'asa warwars lallai
Ummi tayi namijin k'ok'ari
Da k'ar Malam ya had'o miyon bakin shi yace " *BAWAN ALLAH?*"
Sosai sunan ya daki k'ok'on zuciyar Abdallah amma Sam Brain d'in shi ta kasa functioning ,
D'aga idanun shi yayi ya d'orasu kan Malam take tsigar jikin shi ya tashi , brain d'in d'in shi ta
fara mishi flash back nan take ya runtse ido , Dr Ahmad na ganin haka ya danna k'ararrawar
kiran likita zame wa yayi zai fad'i sukayi sauri suka tare shi.
*sorry for this one wayata tana hucking*í ½í±ˆ
.
[1/21, 12:18 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*
*MRS NN ONEí ½í²‹*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
*This page dedicated to you Bawan Allah fans , nagode da addu'oin fatan alkhairi da kuke
agareni lallai Ku k'awayen arzik'i ne nagode Allah ya barmu tare ya sadamu aljannatul firdau*❤
*k'awa*
3⃣7⃣
Gaba d'aya Abdallah ya birkice wasu irin hotuna yake gani black and white wa D'an da bai San
inda suka samo asali ba .
Ko da likita yazo tambayoyi ya runk'a mai amma yace bai San komai ba , haka suka sake masa
allurar bacci ya koma .
Har zuwa wannan lokacin Malam yana asibin mamaki duk ya cika shi .
.
Dr Ahmad ya maida duban shi ga Malam yace " Malam dama ka sanshi ne?"
Murmushin takaici Malam yayi yace "Abdallah haihuwar shi ce kawai banyi ba , kuma har yau
bana bamban tashi da 'ya'yan da na Haifa da ciki na"
Shiru d'akin yayi Malam ne kawai da Dr Ahmad suka san mai suke cewa amma Saifullah da
Aminullah gaba d'aya Kansu s juye yake .
Malam ya kalli Aminullah tare da nuna Abdallah dake kwance yace "wannan shine mijin Ummi
da ya b'ata shekara biyar da suka wuce "
Wayyo Allah zo kuga tashin Hankali a idon Saifullah gaba d'aya yaji maganar ne tamkar saukar
aradu , tabbas da za'a gwada jininshi alokacin da ansha mamaki , domin bai taba zato ba balle
tsammani,
Cikin murya mai cike da firgici yace " Malam mai kake nufi ne wai ?"
Malam bai ce komai ba domin baisan kuma ya zaiyi ya fahimtar dashi ba .
Dr Ahmad yace "Saifullah ka kwantar da hankalinkA gobe insha Allah za kaji komai yanzun dare
yayi "
Sannan ya juya ya ce "Aminullah ka maida Malam gida gobe zamu je gidan dukan mu in Allah
ya kaimu"
Nan suka mik'e Malam yaje wajen kan Abdallah ya tofa masa addu'oi sananan sukayi sallama
amota kuwa Aminullah ne ya damu Malam da tambayoyi domin shi duk ya k'agu yaji gaskiyar
al'amari, amma Malam yak'i Sam suyi magana .
A can gida kuwa su Ummi sun kasa sun tsare , har da Umar ma da ya shigo gidan bayan fitar
su Aminullah da Malam , tun suna tsaye har suka gaji suka zauna amma babu su babu labarin
su, har 10:30am .
Mama ta kalli Umar tace "Umar kaje gida mana kaga dare yayi "
" Mama ko naje gida bazan iya yin bacci ba"
Mama zatayi magana kenan sai sukaji k'arar tsayuwar mota , Umar yace "Mama Bari na duba
nagani"
Ummi kuwa zuciyarta sai k'ara bugu takeyi.
Umar na fita Aminullah har ya ta tada motar shi yayi gaba Malam kuma ya d'auki hanyar k'ofar
gidan shi, cikin sassarfa Umar ya k'arasa gurin Malam yana fad'in "sannu Malam"
"Yauwa Umar "
"Malam Abdallah ne kuka gani ko?"
Murmushi Malam yayi sannan ya dafa kafad'ar Umar yace " ka kwantar da hankalinka gobe
insha Allah zasu zo sai muji koma wane ne"
Ajiyar zuciya ya sauke sannan sukayi sallama , shikuma Umar ya koma gidan su Hafsa dan
sanar dasu yadda sukayi da Malam,
Ranar dai kowa kwanan zullumi yayi musamman ma Ummi da take ganin ga k'oshi ga kwanan
yunwa.
*Da safe*
Misalin k'arfe Tara na safe Abdallah ya fito wanka ya shirya cikin shigarshi ta k'ananan kaya
maroon din T-shirt ce ajikinshi sa navy blue d'in jeans kalar yayi matuk'ar amsar jikinshi Kasan
cewar shi faran saurayi kan kujerar robar da aka tanada dan masu dubiya ya zauna tare d'aukar
wayarshi ya fara dannawa .
Aminullah ne ya bud'e k'ofa ya Shiga tare da sallama , batare da ya juyo ba ya amsa sallamar ,
"Bros Dr yace mu same shi awaje " cewar Aminullah yana kallon Abdallah da ya kyab'e fuska
"Ina zamu je ne?"
Aminullah zai yi magana kenan wayar Abdallah ta fara ringing , cikin sanyi ya d'aga wayar gami
da sallama , bayan D'an shiru kuma sai ya mik'e ya kashe wayar ba tare da yace komai ba ,
Aminullah ne ya d'auki wata 'yar k'aramar traveling bag dake gefen gadon suka fita
A parking space na cikin asibitin suka tarar da Dr Ahmad da Saifullah suna jiran su Saifullah ya
Shiga mazaunin driver , Abdallah ya Shiga b'arayin me zaman banza , yayin da Dr da Aminullah
suka Shiga baya .
Tunda suka d'auki hanya Abdallah ya tattare hankalin shi da natsuwar shi yaba titi amana,
runtse idanun shi yake yi yayinda wasu hotuna keta masa yawo a kwanyar shi wasu kalamai
suna ta mashi yawo a dodon kunan shi , hannu ya sa ya toshe kunan shi idon shi kuwa runtse
shi yayi kamar k'aramin yaro , duk suna lura dashi amma Sam Dr ya hana su tab'a shi sai dai
suka bishi da fuskar tausayi , har suka iso k'ofar gidan bai ma San sunzo ba , sai da Saifullah
yayi mishi magana sannan d'ago jajayen idanuwan shi ya kalle shi
"Mun iso fa" cewar sai ya bud'e murfin motar zai fita , shima murfin ya bud'e ya fita k'ofar gidan
su ya ci karo dashi take wasu abubuwa daban daban suka runk'a yi mishi yawa akai gaba d'aya
ya daina ganin zahiri sai bad'ini
Malam dake ta karatu da almajirai ba shiri ya sallame su suka tafi sannan ya k'araso fuska
d'auke da farinciki
Umar ya fito daga cikin gidan su Hafsa sakamakon tsayiwar motar da yaji yana fitowa yayi arba
da Abdallah jingine jikin mota aiko da gudu yaje ya k'wak'wu-meshi , shi dai Abdallah ji kawai
yayi an rungume shi , shikam Umar ji yake kamar in yasaki Abdallah bazai sake ganinshi ba ,
rungumar da Umar ya ma Abdallah sai da yajiyo bugun zuciyar shi domin yi take zamar zata
fasa k'irjin ta fito
Cikin dauriya Abdallah ya b'amb'are Umar daga jikinshi , kallon juna suke ido cikin ido , da
k'yar Abdallah ya k'ak'alo wani murmushi ya jefa asaman fuskarshi , Umar ya kalli Abdallah
cikin kewa yace "nayi kewarka aboki na , kai kam ko nema na baka yi "
Shikam Abdallah bubbuga kafad'ar Umar kawai yayi amma Sam bai ma San koshi waye be .
Malam ne ya katsesu da cewa " mu Shiga daga ciki ".
Hafsa da tafito ta basu izinin Shiga sai kallon Abdallah take kamar taga sabon hallita , suna
had'a ido dashi ya balla mata harara azuciyar ta tace"bari na kama kaina tun kafin ya jizga ni
dan naga ya k'aro wulak'anci"
Juyawa tayi sukuma suna binta abaya tana tafe tana tuntub'e , shiko Aminullah sai dariya yake
kwasa aranshi yace ya samu na tsokana
[1/22, 5:11 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*
*MRS NN ONEí ½í²‹*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
38
Hafsa na k'arasa Shiga gida ta runtuma aguje sai d'akin Ummi ko sallama bata tsaya yi ba ta
yaye labule ta afka , Ummi dake ta cikiniyar sa kaya Wanda da alama yanzun ta fito wanka ta
kalli Hafsa tace "ke dai banga ranar da zaki girma ba ke kullum aguje kamar y'ar gudun hijira "
Hafsa ta had'a girar sama da ta k'asa tafara magana cikin hasala "ke fa gaba d'aya ba'a miki
gwaninta daga zuwa yi miki albishir sai Ki hau gwasale mutum , to ni kinga tafiya ta nama fasa
fad'a " ashagwab'e ta k'arasa maganar
Cikin marai-raice murya Ummi tace "ayya *k'walli* ta yi hak'uri zo Ki fad'a min "
Hafsa ta had'e rai tace " a nawa ?,"
Ummi tayi dariyar mugunta tace "a arba'in"
Du Kansu suka kwashe da dariya .
*Bawan Allah* kuwa tunda suka shigo gidan ya k'ara birkicewa musamman ma da yayi arba da
Mama tana shimfid'a tabarma k'uri ya k'ura mata ido tamkar mai son ya fahimci wani Abu amma
Sam ya kasa
Saifullah ne ya jashi ya zaunar dashi, har wannan lokacin idonshi yana kan Mama , ko da
Mama ta juyo suka had'a ido sai da taji gaban ta ya fad'i , azuciyarta tace "tabbas wannan
bawan Allah ne"
Bayan 'yan gaishe-gaishe Mama ta mik'e taje ta kira su Ummi domin ayi komai a gaban su ,
Ummi ce agaba Hafsa tana binta a baya ahankali take takun ta kamar me tsoron kar ta taka
wani abun , dai dai lokacin Abdallah ya juyar da fuskarsa b'angaren , tundaga k'afafuwan ta
yake kallon ta har sai da ya dire idanuwan shi cikin Nata Sam yakasa daina kallon ta wani Abu
yake ji tamkar magnet yana fizgarshi zuwa gareta badan ya danne zuciyarshi ba to tabbas zai
iya mik'e wa zuwa gareta , cikin natsuwa tagaishe sannan ta nemi wuri chan gefe ta rakub'e
Malam ya kalli Aminullah da yayi shiru amma idanuwan shi k'yar akan Ummi yayi murmushi
kawai ya maida duban shi ga Saifullah da kawai pretending yayi amma zuciyar shi Sam bata
mishi dad'i ,
Malam ya Kali Dr Ahmad yace " Alhaji zamuso muji ya akayi ka had'u da Abdallah?"
Cike da fahinta Dr Ahmad yafara magana sai alokacin Abdallah ya maida dubanshi wurin, Dr
yace" akwai wata rana ina hanyata ta dawowa kano daga Kaduna Kasan cewar tafiyar asuba
nayi k'arfe shida da Rabi nakusa Shiga kano ina daf da shiga gari sai naga cincirundon jama'a a
gefen titi har zan wuce kuma sai naji zuciyata tana fizgata akan naje wajen koda na fita nayi
parking mota ta a gefen titi na tsallaka abunda nagani ba k'aramin tayar min da hakali yayi
mutane ne kwance kamar matattu cikin gaggawa na kira motar asibitin my nan da nan sai gasu
sunzo akwashe su sai asibitin aminu kano , to nikam tunda na