Showing 12001 words to 15000 words out of 43330 words

Chapter 5 - Bawan Allah Book Compelet Maman Muhammad

01 Aug 2026

445

,


Bayan sun idar da sallar asuba ne Abdallah ya tuna da wani Abu bashiri ya mik'e kamar an
tsikare shi yace ma Umar bari yaje ya dawo


🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔
[12/22/2017, 12:23 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*


*MRS NN ONE💋*


*INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN*


*KULLU NAFSIN ZA'IK'ATUL MAUT ( dukkan wata rai sai ta d'and'ani mutuwa)*

*AMADADINA DA SAURAURAN 'YAN UWANA WRITERS NA PURE MOMENT OF LIFE
WRITERS MUNA MIK'A SAK'ON TA'AZIYYAR MU GA 'YAN UWAN ZAINAB MUHAMMAD
(ZEE SOBA) ALLAH YAJIK'ANTA YAYI MATA RAHMA ALLAH KA GAFARTA MATA ALLAH KA
KYUTATA MAKWANCIN TA ALLAH KA WANKE TA DA RUWA MAI SANYI DA K'ANK'ARA
ALLAH KA GOGE MATA ZUNUBAN TA KAMAR YADDA KAKE GOGE FARIN TUFA DAGA
DATTI , KA MUSANYA MATA GIDA MAFI ALKHAIRIN GIDAN TA , DA IYALAI MAFI
ALKHAIRIN IYALAN TA ALLAH KASHIGAR DA ITA CIKIN AJANNAR KA , KAKARETA DAGA
AZABAR WUTA . AMIN YA ARHAMARRAHIM*�



® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ �ųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com



17++++18


Abdallah na fita be zame ko ina ba sai tasha cikin sa'a saura mutum biyu motar ta cika , wata
mace ce tazo ta shiga sannan driver ya ja suka wuce k'auyen su Abdallah,


Yana sauka gidan Baban Hafsa ya wuce yana zuwa yayi sa'a ko ya sameshi a gida bayan
gaishe-gaishe ya gaya masa abun da ke damun sa sannan ya ce yazo ne ya bada jinginar
gonar mahaifiyar su ta gado domin su samu kud'in da zasu biya ama Ummi aiki ,

Bamusu kawun nashi ya amince sukaje wurin me gari aka samu Wanda zai amshi gonar aka
buk'aci Abdallah ya fad'i ko nawa yake so abashi , yace dubu d'ari uku nan akayi yarjejeniya
aka mik'a mai kud'i daganan yayi godiya ya kamo hanyar zaria ,


Ya shigo Zaria bayan la'asar gida ya wuce Hafsat kad'ai ya tarar a gidan tana ganinshi ta taso
"yaya ya jikin Aunty Ummi?"

"Da sauk'i "kawai ya iya ce mata ya karb'i mukullin d'akin su ya shiga, dubu d'ari da hamsin ya
d'auka sannan yayi sallolinshi a gida ya kulle d'akin ya tafi da mukullin , yana fita mashin ya hau
har k'ofar asibitin ya k'arasa shiga ciki ,

Umar ne ya hango shi yayi sauri ya k'araso yana fad'in "ustaz ina kaje ne har yi ma Ummi aiki
baka nan"


Murmushi yayi yace "naje Neman kud'i ne "

"Abdallah Dan Allah karka je ka sama kanka damuwar da ta fi k'arfin ka , kaga yadda ka koma
kuwa daga jiya zuwa yau?"


"Umar damuwa dole ce agareni , kanaganin 'yar mutane zata mutu ta dalilin gazawa ta dole na
shiga tashin hankali "


"Hakane amma Kasan rayuwa da mutuwa duk na Allah ne idan kwanan mutum ya k'are ba
tsumi ba dabara dole sai ya tafi"


"Allah kasa mudace " Cewar Abdallah yana rik'e hannun Umar suka k'arasa ciki


Har a lokacin bacci take yi Mama ce kad'ai AD'akin ta zabga uban tagumi ga carbi tana ja , har
suka shigo ma bata sani ba ,


Sai da yace "sannu Mama "

Da sauri ta d'ago kanta tana fad'in "Bawan Allah ina ka jene?"


"Mama naje Neman kud'i ne kuma Alhamdulillah na samu"


"Ina ka samo kud'i?" Cewar Mama tana zare ido

"Bashi na samo kuma Dan Allah karki d'aga hankalin Ki nan bada jimawa ba zan mayar musu
da kud'in su"

Shiru Mama tayi tana tunanin ina d'anta zai samo wad'annan kud'in harya ya biya , azahiri kuma

saita bishi da fatan alkhairi,


Mik'e wa yayi yace ma Umar suzo suje su biya kud'in su dawo dayake akwai receipt a hannun
su direct bank din cikin asibitin suka je suka biya kud'in , tare da siyan magunguna suka dawo ,


Satin su d'aya a asibitin aka sallame su duk wannan lokacin Abdallah be gayama mahaifiyar shi
cewar gonar ta ya siyar Dan ya sama matar shi lafiya ba ,


Ummi kuwa kyakyawan kulawa take samu awaurin mijinta da Mama Hafsa ma ba'a barta a
baya ba domin kullum ita ke kai mata ruwan wanka , bayan sati biyu da sallamo Ummi Abdallah
yaje ya samu mahaifiyar shi ya sanar mata da gaskiyar inda ya samu kud'i , amadadin ya tayi
fushi sai yaga murmushi a fuskarta tace " Abdallah banida wani magaji aduniyar nan sai kai duk
abinda na mallaka halalin ka ne , Allah yayi maka albarka , ita kuma Allah ya bata lafiya , "

"Amin Mama na gode"

"Yanzun ina sauran kud'in suke?"

"Suna d'aki"

"To Sana'a ya kamata ka fara"

"Eh hakane Mama ni anawa tunanin me zai hana inrunk'a zuwa kano ina saro kayan provision "

"Hakane amma shago fa ?"

"Insha Allah ba matsala zan ma hadi me shago magana naji yace zai saida nashi zai koma
k'auyen su".


"To shikenan Allah ya bada sa'a "

"Amin , bari naje na nemi Umar naji ya tafiyar zata Kasan ce mana"

"To adawo lafiya "

"Allah yasa" nan ya fita ,

Ya samu Umar yana shirin fita kasuwa inda yake tsaron shago,

Nan suka sauna suka tattauna suka tsaida ranar laraba zasuje kano , danan suka wuce gurin
me shago suka fara ciniki Wanda da k'yar ya karb'i dubu ashirin ,



*LARABA*

Da safe bayan sun gama karyawa ,Abdallah yayi wanka , Dan sunyi da Umar karfe goma zasu
bar gida , Abdallah ne ya d'aga waya ya kira Umar yake sanar masa da ya shirya Dan haka
yafito su tafi ,


Bayan ya aje wayar ne Ummi dake kwance jikin Abdallah tace"yaya ji nake kamar karka tafi"


Murmushi yayi yace"bakiso naje Neman kud'i ko?"

"A 'ah ba haka bane kawai dai..."sai kuma tayi shiru


"Kawai mene ? K'arasa mana"

"Kawai inajin jikina ba dad'i ne?

Cikin sauri yace"bakida lafiya ne?"

"Lafiya ta k'alau yaya kawai dai tafiyar taku ce bana jin dad'in ta a raina"


"Kiyi hak'uri Ummi na nima yau tunda na tashi nake jin jikina duk ba k'wari kiyi min addu'a"

Wata k'walla ta share idon ta sannan tayi masa addu'ar fatan alkhairi , suna fitowa d'aki Umar
yana shigowa gidan , yana ganin su ya saki wani murmushi, nan suka gaisa da Ummi sannan
suka lek'a d'akin Mama fatan alkhairi tayi musu sannan suka fita Ummi sai da ta raka su k'ofar
gida sannan Abdallah yace mata ta koma amma ta nok'e kafad'a ita baza ta koma ba

Azaure ta tsaya tana hangen su har sai da suka b'ace ma ganin ta sannan ta koma gida jiki a
sanyaye , bata tsaya fira ba ta wuce d'akin ta tana ta juyi a gado irin wasan da suka yi jiya da
Abdallah ne ya ke ta mata yawo a k'wak'walwa sai murmushi take tana dad'a matse pillown
data rungumo

Abdallah da Umar kuwa bayan sun rabu da Ummi Umar yace ma Abdallah akwai mutumin da
Alhaji Bello yake siyan kaya awajen shi a kantin kwari Dan haka suje chan d'in ,


Sun isa kano azahar tayi kawai sai suka tsaya wani masallaci suka yi sallah sannan suka
k'arasa cikin kasuwa dayake Umar yasan shagon kai tsaye chan suka nufa,


Alokacin da suka isa ana sauk'e ma Alhaji Mati kaya Dan haka ya rok'esu da sujira agama Dan
kar lissafi ya kwace masa ,

Bayan ya gama ya hau sallamar mutane sannan ya waiwayo kan su Abdallah lokacin had
la'asar ta wuce , siyayyan kayan ciyaciye na yara su suka fi yawa sannan su omo da sabulai
kaya dai sosai ya had'o , ko kafin su gama magrib tayi Umar ya kalli Abdallah ya ce "ustaz dare
fa yayi mu kwana a garin nan da safe sai muyi sammako"

"Gaskiya bazan iya ba yau duk dare gida zan kwana "

Umar yayi dariya yace " kafiso kullum ka jika gaka ga 'yar k'anwar ka"

"To ya San ranka , dalla Malam wuce muje"

'Yan dako biyu suka samu suka d'aukan musu kayan sannan suka fita kasuwa suka hau
adaidaita suka nufi tasha suna shiga wata motar Zaria tana tashi Dan haka dole sujira ayi sabon
Lodi ,

Sai k'arfe Tara sannan motar ta cika akayi duk abinda ya dace mota ta tashi bayan sunyi kamar
tafiyar awa d'aya kawai sai motar ta mutu da kanta , nan fa driver yayi duk iya dabarun shi tak'i
tashi gashi sunyi nisa da gari gasu a k'ungurmin daji,

Sunan nan tsaye masu salati nayi masu zagin driver nayi wai lefinshi ne da bai duba mota ba ya
kwaso su ,

Abdallah kuwa shiru yayi kamar ruwa ya cishi,

Kwai sai suka ga ana ta kashe musu ido da wani haske me shiga k'wak'walwa , wata
razananniyar murya suka tsinkaya ana ce musu "sit on your kneels!"

AI sai kowa ya hau salati Ashe 'yan fashi ne,

Haka suka ruk'a rashin mutumci harzuwa wannan lokacin Abdallah yana cikin motar be fito ba
sai da wani yazo ta jikin window ya hasko ko shi yace "oga kaga wani D'an iska ana magana ya

zaune , "


Ogan yace fito min dashi na ragaje shi kawai zagayowa yayi ya damk'o wiyan Abdallah ya fito
dashi dai dai lokacin idon Abdallah yakai kan Umar dake kwance jini yana ta zuba a hancin shi
da alama suma yayi fincikewa yayi daga ruk'on da suka mai ya tafi wajen Umar aguje yana
fad'in "Umar meya same ka ta...." Wani irin zafi yaji Wanda saida jini ya fito ta hancin shi Ashe
bakin bindiga suka buga ma a kai

"Muzaka yi ma taurin kai to ba irin mu ake yima ba" haka suka yita dukan Abdallah duk da ya
suma basu k'yale shi ba , saida suka tabbata sunyi mishi babbar illa sannan suka k'yale shi

Matan kuwa Dama su biyu ne nan suka tasa k'eyar su suka tafi dasu mazan kuma suka barsu
kwance tare da k'wace duk wata dukiya dake tare dasu
[12/26/2017, 8:56 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*


*MRS NN ONE💋*

*This page is mine💃💃 💃💃happy anniversary to my self I hope you ga _ys will wishes me*_
😘🏌�♀


® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ �ųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com



Kasan cewar dare ne kuma wurin ba wurin tsayawar mutane bane shiya sa basu samu temako
ba sai da safe , wani me mota ne yazo wuce wa yaga mutane kwance kamar mattatu , nan da
nan ya d'aga waya ya kira 'yan sanda , ba b'ata lokaci aka kwashe su sai asibitin Aminu kano ,
direct emergency aka wuce da su ,

Da bincike da bincike kowa D'an uwan sa ya runk'a zuwa amma banda mutum biyu , wato
Umar da Abdallah , Umar ya farka sai dai be San inda kanshi yake ba , Abdallah kuwa har

yanzun bema ko motsa ba, likitoci suna iya k'ok'arin su akan shi domin duk ciki ya fisu shan a
zaba,



*ZARIA*


Ummi , Mama da kuma Hafsa kowa yayi cirko-cirko a tsakar gida , kowanan su da a binda yake
sak'awa acikin ransa , iya k'ololuwar tashin hankali suna cikin su ,


"Ummi sake Kiran wayar muji" Mama ta fad'i cikin wata murya me ban tausayi


Ummi jiki ba k'wari ta danna number Abdallah , still a kashe wasu hawaye ne suka sake yi
mata ambaliya a fuska ,

"Aunty Ummi swich up ko?"

Ita dai Ummi d'aga kawai tayi domin Sam ta kasa bada amsa ,


Haka suka zauna a wajen har kusan k'arfe biyu na dare , Ummi ce taga kukan ba zai fisheta ta
ba ta mik'e ta d'auki buta yau ko tsoron ba ta ji , ta nufi bayi , tana fitowa ta d'aura alwala duk sai
suka bita da ido , Mama a zuciyar ta tace "wannan ita kad'ai ce mafita"


Duk sai sukayi alwala suka shige d'aki, kowa ya kai kukan shi ga Allah Wanda shi kad'ai ne
buwayi gagara misali mai biyan buk'atun bayin sa,


Koda safiya tayi suna zaune a tsakar gida sunyi jigum gidan tamkar ba mutane ,

A haka Maman Umar ta shigo da sallama Wanda da ganinta ita ma Kasan batayi kwanan dad'i
ba , bayan sun gaisa sama-sama sai tace


"Wai yaran nan basu dawo bane? "

Mama cikin jimami tace"wallahi bamu gansu ba jiya kwana ne kawai ba muyi a tsakar gidan nan
ba "

"Inalillahi wa inna'ilaihir raji'un, ya Allah ka sa muji alkhairi" cewar Maman Umar

"Amin " duk suka amsa


Hafsa ce tace "Mama ya kamata aje a fad'a ma Malam ko da temakon da zai iya yi"


"Hakane Hafsa kinyi tunani me kyau , yanzun tashi kije Ki sanar mishi "

"To Mama" ta mik'e jiki ba kwari ta fita ,

Ummi kuwa wata alwalar ta sake yi ta nufi d'aki ,


Mama ta kalli Maman Umar tace " ina jin tausayin kaina ina jin tausayin yarinyar nan jiya haka
ta kwana banda kuka da sallah babu abin da take yi "


Maman Umar tace "wallah jibi yadda duk ta susuce , Ya Allah ka bayyanar mana da yaran"

"Amin" dukkan su suka amsa


Bayan Hafsa ta sanar ma da Malam halin da ake ciki ba shiri ya bazamo ya taho gidan Dan jin
cikakken bayani ,


Mama ta fara magana "wallah Malam tunda suka fita jiya babu su ba labarin su har yau"


"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un , ai ni Da naga ban gansu a masallaci ba da asuba inace ko
gajiyar hanyace , Allah ka bayyanar mana da su"

"Amin" kowa yace

Dai-dai nan Ummi ta fito daga d'aki Dan ta jiyo muryar mahaifin nata , ahankali ta tako gefen
Hafsa ta zauna tare da gaishe shi , bayan ya gaisa ya fara yi musu nasiha tare da kwantar da
hankali , gami da cewar" Idan har dare yayi basu dawo ba to gobe shida wasu almajiran shi
zasu tafi kano Neman su"
Nan dai sukayi godiya ya tafi ,

Mama ta kalli Hafsa ta ce "je Ki dama ma Ummi koko tasha magani"

"Mama nak'oshi"Ummi tace tana kifa kanta akan gwuiwoyinta


"Baki CI komai bafa Ummi rabon Ki da abinci tun jiya da rana shi d'in ma ba wani ci ka kayi ba
kina ta jagwal-gwalawa , "

Ummi dai shiru tayi

Maman Umar tace " haba Ummi Ki yi hak'uri ko kokon Ki sha kinga ba lafiya ce ta wada ce Ki
ba "

"To"kawai tace

"Ke Hafsa je Ki damo mata"


Wasa-wasa har dare ba wani chanji hakan yasa Malam ya nemi biyu daga cikin manyan
almajiran shi da su raka shi kano , safiya nayi kuwa suka bazama,



*_kano_*


Tunda likitoci suka yi iya bakin k'ok'arin su akan Abdallah cikin ikon Allah numfashin shi ya
dawo amma kuma gashi nan kwance kamar gawa , wani Babban Doctor suka kari yazo ya duba
shi , koda yazo yaga Abdallah Sam ya kasa d'auke idanun shi a kansa , wani Doctor ne ya
matso kusa yana magana

"Ka sanshi ne Doctor?"

Shiru yayi yana tunanin abinda zai ce sai kuma yace"ina 'yan uwansa suke?"


Nan wancen Doctor din ya kwashe duk tsautsayin da ya faru da su Abdallah ya fad'a masa ,

Cikin tausaya wa Doctor ya ce "wannan yaron wani mak'oci nane , ayi masa duk abinda ya
dace",

Suka chanja Abdallah d'aki , ana fita dashi Umar ya farka , babu Wanda ya fara kira sai
Abdallah ,


Bayan ya D'an huta suka fara yi mishi tambayoyi kamar haka


Wani Doctor Usman ya fara cewa "ya sunan ka?"

"Umar" a tak'aice ya bashi amsar

"Inane garinku?"

"Zaria"

"Mekazo yi a kano?"


"Munzo Sarin kaya ne nida d'an'uwa na Abdallah"

Doctor Usman ya maimaita Kalmar "D'an uwa fa kace?"

"Eh" inji Umar yana dad'a kallon Doctor d'in

"To gaskiya duk cikin Ku ku goma da aka kawo babu Wanda 'yan'uwan shi basu zo ne manshi
ba sai kai"

"A'ah likita indai ina cikin asibitin nan to na tabbata Abdallah na ciki iyayen mu d'aya da shi "

"To mudai kai kad'ai ka rage mana anan "

Wani mugun fad'uwar gaba ne ya ziyarci Umar shidai yasan last seen d'inshi da Abdallah ya
ganshi cikin mota tsaye kuma yaji sanda d'aya daga cikin 'yanfashin yayi magana akan
Abdallah afili ya furta "innalillahi wa inna'ilaihirraji'un, Allah kasa ba sun tafi min da d'an'uwa na
ba"

"Maybe sunzo basu gane ka bane dubi yadda ka chanja kammani gaba d'aya" Doctor ya fad'i
yana nuna masa wani d'an k'aramin madubi


Daya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0