Showing 9001 words to 12000 words out of 43330 words

Chapter 4 - Bawan Allah Book Compelet Maman Muhammad

01 Aug 2026

443

zaki cire ba, ni ba zan baki kije kiyi
amai ba"

"Ayya yaya da gaske bana son Fushin ka bari na ciri"

Yaye hijab d'in tayi dai-dai wuyan ta sannan ta ce "na cire "

Hannu ya sa ya yaye hijab d'in , wata vest ce ajikin ta mai santsi da leshi agaban ta ta kwanta
tayi luf ajikin ta , kayan arzik'i ne ya tsaya kallo har yana had'iye wani yawu mak'wat gaba d'aya
imanin shi ya tafi awajen k'irjinta , ga dai su ba masu girma bane amma akwai d'aukan hankali,


Sai da Ummi ta kira Abdallah sau uku be jita ta ba , sam ita bata lura da inda yake kallo ba,

Tab'ashi tayi tana fad'in "yaya ina ta magana shiru"

Bece mata komai ba , ya sa mata maganin abaki dan gani yake ko magana yayi za'a gane halin
da yake ciki

Ruwa ya sanya mata a baki sannan ya k'ara janyo ta jikin shi , tana jin ya tab'a ta tayi sauri taja
baya , madadin ya kyale ta sai ma k'ara janyo ta da yayi ta kwanta a k'irjin shi yana shafa bayan
ta ahankali cikin wani irin salo yana fad'in

Yazo dai-dai saitin kunnan ta ya na rad'a mata"k'iyi hak'uri Ummi kishanye ko kya samu lafiya"

Sai da suka kusa minti goma a haka Abdallah dauriya kawai yake yi amma ga ba d'aya notin
jikin shi ya kwance

Ummi kam har ta fara bacci abunta bata ma San yana yi ba ,

"Ummi , Ummi"Abdallah yake kira a hankali

Cikin yanayin bacci tace "uwum Ummi na Ki barni ban gaji da jin d'umin jikin Ki ba " ta sa
hannun ta biyu ta zagayo dasu ta bayan shi tare da dad'a cusa kanta cikin k'irjin shi


"Inalillahi wa 'inna ilaihirraji'un"abinda Abdallah ke mai-maitawa kenan

Acikin ranshi ko fad'i yake" wannan yarinyar zata kashe ni"


Sun jima a haka bai kwantar da ita ba domin zaman ta a jikin nashi na rake mai wata damuwar ,


Ana haka ya tsinkayi muryar Hafsa tana fad'in "eh yana ciki"

Sallamar Umar da yaji duk ta dagula masa lissafi shiko sai rafka sallama yake ,


A hankali ya lallab'a ya kwantar da ita , sannan ya fita,

Umar na ganin shi ya saki wani murmushin rainin wayau , yace "kayi hak'uri fa na katse maka
hanzari"

"Ba hanzari ka katse min ba gudu" ya ja tsaki , yayi hanyar fita , binshi Umar yayi yana fad'in "ai
dai ka tsaya kaji me ya kawo ni ko ?"

Cikin murtuke fuska Abdallah yace" Umar muddin kana son zaman lafiya tsakani na da kai to
dole daina min shakk'iyancin nan naka , wallah har cikin raina bana jin dad'i shiya sa kaga gaba
d'aya na fita harkarka domin b'ata min rai kake"


Umar yace "uhum Bawan Allah kenan indai wannan ne mai sauk'i ne , amma babu yadda za'ayi
na ganka a cikin irin yanayin da na ganka a yanzun ban yi dariya ba"


"Mtsww yanzun dai gaya min meya kawo ka?"


"Dama Alhaji bello ne ya kirani yana ta Neman wayar ka be shiga shine ya bada wankin shi na
kawo maka , amma wai gobe yake so da safe zaiyi tafiya"


"Shikenan ba damuwa , ina wanki suke?"

"Suna nan tsakar gida na barsu "


Nan dai suka D'an yi fira sannan Umar yace " bari naje kasuwar nan kaji"

Sukayi sallama , Abdallah ya koma gida , Mama da Hafsa ne keta kiciniyar d'aura tuwon rana ,

yayi musu sannu ya wuce d'aki , kaya ya chanja zuwa wata tsohuwar T-shirt , ya nannad'e
k'afar wandon sa ya hau sana'ar shi ta wanki ,


Ummi kuwa ba ita ta farka ba sai d'aya saura , lokacin har Abdallah ya gama wankin shi yayi
wanka yana shirin fita masallaci tana kwance tana kallon shi sai da ya gama shirin shi ya fita
sannan ta mik'e ta d'auki bokitin ta da buta ta nufi rijiya , a nan waje ta tarar da Hafsa tana
kwasar tuwo
Ummi cikin tsokana tace "yau manya ne a kitchen d'in "

Hafsa ta juyo ta watsa mata wata harara sannan tace " kuma dole aci ko be dahu ba ba"

"Yi hak'uri maida wuk'ar" ta duk'a ta d'ibi ruwan ta sannan ta wuce bayi tayi wanka da alwala
tayi sallah sai da ta idar ne ma ta lura da kwanon abincin nan ta D'an yafita ta barshi ,

Hirar su Mama da Hafsa ne da taji ya sata fita don ta gaji da zaman shirun,
[12/20/2017, 9:27 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*


*MRS NN ONE💋*

*Dedicated to*
*MAMAN Tahir*
*Maman Hanan*
*Maman mamy*
*Maman adhil*
*Meenat*
*Rukkaya maijega*
*Amne*
*Aisha Muhd Namadina*
*Sadiya Illa*

Agaskiya sunan ku ba zai lissafu ba I really appreciate your kind and support *Ina mugun
k'aunar ku*�💋


*Thanks for your well wishes*💋

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ �ųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com



Page 13___14


Shiko Abdallah tunda ya fita be dawo ba sai dare yana dawo wa ya shiga d'akin Mama ya
gaishe ta sannan ya fita ya kwashe kayan wankin da yayi gashi yayi sa'a akwai wuta , kai tsaye
d'akin su ya nufa , yayi sallama ya shiga , Ummi ya samu kwance tana baccin k'aryan da ta
saba , be tanka mata ba ya shimfid'a sallaya ya hau gugan shi ,
Ita kuwa Ummi kallon mijin ta take yi cike da tausayi , azuciyar ta tace "shi ko gajiya baya yi?"


Abunda bata sani ba shine shima Abdallah hankalin shi yana kanta kuma sarai ya gane ba barci
take yi ba kawai sai ya fuske yaci gaba da gugan shi , har wajen shabiyun dare ,


Ummi ce tayi wata mik'a tamkar me yin bacci sannan tace "yaya fitsari nake ji"


Fuske wa yayi ya ce "kije kiyi mana"

"Wallahi tsoro nake ji"

"Duk tsoron da kike ji da zaran kinyi addu'a zai tafi, ko baki iya addu'ar bane?" Ya k'arasa
maganar kamar zeyi dariya


Zumb'ura baki tayi cikin shagwab'a tace"na iya mana"

" to sai kije kiyi kafin Ki min shi anan"


Ai sai ta hau shura k'afafuwa ita ala dole sai ya raka ta,


"Ya isa haka Sarkin shagwab'a tashi muje "

Zumbur ta mik'e tama manta da d'aukan buta Dan fitsarin ya matseta sosai , Abdallah ne ya
d'auki butar ya bita da shi,


Bayan ta gama ta fito alwala ta d'auro sannan yayi gaba tana bin shi a baya kamar rak'umi da
akala


Tana shiga d'aki ta hau katifar ta tayi addu'oi ta shafe jikinta dashi sannan ta kwanta , nan kuwa
bacci yayi awon gaba da ita ,

Shiko Abdallah bayan ya gama gugan shi alwala yayi , yayi nafilfili sannan ya kwanta ak'asa ,
bayan ya kwanta kuma me ya tuna oho ya mik'e kamar an tsikare shi ya lallab'a ya kwanta kusa
da Ummi ya D'an janyo ta jikin shi kad'an , ita ko mage Sarkin son jiki ai sai ta k'ara shige masa
,

Can acikin baccin ta take jin wani Abu yana ratsa ta , tadai ji kamar ana mata waiwayi , har wani
D'an zillo take , bata k'ara dawo wa hayyacin ta ba sai da taji yana k'ara mulmula ta, cikin
fargaba ta cire hanunshi da ke kan k'irjin ta ,


Shi kuma kunya ce ta kama shi yaji kamar k'asa ta tsaye ya shige , kawai sai ya juya mata baya
,


Ummi ta kira shi a hankali " yaya?"

Da k'yar ya iya cewa "uhum"

"Dan Allah kada kayi fushi dani da gaske tsoro nake ji"


Abdallah najin ta ce haka a zuciyar shi sai yayi hamdala yace "bari na buga sabon wasa" ya
k'arike da murmushi

Juyo wa yayi ya kalle ta sannan ya ce "idan bakya so nayi fushi da ke to Ki barni na gama
abinda na fara"

"Yaya da zafi fa"

"Karki damu zanyi miki a hankali ba zaki ji zafi ba "

Da haka ta yarda yana ta wasa da ita a hankali har bacci yayi awon gaba dasu ,


Da safiya tayi Ummi kunya Abdallah kunya , shi atunanin shi zata gaya ma Hafsa abinda yayi
mata shi yasa yak'i sake wa ,

��������


Lokaci yana ta tafiya yanzun auran Abdallah da Ummi ana Neman wata biyu , kullum zaiyi 'yan
wasanninshi da ita domin wai a cewar shi tausayi take bashi k'aramar yarinya ce ,

Ummi ce kwance akan cinyar Abdallah yana yi mata tsifa duk da ba iyawa yayi ba amma tasa
daru ita sai ya mata ,


Bayan ya gama na ta ce "yaya juya bayan ka kaga wani Abu "


Shi ko yace "a ina?"

"D'an duk'awa za kayi wani Abu zan cire maka"

Juya wa yayi yace" gani cire min"


AI sai ta d'are bayan shi tana fad'in "na mishi wayau" harda gwalon ta


Murmushi yayi yace "sauka min abaya ke kullum ba kya girma"


Nok'e kafad'ar ta tayi a lamar A'ah


"Ummi kin cika rigima kamar wata 'yar yaye"


Dariya tayi tace "ka manta yaye na aka kawo maka"


Juyo da ita yayi yace "yarinya karki damu naku sa yaye Ki" ya k'arike yana kashe mata ido

d'aya


Duka ta kai mai abaya tana fad'in" wallahi ni bana so"

Dire ta yayi yana dariya yace "wannan kuma ke kika sani ni na tafi masallaci"


Cikin dare suna cikin barci manne da juna kamar tip da tyre sai Abdallah yaji motsin Ummi yayi
yawa , janyo ta yayi ya sake k'ank'ame ta yana fad'in "Ummi Ki natsu mana"


Sai da tayi wani D'an k'ara tace "wayyo yaya cikina zan mutu"

Zumbur ya mike ko da ya duba ta Ashe ta galabaita sai murk'usu take yarik'e ta yana fad'in "ina
ne " amma ta kasa magana , kwantar da ita yayi sannan ya hau Neman maganin ta cikin kaya
be sha wahala ba ya gansu cikin hanzari ya d'ebo ruwa ya d'aga ta ya na bata yana shafa
bayan ta ahaka har ta shanye ,
Ahankali taji ciwon na sauka tare da wani bacci , a haka ya k'arasa baccin da ita a nannad'e
ajikin shi,


Da safiya tayi ya je ya gaida Mama ya ke gaya mata ciwon Ummi ya tashi Dan haka zai je
kasuwa ko zai samu dako , ya kaita k'aramin asibiti ,


Mama tayi mishi fatan alkhairi ya fita a hanya ya gamu da Umar shima kasuwar ya nufa bayan
sun gaisa Umar ya D'an tab'a shakk'iyyancin shi sannan yace "ustaz sai ina haka"

Nan Abdallah ya gaya mishi dalilin fitowar shi gida Dama inda ya yanufa


"Allah Sarki Allah ya bata lafiya"

"Amin "Abdallah ya amsa

"Dama yau za'a sauke ma Alhaji Bello kaya a store d'in shi , yanzun ya kirani kayan sun iso
muje mu rok'e shi ya bamu kayan mu sauke sai ya biya mu"

"To" kawai Abdallah yace Dan shi mafita kawai yake nema

Da suka je suka samu Alhaji Bello be hana su ba ya ce suyi domin shi mutum ne tausayi


Suna cikin kwashe kayan ne , wayar Abdallah ta hau ruri , bak'uwar number da ya gani sai da
gaban shi ya fad'i

Yana d'aga wa muryar Mama tayi mai sallama tana fad'in " Abdallah ka dawo gida Ummi ba
lafiya" Mama tayi maganar cikin muryar kuka sannan ta katse wayar


Juyawa yayi a dabur ce yace "Umar jikin Ummi ya tashi" AI sai ya kwasa a guje

Shima Umar ya runtuma ya bishi


🙆�♀🙆�♀🙆�♀🙆�♀🙆�♀🙆�♀🙆�♀🙆�♀
[12/21/2017, 1:12 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*


*MRS NN ONE💋*

*Dedicated to Bawan Allah fans , kusani ina sonku ina k'aunar kuma saboda ku nake rubuta
wannan labarin , Allah ya bar zumunci ya k'ara mana dank'on soyayyah�🏹 one luv*🏌�com


® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ �ųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com



15+++16


Koda suka k'ara sa gida Ummi a sume take bata San ma inda kanta yake ba , Mama na rik'e da
ita ita kuma hafsa tana duk'e gaban Ummi tana kuka tana fad'in "Dan Allah Aunty Ummi kar Ki
tafi Ki barni inkika mutu bansan yadda zanyi ba "

Hankalin Abdallah yayi k'ololuwa gurin tashi , kasa yin komai yayi , Umar ne yayi k'arfin halin fita
waje a guje cikin sa'a kuwa yaci karo da me Napep nan ya tsayar da shi ya gaya mishi asibitin
da zai kaisu sannan ya juya dashi suka koma , inda Umar ya bar Abdallah nan ya dawo ya
same shi , dafa kafad'ar shi yayi yace "aboki ga me Napep can na samo a waje ku kama ta ku
saka"


Haka nan jiki ba k'awari suka saka ta a napep suka nafi wani primary health care da yake kusa
da su ,


Suna zuwa wani likita ya duba ta yace musu ba zasu iya yi mata komai anan ba saboda ba
suda kayan aiki , nan likitan ya rubuta ta musu transfer zuwa A B U teaching hospital dake
tudun wada , hakalin kowa ya k'ara tashi sai alokacin ne Umar ya d'aga waya ya sanar ma
Malam abinda yake faruwa yace gashinan zuwa shiko Abdallah ya zama kamar photo domin
D'an zaman da yayi da Ummi ta riga ta zama wani jigo na rayuwar shi, tunanin shi d'aya idan ya
rasa Ummi ba Wanda zai k'ara bashi 'yarshi ya aura , shi yasa kullum idan ya tuna da Ummi
yake k'ara sonta gashi ita kuma halin da take ciki ,


Dai-dai nan Mama tazo ta tab'ashi tare da cewa " kamata muje"

Kasan cewar wurin ba'a rasa abin hawa yasa suna fita suka samu napep sai tudun wada ,


Suna zuwa akayi emergency da ita nan ma likitoci suka shiga aikin su , bayan awa biyu wani
likita yazo ya tambayesu sune 'yan uwan Zainab Kabir? Suka amsa masa yace su biyo shi
office d'inshi


Bayan suje office d'inne ya basu izinin zama sannan ya fara bayani cewar "wani k'ari ne ya fito
mata a gefen k'odar ta kuma yayi girma Dan haka dole ayanke , amma kuma ba zamu iya yi
mata aikin nan ba dole zamu tura ta Babban asibitin mu dake *Shika* Dan haka ku shirya"


Tunda doctor ya fara maganar Abdallah ke karanto "Inalillahi wa inna ilaihirraji'un"


Bayan fitowar su daga office d'in Mama tace suje suyi sallah , Hafsa kuma ta koma gida tunda
sun bar gidan ba kowa ,

Bayan Abdallah da Umar sunyi sallah ne sai Umar yace "ustaz bari naje gida na dawo ba
jimawa zanyi ba"

Kai kawai Abdallah ya d'aga masa , sannan Umar ya tafi ,


Yana zuwa gida ya fasa asusun da yake Tara kud'in auren shi duk da dai beda budur war��


Ya fito kenan zai fita sai Maman su ta kirashi "ina zaka je ne haka?"
.

Nan ya Sanar da ita meke faruwa , ita tace bata ga ta zama ba,


Ko da suka koma asibiti sun tarar da Malam da uwar gidan shi can Wanda har yanzun ba'a
basu ikon ganin Ummin ba


Daf da la'asar wani likita yazo yace ga Ambulance cen suje su shiga za'a wuce da Ummi Shika ,
Umar ne yaje yayi clearing komai ba tare da sun sani ba ,nan suka d'unguma suka wuce asibitin


Nan ma wani gwajin aka sake yi likitoci suka tabbatar da lallai saidai ayima Ummi surgery gobe
domin abin yana gab da fashe wa kuma idan ya fashe mutuwa zatayi ,


Abdallah najin hakan yayi sauri yace "likita kuyi duk abinda ya kamata ni zan biya kud'in"


Kowa ya juya ya kalleshi tare da mamakin abin yace

Doctor yace shikenan ba damuwa ,


Abdallah ya sake cewa "kud'in zasu kai kamar nawa ?"

"Zaku iya kashe kamar dubu d'ari da goma "

"Shi kenan doctor kuyi duk yadda ya kamata"

Mama dai suman tsaye tayi da jin kalaman D'an nata ,

Umar kuwa cewa yayi "Allah yasa abokina ba haukace wa kayi ba"

Juyawa yayi ya kalli Umar yayi masa wani murmushi me wuyan fassara


Malam ne yayi k'arfin halin cemai "Bawan Allah Kasan me kake fad'a kuwa ?"


D'aga kanshi yayi alamar "Eh"


"To ina zaka samo wannan mak'udan kud'in"


Cikin sanyin murya yace"wallah nima bansan inda zan samu ba amma ina rok'on Allah ya bud'a
min hanyar alkhairi kafin safiyar gobe"


Malam ya jinjina kai


Tunda Abdallah ya shiga masallaci sallar magrib ya duk'ufa sallah da addu'ar Allah ya kawo
masa mafita dashi da Umar kwanan tsaye suka yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0