Showing 6001 words to 9000 words out of 43330 words

Chapter 3 - Bawan Allah Book Compelet Maman Muhammad

01 Aug 2026

442

yana fad'in

"Ina wuni Mama ?"

"Lafiya lau " ta fad'i yana k'ok'arin mik'e wa zaune

Sannan ta k'ara cewa "ya jikin naka?"


"Alhamdulillah naji sauk'i"

Nan suka D'an tab'a fira sannan Mama tace mishi" su zasu shiga su kwanta dare yayi "

Mik'e wa yayi yaje kusa da hafsa ya shure ta da k'afa sannan yace " ke baki iya ma mutane
sannu bako?"

Cikin murya me kama da ta barci tace "yaya barci fa nake"

"Dallah rufe min baki tunda ga waje nake jiyo hirar Ki Ki ce min wai barci kike yi"

Mama kuwa tunda suka fara ta kakkab'e tabarmar ta ta shige d'aki

Yana ganin mama ta shige ya juya ya kalli hafsa "to uwar gulma ko anan zaki kwana ne?"

Pillow d'inta d'auka ta runtuma d'aki aguje.


Tsaki yaja , ya nufi k'ofar d'akin shi , yana isa ya d'aga labulen tare da sallama , mutum ya gani
kwance cikin hijab cire takalman sa yayi ya k'arasa shiga d'akin ,


Azuciyar shi yace "lallai ma wannan baccin ta ma take sha"

Pillow ya ja ya kwanta ak'asan Leda , can dai yaji bazai iya hak'uri ba yana son ganin wace ce
amaryar tashi , zaga ya wa yayi ta inda fuskarta ke kallo , ganin ko wace ce ya sa shi yin
taga-taga zai fad'i

Masu karatu kunsan wa ya gani �


Cikin tsananin mamaki yace"Ummi?!"

To fa muje zuwa Dan jin yadda zama zai Kasan ce tsakanin Ummi da Abdallah
[12/16/2017, 9:38 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*


*MRS NN ONE💋*



® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com



Page 7⃣


Jingina da bango yayi yana k'are ma Ummi kallon mamaki , bawai baya son Ummi bane , Ummi
macen rufin asiri ce , yasan halin Ummi akwai hankali natsuwa da sanin yakamata uwa uba
kuma tarbiyya , Ummi mace ce San kowa k'in Wanda ya rasa , tana da kyawu dai-dai
gwar-gwado ba za'a kirata da mummuna ba , ita ba fara bace kuma ba za'a ce mata bak'a ba
zamu iya kiran ta chocolate colour , ba tada tsawo sosai kuma ba gajera bace sannan yatsunta
suna da tsawo , tana da dogon hanci da yalwatattun idanuwa ba tada fad'in fuska sosai,
gakuma D'an k'aramin bakin ta , kai masu karatu Ummi kyakyyawa ce ba laifi🙅🏾‍♀


Wani gwauron numfashi ya ja ya zame agurin ya zauna yana kallon ta kamar wata sabuwar
hallita ,

Ya kai kusan awa biyu a wurin yana kallon ta azuciyar shi yace "tabbas Ummi kyakyyawa ce
amma me yasa yau naga kyanta ya fita daban, ? mutane suna ciwo suyi muzai-muzai , amma
Ummi kyau ta k'ara ko ita din ta daban ce ko kuma ido nane ?"

Duk wad'an nan tambayoyin ba shida amso shin su Dan haka kawai mik'e wa yayi , ya fita yayo
alwala ya raya daran da sallah ,


Ummi kuwa juyin barci tayi ta farka wani irin mugun fitsari taji ya matse ta , ga tsoro tana ji ba
zata iya fita waje ita kad'ai ba sai matse matse take , Abdallah kuma alokacin ya idar da sallah
yana jiran yaji an kira sallar asuba yana jingine idon shi a lumshe amma ba barci ya ke ba ,


Ummi kuwa da taga idan bata je tayi fitsarin nan ba to tabbas zata malale sabuwar katifar ta da
fitsari ,



A hankali take kiran sunan "yaya Abdallah ? Yaya Abdallah? Yaya Abdallah?"


Shi kuwa ya na ji kasa amsawa yayi sakamakon wani Abu da yaji yana sukan zuciyar sa , ana
ukun da ta kira shi ne ya daure ya ce mata

"Na am"

"Fitsari nake ji"

"To kije kiyi mana "

Cikin d'auriya da matse fitsarin tace "wallahi tsoro nake ji "

Azuciyar shi yace " ko a gida wake raka ta oho?"

Afili kuma sai cewa yayi" kiyi addu'a ki fita babu abin da zai same Ki da yardar Allah"


" wayyo Allah yaya zai zubo"


Dafe kanshi yayi a zuciya ya ce "ni kam naga ta kai na "

Azahiri kuma yace " tashi muje "

"To kayi gaba"ta fad'i cikin shagwab'a

Gaba yayi ya barta a baya tana tafe tana hard'e k'afafuwa , har ta isa nesa da bakin bayin ya

tsaya tare da mik'a mata buta , sannan ya ce" adai yi addu'a "


"Uhum" kawai tace ta k'ara sa bayin aciki ma ta k'ara sa addu'ar ,


Bayan ta fito ta gan shi yana alwala cikin sauri ta fara duk Dan gudun kar ya gama ya barta a
wajen , shiko tsaya wa kawai yayi yana kallon ikon Allah , har ta gama ta shige d'aki , nan shima
yayi ya koma d'akin Dan ya dauki hular shi

Ita kuma ta tada kabbara sai ce mata yayi " wato ni da na raka Ki Dodon ya cinye ni ko?"

Bata ce komai ba , shikuma ya d'auki hular shi , ustazu ka fiye naci ya saka ya fita ,


Bayan sun idar da sallah ne ya so ya D'an kwanta a massallacin ya D'an yi barci amma Umar
Sam ya hana shi sai tsokanar shi ya ke yake " Ango Ango sai wani k'yalli kake kamar tauraro"
haka dai yayi ta masa shak'iyyan ci,


Abdallah kuwa tashi yayi ya barshi nan zaune yana dariya da dai ya ga da gaske fita zaiyi sai ya
taso ya biyo shi dai dai kunan shi ya rad'a masa "ya kama ta kaje ka ji d'umin 'yar k'anwar ka"
ya k'ara sa da kashe ido d'aya


Abdallah ko da abun ya bashi haushi sai ya ce " ka manta ne ba d'umin ta zanji ba jikin ta Zan
shige "


"Yauwa mutumi na Ashe ka gane "

Dai-dai nan Abdallah ya shige gida ya bar Umar a tsaye yana dariyar mugunta Dan shi gani
yake kamar an had'a Abdallah da aiki ne ,


Yana shiga gida ya CI karo da Hafsa tana alwala , wata harara ya watsa mata sannan yayi
sallama d'akin Mama suka gaisa take tambayar shi ya Ummi da jiki ya ce mata taji sauki suka
Dan tab'a hira ya ji yana jin barci sai ya mik'e ya ce mata "Mama ina zuwa"


D'akin su ya koma , Ummi kuwa tana jin motsi tayi sauri ta rufe idon ta , ko da yayi sallama yaji
ba Wanda ya amsa mishi , ya yaye labule kutsa kai ,

Yana shiga ya ganta tana barci , ya koma inda yaga dadduma a shimfid'e ya kwanta nan wani
barci yayi awan gaba da su duka ,,


Mama kuwa da taga har takwas tayi Abdallah be futo ba , sai ta aiki Hafsa ta siyo kayan tea a
bakin titi, ta na dawo wa ta d'aura ruwa zafi ta had'a citta da kaninfari da Lipton ya dahu sai
k'amshi yake , , ta juye a wani tsohon plas d'in ruwan zafin su ta juye aciki ta d'iban musu nasu
saura kuma ta had'a da bread tayi k'ofar d'in Ummi
Sai da tayi sallama sau uku taji ba Wanda ya amsa kuma ba ta ji motsin kowa ba , murmushi
tayi sannan ta d'aga labulen kad'an ta ajiye kayan ba tare da ta kalli d'akin ba , gudun kar tayi
mugun gamo,🤣🤣


Ummi ce ta farka lokacin Tara tayi cikin sand'a ta mik'e gudun kar Abdallah ya tashi bata San
shima ya tashi ba baya son yayi motsin da zata ji ne ,


Jakar kayan ta ta bud'e ta Ciro brush da MacLean ta d'auki butar ta ta fita bata lura da kowa a
tsakar gidan ba ta tafi chan inda suke wanke wanke tayi brush d'in ta sai da ta gama ne d'ago
kai suka had'a ido da Hafsa , aiko me Hafsa za tayi in ba dariya ba , Ummi kuwa murtuk'e fuska
tayi Mama ta gansu amma sai tayi kamar bata ma gansu ba .

Jiki a sanyaye Ummi ta k'araso ta zauna kusa da Hafsa , cikin jin kunya ta gaida Mama , ta
amsa cikin sakin fuska Dan Mama tana son Ummi sosai


Hafsa ce ta ce"Aunty Ummi ya jiki"


Ummi da mamaki ta ce "yau kuma Hafsa nice Auntyn Ki?"


"Eh mana AI tunda kin auri yaya Abdallah kin zama Aunty"

Wata hara ra Ummi ta zuba mata ta gefen ido

"Ummi tashi Ki je Ki karya kinji Ki k'yale wannan "


"To Mama"

Ai sai Ummi ta d'auki kofin shayin Hafsa tana fad'in "Mama AI wannan ma ya ishe mu ni da
k'awa ta"


"Malama bani shayi na naki na d'akin ku" cewar Hafsat tana zumb'uro baki


Mama dai bata tanka musu ba


Ummi ta ce cikin k'asa-k'asa da murya "K'awa ta je Ki d'auko min nawa tea d'in , zan aje miki
naki,"

"Tab AI ko ba zan je b....." Bata gama fad'i ba Ummi ta make mata baki


Mama kuwa murmushi kawai tayi


"Ke hafsa nan matsalar Ki ba wayau je Ki d'auko min Ki zo musha fira"


"Eh sannu uwar wayau..." Ummi ta k'ara make mata baki


"Wallah Aunty Ummi kika sake duka na sai na...
." ta sake gwabje bakin ,


Hafsa ta mik'e "Mama kina kallon ta ko ?"

Mama ta ce 'ai ni na gode gwanda ta min maganin Ki , wuce ki je Ki d'auko mata"


Cikin zumb'ura baki ta tafi
[12/17/2017, 8:56 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*


*MRS NN ONE💋*



*Wannan page d'in na sadaukar dashi ne ga masoya novel d'in BAWAN ALLAH aduk inda kuke

Wanda na sani da Wanda bansani na gode Allah ya bar zumunci, ❤*



*BAWAN ALLAH fans wallahi ina matuk'ar jin dad'in comments d'in ku ku sani dani da ku muna
mak'ale da juna�🤙*


*K'awwali ta da Ameenert gaisuwar ku da bance 💋*


® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com



Page 8⃣-----🔟


Sai da tayi sallama sau biyu ba'a amsa mata ba , ana ukun ne ya amsa had'e da cewa,


"Mene ne?"

"Aunty Ummi ce tace na zo na d'auko mata shayin ta da magani"


Chan dai yayi shiru kamar ba zai bada amsa ba sai kuma yace "kije Ki ce mata tazo ta d'auka
da kanta"

Har ta juya zata koma sai kuma yace "zo nan"

Ahankali ta d'aga labulen d'akin ta shiga ,

"Kwashe gasunan inda kika ajiye su"

Ba musu ta d'auka sannan ta fita jikin ta duk kyarma yake ,


Tana zuwa ta dangwarar da kayan a gaban Ummi " gashinan burinki ya cika kin tura ni wurin
wancan zalimun mijin naki"


"Oho ko ma dai mene ne buk'ata ta tabiya tunda kin min abin da nake so" cewar Ummi tana
murgud'a baki ,


"Idan kun gama wasan kwai-kwayon sai ku mayar mai da kayan shayin " Mama ta fad'i yayin da
ta d'au buta tayi hanyar bayi


"To"dukan su suka ce ,

Mama na tafiya musu ya kaure tsanin Ummi da Hafsa akan Wanda zai mai da kayan shayi

Ummi na cewa "ke kika d'auko ke zaki mai da "

"Hafsa na cewa ke kuma ba mijin Ki bane ni ba runa wallah ba zan mayar ba"

Dai dai nan Abdallah ya fito ya , duk yaji me suke cewa , amma sai yayi kamar ma bai San suna
wajen ba , Ya fara brush kenan Mama ta fito daga bayi , anan suka k'ara gaisawa alwala tayi ta
shige d'aki shima alwalar yayi ya shige d'aki , duk da yana wurin musu tsakanin Ummi da Hafsa
be k'are ba sai dai wannan karan a hankali suke yi , yana shiga ya tada sallar mai rabo (salatul
duha),

Ummi ta gama tsumul- mulan shan shayin ta Dan Hafsat tuni ta gudu ta barta,


Hakanan tayi shahada ta d'auki kayan shayin ta nufi d'aki da shi sallama tayi sannan ta shi , ta
same shi akan dadduma yana addu'a , kawai sai ta tsaya tana kallon shi da taga ya gama
addu'ar sai tayi sauri zata fita kamar daga sama taji yace "ina zaki je?"

Sai ta hau kame kame,

"Yau ko gaisuwa ba zan samu ba kenan?" Yawani tsare gidan shi


Cikin sauri tace" yaya ina kwana?"

"Ah'ah Ki rik'e gaisuwar Ki indai sai na rok'a" ya sake murtuk'e fuska


Nan da nan ta tuna da nasihar Malam da ya ke cemata "ta guji b'acin ran mijin ta Dan zai iya
kaita ga azabar Allah"

AI yana tuna wannan sai tayi sauri ta dawo kusa da shi ta zauna

Ta marai-raice murya "yaya Dan Allah kayi hak'uri , Malam yace idan kayi fushi dani zan iya
shiga wuta"


Abin ya bashi dariya amma da yake bata so ya gane sai ya tsare gidan sa , azuciyar shi kuma
cewa yayi "wato tanan kika b'ullo? Muje a haka game d'in zai fi dad'i"

Wani murmushi yayi sannan ya ce "idan kina so na daina fushi da ke kin had'a min shayi"


"Yo AI wannan mai sauk'i ne "cikin minti biyu ta had'a mai tea d'in ta bashi


Tana zaune a gurin ya gama karyawa sannan ya kalleta ya ce " ya jikin naki?"

"Alhamdulillah , naji sauki"

"To masha Allah , kinsha maganin Ki?"

Kai ta girgiza alamar bata sha ba

"Ummi Ki daina wasa da shan magani , tashi Ki d'auka Ki sha"


Ba musu kuwa ta mik'e ta d'auko maganin ta bud'e wata k'aramar randar ta ta d'ibi ruwa kamar
abun arzik'i zata sha ,

Ga maganin ta Tara a gaban ta amma ta kasa sha ,

Shikuwa sai ya bita da na mujiya , wani abun mamaki bai wuce da ya tana zubar da k'walla ba ,
tana hawaye tana kallon maganin ,


"Lafiya? Ki sha maganin mana"

"Wallah yata magungunan ba dad'i "

"Ki daure Ki sha shi dama magani ba Dan dad'i ake shan shi ba"


Mik'e wa tayi tare da d'aukar ledar maganin zata fita ,

"Ina kuma zaki je Kuma?"


Cikin shagwab'a Ummi tace "zan je gurin Ummi name ita kad'ai zata iya bani nasha ba tare da
nayi amai ba"

Shiru yayi na 'yan sakwanni sannan ya ce "zo na baki Ki sha"

"Ummi na fa lallab'ani take"


Wani murmushi yayi sannan yace" nima yayan Ki zan lallab'aki"


Jin hakan yasa Ummi kwasar ledar maganin tayi wurin shi ,

Zaman dirshan tayi a gaban shi sannan ta mik'a mai maganin , ya karb'a yace

"Ya Ummi take baki?"

Sai alokacin itama Ummi ta faki idon shi ta saki wani shu'umin murmushi azuciyar ta tace "anzo
gurin ya ustaz"

"Ina magana kinyi shiru saifa kinsha maganin nan yau" yana magana yana d'aure fuska


"Dama sai ta gutsura maganin gida biyu sannan ta ta saka min d'aya a baki da ruwa , tana
Shafa baya. Na har sai ta gama bani kuma tana yi tana fad'in , kiyi hak'uri Ummi na kisha , haka
take ta fad'i"
�����


Bawan Allah sai da ya zaro ido sannan yace "to naji matso"
[12/18/2017, 1:47 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*



® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_


# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com



Page


1⃣1⃣++++1⃣2⃣



Matso wa tayi daf da shi sannan ya bud'e ledar ya Ciro magungunan ya b'ab'b'alla su , ya ce
"bismillah " D'an k'aramin bakin ta ta bud'e ya saka mata tare da bata suwa tana jira taji ya
shafa bayan ta sai taga yayi mursisi , ai ba shiri ta fara kakarin aman k'arya fita waje tayi da
gudu ta tofar da maganin , ta shigo tana fuskar tausayi, tace
"Yaya ka gani ko ba zaka iya bani ba kamar yadda Ummi na take bani"


"Me yarinyar nan ta mai da nine amma zan nuna mata nafi Ummin iyawa"wannan duk azuciyar
shi yake fad'i


Azahiri kuma cewa yayi " ayya sannu na manta ne zo asake wani"

Ta sake zuwa ta zauna sai cewa yayi "cire wannan hijab d'in ko shima ya shak'e maganin yak'i
wuce wa"

"Me ka ce yaya"ta zaro ido

Ya k'ara k'asa da murya dai-dai kunnan ta yace "nace Ki cire hijab d'in"

"Yaya ai ba zai hana ni sha ba"

B'ata rai yayi ya tura mata maganin ta , "shikenan tunda ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0