Showing 30001 words to 33000 words out of 39120 words

Chapter 11 - Bayan Wuya Book Compelet Rimacool

Rimacool   

04 Aug 2026

543

nan take ta faɗa masa labarinsu tun daga farko har ƙarshe batai masa
ƙarya ba, da tausaya yake binsu da ido shi kanshi yai matuƙar tausaya musu, "Sannu kunji ko,
lallai Ubangiji ya kareku daga ma sharrin shaiɗan da har baku aikata wani abun ba dukda ba
isasshen hankali ne dashi ba amma bai kamata kuna yawo babu aure a tsakaninku ba, abinda
nake gani a karo na biyu zan sake taimakonku, zan ɗaura muku aure a goben nan in sha Allah"



wani dummm gaban Fattu ya faɗi jin kalmomin mutumin taya zata iya rayuwar aure da JODDi?
ita fa a matsayin Yaya ɗan uwanta ta ɗauki Joddinta da kuma soyayya ta Addini musulunci ita
haka take gani, amma komai Ubangiji ya ƙaddara mata mai kyau bata da ikon jayayya akan
lamarin da Ubangiji ya tsara mata, zata amshi ƙaddararta a yadda tazo mata, ita a yanzu
dukkan wata rayuwa da zata zo mata hannu biyu zata saka ta karɓeta ta godewa Ubangiji,
"Ƴata naji kinyi shiru" ɗago da fuskarta tayi tana faɗin "Baba duk hukuncin daka yanke mai kyau
ne yadda ka taimakemu Ubangiji ya baka mafiyinshi mun gode shoshai"


"babu damuwa Ƴar Nan Addinina na hidimta mawa taimako shi wani abu ne mai tsananin lada
a duk lokacin da kaga ɗan uwanka na buƙatar temako kayi ƙoƙarin tai maka masa da iyakar
ƙarfinka kaima Ubangiji zai taimake ka a dukkan wani hali da ka tsinci kanka, rayuwa kake
amma gaba kaima baka san inda zata kaika ba"

ɗaga kanta tayi tana matsa yatsun hannunta, dukkan maganganun da suke tsab JODDi ya
riƙesu yana binsu da ido wani abu na daban na masa yawo a brain ɗinsa tsab kalmomin da
Mutumin yai suka buɗe masa wani abu daya rufe masa ƙwalwarsa "waye Ni?" ya furta yana
dubansu


a mugun razane Fattu ta ɗago idanunta tana kallonsa "Joddi kana magana dama, ka tuno waye
kai??" Tai masa tambayoyin a jere


da ido ya bita yana faɗin "Ni dai ban san waye ni ba nima haka kawai na ganni" jijjiga kai tayi
sannan tai hamdala ga Ubangiji daya buɗewa JODDi bakin yin magana



"Masha Allah tun da Ubangiji ya buɗe masa baki yanzu dare yayi kije wajen mai ɗakina ki

kwanta zuwa gobe da safe zan isa wajen mai gari na sanar masa da buƙatarmu" Dattijon ya
furta



da to ta amsa zuciyarta na bugawa dan bata san kalar matar da zata taras a gidan ba wataƙil
ma ƙara Innaro da ita, bakinta ɗauke da sallama ta shiga amsa mata ƴar Dattijuwar dake zaune
tayi tana furta "shigo ƴar nan kin jiko Malam ya sanar Mani da zuwanki" ta faɗa da Murmushi
tana miƙewa


Ajiyar zuciya Fattu ta sauke ganin Matar ba irin Innaro bace, a ladabce ta gaisar da ita tana
zama, amsa mata matar tayi da fara'ar sosai, kamar ta goyata haka ta dinga nan da nan da ita
harta kwanta tana tunanin halayen Mutanen nan biyu dama akwai mutane irin haka? ta tambayi
kanta, a ranar dai wani bacci mai masifar daɗi ya ɗauke ta wanda zata iya rantsaewa tun da
take bata taɓa yin Bacci mai daɗi irin wannan ba


*Washegari* koda suka tashi daga Fattu har JODDi Mutumin ya kaisu wajen mai gari, tsab cikin
hikima Dattijon ya ɗan faɗa masa wani abu daya saka su baro gida sannan ya kawo musu
buƙatarsa, babu musu mai gari ya Amince sannan ya tara mutanen garin ya faɗa musu
buƙatarsu, mai gari ya bayar da sadaki, kallon JODDi Dattijon yayi yana furta "Ya sunanka?"
kamar wani mai Imagine haka JODDi ya tafi can kuma sai ya cije baki da ƙyar yana furta
"Muhammad"


"Sunan Mahaifinsa fa?" Mai gari ya tambaya "Ahmad" JODDi ya furta, babu ɓata lokaci aka
ɗaura auren JODDi da Fattu





***********************

zaune take bisa Ƴa kujera ta guragu tana kallon fuskar mijin nata da tausayawa wanda take
matsa mata ƙafafuwan ta, Allah kaɗai ya san irin ƙunci da baƙin cikin Abinda take ji idan harta
ga Mijin nata cikin wannan hali kullum hankalinsa ba a kwance ba ga matsanancin ciwon da
yake fama dashi, itama kenan da take kallonsa ina ga A'ishatu wacce yai mata nisa a iya
tsawon shekaru to ita wane baƙin ciki ma ne bata ƙunsa ba?

hawaye ta share tana jana Majina, ɗago da idonsa Abbie yai yana kallonta "Mansura kukan ne
baki daina ba, ita fa ƙaddara babu yadda bata zuwar wa mutum ko wane bawa kika gani da
tashi jarbtar sai dai wata tafi wata kiyi haƙuri da rayuwar da kika gammu a ciki, kiyi tunani da
Ƴar Uwarki Aysher mana ki hasaso dake ke cikin halin da take ciki ya zakiyi? amma tai haƙuri ta
jure taci gaba da rayuwarta ba wai dan bata jin ɗaci da zafi bane a a sai ɗan wadatar zuciya da
Ubangiji yai mata,nayi Imani da mahaliccina babu ranar da zata fito ta koma Aysher ba tayi
tunanimmu ba ko kuma kewarmu, tabbas akwai ciwo ke kin rasa ƙafa da baƙi ita ta rasa
idanuwa, kin san ma kuwa irin tsangwamar da take fuskanta a Al'umma da ita da yaranta ƙazafi
babu wanda Aysher bata gani ba, kuma duk ina kallo amma babu halin taimaka mata abin na
man zafi da ciwo yadda baki tunani, babu ranar da zata fito ban zubar da hawaye ba,amma a
haka Mansura kullum ƙara godewa Ubangiji nake"Abbie ya ƙarashe da murmushi mai ciwo



tunda yake zancen hawaye masu raɗaɗi da zafi ke biyo kuncinta tabbas ita tafi tausayin
A'ishatu a kanta A'ishatu Ƴar uwa ta ɗauke ta ba a matsayin kishiya ba, tabbas tasan duk ɗaci
da raɗaɗin da take ciki A'ishatu ta fita shiga cikinsa shin ita ya take ji? share hawayen tayi tana
mai kawar da kanta


haka shima Abbie bai ƙara magana ba kasancewar Abinda Ya tsaya masa a maƙoshi ga
zuciyarsa dake wani harba masa da sauri_sauri daman ya san za'a rina domin duk lkcn da yai
maganar A'ishatu haka ce take faruwa dashi, Anya zai iya wannan rayuwar tabbas zai karya
Alqawarin daya ɗauka ya fito da gaskiya fili sannan ya fashe rufaffen ƙwan daya daɗe ba a
ƙyanƙyasa sa ba sai dai komi zai faru ya faru koda kuwa hakan yana nufin zai rasa nasa
numfashin ne






*********************************

Alhamdulillahi anyi biki lafiya an ƙarashe lafiya inda Maheer ta zama matar Bobbi, ba ƙaramin
farinciki Maheer ta tsinci kanta ba a lokacin da ta zama mallakin Bobbi sai dai zullumin ta ɗaya
ne yadda zata sace zuciyar BOBBI ta tabbatar abu ne mai wahala sace zuciyar mutum kamar
Bobbi

ba ƙaramin kuka da dana sanin son maso wani Maheer tai ba a lokacin data kwana ɗaya bata
ga Bobbi yazo gunta ba da niyyar raya wannan dare, ko wace Amarya na farinciki A daren

farkon data kwana ɗakin mijinta amma ita sai tarin baƙin ciki da takaici ta ƙunsa tabbas ta
shiryawa wannan rana domin fayyacewa Bobbi soyayyar da tayi mata mugun kamu tayi niyyar
fayyace masa dukkan wani sirri na zuciyarta a daren farkon ta amma sai dai kash bata samu
wanna ikon da damar ba


kwance dake jikinta lulluɓe da blancked idanunwanta sunyi luhu_luhu saboda kukan data sha
Nocking ɗin da taji anyi ne ya sakata miƙewa da ƙyar tana gyara gashinta "come in" ta furta a
hankali,

kanta a sunkuye ta ɗago tana duban Maheer tace "Am Hajiya tace ki sabko kici Abinci" fuskarta
da ɗan murmushi tace "ok you can go"



harta tafi kuma sai taji Yarinyar ta birgeta cikin ɗan ɗaga murya tace "Nace ba" ɗan juyowa tayi
tana haɗiye abinda ya tsaya mata a maƙoshi tace "na'am" tana kallon Maheer wacce ke
murmushi "Ya sunanki?" Maheer ta tambaya tana kallonta



"Muneebba" ta furta ba tare data kalleta ba "wow nice Name you can to be my friend?"



"Yes Mah" ta furta tana ƴar dariya, itama dariyar tayi "ok you can go pretty" ok ta furta tana fita
tana mamakin halayen Maheer a farko ta saka zata yi girman kai da wulaƙanci amma sai taga
saɓanin hakan, a yau da ta samu wacce ta ɗan sake mata fuska sai taji ta wata ta daban,duk
damuwar da take ciki sai taji ta ɗan rage, amma sai dai idan tasan da cewar ita ɗin ko wacece
ta tabbatar sai ta sauya mata ta musguna mata may be tama fi su Mom ƙuntata mata Dan
ganin Mijinta take aure da wannan tunanin harta safka ƙasa ba tare dama tasan ta safka ba
"ke!!!" taji daka tsawar Mom



A hanzarce ta ɗago tana dubanta "na'am Mah" ta furta bakinta na kyarma, a wulaƙance Mom ta
bita da kallo "gidan Uban wa zaki tafi? baki isar man da saƙon dana aikeki dashi ba"


baki na rawa ta furta "Sorry Mah, tace gata nan sabkowa" taɓe baki tayi tana furta "da tsiya sai
kinyi turanci kina ƴar matsiyata faƙiriya, maza zo yi Saving namu" dariya su Aunty Meera suka
fashe da ita, sosai Muneebba taji ta muzanta da kalar cin mutuncin da sukai mata ga Mazan

dake zaune waɗan da suke Binta da kallo hakan ya saka taji ta ƙara muzanta jiki ba ƙwari ta iso
wajensu kamar ta fasa ihu, kallonsu ABEED yai yana ɓata rai "haba Mom miye laifinta za kuyi
mata wannan cin mutuncin, shin shi talaka dan ya zama Silifas abin takawa? zakuna dinga
mata cin mutuncin laifi ne dan tazo nema a karkashinku zaku wulaƙantata kunsan gaba yadda
Ubangiji zaiyi daku ne, shin kun san kalar baiwa da ni'imar da Ubangiji zai mata nan gaba ne?"

harara Mom ta zabga masa tana furta "to sannu Malam, wace baiwa Ubangiji yaiwa talaka idan
banda baiwar faƙiranci kaga riƙe wa'azinka"


shiru kawai yai yana danna wayarsa dan yasan ba zasu gane ba "Mom a kira Indo tai man
Peppersoup" Zameer dake ida safkowa daga Step ɗin benen ya furta, hakan ya saka
Muneebba ɗagowa tana dubansa "wow bala'in can Mom Ina kuka samu House maid
balarabiya?" Zameer ya furta yana kafeta da ido, kawar da kanta ƙasa tayi taci gaba da yin
Saving nasu, wata uwar harara Mom ta zabga masa "to na Mamajo sarki mata kai dai mace
indai fara ce koda Mayya ce tana burgeka, ina ruwanka dama ko wace kala ce inda ƴar aiki ce"



"To ita ƴar aikin ba mace bace?" ARYAN ya furta , Zameer ne yace "a to gane Mani hanya, ke
Ƴar nan ban son naga farar mace balarabiya kamarki tana wahala ajiye na ida Saving nasu ni
dai indai akan farar mace ne na zama bawa daga yanzu"



"Alqur'an ban ga laifinka ba, dama baƙaƙen Ƴan aiki sunyi wa gidan nan yawa babu ƴan
Farare" Afif ya furta yana dariya, dariya dukkansu saka saki harda shewa kamar wasu mata,
Mom kuwa bata ƙara cewa ƙala ba, Maheer ce ta safko fuskarta wasai babu wanda zai kalleta
yace ta sha kuka, a ladabce ta gaida Mom sannan taja kujera tana zama,dasu Aunty Meera
suka gaisa a mutunce sannan su Zameer, Muneebba dake tsaye ta jawo Warmer tai saving
ɗin Maheer "tnx pretty" Maheer ta furta da murmushi itama murmushin tayi tana ja baya ta
tsaya, Tunda Zaidu ke sabkowa yake kallon Muneebba da kuma Mamakin abinda ya sakata
sanya kayan House maid ya dai tabbatar wannan ɗin ita ce Matar Bobbi ba wata ba,
Murmushin gefen baki ya saki yana kallon Muneebba, babu wan da yaiwa Magana,ya kalli Mom
yana furta "Mom ki aika wannan House maid ɗin takai man Abinci a ɗakina" ya furta fuskarsa
ɗaure tamau



tsam Zameer ya miƙe yana jawo Warmer ɗin Abincin yace "Yah Zaidu bari na kai maka Alharam
abinda za'a aikata kasan muna kare martabar Musulunci babu yadda za'ayi zuƙeƙiyar budurwa
fara tas jinin larabawa taje kai maka Abinci a Bedroom"..................

*Riamcool ce*
[5/21, 8:18 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*


*Book 1*


*By: RIAMCOOL*



*MIKIYA WRITTER'S ASSOCIATION*


*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHIM*




*P.37&38*


Da wani kalar kallo Zaidu yabi Zameer yana tauna leɓe,basarwa yai yana ɗaga kafaɗa "ok kai
man a ɗaki"


Wata wahalalliyar Ajiyar zuciya Muneebba ta saki tana hamdala ga Ubangiji, "Mah an gama zan
iya tafiya" ta tambaya bakinta na kyarma, wani banzan kallo Mom ta watsa mata tana faɗin
"daman na riƙe maki ƙafafu ne na hanaki tafiya?"


jiki a sanyaye ta fita tana matso hawayen da suka tarar mata a fuska, da wani kalar sheɗanin
kallo Zaidu ya bita yana sakin murmushin gefen baki


Koda ta fita kai tsaye Part ɗin da zai sada ta da ɗakin Bobbi ta nufa key ta zaro tana buɗe
ɗakin, a hankali ta furzar da iskar bakinta tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce tai gudun
tseral, bisa ɗaya daga kujerun Falon ta samu tana zama tare da dafe kanta dake mata
Azababben ciwo,ɗan kwanciya ta samu tayi ko taji sawaba nan take bacci mai masifar nauyi ya
ɗauke ta ba ita ta samu ta farka ba sai wajen 1:30pm sannan ta fara buɗe lumsassun

idanunta,a hankali ta ida ware su tana miƙa tare da furta Addu'a, wata irin zabura tayi tana
miƙewa jikinta na kyarma ganin wanda ke cikin Falon yana dannan Laptop ɗin sa hankali
kwance, "ina....wuni" ta furta a rarrabe cikin tsoro, ba tare da Bobbi ya ɗago ba ya furta "miye ya
shigo dake ɗakina?"

"gyara zanyi" ta furta tana matsa yatsun hannunta wanda wannan ya zame mata Al'ada cikin
kallon tarin tsanar mace ya ɗago da fuskar sa yana dubanta fuska a haɗe tamau babu alamar
sassauci ko rahama ya furta "daga yau bana buƙatar sake ganinki a koda sashen nan, kar ki
ƙara shigo man ɗaki da niyyar gyara idan ba haka ba ranki zaiyi mummunan ɓaci"

murya a can ƙasa ta furta "ok sir" tana jifanshi da kallon tsana wanda lokaci guda wata kalar
muguwar tsanar Bobbi ta dirar mata a zuciya,

cikin daka tsawa ya furta "miye na tsaya man a kai kina kallona maza fice man a Falo" ya faɗa
kamar yai mata dan banzan duka



A hanzarce ta fice ta fita daga side ɗin ma baki ɗaya, waje ta samu tana fashewa da kuka, ita
shi kenan duniyar nan kowa ya tsaneta kowa ta raɓa sai ya nuna mata tsana, duniyar nan wane
laifi ta aikatawa Mutane da har suke nuna mata tsana har haka? kuka taci sosai dan sai da taji
kanta na neman tsagewa sannan tai shiru tana nufar famfan dake gefe ta wanke fuskarta,

*Maheer*


tun shigowar Bobbi Maheer ta gani hakan ya sakata shiga bathroom ta wanka sannan tazo ta
cancanɗa uwar kwalliya kamar zata tafi gasar kyau, ƙara kallon kanta take jikinta sanye da rigar
dakakkiyar Shadda Arsh color ɗinkin Straight gown wacce taji aiki da Ado sai walwali take gashi
ba ƙaramin fito da ainahin hasken fatarta tayi ba da kuma surarta, wuyanta sanye da sarƙar
Gold wacce keta walwali da sheƙi, jikinta tabi da manyan turaruka ta feshe shi, Agogon
Diamond ta ɗauka tana ɗaurawa a haɗaɗɗen tsintsiyar hannunta, ba ƙaramin kyau tayi ba dan
babu namijin da zai ganta bai ji wani abu a kanta ba, ƙayataccen murmushi ta saki, tana
ficewa daga ɗakin nata, kai tsaye Part ɗin sa ta nufa gabanta na tsananta faɗuwa koda tazo kan
ƙofar shiga ja tayi ta tsaya tana furta sunan Allah shahada tayi tai Nocking,ta ɗan jima tana yi
kafin taji an furta "come in" A hankali ta tura ƙofar Falon kanta a sunkuye tana tafiya cikin
nutsuwa da kuma birgewa, cikin ɗaya daga cikin kujerun Falon ta samu ta zauna tana kallon
Bobbi kamar ta cinyesa, sun ɗauki tsawon lokaci babu wanda ya cewa wani ci kanka, ɗan
ɗagowa yayi yana furta "mi ke tafe dake?"

hawayen da take riƙewa ne suka samu damar zubo mata a kunci zuciyarta na mata zafi da
ƙuna "Au haka ma zaka ce Yah BObbi? shin laifi ne dan kaso wanda zuciyarka ta Aminta dashi,
dacewa ne Abin da ka aikata ace A daren farkommu baka ziyarceni ba,ina ga ko auren ƙiyayya
mukai da kai bai kamata kai man haka ba akwai ciwo abinda ka aikata man" ta furta wani sabon
kukan na sake kubce mata


tun da take kukan Bobbi ke jifanta da wani kalar mugun kallo mai rikita wanda ake mawa,
"yaushe mace ta samu damar da zata furta masa haka, yaushe mace ta samu zarran kallon
ƙwayar idonsa harta furta masa haka, mace ita ce wacce yafi tsana a rayuwarsa, Abinda ya
ɗauki Mace maƙaryaciya maci Amana muguwa kuma Azzaluma, makira, mace ce mafarin
tarwatsa masa dukkan wani farin ciki, shi yasa bama zai taɓa bawa mace damar da zata furta
masa koda kalma ɗaya bace" ya furta a zuciyarsa yana sake bin Maheer da kallon tsana


tun da yake bin ta da kallon jikinta yai sanyi wani kalar tsoronsa da shakkarsa ta shigeta,ba tare
daya tanka Mata ba ya miƙe yana tattara Laptop ɗinsa ya shige bedroom,da kallo ta bisa tana
miƙewa itama fuskarta tayi jawur ɗan sai ta nutsuwarta tayi tana fita,kai tsaye wajen Mom ta
nufa tana shiga Falon ta faɗa cinyar Mom tana fashewa da wani kalar sabon kukan, "Maheer mi
ya faru" Mom ta tambaya hankalinta a tashe


"Mom wallahi ba zan iya jurewa ba,Yah BObbi har yanzu bai damu dani ba,yanzu haka da naje
wulaƙanci yai man" Maheer ta faɗa kamar zuciyarta zata faɗo ƙasa dan takaici da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0