Showing 6001 words to 9000 words out of 39120 words
ya auri Mahaifiyar Muhammad Hajiya Zinatu wacce babu ruwanta suna zamansu lafiya da
mijinta harta haifi Khadijah ita ce ƴarta ta farko sannan ta haifi Sagir sannan Abdulkarim sannan
autanta Muhammad wanda shima yai karatunsa har yai digiri ɗinsa, sannan ya auri Mansura
wacce ita ce ta liƙe masa harya aureta suna da ɗansu ɗaya, haɗuwarsa da Shatu ita ce ta fara
sauya masa rayuwa ta maida shi mai son jama'a da son taimakon Al'umma ta maida shi mai
wasa da dariya ga dukkan wanda ya gani cikin ƙunci, ya faɗa cikin tarkon sonta da ƙaunarta
haka zalika da son kasancewa da ita yai kwaɗayin zama da ita,ya bata ilimin da bata samu ba,
wanda kullum cike yake da mafarkin son kasancewa a tare da ita sai dai kash Mama Ladiyo ta
riga tai mai katanga da dukkan wani cikar burinshi akan Shatu, ya shiga cikin damuwa sosai
harya kai ga ko walwala ba yayi
ɓangaren Shatu ma haka yake kullum cikin kuka take wanda ta ida lalacewa tai baƙi ta ƙara
rama, amma a haka Mama Ladiyo babu tausai ta saka Sati guda da bikin Shafu da Idi ɗan
Jimmai, hankalin Shatu ba ƙaramin sake tashi yayi ba, tana ji tana gani aka ɗaura mata aure da
Idirisa wanda taci kuka ta tabbatar data riga ta rasa gatanta iyayenta, haka aka kaita gidan Idi
wanda shima ya ƙara zame mata baƙin kurkuku wanda kullum cikin cin dukan Idirisa take ga cin
zalinta da yake dan ko kwanciyar aure sai dai ace fyaɗe yake mata wanda ta ƙara lalacewa
sosai ga shaye'_shaye da yake wanda har giya yake sha idan ya shawo haka zai zo ya malaya
mata Amai a yace kuma dole sai ta shanye sa,idan taƙi yai mata ɗan banzan duka da taji
wahala haka ta gudu ta koma gidan Mama Ladiyo ta faɗa mata komai, amma sai Mama Ladiyo
tace mata tayi haƙuri ta komawa nan ai shine zaman auren haka Mama Ladiyo da kanta ta tisa
Shatu ta maida ita gidan Idirisa, Abinci kanshi Idirisa bai damu daya bata ba, ganin yunwa zata
kasheta yasa ta dinga bin makwabta tana amso wankau tana masu ,wasu tai masu
wanke_wanke shine zata samu ɗan Abinci, randa kuma babu ta kwana da yunwa, ta samu ciki
ya kai biyu amma fyaɗe Idirsa shike zubar da cikin..........
By Riamcool Star of the Squad
08109554986,only call
[5/21, 8:09 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*
*Book 1*
*By Mariam sani Riamcool*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
Bismillahirrahmanirrahim
*P.11&12*
__________✍️Wahala ba kad'an take sha ba ta shirya guduwa sau ba adadi amma sanin bata
da inda zata yasa ta haƙura a haka har suka cimma shekaru biyu da aure tana cikin uk'uba duk
ta ƙara lalacewa idan ka ganta ba zaka taɓa cewa Yarinyar mace bace kuma wacce bata tab'a
haihuwa ba,haka zalika dukda ni san da Muhammad yai mata zuciyarta bata taɓa mancewa
dashi ba koda da second guda ne
kullum cikin kuka take da fatan mutuwa, wata ranar Alhamis tana zaune lokacin Idirisa yayo
shaye_shayensa yazo yai mata mugun duka sannan ya had'a mata da saki ukku cir,ba ƙaramin
farinciki tayi ba na rabuwa da k'addararren auren, sai dai tunawa da Mamma Ladiyo yasa
murna tata komawa ciki dan tasan ta koma za'a dasa aya daga inda aka tsaya don muguntar
Mamma Ladiyo ba zata canza zani ba, koda taje ta faɗa mata abinda ya faru, ga mamakinta sai
taga tayi murmushi tana lallashinta abin sosai ya d'aure mata kai sai dai tasan wannan
murmushin na Mamma Ladiyo ba Alkhairi bane gareta, hakan yasa taci gaba da neman tsari
gareta, wani abinda ya ƙara d'aure mata kai bai wuci yadda take bata Abinci akai akai ba, don
tun tana tsoron kar tasa mata guba abinci harta dayaye take ci, amma bata saki jiki ba, wani
k'arin abinda ya d'aure mata kai harta yarda Mamma Ladiyo tuba tayi shine kukan da take
fashewa ta nemi gafararta, wani mugun dad'i Shatu taji ganin cewar Marik'iyar tata ta dawo
daga daga rakiyar shed'an wata kalar tarairaya take sha don harta kammala Idda amma
Mamma Ladiyo bata d'ora mata talla don Mamma Ladiyo kud'i tayi sosai wanda ta rasa ta inda
take samunsa ga fitar daren da takeyi kullum hakan yasa ta dasa mata ayar tambaya da
bincikenta a b'oye amma bata gano komai ba
tunda A'ishatu ta gama idda take zuwa inda take tallan goro a da wai ko zata ga Muhammad
amma shuru kakeji tayi kuka don tasan ta riga da ta rasashi
Zaune take fatar nan tata data yamushe a baya yanzu tayi luwai saboda cimar da take samu
wajen Mamma Ladiyo hakan yasa ta ƙara fitowa shar da ita fatar nan tata ta buzaye kamar ka
latsa jini ya fito, sanye take da wata Atamfa ja mai ratsin yellow riga da zani wacce Mamma
Ladiyo ta d'inka mata, fitowar Mamma Ladiyo da shirinta na Alfarma yasa ta maida hankalinta
wajen Murmushi Mamma Ladiyo tai mata tana shafa kumatunta tana kallonta da ƴan jajayen
idanunta kamar na Mayu harshe ta fiddo sai dai tunawa da wani abin yasa tai control d'in kanta
tace "am ki zauna zanje wani bikin d'an k'awata kila na dawo yau ko kuma gobe" ta faɗa tana
ficewa da sauri don jin idan ta tsaya ba zata iya dakatar da kanta daga umarnin zuciyarta ba
da kallo kawai A'isha tabita zuciyarta na harbawa da sauri tana faɗin Allah yasa kar zarginta ya
tabbata don ta tsorata da yadda idanunta sukai ja da tana kallonta hawaye ta share tana zama,
sosai ta lula cikin tunani har yaro ya shigo yana sallama bata ji ba sai da yai mata ukku sannan
firgigit ta dawo tana tambayarshi me za'a bashi
"Ance ana sallama da A'ishatu" da mamaki take kallon yaron don tunda take babu wanda ya
tab'a cewa yana sallama da ita idan ba Muhammad ba kuma tasan shi ya riga da yai mata nisa
"Kaje kace ba nan gidan bane" ta faɗa tana shigewa d'aki ba da daɗewa ba saiga yaron ya
dawo yace "wai ance nan ne ki fito ki ganshi"
Ƙaramin tsaki taja tana dauko mayafi ta yafa ta fita sai dai ganin dalleliyar motar dake wajen ya
sata zaro ido don tasan anyi b'atan kai ba dai wajenta ba juyawa yayi da nufin komawa taji an
rik'e mayafinta k'amshin da taji da bugawar zuciyarta ya tabbatar mata da ko waye a hanzarce
ta juyo tana kallonshi yadda ya kafeta da ido yana sakar mata da wani lallausan murmushi ita
kuwa k'a waro masa manyan idanunta take don tabbatar da shi d'inne hawayen da take riƙewa
ne suka samu damar sauka a kuncinta a hankali yasa hannu yana dauke mata su, "haba
Aysher ki daina kukan nan haka nan kinsan fa a halin yanzu ke babba ce da da rabo da kin
ajiye babba kamata" ya faɗa da sigar zolaya
ba shiri tai dariya tana k'ara kallonsa tana matsa yatsun hannunta wanda yasha ƙunshin ja, "Ina
ka shiga?" ita ce tambayar da taji ta fito a bakinta wani murmushi mai ciwo yayi yana share
zancen da jawo mata wata fira, itama ganin bai bata amsa ba yasa ta share, a wannan karon
ma ya ƙara mata maganar aure wanda zuciyarta taji ta tsinke don tana gudun Mamma Ladiyo ta
ƙara yi mata auren dole wanda ba zata jura ba k'ara ta gudu tabar gidan da ta rasa Muhammad
a karo na biyu
ha sukai sallama jikinta a mace yake tana cikin zullumi, kwanciya tayi tana sak'e_sak'e a ranta
bacci ya fara d'aukanta taji ana lashe mata fuska wanda firgigit ta buɗe idonta tana kallon baƙar
magen da ke tsaye tak'i matsawa ta kafeta da idanunta juyayi tana fito da jan harshenta tana
tand'e bakinta, Addu'a take son yi amma ta kasa da ƙyar ta samu taja wata Addu'a wacce yasa
magen ja da baya tana mata Murmushi sannan ta jijjiga kai ta haura katanga,wata kalar zufa ce
ta dinga tsatsafo mata cikin tsoro ta samu tayo Arwalla tayi salloli tare da Azkhar har bacci ya
ƙara kwasheta
da safe Mamma Ladiyo ta dawo ganin jikin A'ishatu na kyarma alamun zazzaɓi ya sata
tunkararta tana tambayar ta abinda ya sameta cikin tashin hankali, magani ta bata tasha ta
gasa mata jikin
haka ta kwana biyu sannan ta warware ga Muhimman bai dawo ba,zaune take tana matsa
hannunta bakinta na motsi alamar son ta yiwa Mamma Ladiyo magana, lura da hakan yasa
Mamma Ladiyo fad'in "faɗi maganarki mana ƴata naga har yanzun kamar baki ida sakin jiki dani
ba"
murmushi kawai tai mata cikin shakku ta faɗa mata yadda sukai da Muhammad, a mamakinta
murmushi tayi nan take ta amince ta kuma nunawa Shatu jin daɗinta
sai da akai sati Sannan Muhammad ya dawo wajen Shatu ba ɓata lkc ta faɗa masa amincewar
Mamma Ladiyo wanda yai murna kamar ya taka rawa haka yake ji, ba ɓata lokaci ya turo
magabatansa aka tsaida ranaku wanda iya Sati aka saka, sati na zagayowa aka ɗaura auren
A'ishatu da Muhammad wanda faɗa maku irin farincikin da masoyan suka shiga ɓata baki ne,
wani satin na zuwa ta tare a katafaren gidanta wanda Part biyu ne nata saina Mansura sosai
suke zuba soyayya wacce a gaban kowa basa jin kunyar nunawa junansu ita
haka sosai dangin Muhammad suke nuna mata harma da Abokiyar zaman ta Mansura wacce ta
riƙeta da Amana, da kanshi Muhammad ya samo mata mai koyamata karatun Addini dana
zamani, a haka har suka kwashe tsawon shekaru biyu A'isatu na samun ciki yana ɓarewa,
wanda anyi na Asibiti dana gida amma babu sauyi, don duk lokacin data samu ciki haka zatai
mafarkin magen nan wacce ta taɓa gani tana zaƙulo ɗan cikinta tana cinsa, da tashi cikin jikinta
ke zubewa
da ƙyar aka samu cikin ikon Allah ciki ya tsaya a jikinta harta haifi Kyakkyawan yaronta mai
kamar ubansa wato Khabir wanda duk wata kulawa tashi tana hannun Mansura, haka Habib
shima yake kula dashi tamkar wanda suka fito ciki guda
sai da yai 7 years sannan A'isha ta samu wani cikin inda ta haifi ƴarta mace sak ita ta biyo,
ranar suna yarinya taci suna Muneebba, wanda Muhammad yayi bajinta yai hidima tamkar bai
san ciwon kuɗi ba, don tun ranar da Muneebba tazo duniya yake jin sonta daban a cikin
yaransa, bayan kwanaki kaɗan itama Mansura ta haifi ƴan biyunta Mata waɗanda suka ci suna
Hanifah da Sharifah, haka rayuwa ta gangara har Muneebba ta cika 3 year
misalin ƙarfe biyun dare gudu yake sosai harya ƙaraso Part ɗin A'ishatu yana zuwa ya saɓi
Muneebba yana tashin Mamma, (wato A'ishatu) a firgice ta miƙe zatai magana ya rufe mata
baki ya tado Khabir, a galabaice ya buɗe get ɗin gidan yana Aman jini haka yaja hannunsu suka
dinga gudu har suka isa wani wajen Motar da yai parking shiga sukai ya fizgesu Ita dai A'ishatu
ta kasa magana illa binshi da ido da take dan ta kasa gane me ke faruwa, ga bakinta yai mata
nauyi ta kasa furta kalma koda guda ce wanda take ji tamkar an datse mata baki ne, tun dare
suke tafiya sai gab da Asuba suka shigo garin Kano wanda ya saukesu a wata tshohuwar
unguwa ya bata maƙuddan kuɗaɗen, ganin da gaske tafiya zaiyi ba mafarki take ba ya sata riƙo
rigarsa ta baya wasu hawaye na bin kuncinta, shima kallonsu yake yana hawaye "ba nida zaɓi
ne Aysher illa hakan, shine zai baku damar tsira da rayuwarku tabbas rayukanku na cikin
haɗari, ba don ina so zan nesanta kaina daga gareku ba, saduwar Alkhairi" yana gama faɗin
hakan ya janye hannunta yana shiga Motar ya wuce
durƙushewa wajen tayi ta fashe da kuka, da ƙyar ta rarrashi kanta har, tayi shiru.
kasancewar unguwar da jama'a yasa ta nemi temakon Jama'a ganin hada yara yasa wani
Alhaji Mamman temakonta ta zauna a gidansa har saida ya samo musu gida da kansa, wanda
ɗan zamanta a gidan tasha tsangwamar Maman Nazeer wato Matar Mamman wanda ko ɗanta
yazo wajen Muneebba da zummar yi masa wasa zata dinga masa faɗa wani sa'in harda duka
amma bai daddara haka washe gari zai ƙara zowa gun Muneebba da Khabir
Bayan sun dawo gidan sosai abubuwan suka rincaɓewa A'ishah Abinci kanshi na neman
gagararsu sai wanda yaga Allah zai taimakesu a hakan ta saka ƴaƴanta makaranta, wanda tun
dawowarsu taji mutane na faɗin wai wani yazo ya faɗawa mai unguwa a tada ita don ƴar bariki
ce ƴaƴanta ma duka a hanyar bariki ta samesu, nan danan unguwar ta ɗauka wanda taci kuka
sosai ta kuma daɗe kunnuwanta dana ƴaƴanta, sosai rayuwa ta ƙara juyewa Mamma a ciki
kuwa harda makantarta wacce ta wayi gari kawai ta ganta taje anyi maganin amma duk a
banza, ganin bata da isasshen kuɗi yasa ta haƙura,
dukda warning ɗinda Maman Nazeer taiwa Nazeer ɗin bai hanasa silalawo yazo gurin
Muneebba da kawo mata kayan wasa dukkan wani abu ya samu Muneebba yake kawo mawa
harta fara mallakar hankalinta wata kalar shaƙuwa ce ta shiga tsakaninsu da Muneebba, harta
fara mallakar hankalinta ta wayi gari da soyayyarsa wanda bata san lkcn data shiga ba, a lkcn
Khabir ya fara aiki wani gareji ciki ne suke samun nacin Abinci da ƴan buƙatunsu
tun da Muneebba ta wayi gari ta, ta shi da tsanar Mahaifinta wanda a ganinta da gangan ya
barsu dan jawo musu rayuwar tozarci, wanda ta Alƙawartawa kanta koda taga mahaifinta ba
zata ɗaukesa a matsayin Uba ba, duk lkcn da taga Mamma na kuka takan ƙara tsantar kanta da
jin tsanar Mahaifinta, a haka ta taso da tsanar Mahaifinta har kawowar yanzun wanda babu
mahaluƙin da take gani cikakken mara tausayi irin Mahaifinta.......
(tabɗi rigiji gabji, a kafta wasa farin girki ba'a fara wasan ba)
Love U all my Habibties a daure a dinga Shareí ¾íµ°plz Ina godiya ga masu ƙoƙarin Comments
Dawowa labari
Mu haɗu a next Page
[5/21, 8:10 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*
*Book 1*
*By Mariam sani Riamcool*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
Bismillahirrahmanirrahim
*P.13&14*
*DAWOWA LBR*
_______Tun da ta shiga ɗakin take faman rizgar kuka wanda tana ƙara jin zuciyarta na
hauhawa da farashin tsanar Mahaifinta, jin gyaran muryan Mamma yasa ta ɗago da fuskarta
wacce tai jawur saboda kuka share hawayen tayi tana kama Mamma ta zauna faɗa Mamma ta
soma yi mata kamar zata ari baki, wani kukan ta sake fashewa dashi, banza Mamma tai mata
har tayi mai isarta
koda Khabir ya dawo yai lallashin duniya amma taƙi sakin jiki taci koda Abinci ne gani take a
Silar rashin mahaifinta zata rasa Nazeer wanda ba zata iya juran hakan ba, waya ta ɗauka tana
danna masa kira wanda tayi yafi a ƙirga amma bai maido ba, zuciyarta ce ta sake tsinkewa tex
ta tura mishi nan ma babu reply shiru,
Kwance yake yana juyi bisa makeken gadonsa yana ganin kiran Muneebba na shigowa a
wayarsa amma ya gaza ɗauka saboda Hajiya data kasa ta tsare wayar ma hannunta take,
kallonsa Hajiya tayi tana taɓe baki tace "wai ni Nazeer na rasa me ka gani a jikin yarinyar nan
duk kyau da izzarka amma ace ga ita ka liƙe ita ɗimma ƴar zina marar asali da galihu ga ƴaƴan
Manya masu asali da dukiya suna binka amma kaƙi kulasu to bari kaji wallahi indai kaga kayi
auren nan bana numfashi, amma aure kasa niyya ban hanaka ba" tana kaiwa nan ta miƙe ta
fice
da kallo kawai ya bita yana jin wasu siraran hawaye na biyo kuncinsa ko kaɗan baya son
kalmar rabuwa ta gifta tsakaninsa da Muneebba da zai iya rabuwa da Muneebba da tun yana
ɗan ƙanƙani zai rabu da ita ko dan dukan da yake sha a gurin Mahaifiyarsa amma ina bazai iya
ba sonta ya riga da yai masa mugun kamu wanda ya zamto guba a jikinsa, ɗauke hawayen
yayi da yatsan hannunsa yana miƙewa ya shiga Toilet Alwalla yayi yai nafila yana fawwalawa
Ubangiji lamurransa bacci a ranar sai dai ɓarawo ya ɗaukesa
A ɓangaren Muneebba ma hakan ta kasance
*ASAD BOBBI*
Jerin gwano motoci ƙirar Marcedes Benz farare sol ke tsula gudu a titin wanda ganin irin gudun
da suke ne zai tabbatar da ba lafiya ba, hakimce yake a bayan Motar ya lumshe kyawawan
idanunsa yana yamutsa sumar kansa gani yake kamar motocin basa gudu buɗe lumsassun
idanunsa yayi yana kallon wani gefe daban wanda a zahiri ba can yake kallo ba ya tafi wata
duniya ta daban jin tsayuwar Motar yasa hankalinsa ya dawo a gangar jikinsa, a hankali yakai
dubansa ga wajen yadda mutane sukai cincirindon da ƴan jaridu kallon Company yake yadda
gobarar ta ƙonesa ƙurumis ga kayayyakin da suka ƙone suma ana fito dasu rufe idonsa yai
yana ƙara buɗesu, duk fitowa na cikin Motar sukai Sai Motar da yake ciki ce ba buɗe ba, tun
tsayuwar Motocin mutane da ƴan jaridu suka zuba ido da son ganin wanda ke ciki har akai 5
Minute, a hankali aka buɗe Motar yana zuro da Kyakkyawar ƙafarsa wacce take cikin takalmi
Cover shues masu azababben kyau saida yai wasu ƴan mimtuna sannan ya zuro da gudar
ƙafar tasa yana ida fitowa, kowa na wajen kallonsa yake