Showing 21001 words to 24000 words out of 39120 words
ba) fitowa mutanen suka fara yi, sannan Muneebba ta fara zuro da farar ƙafarta wacce
ke cikin flat shues haɗaɗɗu ƙafarta tasha jan lalle wanda ya ƙara ƙayata kyakkyawar ƙafarta a
hankali ta ida zurowa da gudar tana fitowa Rabi da Hafsat ne suka kamata suna bin su Seemah
wanda suka nufi wani Coridor wanda ya sada su da wani haɗadden Part mai kyau................
Only call me 08109554986
Chat me 09074759493
[5/21, 8:12 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*
Book 1
By: RIAMCOOL
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
Bismillahirrahmanirrahim
*P.25&26*
____________Wani Coridor suka bi wanda ya sa da su da haɗaɗɗen Part, Ƙofar Seemah ta
tsaya tana danna wasu Numbers nan take kofar Falon ta buɗe
haɗaɗɗen Falo ne wanda yaji Funiture da kayan more rayuwa, ga wani uban sanyi da ƙamshi
dake tashi, A hankali kowa ya shiga suna zama kan lallausan Cafet ɗin dake Malaye a tsakiyar
Falon,
ɗago da kanta Muneebba tayi ta cikin mayafin lifayar tana duban Falon wani iska mai zafi ta
fuzar hawaye na bin kuncinta, duk daular da ta shigo ji take kamar ta shigo a matsatsin kurku
ne, hatta sanyin Ac dake fita ji take kamar ana buso mata da hucin zafi, lallausan Cafet ɗin da
take zaune ji take kamar tana zaune a bisa ƙaya ne, ta ina zata fara karɓar ƙaddarar data
tunkarota?ta riga da tasan yanzu ne zata fara buɗe babin kundin ƙaddararta
ƙwas ƙwas ƙwas sautin ƙarar takalminta ke badawa tana bin step ɗin a hankali tare da tauna
Chewingum jikinta sanye da dakakkiyar Shadda blue color wacce taji aiki da Stone sai walwali
take,wuyanta sanye da sarƙar Gold, hannunta ɗaure da Watch ɗin Diamond yatsunta ma ɗauke
da zabban Diamond sai walwali suke,wani kallon ƙasƙanci da ƙyama Momm ta bisu dashi tana
zama ɗaya daga cikin kujerun Falon ta ɗora ƙafa ɗaya bisa ɗaya tana ƙare masu kallo,
"Meera!!! Meera!!!" ta faɗa da ƙarfi
fitowa Aunty Meera tayi,"Meera me yasa zaki kawo man jinin talauci a Falo? kamar ba ki san
inda zaki saka ƴan aiki su kaisu ba" ta faɗa da ɓacin rai
kamar ba Mahaifiyarta ba haka Aunty Meera ta taɓe baki tana faɗin "To Ni miye laifina zaki iya
sakawa a kaita a Falon" ta faɗawa tana shigewa wani Coridor
Indo ta ƙwalawa kira tana sakawa ta nunawa su Muneebba Part ɗinta,tare da ƙaresu da zagi da
cin mutunci, Indo na gaba suna biye har suka iso Part ɗin mai kyau da tsari shima,Falon suka
shiga wanda komai na ƙawa da kayan more rayuwa yaji, kamar wacce ƙwai ya fashewa haka
Muneebba taja ƙafafunta tana faɗawa bisa ɗaya daga cikin kujerun Falon ta fashe da kuka mai
tsuma zuciya,
kama hannunta Mamma Ladiyo tayi tana faɗin "Muneebba kiyi haƙuri da kalar rayuwar da kika
tsinci kanki komai na rayuwa muƙaddarine da Ubangiji ya riga ya rubutasa tun kafin dirowarki a
doron duniya, ki sani shi bawa baya wuce ƙaddararsa,duk yadda kika tsinci kanki a rayuwa ki
godewa Mahaliccinki,sannan kiyi haƙuri da juriwa wajen zaman aurenki mu muna miki fatan
Alkhairi zamu tafi dan ba zamu tsaya a ƙara ci man mutunci ba"
wani kukan ta sake saki tana kama hannun Hafsah tare da furta "Hafsat kema tafiya zaki yi ki
barni a cikin wannan baƙin gida mai cike da tarin Azababbiyar jarabta,na san ke masoyiyata ce
ta gsky Hafsat kada ki barni a gidan nan mu tafi a tare wallahi ba nison auren nan mai cike da
tarin ma'anoni da ƙangin bauta tun a saka ƙafata gidan nan nasan da cewar na riga da na shigo
baƙin kurku, akwai abinda zai sameni Hafsat idan kuka barni ku tafi dani"
Kuka Hafsat ta fashe dashi tana girgiza mata kai "don't say that Muneebba kiyi haƙuri in sha
Allah komai mai wucewa ne,kiyi haƙuri kiyi zaman aurenki da zuciya ɗaya, mu zamu tafi
saduwar Alkhairi" ta faɗa tana ɓanɓare hannunta da fita da sauri wani kukan na tafo mata don
ba zata iya jurar ganin halin da ƙawar tata take ba
tana ji tana gani haka suka fice kowa jikinsa mace laƙwas, sulalewa tayi tana gunsheƙar kuka
mai ban tausayi wanda har muryarta ta sauya, sbd tsabar kuka
shigowar da aka yi ce ta sakata ɗago da fuskarta tana duban Indo wacce itama ita ɗin take kallo
"ga Abinci Hajiya kici" ta faɗa tana ajiye mata warmer ɗin a gabanta
Ɗaga kai kaɗai ta iya mata, da tausayawa Indo ta bar Falon tana ja mata ƙofar, miƙewa tayi
kamar wacce aka yiwa shegen duka, Bedroom ɗin da ke Falon na gefe ta faɗa tana ƙarewa
ɗakin kallo, zuciyarta taji ta ƙara cunkushewa da wani Azababben baƙin ciki da ɗaci, Toilet t
faɗa tayi wanka da Arwalla ta mayar da sallar Magriba da Ishsha'i, Abinci kuwa kaɗan ta ɗan
tsakureshi tana jiran shigowar Mijin da aka ce an ɗaura mata aure
ganin har 10pm ta wuce ya saka ta kulle ƙofar ɗakin tana kwanciya don jin kanta na ciwo kamar
ya tsage gida biyu
*MAHEER*
kwance take bisa cinyar Mammi idanunwanta na tsiyayar da hawaye "Mammi wata ta fara shiga
rayuwar Yaya Bobbi ba ni ba, wata ce ta fara zama uwar gidan sa kafin ni, amma na san haka
Allah y ƙaddara man, Mammi na tashi da soyayyar mutun biyu na kaunacesu a lokaci guda
sannan nake tsantsar kishinsu su biyu kafin Mutuwar Yah DEEN na soshi na ƙaunacesa da
tsatsagwaron kishinsa,shi da Yah Bobbi, cikin ɗayan biyu na rasa wane nafi so"
shafa kanta Mammi tayi cikin tausayin ƴar tata, "Daughter zanyi komai domin ganin farincikinki
tabbas zan raba Auren Bobbi dashi da yarinyar ke ɗaya ce ƙwal a wurinsa "
"Mammi ba zan barki ki aikata wannan zunubin ba a kaina zan zauna da Yah Bobbi ko da ace
yana da Mata 3 ne ni zan zauna a ta 4, saboda ƙaunar da nake masa dukda bai san dani ba,
Mammi na kasa samun zuciyar Yah Bobbi"
"Daughter zaki samu zuciyar BOBBI, zan samar miki da ita tabbas zan mallaka miki zuciyar
BOBBI ko da ace zan rasa rayuwata ta wannan hanyar, sannan ko da ace DEEN na raye
tabbas zaki zauna dasu su biyun zaki mallaki zuciyarsu"
wata doguwar Ajiyar zuciya Maheer ta saki tana du ban Mammi da mamaki "Mammi me kike
nufi"
"ba zaki gane abinda nake nufi ba Maheer"
Numfashi Maheer ta ja, tana tashi daga cinyar Mammi, hawayen dake ambaliyar a kuncinta, ta
saka hannun ta share, tare da miƙewa ta nufi ɗakinta dan jin tsohon mikin daya daɗe mata a
zuciya na tashi, wato Soyayyar DEEN wanda ba tasan shi da BObbi waye tafi ƙauna ba, jiki a
mace ta faɗa bedroom ɗin ta tare da faɗawa bisa makeken Bed ɗinta ta fashe da kukan
tausayin kanta,zuciyarta na azabtar da ita da soyayyar mutum biyu, sai da taji kamar kanta zai
tsage gida biyu sannan tai shiru tana mayar da numfashi,bacci ɓarawo na ɗaukar ta
**********************
*ASAD BOBBI*
Ƙit ƙit ƙit sautin ƙarar agogon ɗakin ke badawa a daidai ƙarfe 2:00Am na dare a dai_dai lokacin
ne kuma wayarsa ta fara ƙara Alamar Alarm ne ya buga,
A hankali ya fara ware manyan idanunsa tare da motsa bakinsa A hankali yana karanto Addu'a,
kamar an tsikaresa yai wuf yana miƙewa da azama, Bathroom ya faɗa ya fito, wasu kaya da ke
gefe baƙaƙe wuluk ya ɗauka yana sakawa sannan ya ɗauki baƙin ƙyalle yana rufe fuskarsa,
komai na jikinsa sai da ya rufe da baƙin ƙyalle, wayoyinsa ya kashe yana ajiyesu a gefe ya fice
wani Coridor yabi yana tafiya har ya isa ɗan ɗakin,mabuɗi ya saka yana buɗewa tare da haska
Tocilan ɗin hannunsa, du bansa ya maida gefe yana kallon Mutumen dake kwance shi ma da
kalar shigarsa, cikin tafiyarsa ta Jaruman maza ya tunkarosa, duƙawa yai yana yaye baƙin
ƙyallen daya rufe fuskarsa ya kware, ƙare masa kallo yai yana sakin wani Miskilin Murmushi,
tare da zare ID card ɗin da ke gaban rigar mutumin da kuma phone ɗin sa, da azama ya fito
yana rufe ɗakin tare da bi ta ƙofar baya, wanda babu wanda zai taɓa cewa akwai wata ƙofa a
tanan, ɗan gudu gudu yake haɗawa, harya fice bakin layin gidan nasa, wayar y kunna yana
turawa Number dake cikin Sim ɗin message,
kamar jira ake sai ga wata mota baƙa wuluk, dai dai wajensa ta tsaya ana buɗe masa murfi, da
Azama ya faɗa cikin motar, rufe marfin Motar aka yi mutumen dake gefensa yana saka masa
baƙin ƙyalle ya rufe masa Idanu, da ƙarfin gaske suka figi mota suna sharara Uban gudu kamar
zasu tashi sama,sunyi tafiya ba ta wasa ba sannan suka isa mugun ƙungurmin jejejin wanda ba
zaka taɓa tsammanin mutum zai kawo kansa a gurin ba
Fitowa sukai suna tsayawa bakin gidan tare shigewa a ciki,taresu wasu ƙazdawan Mutane sukai
tare cewa su nuna ID card nash, nunawa sukai sannan suka shige, wata ƴar hanya suka bi
wacce ta sadasu da wani ɗan ƙaramin Holl, da bismillah ya ɗaga ƙafafunsa yana shiga, kujera
ya ja ya zauna suma haka mutanen da suka tafo a tare, Mutane nen wajen ya kalla a ƙalla sun
kai 12 a wajen taune lips ɗinsa na ƙasa yai yana bin kowa da ido
Miƙewa wani mutum yai yana zagayasu tare da ƙirga su, sannan ya dawo ya zauna, tare da
gyaran murya ya fara magana da muryan mugaye masu ji da ta'addanci "As you know, every
beginning of the year we have this meeting bcos muna son ƙara ƙwatarwa wannan ƙungiya
tamu ƴanci, sannan muna kawar da duk wanda ya shige mana gaba,a wannan shekarar muna
buƙatar akwatin wasiƙar sirrikan Company A.A.B limited don shine ya shige mana gaba yanzu
ya hana masana'antummu ci gaba, shi ne ya saka aka fara zaƙulu gurɓatattun Company mu, da
wasiƙar ce kaɗai za mu iya cin galaba a kansu, wannan shi ne Step one wanda idan yai za
muje a Step 2, ina son a fitar da gwarzon Namiji wanda zai iya satar Akwatin wasiƙar a ƙasar
Italian"
wajen tsit yai kowa na Imagine cikin dakiya da murmushi Bobbi ya miƙe yana sauya muryarsa
ya zuwa ta gwarazan maza da tantirai "Can I choose someone who can do this job for you?"
da kallo mutumin ya bisa yana miƙewa ya daki kafaɗarsa "Yes you can as long as we have a
mailbox"
Murmushi ya saki yana furta "ok Sir" fitowa yai yana zagayasu, kafin ya ƙure ƙazdin Mutumin
dake zaune a wajen wanda tabbas ya ganesa kuma ya sansa gun a jajircewa wajen ta'addanci
da cin galaba yana son a kara a wasan shi ya sa zai zaɓesa, hannu ya saka yana nuna sa "Of
course wannan zai iya, in har yai nashin nasara nine zan karɓi hukuncinsa ina da sure akan zai
mana abinda muke so"
Shiru shugaban yai yana furta " rashin nasara fa yana dai_dai da fitar numfashinka, muddin
muka faɗi a matakin farkon nan za kayi ban kwana da rayuwarka, ka san mu kammu abin sai ya
shafemu a wajen manyan Shuwagabannin ƙungiyar nan"
"Yes na Amince" ya faɗa yana zama tare da danna zoben hannunsa yana binsu da ido,
kowa bashi dama akayi akan su faɗi ra'ayoyin su akan zaɓen wanda zai saci mailbox din, wasu
suce bai yi ba wasu suce yayi, waɗanda suka fi raja'a shine zaben da akayi yayi shi yasa aka
bar wanda Bobbi y zaɓa
**************
*YOLA*
Fattu
cikin tsoro da razana Fattu ke bin Ja'e da su Sa'adu da kallo, girgiza kai tayi hawaye na biyo
kuncinta, wani wawan mari Ja'e ya kwalfa mata, yana ƙara sauke mata wani a kunci, "Fattu
dama ke ƴar iska ce? Wato iskancin naki ya fi ƙarfin ki bi na gari sai dai ki jawo mana baren
kwarto ki kawo mana,to wallahi yayi ta rayuwarsa zan rabasa da duniyar, sannan nayi abinda
nake son yi dake a yanzu kafin aurena dake, zan yaga miki rigar mutunci Fattu" ya faɗa yana
kai hannunsa jikinta yana kince zanin jikinta
durƙushewa tayi a wajen tana fashewa da wani kalar marayan kuka mai ban tausayi tare da
girgiza masa kai..........
[5/21, 8:13 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*
*Book 1*
*By: RIAMCOOL*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*P.27&28*
_____________Durƙushewa tayi a wajen tana sakin wani marayan kuka tare da ƙanƙame
jikinta tana girgizawa Ja'e kai bakinta na karkarwa
"Wallahi ban taɓa abinda kake zato ba, haka zalika ban taɓa kusantar zina ba, ina ƙyamatar
zina ina ƙyamatar mai yin ta, kamar yadda Ja'e kai ma nake ƙyamatarka na tsani halayyarka ta
zinar" ta faɗa tana zubar da hawayen takaici
wani wawan mari ya sake kwalfa mata wanda ya saka bakinta fashewa yana tsartuwar jini,
dogon gashin kanta yaja da ƙarfi yana ɗagota kafin ya fashe da wata muguwar dariya yana bin
manyan Boobs ɗin ta da kallon haɗama,fuskarsa ya kai dai_dai sai tinsu yana gogawa, wanda
nan take wani matsanancin ɓacin rai ya ziyarci Fattu, turesa take da iya ƙarfinta tana ihu, tare
da kiran JODDi wanda tunda Ja'e ya riƙe Fattu ya ke dubansa da rinannun idanunsa bakinsa na
karkarwa tare da jikinsa kamar mazari
rigar jikinta yake ƙoƙarin zarewa wanda ya riƙeta da iya ƙarfinsa yana son cimma burinsa,
kamar mai nazari haka JODDi ya lula yana kallon dutsen dake gabansa, hannun ya saka yana
ɗaga ƙaton dutsen da iya ƙarfinsa yana saukewa Ja'e a kai, wata muguwar ƙara Ja'e ya saki
yana dafe sai tin gefen kansa wanda ya fashe yana tsartuwar jini, cikin dakiya da tafiyar
ƙarfafan maza ya tako ya zuwa gun Ja'e yana ƙara shaƙosa da iya ƙarfinsa, ya ƙara kai masa
wani wawan duka a gefen wuyansa wanda ya saka sa tafiya luuuu yana faɗuwa idanunsa na
rufewa wanda numfashinsa ya tsaya cak
cikin razana Sa'adu yaja da baya yana
yada makaminsa,yana barin wajen da gudu cikin tashin hankali, jikin Fattu na karkarwa ta miƙe
tana ja da baya tare da ɗora hannu a ka, kallonta JODDi yai yana ɗaukar zaninta ya miƙa mata
tare da kauda kansa gefe yana shigewa bukkar
Zanin ta ɗora tana duƙewa wajen ta fashewa da kukan tashin hankali,domin tabbas ta san
akwai babban Abin da zai biyo baya muddin Ja'e ya mutu, yan zun ta san da cewar rayuwar
Joddinta na akan haɗari, amma taya zatai ta cecesa daga wannan ƙangin daya jefa kansa a ciki
ta ina zata ja sa su gudu domin tsira da rayukansu waɗanda suke daf da gangara
*************************
MUNEEBBA
Kiran sallar Asuba ne ya tasheta daga barcin wahalar daya kwasheta mai cike da mugayen
mafarkai masu firgitarwa
bakinta ɗauke da Addu'a ta miƙe tana ƙara buɗe idanunta waɗan da su kayi mata nauyi ta kasa
buɗesu saboda kumburin da su kayi
kamar wacce aka yiwa shegen duka haka ta miƙe ko ina na mata ciwo Toilet ta faɗa tana wanka
da ɗauro Arwalla tare da kabbara salla, bayan ta idar ta hau rera karatun Alqur'ani wanda ya
fara sanyaya mata zuciya, ta daɗe tana karatu kafin ta ɗaga hannayenta sama tana kaiwa
Ubangiji kukanta,bata tashi daga kan sallayar ba sai da rana ta fara fitowa sannan ta fito Falo
tana kwanciya nan take wani sabon baccin ya sake kwasheta
ruwan sanyin da taji an zuba mata ya sakata tashi a razane tana furta sunan Ubangiji, bata ida
dawowa ba taji an kwasheta da mari tare da ƙara mata wani,hannunta dafe da kunci ta ɗago
tana kallon Mommi wacce take Binta da kallon wulaƙanci "ke har kin samu wajen zama ki
kwanta ki huta ko? to ki sani wallahi tun yanzu zaki fara karɓar hukuncinki, na aurar man Yaro
da ki kayi, ke da rayuwar jin daɗi a gidannan har abada, ki sani Auren bauta ne ya kawoki gidan
nan domin bauta ce zaki ci gaba da yi mana tun daga yau"
tun da Mommi ke maganar Muneebba ta mayar da kanta ƙasa hawaye na mata ambaliya a
kunci "Ya Allah wannan wace kalar ƙaddarariyar jarabawa ce ka jarabceni da ita a lokaci guda?
baya ga wacce nake ciki"ta tambayi kanta
"Maza tashi ki sauya kayan jikinki ya zuwa na hause mad kizo ki shige cikin ƴan aiki domin tun
daga yau zaki fara aiki,yau ko mai kece za kiyi, sannan tun daga yanzu ina son duk wanda zai
zo ki nuna masa cewar ke ƴar aiki ce, har Mijin naki karki nuna masa cewar kece matarsa zan
san yanda zanyi"
kamar wata taɓaɓɓiya haka Muneebba ke bin Mommi da ido da mamaki, wanda marin da ta
sake ɗauketa dashi ne ya sakata dawowa hayyacinta, da yatsa Mommi ta nuna ta tana furta "ke
ki bini a sannu wallahi ba'a min da wasa ki aiwatar da abinda na umarceki ga kaya nan na baki
nan da 5 Minute ki canja ki fito" ta faɗa tana juyawa
kamar jira Muneebba take ta fita ta fashe da kukan da sai yanzu ta samu ya fito, wace kalar
baƙar rayuwa ce ke shirin tunkarota? baya ga ƙaddarar rabuwarta da Nazeer,ga kuma wata na
shirin ɓullo mata ta ɓoye kanta a gurin Mijinta, hawayen ta share tana cire kayan jikinta ta
mayar dana house mad wanda riga da skert ne blue color, hular ta ɗauka tana saka ma kanta,
kamar wacce ƙwai ya fashewa haka ta fito tana tafiya a hankali
tsayawa tayi ta rasa ta hanyar da zata bi taje Part ɗin Mommi, bubbuga bayanta da taji anyi ya
sakata juyowa tana kallon