Showing 15001 words to 18000 words out of 39120 words
meeting daya haɗa na manyan ƴan kasuwa masu neman Share
na Company sa wanda harda turawa, tunda ya shiga idonsa ya shiga kan na Alhaji Madu
wanda ya hakimce waje guda, murmushi ya saki ganin wasan na tafiya yadda ya kamata zama
yai suka fara tattaunawa tareda faɗin duk wanda ke son Share na A.A.B Company dole sai ya
zuba kaso 50 na rabin dukiyarsa, ba tareda ɓata lokaci ba suka zuba dukkansu, da kallo Alhaji
Madu ke bin Bobbi,Wanda Bobbi na lura da hakan ɗage gira guda yai yana ɗan murmushi ya
miƙa masa hannu cikin wayancewa sukai musabaha, tare da ɗan taɓa firar kasuwanci wanda
duk dan Alhaji Madu ya fidda tantama a kansa ne
Bayan kwana biyu anyi baikon Maheer da Bobbi iya one month aka saka, wanda tunda tazo
koda so guda ne basu haɗu ba, danshi gogan mantawa ma yake da wani baiko nasa, su Mom
ne kaɗai ke rawar gaban hantsi, haka kwanakin keta tafiya harya rage saura sati biyu
*MUNEEBBA*
Zaune take ana mata dilka wanda tayi wani haske na ban mamaki kyau bana kaɗan ta ƙara ba
saboda gyaran da take sha wajen wata maƙociyarsu wacce take gyarata saboda gabatowar
auren wanda bai wuci 3 days ba, Kasancewar Muneebba bata da wasu ƙawaye ya sata bata
wani shirya event ba............. [5/21, 8:11 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*
book 1
*By Mariam sani Riamcool*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*P.19&20*
________Kasancewar Muneebba ba tada wasu ƙawaye ya sata bata wani shirya event ba, tun
bayan Sati aka kawo lefe wanda akwati goma sha biyu haka yai mata kuma dukkan kayan
masu tsada ne wanda Hajiya da kanta ita ta haɗa don tasan abinda take shiryawa shi yasa ta
nuna ta saduda,
Kallonta Hafsat tayi tana faɗin "wai kinga kuwa wani kyau na ban mamaki da kikai Muneebba,
wannan idan Nazeer ɗin ya ganki anya zai ganeki?"
dariya Muneebba tai tana miƙewa, sallama sukai wa Matar sannan suka nufi gida, da sallama
ɗauke a bakinta ta shiga sai dai fara'arta ce ta ɗauke sakamakon ganin Mamma Ladiyo wacece
ta wani caɓa ado Alamun kuɗi da hutu sun zauna mata, harga Allah Matar batai mata ba, sai
dai ta danganta hakan da azabar data bawa Mahaifiyarta shi yasa bata sonta
kallon Mamma Ladiyo Muneebba tai tana gaisar da ita da ƙyar, fuska a sake ta amsa tana binta
da kallo ƙasa_ƙasa wanda take ayyana abubuwa da dama a ranta, shafa haɓar wuyanta tai
tana maida kallonta ga Mamma, wani Munafukin murmushi ta saki ko iya haka tabar A'ishatu
tayi farinciki sai dai dukkan wani abu da zai kawowa Shatu kwanciyar hankali da jin daɗi ba
sonsa take ba, ya zama dole kuwa ta ƙara tashi tsaye
Washe gari Mutane ne cike da gidan anata hada_hadar buki wanda yawancinsu duk ƴan
unguwar ne sai kuma ƙawayen Mamma Ladiyo
Sanye take da wani material fari tas ɗinkin Fitted gown na bride an zuba mata Make up fuskar
nan sai sheƙi take da haske ga jan lallen da aka zana mata wanda ya ida fiddota sosai, kallonta
Nazeer yake ta Vedio call yana ƙara tazbihi ga Ubangiji da zai mallaka masa wannan
Kyakkyawar halitta "Masha Allah Hayatee nagodewa Ubangiji sarki gagara misali da zai mallaka
man wanna haɗaɗɗiyar kyauta, Muneebba ba zan kwatanta miki yanda nake ji a raina ba
kwatankwacin yadda nake sonki ba zai faɗu ba bana fatan wani abinda zai gifta a tsakanina
dake bana fatan kalmar rabuwa ta gifta a tsakanimmu, zan riƙe ki na tarairayeki kamar tsoka
ɗaya a miya zan kula dake mu haifi ƴaƴa mu tarbiyantar dasu"
Wani murmushi ta saki mai kashe zuciya tana lumshe ido ta waresu a fuskarsa "Thanks dear
insha Allah dani da kai mutu ka raba" murmushi yai yana mata sallama dan zuwa yai wanka,
"ok bye take care" ya furta tare da kashe mata ido
Murmushi tai tana rufe fuskarta da tafin hannunta, da ƙyar ya kashe wayar shima dan Abokansa
na masa tsiya ne kar lkc ya ƙure ango ya makara
Ajiyar zuciya ta saki yau jinta take cikin maɗaukakin farincikin da bazai musaltu ba, miƙewa tai
Hafsat na ɗaukar su Photo wanda sunyi kyau sosai
Ƙarfe 2:30 wajen ɗaurin auren damƙam yake da mutane da manyan jiga_jigan motoci na
alfarma wanda kowa sai da yai mamakin ganin manyan Mutane da suka zo ɗaurin auren
Zaune yake a bayan mota mai baƙin glass Wanda babu wanda ke ganisa fuskarsa sanye da
farin gilashi janye gilashi yai yana share hawaye, ya gaji da wannan bakar rayuwar da yake ciki
wanda dashi da iyalinsa sai dai kallo daga nesa Anya zai iya kuwa? ace ana ɗaura auren Ƴarsa
guda wacce take mafi soyuwa a rayuwarsa amma ba zaije ba, kamar ba babban mutum ba
haka ya fashe da kuka mai ban tausayi, Manyan Motocin da suka Kunno Kai su suka saka sa
tsayawa da kukansa yana kallonsu, fitowa na cikin Motar yai tareda Securities murmushi ya
saki ganin Ahmed A Sadis ya hallara
tunda Motocin suka hallara gaba ɗayan Mutanen wajen hankalinsu ya dawo wajen ganin
shahararren ɗan kasuwa mai ji da kuɗi, murmushi yai ya samu waje ya zauna, nan ya bayyana
musu shi ɗan uwan Mamma ne yana so a bashi waliccin babu ɓata lokaci za'a fara gudanar da
ɗaurin aure
cikin hamzari Nazeer ya miƙe jikinsa har ɓari yake jijiyoyin kansa sunyi ruɗu_ruɗu "bana buƙatar
auren nan bana so na fasa auren kada a ɗaura man aure da Muneebba wallahi bana so na
fasa" ya faɗa da ƙarfi kamar zuciyarsa zata fito
tsit wajen yai kowa na kallonsa da mamaki yanda yake kuka riris tareda sheshsheƙa, da gudu
Alhaji Mamman yazo yana faɗin "Nazeer kana cikin hankalinka kuwa? idan baka cikin
hankalinka ka dawo, ko wani abun Muneebba ta aikata?"
"Wallahi bana sonta kawai na fasa dan Allah a janye auren nan kowa ya tafi" Nazeer ya faɗa,
babu yadda ba'ai da Nazeer ba amma yaƙi hakan yasa Mutane fara haramar tafiya, sai dai ɗan
shelar da yai magana ne akan kowa ya dawo za'a ɗaura aure yasa su dawowa ana zama, Nan
take Dad ya fiddo 500k yana bada sadaki bai tsaya wani dogon tunani ba, Sbd ɓacin rai,
mutane saiji sukai ana faɗin an ɗaura Auren Muneebba Muhammad tareda Asad Ahmad Bobbi
akan sadaki 500k lakadan ba bashi,
Nan take wajen ya kaure da hayaniya ganin abinda Dad yai tare da mamakin babban millionaire
Asad BObbi da Muneebba ta aura nan take yanke ƴan faɗi ba'a tambaya ba suka fara watsawa
a media, ana gama ɗaurawa Dad ya miƙe da nufin zuwa gidan su Muneebba dafashin da yaji
anyi ya sashi juyawa yana kallon Abbie wanda ya dora kansa a kafaɗa yana kuka riris tareda
Habib shima wanda kukan yake, ɗago da Abbie Dad yai shima hawayen nason taruwar sai dai
yai ƙoƙarin shanyesu yana ƙaƙalo murmushin dole, "haba Muhammad miye na kuka kamar
ƙaramin yaro kaga yadda mutane hankalinsu ya fara dawowa wajenmmu, kayi shiru mana"
"Dad wallahi dole Abbie damu kammu muyi kuka baka san halin da muke tsintar kammu ba har
yanzu kasan kuwa ita kanta halin da Ummi ta shiga dalilin haka fa har yanzu Ummi ko magana
ba tai, ita Mamma makanta Ita Ummi rashin magana, shi Abbie Aman jini, shin Dad ka faɗa
mana wanna ba abin ai kuka bane?" Habib ya faɗa tareda share hawayensa
"bani da abinda zance maka Yah Ahmad haƙiƙa ji nake a yau ka maye mani gurbin yayyena
banda abinda zance maka na fitar da ƴata kunya dakai, bani da bakin gode maka" Abbie ya
faɗa tare da share hawayensa
Murmushi Dad yai yana dafa kafaɗarsa tareda ɗago haɓarsa yana share masa hawayen yace
"Muhammad ba batun gdy a tsakanimmu nima ai ƴata ce bata da wani banbanci tsakaninta
dasu Iftihar kamar yadda suke ƴaƴa itama haka take a wajena, kayi haƙuri komai mai wucewa
ne"
A can gidan kuwa gidan ya kacame da guɗa ana faɗin an ɗaura aure, Muneebba dake ɗaki
wani irin farinciki ya kamata tana tashi ta rungume Hafsat tace "Alhmdllh yau burina ya cika na
zama matar Nazeer Hafsah ko yanzu na koma ga mahaliccina nayi farinciki" ta faɗa tana dariya,
dariya itama Hafsat ta saki tana tsokanarta tare da kingin Abokansu,
Khabir ne ya shigo jiki a sanyaye jiki ba ƙwari "bada Nazeer aka ɗaura ba Mamma wallahi bada
Nazeer bane" Khabir ya faɗa yana fashewa da kuka tareda rungume Mamma kamar wani
ƙaramin yaro, Salati Mamma Ladiyo ta saki da ƙarfi yadda kowa zai iya jiyowa har maƙota tace
"Nazeer kana nufin bada Nazeer aka ɗaura auren Muneebba ba, to waye mijin??? Innnalilahi
wa'inna ilaihirraji'un A'ishah kuna ganin jarabta" Mamma Ladiyo ta ƙarasa zancen sa fashewa
da kukan Munafurci wanda kowa zaiyi zaton daga zuciyarta yake fitowa
MUNEEBBA dake ɗaki tana dariya jin zancen da Mamma Ladiyo tai ya sata fitowa ɗakin da
gudu tana kallon Yah Kahabir da Mamma wanda suke hawaye, kallon Mamma Ladiyo Khabir
yai yana faɗin "Mamma Ladiyo Nazeer cewa yai ya fasa baya son Muneebba wallahi da kansa
ya furta ya fasa" wani irin zillo zuciyar Muneebba tai tareda harbawa baki na karkarwa da jikinta
tace "Yah Khabir wallahi ba gsky ka faɗa ba, ka gyara kalamanka Nazeer bai taɓa ƙina ni nasan
da Nazeer aka ɗaura man aure kada ka ƙara danganta igiyar aurena tare da wani Yah Kahabir
Nazeer ya riga daya zama nawa" ta faɗa tare da durƙuahewa wajen tana sakin wani marayan
kuka tareda fatan Allah yasa ba dai dai kunnuwanta suka ji mata ba,
"Ai kam Muneebba sai haƙuri yanzu Rabilu kefa ce man bada Nazeer aka ɗaura ba da wani
Asad BObbi ne wanda duniya tasan dashi, kuji ikon Allah" Rabi maƙociyarsu data yafo zani ta
faɗa
basu ankara ba sai jin faɗuwar Muneebba sukai ta zube ba numfashi a tare da ita, idanunta sun
wani ƙaƙƙafe, "Innnalilahi wa'inna ilaihirraji'un Muneebba ki tashi dan Allah, mukaita asibiti"
Hafsah ta faɗa tana kuka, Mamma ma kukan take ita da Khabir wanda ya ɗauki Muneebba da
gudu ya nufi ƙofar fita da ita, karo suka ci da Dad Wanda yake yunƙurin shigowa hankali a tashe
shima ya amshi Muneebba yana nufar motar da ita Sbd tashin hankali da ƙyar Mamma tasa
Hijab ita da Hafsat suna shiga Motar tareda Khabir Dad kuma na wata motar wani gudu suke
shararawa har suka isa Private hospital Wanda aka karɓeta da gaggawa ganin halin da take ciki
kuka Mamma keyi riris Hafsat na bata baki, taƙi tai shiru, dukansu zaune suke sunyi
jugum_jugum, Abbie dake daga gefe can yana kallonsu hawaye na bin kuncinsa, dashi da
Habib wanda babu halin zuwa wajensu su duka, kallonta yake zuciyarsa na masa zafin yadda
take zubar da hawaye, " wannan ma na gani Aysher ban san iya kukan rashina da kikai ba, dole
nazo wajenki koda kuwa a yau ɗin nan zan fitar da numfashin ƙarshe ba zan juri ganin
hawayenki ba Aysher na kasa jurewa" ya faɗa da ƙoƙarin tunkaro inda take, Habib ne ya
jawosa yana girgiza masa kai hawaye na zuba yace "Abbie na roƙeka kada kaje zamu iya
rasaka kasan kuwa iya jinin da kake zubarwa wajen yunƙurin zuwa garesu? Abbie kada ka ƙara
cilla mu a wata matsalar ka barmu da iya wacce muke ciki ba dammu ba sai dan Mamma da
kuma Ummi da suke buƙatar ka samo musu mafita" ya faɗa tareda riƙe ƙafar Abbie yana kuka
shima, hawaye Abbie ya share yana dawowa ya ɗago Habib yana kallo yace "naji Habib ba
zanje ba amma zanyi nesa da ƙasar nan ko dan ku da iyayenku, zan bar ƙasar gaba ɗaya na
nisanci kaina daga Iyalina tunda hakan shine mafitata" ya faɗa yana barin wajen da sauri, da
kallo Habib ya bisa yana share hawaye shima yabi bayansa
dukkan wata zirga_zirga Dad ne ya dinga yinsa wannan ne ya tabbatarwa Mamma lallai zasu
iya kular mata da ƴarta, hakan yasa hankalinta ɗan kwanciya suna jiran tsammani don Doctor
ya Kira Khabir da Dad, ganin sun fito fuskarsu da ƴar walwala yasa Hafsat sauke ajiyar zuciya,
kallon Mamma Dad yai da tausaya a fakaice yana share hawaye yace
"Alhamdulillahi tunda an samu nasar daidaita Numfashinta, dama shine yake barazanar
ɗaukewa yanzun anyi nasarar daidaita sa, bacci take yanzu sai tsawon 3 hours ta farka, sai dai
na sake baku haƙuri akan abinda ya faru tunda lallai wannan auren sai dai muce nufin Allah ne
wanda ba muyi zato da tsammani ba haka zalika shine mijin da Ubangiji ya rubuta zata aura
tun dirowarta a doron duniya, ita ƙaddara zanen zabo ce, kuyi haƙuri da kalar rayuwar da kuka
tsinci kanku insha Allah komai mai wucewa ne Bayan wuya sai daɗi" ya faɗa da Murmushi
hawaye Mamma ta sake sharewa tana faɗin "bawan Allah ni bani da abinda zan gode maka
dan ka fitar da ƴata kunya dani kaina da ka rufa mana asiri lallai na yadda da cewa komai a
rubuce yake bawa bai isa ya sauya zanen ƙaddararsa ba, haka Allah ya tsarawa Muneebba
bama da tsimi da dubara, Allah yasa hakan shine mafi Alkhairi yasa kuma Abokin rayuwa ne"
Mamma ta faɗa cikin dauriya
Murmushi Dad yai yana ƙara jinjinawa Mamma akan tawakalli da yarda da ƙaddara, take away
yai musu da yi musu sallama akan gobe zashi dawo, ɗakin da take kwance suka shiga,kwance
take fuskar nan tayi fari fat hancinga sanye da oxygen hawaye Hafsat ta share tana duƙawa a
wajen ta kama hannunta tana riƙewa gam, Alwalla Mamma tai tana salla la'asar da Magriba
wanda tashin hankali bai barta tayi ba sai da daddare Khabir shima ya tafi zuciyarsa cunkushe
da damuwa
Misalin ƙarfe 3:30Am a hankali take ware manyan idanunta harta waresu duka akan farin silin
ɗin Idanunta na zubar da hawaye wanda ta tabbatar da lallai ba Nazeer bane Mijin nata wani
ne daban aka ɗaura mata igiyar aurensa a kanta, "Ya halayyarsa take, wane kalar mutum ne,
wanene shi, wace sabuwar rayuwar ƙaddara zata gudanar, shin mai kyau ko akasin
hakan?????" Waɗannan tambayoyi sune ta ɗinda maimaitawa kanta tana hawaye
Gidan Mom sosai ya kacame da hayaniyar Mom tun la'asar take abu guda wanda ganin auren
Bobbi na yawo a media ga kuma fuskar Dad wanda ke murmushi wannan ya tabbatar mata da
lallai auren Bobbi ɗinne su kansu su Zameer abin ya ɗaure musu kai,uwa uba Maheer wacce
take kuka taƙi magana sai dai bin kowa da ido, wannan ne ya ƙara tada hankalin Mom ta dinga
kiran Dad da Bobbi ba ji ba gani.......
Wayyo akwai fa cakwakiya, ina uban gayyar yake maí ¾íµºku dai yi haƙuri yau ba'a taɓo ɓangaren
Fattu ba da kuma Bobbi
[5/21, 8:12 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*
Book 1
*By Riamcool*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*P.21&22*
___________Tayi kiran iya kira babu wanda ya ɗaga a cikinsu daga baya ma Bobbi kashe
wayoyinsa yai dan lokaci shi kanshi yana buƙatar keɓewa Dad kuwa lokacin yana Asibiti wajen
Muneebba sai daga baya yaga kiran kai tsaye gidan ya nufa
da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga fuskarsa a haɗe tamau babu alamun wasa ko rahama
kallon ƙasa da sama Mom tai masa cikin ɓacin rai ta miƙe "mi kayi haka? wannan wane kalar
tozarci da cin mutuncin kaja mana kasan kuwa abinda ka aikata?" ta ƙarashe zancen da huci
"Yes nasan abinda na aikata dan na isa ne shi yasa na aikata aure na yiwa yarona kuma ita ce
wacce na zaɓa masa abokiyar rayuwa ta har abada babu wanda ya isa ya hanasa zama da ita"
ya faɗa yana haura up stairs
binshi tai da azama tana faɗin "wallahi ba zai zauna da wata shegiyar ƴa ba in ba Maheer ba
Maheer ce zaɓina kuma ita zai aura wannan kuwa ranar da tazo gidan a ranar zata barshi dan
sai ya mata saki ukku cir, wanna wane kalar rayuwa ne ka saka ƴar mutane a damuwa gashi
tunda Maheer taji auren nan ko Abinci bata ci ba ƙarshe ma kulle kanta tayi a ɗaki to wallahi
tallahi indai ni na haifi Bobbi sai na saka ya saki ƴar matsiyatan can kuma zanyi bincike"
kallonta yai yana kauda kansa gefe guda Sbd ɓacin rai "idan bake kika haifesa ba fa?" yai mata
tambayar yana kafeta da ido, itama kallonsa tai tana sakar masa wani Miskilin Murmushi daga
bisani kuma ta jijjiga masa kai tana barin wajen da sauri, da kallo ya bita har shiɗa, haurawa
sama yai yana shigewa bedroom ɗinsa zama bisa bed yai yana dafe kansa dake masa ciwo
Mom kuwa tana shiɗa dasu ABEED ta fara cin karo suma sunyi jugum_jugum kallonsu kawai tai
ta wuce, duk lkcn data gansu ranta yana sosuwa sbd ta tsani Mahaifiyarsu ganinsu kansa tuna
mata yake da Mahaifiyarsu, ita ce mafarin tarwatsa mata farinciki ita ce sarauniyar Ahmad ita ce
magadiyar wannan gida Sbd haifafar ƴaƴa Mazan da tayi taya zata ma bari su kansu ƴaƴan
nata suyi farinciki wasan na nan zuwa kansu
*Asad BObbi*
A hankali yake saukowa daga Step ɗin haɗaɗɗen benen wanda ƙarafen benen kanshi na zallar
azurfa ne cikin gadararriyar tafiyarsa ta ƙarfafan maza yake saukowa harya ƙarasa saukowa a