Showing 9001 words to 12000 words out of 39120 words
yadda ya wani haɗe rai kwarjini da
haiba sun taru a jikinsa, uwa uba Izza da jin kai wanda a jininsa suke, a hankali yake takowa
ƴan Jarida nayo masa caaaa ko wane na wullo masa tambaya, wani ɗan Jaridan ne yasha
gabansa yana ƙara gyara farin gilashi idonsa "me zaka iya faɗa mana game da ƙonewar
Company ka, shin da gaske abokan hamayyarka sune sukai ta'addin ƙonewarsa, sannan..." bai
idasa ba saboda wani kallo da Bobbi ya jefeshi dashi wanda yasa shi haɗiye kingin
tambayoyinsa yana bashi hanya
Kallon ɗan Jaridan yayi yana sakar masa wani killer smile wanda shi kaɗai yasan ma'anarsa,
kai tsaiye ya shiga Company da securities ɗinsa kallon Company yake ganin yadda har iyanzu
bai daina hayaƙi ba, cije lips ɗinsa na ƙasa yayi sannan ya sake sakin wani shu'umin murmushi
"Zaidu" ya furta a hankali
Ma'aikan Company ne suka taru suna miƙo gaisuwa babu wanda ya amsa mawa kallonsu yake
ɗaya bayan ɗaya yana nazartarsu, wanda kowa cikinsa ya ɗuri ruwa uwa uba Manager
Company, bai ce uffan ba har manager ya miƙe yana magana tare da saddar da kansa yace
"Oga ka gafarce mu wallahi dukkammu ba musan yadda akai gobaran ta tashi ba"
shiru ya ƙara yi na wasu daƙiƙu dan sun fidda ran da zai basu amsa "Ok ban tambayeku ba'asin
yadda akai gobaran ta kama ba, bana buƙatar jin wani ƙarin zance daga gareku haka Allah ya
riga ya tsara mana" suka ji saukan muryanshi wanda yake yi kamar baya son buɗe bakin nasa
don shi magana wahala take masa
yana gama faɗa ya miƙe yana fitowa wani ƙaramin tsaki yaja ganin yadda mutane ke kallonsa
kamar ba Mutum ba ga hayaniyarsu data fara isarsa sai da ya ɗan ƙara zagaya Company
sannan ya futo, buɗe masa Motar akai ya shige sannan kingin suka shiga kai tsaye Guest
house ɗinsa suka nufa don yana buƙatar hutu
*********
*Yola*
*FATTU*
wata kalar busa sarewa ce ke tashi a cikin jeji wacce Fattu keyi a duk lokacin data fito kiwon
Shanu data fara busa jejin zaiyi tsit tsuntsaye za suna dinga safkowa tana watsa musu tsaba
suna ci tana ƙara busawa, wani juyi take ƙara yi tana rugawa da gudu ta hau wani ƙaton dutse
dariya tayi tana ƙara kai sarewar a bakinta ta fara busata cikin ƙwarewa da iyawa, wani sautin
na daban mai ratsa dukkan gaɓukkan mai sauraro Fattu keyi jejin ne ya ƙara yin shiru yi take
harta fara gajiya
ganin babu alamunsa yasa Fattu raurau da ido ta buɗe baki tana faɗin "JODDI!!!JODDi!!!
JODDI!!!" da ƙarfi take kiran sunansa namma shiru babu alamunsa sarewar ta ƙara kaiwa
bakinta ta fara busan da tasan indai yana kusa to tabbas zaizo wata kalar busa yanayinta mai
taken ban tausayi take yi
Wata kalar feɗuwa aka yi wacce ya sata sauka daga saman dutsen tana bin hanyar da feɗuwar
ke fitowa tasan tabbas shine wata kalar busa tayi wanda zaka rantse da usur akayita amma da
baki tayi shi nufar hanyar tayi tana ƙara yin wata shi kuma yana feɗuwa da wani kalar sauti,
yana ganinta ya nufota da gudu itama da gudun ta nufesa tana kallon yadda yake dafe cikinsa
kamo Hannunsa tayi da Yaren fulatanci take faɗin "JODDI ina ka tafi? yau kayi nisa" dukda
tasan bazai maido mata amsa ba kuma ba zai fahimci abinda take nufi ba tunda ba hankali ne
dashi ba,mamadin ya bata amsa saima haɗe rai da yayi yana nuna mata cikinsa, murmushi ta
saki tana jawo hannunsa suka nufo inda ta ajiye masa ƙwaryar furar data damo masa tasha
kindirmon Nono zaunar dashi tayi ta ɗauki ludayin ta dinga ɗebowa tana bashi a baki har sai da
ya ƙoshi sannan ta ƙyalesa miƙewa yayi da nufin komawa inda ya fito, dama tasan daya sha zai
tafi saboda shi kullum take zuwa nan kiwon Shanu wanda ta rasa baya ga tausayinsa me take ji
da kanta ta rakasa bukkar data kafa masa tun farkon ganinta dashi sai da ya shiga sannan ta
dawo tana kaɗa Shanunta suka sha ruwa sannan ta kaɗasu suka bi hanyar gida kasancewar
Magriba data doso sai dai tana tunkarar gidan gabanta ya fara faɗuwa don tasan yau Innaro da
Baffalo sai sunyi farfesun Namanta tunda ta ibarwa Innaro fura a ɓoye kuma Saro ta ganta
tasan zata faɗa "Ya Allah" ta furta tana nufar garken shanun dasu sannan ta nufi bukkarsu da
nufin ta saɗaɗa ta shiga sai dai jin saukar Sanda a ƙwabrin ƙafarta ya sata durƙushewa Baffalo
ne ke kallonta cikin Yaren fulatanci yace "ke Fattu yaushe kika koyi sata? furan Innaro irgagga
da zata tafi kasuwa ta siyar ita kika ɗiba to yau sai na miki ligib ƴar jakar uba" yana gama faɗin
hakan ya ɗaga sandarsa ya dinga sauke mata tun tana ihu a hankali har yakai ga tana yi da
ƙarfi sai da ta daku sannan ya ƙyaleta
Bukkarta ta shiga tana share hawaye tana ji Innaro da ƴarta Saro suna yada mata habaici ta
shige, murmushi ta saki tunawa da JODDi wanda akansa ne akai mata wannan duka ji tayi ma
dukkan haushin dukan ya fice, sandarta ta ajiye tana nufar rafi don tayi wanka
*Wacece Fattu*
FATTU dai ƴa ce ga Mlm Isah Baffalo wanda matansa biyu Innaro da mairo Mahaifiyar Fattu
wacce tun tana shan Nono Mamanta ta rasu wanda ta taso cikin uƙubar Innaro tun tana ƙarama
take ɗaukar Sarewar Baffalo wanda sana'arsa ce busa Sarewa , hakan yasa itama ta gada,
zuwa kiwon Shanun da take ta haɗu da wani mahaukaci cikin jeji wanda ta saka masa sunan
JODDI busa Sarewar da take yasa kullum yake zuwa wajenta ita kuma ta tausaya masa tana
kawo masa Abinci duk lkcn da zata fito kiwo,
tana gama wankan ta shiga jeji ta hau bishiya don can take kwana
*KANO*
Zaune take bisa bed ɗinta fararen idonta sanye da farin gilashi ta kafe Photon dake jikin Laptop
ɗin da ido tana sakin Murmushi tea ta kurɓa tana ƙara zooming ɗin Photon "Yah Bobbi" ta furta
a hankali tana lumshe manyan idanunta "Maheer Maheer Maheer" taji Mami na ƙwala mata
kira rufe loptop ɗin tayi tana ajiye tana fitowa a hankali take bin step ɗin benen kamar bata son
taka ƙasa, ida sakkowa tayi ta nufi Mami tana faɗawa jikinta "Mammi gani" shafa kanta Mammi
tayi tace "ki shirya gobe zaki je gidan Mommy, ayi dayi danni na fara gajiya ƙara kije ya dinga
ganinki kusa kafin ayi muku baiko, har ya saba dake sannan wannan muskilancin naki da aji ki
ajiye shi ki dinga shishige masa ta hakan ne zaki samu shiga gurinsa" tashi tayi daga jikin
Mammi tana kallon Mammi tace "Mammi gsky ba zan iya shishige masa ba kinsan Yah Bobbi
da diz gi da muskilancin kawai dai zan je gidan" ta faɗa tana miƙewa, da kallo Mammi ta bita
har ta haye.....
Ba kwa man share faí ½í¸ž Habibties ku daure ku dinga man share dan Allah
[5/21, 8:10 PM] RIAMCOOL: *BAYAN WUYA*
BOOK 1
*BY MARIAM SANI RIAMCOOL*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*P.15&16*
__________koda ta shiga haɗa kayanta taci gaba da yi saida ta haɗasu tsaf cikin Akwati
sannan ta faɗa Toilet tayi wanka saida tai nafilfilu da karatun qur'ani sannan ta kwanta
Washe gari tana tashi ta faɗa kichen ta haɗa musu break fast a gurguje ta faɗa Toilet tayo
wanka haɗaɗɗun Lotion ta shafa sannan ta ɗauki wani Blue ɗin material mai ratsin baƙi ɗinki A
shape wanda tasan zai karɓi jikinta, ba wata kwalliya tayi ba amma tayi kyau sosai fuskar nan
tata ɗauke da yalwataccen murmushi, parking ɗin dogon gashinta tayi ta ɗauki mayafin Material
ɗin ta yana a kanta, ta aza farin gilashin ido wanda yake ƙara fito da ainahin kyanta duban
kanta tayi a Mirror tana sakin wani ƙayataccen murmushi Hand back ɗinta da wayarta ta ɗauka
ta fito
Koda ta fito zaune ta iske Mammi da Daddynta suna break "Morning Mom nd Dad" ta faɗa tana
manna musu sumba " da murmushi suka amsa mata ɗaya daga cikin kujerun Dinnig taja tana
zama Chips nd plantain kawai taci ta miƙe kallon Mammi tayi tace mata zata wuce "Ok ki
gaisheta ki kula da abinda ya kaiki" Mammi ta faɗa tana duban ƴar tata, da to ta amsa tana
ficewa da kanta tai Driving koda taje bata wani sha wahalan shiga ba kasancewar an santa
parking Space ta nufa ta ajiye motar sannan ta wuce kai tsaye ta wuce sama kasancewar
ma'aikatan gidan sun santa ko wane miƙo mata gaisuwa suke, da fara duka take amsa musu, a
hankali ta tura ƙofan Falon ta shiga, zaune ta iske mazan gidan JUNAID AFIF ARYAN ZAMEER
ABEED HAROON sai IFTIHAR dake gefen ARYAN ana caftar da ita, ganin basu lura da ita ba
ya sata gyaran murya tana Sallama, da gudu IFTIHAR ta taso tana rungumeta tana faɗin
"Oyoyo Matar BIg bro" dariya tayi tana faɗin "lallai IFTIHAR kina da aiki a gabanki fa ta ina shi
Yah Bobbi yasan dama ni" dukan kafaɗarta tayi tana faɗin "lallai kuwa Aunty Maheer kina nufin
Mom bata faɗawa Mammi amincewar Yah Bobbi ba?"
Kallonsu Zameer yayi yana taɓe baki yace "ke IFTIHAR kiji tsoron Allah yaushe shi Yah Bobbi
harya amince kina gani fa saboda auren ya ƙauracewa gidan nan sannan akan auren fa yaiwa
Mom hijira wanda har iyanzu bai shiga shirgin Mom a yanzu" dariya ARYAN yayi yana miƙewa
yace "kudai ake ji inaga Aljana ta auresa har iyanzu shi yasa"
wani kalar dum Maheer taji zuciyarta tayi jin zancen Zameer wato saboda itama ya bar ya bar
gida a dalilinta ya bar shiga shirgin Mom, "tabbas ya zama dole ne nabi shawarar Mammi ta
haka ne kaɗai zan iya samun Yah Bobbi tunda YAH DEEN ya kubce mini wannan bazan barshi
ya kuncemin a karo na biyu ba" ta faɗa a zuciyarta
dafata Iftihar tayi tace "tunanin me kikeyi ne?" "Nothing" ta faɗa tana ɗaga kafaɗa tunda Zameer
yai maganar JUNAID ya karanci yanayin Maheer dariya yayo yanawa HAROON da ABEED
signal da ido dariya sukai HAROON na faɗin "cabɗijam lallai kam da sauran ruwa a kaba, akwai
fa wasan game a gidanmu"
Maheer da bata fahimci abinda suke nufi ba ta haura sama ɗakin Iftihar ta ajiye akwatin sannan
ta zame gilashin idonta tana share hawayen da suka samu damar gangarowa a kuncinta share
hawayen tayi, ta fito koda ta fito ta samu Aunty Samha da Aunty Meera waɗanda suna kan
ibadar tasu wato danna waya da gudu ta isa wajensu tana rungumesu da murna sosai suka
rungumeta suna mata ƙorafin rashi zuwa da ba tayi kwana biyu,Mom ta tambaya aka faɗa mata
bata nan tana gun aiki ita da Samha da Seemah
********************
*ASAD BOBBI*
Kwance yake a baki Swimming pool ya lumshe idonsa ya ɗauki kusan 10 minute buɗe
idanuwan nasa yayi waɗanda sukai masa jajir saboda ƙunci da takaicin da yake ciki, wanda duk
da hakan bai hana ainahin kyawun nasa fita ba da sirrin kyawun idanunsa, ba wai yana takaicin
rasa dukiyarsa da yai ba, sai don takaicin abinda akai masa meya tare musu? Wanda suke son
karyasa kafin su ɗauki rayuwarsa kamar yadda suka ɗauki ta ɗan uwansa Deen wanda har
gobe yake cikin raɗaɗi da zafin zuciya na rashin ɗan uwansa wanda suka zauna ciki guda
wanda daƙiƙu kaɗan ne a tsakaninsu, ko bacci bai taɓa rabasu ba amma yau azzalumai sunyi
nasarar rabasa da wanda yafi ƙauna a rayuwarsa, yasan target ɗinsu na gaba a kansa ne sai
dai ina bazai taɓa basu wata dama ba wacce zasu samu ɓaraka a gurinsu, rintse idanunsa ya
ƙara yi tunowa da auren Maheer wanda ya ida dagular da zuciyarsa amma zai bi komai a sannu
ya warware, miƙewa yayi tare da fara tafiya cikin taƙama da kuzari, tafiya irin ta ƙarfafan masu ji
da kansu da cikakkiyar izza,kai tsaye wani ƙofan ya shiga sai gashi ya faɗa a bedroom,
bathroom ya faɗa yai wanka ya fito ƙugunsa ɗaure da towel mirɗaɗɗiyar ƙiran tashi duk a waje
ga skin ɗinsa se sheƙi take kai tsaye shiryawa yai cikin wasu arnayen ƙananan kaya masu
masifar kyau yai parking ɗin gashin kansa tare da ɗauresa kyau bana kaɗan ba Bobbi yayi
dukkan wata mace ta gansa sai tayi suman wucin gadi kafin ta dawo hayyacinta, wayoyinsa da
keys nasa ya ɗauka har zai fita sai kuma ya juyo a hankali ya tako har zuwa inda wani makeken
photo yake wanda sak kamannisa ne keda na jikin Photon sai dai shi wannan Photon anyi sa da
fara'a ne, ɗaukar Photon yai yana shafawa "DEEN" ya faɗa a hankali rungume Photon yai yana
sakin ajiyar zuciya "bazan kyalesu ba DEEN zan ɗaukar maka fansar ranka" ya faɗa da fitar da
wani huci mai zafi ya ɗau kusan daƙiƙu kafin ya ɗauke photon daga ƙirjinsa, ganin zai makara a
meeting ɗinsu wanda aka shirya na manyan ƴan kasuwa harma dana waje yasa shi fita a
gurguje Securities na take masa baya
Manyan jigagan Motoci na Alfarma suka shiga baƙaƙe wuluk dasu guda biyar ta tsakiyar ya
shiga Driver naja suka nufi wajen Meeting ɗin ga baki ɗaya kowa ya hallara a wajen shine kawai
babu kowa na wajen zuciyarsa cike take da takaicin Bobbi ganin ɓata musu lokacin da yayi
wanda kuma koda yazo idan banda Hy daya furta bai sake faɗin komai ba, Zaidu dake gefen
Mas'ud ne cikin takaici yace "BObbi wane kalar wulaƙanci ne haka zaka ɓata mana lokaci kuma
fa kasan a kanka za'ai wannan Meeting ɗin"ya faɗa da ɓacin rai
"Ohh kuma fa so kuyi abinda ya kawo mu kuna ƙara ɓata man lokaci muddin lokacin dana
ibarwa kaina ya ƙare zan tafiyata fa 15 minute gareku" ya faɗa kamar baya son maganar yana
ɗagewa Zaidu gira tare da kashesa da wani Munafukin murmushi
Nan da nan kowa ya fara masifa kan rainin wayon Bobbi, cikin masifa Alhaji Habu ya dubesa
yana faɗin "ASAD AHMAD BOBBI na kiraka da manyan baƙi kaji kuma ka ƙara ji ba wani abu
bane yasa mu zaman meeting ɗinnan sai don kashe mana companies da kake bamu kaɗai ba
har ƴan waje kana neman kashe nasu companies to bari kaji kamar yadda muke saka farashin
kayammu da kuma yadda muke sarrafa su kaima haka zakai, bata yuwa kazo ka tarwatsa
mana companies na tsawon shekaru"
kallonshi yake da rinannu idanunsa waɗanda suka sauya kala ya zuwa na ɓacin rai "shawara
kake bani ko umarni?" Bobbi ya faɗa yana ƙare mashi kallon rainin wayo dariyar takaici Alhaji
Habu yai yana faɗin "duk yadda ka ɗauka Bobbi, amma ba shawara bace umarnimmu ne yadda
kowa yake kaima haka zakai"
Kallon agogon hannunsa yai yana faɗin "Time up, lokacinku ya ƙare yana gama faɗar hakan ya
miƙe ya fice
Kowa da kallo sake da baki ya bisa suna ƙara jinjina rainin wayonsa da kuma taurin kai irin na
ɗan uwansa Deen kowa da takaicin abin ya bar wajen tareda alwashin baƙin ƙudiri akan Bobbi
Tunda Bobbi ya fita kai tsaye Company B.D Wanda gobara ta kama yaje, Company duka an
fara gyarasa an canza masa wani sabon design mai jan hankali Murmushi ya saki yana lumshe
idonsa ya buɗe
jin kiran waya yasa sa ɗaukar wayar yana dubawa Dad ya gani shiru yai na wasu ƴan daƙiƙu
"Asad ni kake so na fara gaisar da kai koya?" Dad ya faɗa
shafa dogon gashin kansa yai yana faɗi "No Dad, Afterning Dad" murmushi kawai yai yana ƙara
mamakin halin yaron nasa "ok kaje Meeting ɗinne?" "eh" ya furta "ba kadai nuna musu rashin
ɗa'ar daka saba ba ko?" "Saidai kar a kuma Dad" dariya kawai Dad yai ya kashe wayar daman
yasan Asad ne dai_dai dasu ɗin
********************
MUNEEBBA
ranar haka ta kwanta sukuku ta tashi ba walwala Abinci ma don kar Mamma ta shiga cikin
damuwa yasa taci, tunda Hajiyar Nazeer tazo tasan ta riga data rasashi kenan inama zata iya
fitar da son Nazeer da tuni ta fitar dashi
kwance take tayi luf abin duniya dukya isheta jin wayarta na ring ya sata miƙa hannu ta ɗauke
ta saman katifa, sunan wanda ta gani ne ya sata miƙewa tana sauke ajiyar zuciya a hankali tai
picking call ɗin da sallama ɗauke a bakinta,
wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya Nazeer ya saki "Hayatee" ya kirata da wata kalar sassanyar murya
wacce ta sata lumshe idanunta tana buɗewa, "mi ya hana kai picking call ɗina?" yaji saukar
tambayarta
babu abinda ya ɓoye mata ya faɗa mata dukkan abinda ya faru, murmushin takaici tayi tana
share hawaye, tare da barin zancen ta jawo musu wata firar sun jima kamar koda yaushe suna
wayar kafin suyi sallama da juna
dukkan abinda Muneebba keyi Mamma na saurarenta girgiza kai tayi kawai "Muneebba"
Mamma ta Kira sunanta da na'am ta amsa tana zama kusa da Mamma wacce Mamma ta tsira
mata ido kamar tana ganinta dafa kafaɗarta tayi tace "Muneebba tabbas ni uwa ce kuma ina jin
zafin dukkan abinda ake miki, yadda banyi rayuwar farinciki bana so kema ki taso cikin rayuwar
ƙunci, domin duk yadda Mijinki ke sonki indai uwarsa bata sonki to babu kwanciyar hankali da
zaman lafiya a rayuwar auratayya,