Showing 18001 words to 21000 words out of 42194 words

Chapter 7 - Cheaters Club Book 1 Compelet

19 Aug 2026

494



Dawani irin gudu nurses suka gungunro wani gado aka karbeta daga hannunsu duka suka
dagata suka daurata akan gadon akai ciki da ita.

shemau ke rungume da hadiza dan kuka kawai takeyi. Victoria kuma jeka ka dawo kawai takeyi
hankli tashe tanayi tana adduarsu ta christoci.

Meenal ce tabi har kofar room din ta tsaya duk ta rasa me ke mata dadi.

Jikinsu duk na basu cewa magangnun da kawu ya gayama halisa shiya dada cusa mata baqin
ciki snn ya sakata ragwabewa. Dan Rabon halisa data kwanta a asibiti zai iya kaiwa shekaru
bakwai da suka wuce dan bata fiye ciwo ba.

Awani babban examination room aka shiga da ita meenal din zata bisu aka hanata shiga snn
daya daga cikin nurses din tafito tashiga wani hadadden consultation room saigata tafito tareda
wani Dr dabazai wuce 45yrs ba yana sanye da farin glasses a idanunshi wuyanshi sanye da
clinical stethoscope.
wajen aljihun Lab coat dinshi ta gaban rigan anrubuta Dr Ahmed Damilare jimada, da sauri sauri
sauri gudu gudu ya fito nurse nabinshi abaya daidai zasu shiga dakin kenan uztaz drivern halisa
yariko hannunshi gam gamm hakan yasa docton yajuyo tareda tsayawa yana kallonsa snn
yakuma kallon hannunshi daya yarike da karfi ba acikin hayyacin shi ba, irin malam lafiya???
kaman wanda yazare ustaz ya damkeshi cikin wata irin raunanniyar murya yace "likita kayi
hakuri, wann matar itace gatata kuma yar uwata kwalli daya a duniya dan Allah kataimaka mata
kar ka bari wani abu ya sameta..

wani irin calm smile Dr din yayi tareda janye hannunshi daga na uztaz da idanunsa suka ciko da
ruwan hawaye sosai snn ya zaunar da shi akan kujeran dake wajen dan izuwa yanzu baida
wani karfi jikinshi rawa yakey sosai ..

Doc yace "cmon be hopeful iya abinda nakeso dakai shine ka kwantar da hankalin ka kazauna
anan kamata addu'a. I assure u abangarena kuma namaka alkawari zanyi duk abinda zan iya
naga na ceto rayuwar........."

bai karasa maganan ba wata nurse tafito a mugun razane ta na cewa "Doctor, doctor Ahmed
please come quclky the patient is
Going offf der is no pulse..

Jin haka Jiri ne ya debe Meenal da tunanin cewa itace tai silar mutuwar halisa, hakan ne yahau
yawo a brain dinta nan tay kamar zata zube kasa aragwbe vicky ta tarota jikinta tajawota gefe,
hadiza da shemau kuwa ba a magana dan har sun kai kasa suna furta innalillahi wa inna ilaihi
rajiun..hadiza dake da rauni sosai bakaramin kuka takeyi awajen ba
da sauri doctor yay ciki yana kallon uztaz daya dora hannu aka cikin rudewa yana kuka kamar
dan karamin yaro yace malam kadena kuka kayi mata addua kaji.nan da nan uztaz ya kama
rokon Allah akan ya bawa halisarsa sauki.

Da sauri Dr ya shige cikin dakin ya karbi abun gwaji din da wata nurse ke mikamai agurguje
yana sakawa a hannu yana kallon patient din sanan yace "ya za'ayi mufara tabata bayan tana
kan suffocating, bazaku cire mata wannn gown din ba,pls ku cire matashi and someone should
on the Air cone we need vent..
Nurse tace okay sir
Nan da nan suka hau
Yin abunda yace musu

Movable Medical barrier curtain sukaja snn suka sauya mata kaya izuwa na asibiti dark green
colour irinna masu operation.

Lkcin halisa bata numfashi ko kadan bare motsi.

Suna gamawa doc ya taho kanta yana kallonta babu karya halisa ta hadu wanke hannu ka taɓa
ce, ahankali yakai hannunshi yajuyo da ita tareda karban wani kalan minor shocker da nurse
tabashi yakama yay chargin dinsa snn ya danna akan kirjinta.

Saida yay haka kamar sau uku kafin pulse din halisa ya soma dawowa

Wani irin zafin dayaji ajikinta saida yabashi tsoro, babu shiri ya karbi alluran dayasa ahada
masa yakama hannunta yanemo jijiyanta yamata allurar awajen dan yay saurin zagayawa
jikinta,

ko minti goma ba'a daukaba yay stabilising nata snn ya lankaya mata engine taya numfashi.
yasake saka wani sabon alluran ya debo jininta awani a syringe din yabama nurse yace takai
lab.

fita yayi bai jimaba suka shigo tareda su meenal kallo daya zaka musu kasan duk sun razana.

Nan yadauki wani paper da biro ya kalli meenal yace "hajiya ya sunanta?

batare da ta kalleshi ba har lokacin idanunta nakan halisa ahnkli cikin sanyin murya tace
"sunanta Halisa Roberts mansa .

Yan tambayoyi ya musu gameda abunda ya jefata cikin wann halin suka gayamai sama sama
snn sukayi demanding din security dazaina gadin ta sabida yan jarida.

rubuce rubuce yayi sann ya ijiye takardan yadauko wata paper yay rubuce rubuce sanan
yamikama uztaz ganin shikadaine namiji awajen Bayan ya sauke ajiyn zuciya yace "yanzu dai
afara zuwa asayo wayan nan Alluran anan pharmacyn mu kafin result din test dinta yafito
mufara treatment. yanzu kawai stabilising condition dinta nayi ba'a mata komiba tukunna.
sai aje abiya kudin gado dana folder abaka ka kawomin anan da ruwan Alluran dana rubuta.

Ko scnds uztaz bai kqara awajen ba yana amsar paprn agurguje ya fice domin aikata hakan.

Ajiyar zuciya doc ya sauke zai fita shemau ta tsareshi tana cewa Doc baka gayamana conditon
nata ba, is she going to be fine.???

Yay shiru yanata kallonta
Sai can yy murmushi snn yace "lets hope for the best hajiya.

Irin kallon da vicky da hadiza suka mai yasaka a baiyi niyyar bude musu bayanin matsalar ba
yaga kawai gara ya fada.

Ppr dake hannun shi yake kalla calmy yana cewa uhmmm She is actually in serious Nervous
break down due to depression and mental torture. Sann kamata yay ace mun bukace ganin
hukuma a wann lamarin sabida inhar bata farfado nan da kwana uku ba zata iya rasa ranta
sabida halinda take ciki yaso ya taba mata jijiyoyin zuciyarta bana wasa ba..but ku kwantar da
hanklinku zamu iya bakin kkrin mu akanta, Zuwa anjima zanyi wasu kwaje kwaje dan mu
tabbatar da cewa jijiyoyin zuciyar nata da suka jigata basu raunatu ko sun tsinke ba.

Har ya kammala bayanin babu wacce tace masa komi sai kallonshi da sukeyi kamar TV
kowacce tana ji da abunda yake mata ciwo aranta...

Dama tuntuni seda hadiza ta gaya musu muddin wani abu ya same halisa ayau kowa acikinsu
zaiji babu dadi gashi kuwa hakan ya faru dasu. They all look emotional and moody kowa
aransa wahalar da halisa tasha na fadi tashi da rayuwarta yake aunawa acikin ransa sunajin
kamar rayuwa baimata adalci ba.
Ganin sunyi shiru yasaka doc yay excusing dinsu ya fice waje..

Gaban halisan suka karasa dukansu kusan atare kowa cikinsu saida ya rungumeta yay kuka
sann suka yi mata addua da magana suna mai bata karfin gwiwa akan ta fizge kanta a cikin
wnnn halin ta dawo ta cigaba da rayuwanta.

Bayan nan nurse ce ta shigo cikin room din cikin girmamawa tace musu su dan fita waje domin
halisar ta samu hutu...

Jikinsu a mugun sanyaye suka fito waje gabaki daya sukaji sun kasa iya ficewa daga harabar
asibitin haka kowacce ta nemi waje ta zauna ta kife kanta wasu kuma sukayi tagumi.

Nurse na shiga room din halisa ta hau sauya mata gado izuwa na taya daganan aka kaita
private ICU room aka jona mata enginan da zasuna auna yanayin da kwakwalta yake ciki.

Koda nurse din tagama lankaya mata taga yadda kwakwalta yay sanyi da yadda zuciyarta yake
kkrin yay fighting wani irin kurawa wa halisar ido tayi snn ta girgiza kanta cikin yanayin
tausayawa sosai bayan nan ta fice ta koma bakin aikinta tana jinjina mata aranta.


After some few minutes Doctor Ahmed jimada yana office dinshi yaji sautin knock alaman ana
buga masa kofa.

Umarni ya bayar a shigo batare da ya dago kansa akan computersa ba.

Uztax ne yay sallama hannun shi dauke ledojin ruwan allurai da kuma file da aka umarce sa ya
siya.

Suna hade ido yace mai
"Have a seat please.
babu wani musu uztaz ya ja kujera ya zauna yanamai sauraronsa.

Within some min Doc ya kammala danne dannen sa a computer sann ya juyo yana kallon
uztaz.
Uztaz baice komi ba ya mika masa ledojin da file din..amsa yay ya dudduba yaga komi dede
snn ya ajesu agefe ya bude file din ya soma rubuce rubuce aciki.

Tashi uztaz yay zai fice doc ya dago yace excuse me malam dan tsaya ai bangama dakai ba.

A mamakance uztax ya dawo ya zauna adan rude yanamai cewa i hope babu wata matsala da
jikin nata?

Katse rubutun doc ahmed yay calmy yace noo babu wata matsala
..dama wasu yan tambayoyi kawai nake so na maka..naga kamar kai dan uwanta ne ko?

Murmushi uztaz yay yana mai girgiza kai yace eh to,ni dan uwane agareta amma bana jini ba.
Hasalima ni driverta ne kuma personal asisstant inta. Dukkan wani abu indai ya shafeta ninake
kulawa dashi.

Tsatsar Mamaki dayazo ma doc Ahmad a bazata shiya kafesa ya hanashi iya budan bakinshi
yay wata magana yabi ya kurawa uztaz din manyan idanuwanshi dake cikin gilashi ganin
yanayin shi dabaima yi kama da na mai aiki ba.

Uztaz namiji ne har namiji,Farinshi irin fresh din nan ne, shi ba dau ba shi ba light ba. gashi
dogone kakkarfa mai cikar halitta masha Allah, kwantaccen sajensa da gemunsa suke bashi
wani irin kamanni mai aji irinna masu kudi.

Halisa bata barinsa hakanan kayan aikinsa co-operate suit ne bakake masu tsada da kyau yake
sawa ajikinsa kamar mai aikin gwamnati.

Ko gyaran fatar jikinta zataje a spa takan sakashi dole shima yay irin nasu na maza, haka za'a
wankeshi a masa massage snn agyara masa fuskarsa shima ya fito tas tasss, ita classy ce
tafison akoyaushe su kasance cikin tsafta da kyau,a cewarta kyau da tsaftar jikin mutum shine
mutuncin sa a idon jama'a. Snn iya saka kyakkwan suturarka shine asalin darajarka da gwarin
gwiwarka agaban duniya, acewar halisa koda baka da arziki iya dressing dinka kacal na sakawa
kafi karfin raini. Shiyasa sam bataso araina ta bare wanda take yawo dashi.

Shakuwar Yau da gobe yasaka Uztaz idris ya zamo cikakken garkuwan ta da abokinta da dan
uwanta da me aikinta.

Itace ta sakamai sunanshi ma uztaz idris din dan Ta sameshi ne awani gidan mahaukata ya
bacene ayayin da ya rasa familynsa a wutar gobara a kauyensu sai ya samu tabon hankli
amma aka rasa me kulawa dashi, ita tayi jinyarsa da kudinta ta warkan dashi har ya zamo
mutum shiyasa akoyaushe zaka gansa atare da ita yana mai mata hidimar rayuwa.
Tun kafin arzikinta halisa ya bunkasa yake tare da ita, yasan kowani irin halayyarta kamar
yadda itama tasan nashi kuma ta yadda dashi sosai.

Koda yay hankli sosai yay aure still itace take masa komi take kuma daukar nauyin cinsu da
shansu har iyanzu shiyasa yake bata matsayin yar uwansa aransa dan kodede a wasa wani
abu nacin zarafi da walakanci wanda ya taɓa shiga tskananinsu, wani binma dashi take zama
tay shawara ko tay sharing wasu matsalolinta na rayuwa.
Abunda ya sameta ayau ya taɓa masa zcyarsa fiyeda da yadda ake tsammani amma dake shi
namiji bai wani nunawa sosai, aransa ji yake kamar duk sanda yay ido hudu da zach sai ya
make sure ya kakkryashi.

Doc Ahmad yy gyaran murya fuskansa dauke da mamaki yana mai cewa i understand but how
can i contact her family dan tambyar da zanyi is kind of personal.

Uztaz yay murmushi yace Doc am her family for now ,Sai kuma kawayenta dakagani dazu
awaje,madam halisa tacemin iyayenta sun rasu tun tana yar karama batada kowa .

Doc ya jinjina kai yace i see..so inba matsala zaka iya amsa dukkan tambayoyina kenan ko sai
an kirawo kawayen nata.

Yace no ni zan amsa.

Sake Daukar biro doc yay ya soma tambayarsa ko halisa ta taɓa samun wani hatsari daya taba
brain dinta.

Uztaz Yace ma likitan a'a bata taɓayin wani hatsari irin hka ba. Nan ma ya tambaye shi medical
history dinta duk uztaz ya gaya masa.

Nan doc ya duba yagani a harsashen sa yaga alaman gaskiya akan binciken da yay da zu

..iyakar abunda ya gane gameda halisa shine tana fama da boyayyar depression da yay nisa
amma halin datake ciki yanzu yana neman saka mata harda ciwon zuciya.

Nan Doc Ahmed ya zauna ya babbawa uztaz shawarwari masu yawa sabida tausaya ma halin
halisa dayay, nan yace masa daga ta farfado ya sauya mata tsarin cin abincinta ya zamo zallan
gangayaki da yayan itatuwa da mai mai tsafta. Snn kar ya barta ta sha giya ko tana zama ita
kadai.

Shawarwari dayawa ya bashi kafin man uztaz ya masa godya ya fice izuwa bakin ICU ya dau
lokci tana kallon halisa ata windown kfin can ya sauke ajiyan zcya ya nemi waje ya zauna a bkin
kofar yanata tunanin rayuwarsu ta baya me dadi lkcin da zach bai shigo rayuwarta ba .


Har wajajen goma na dare halisa bata motsaba meenal da hadiza ne ke ziriya a asibitin, victoria
da shemau kuma sunkai report wajen hukuma domin a dakile yn jarida daga yaɗa labarin halisa
a kafafen sada zumunta.

Tsantsar Darajarsu da kimarsu na masu kudi kuma matayen masu kudi yasaka aka musu komi
acikin sauki, all the expenses na bribe da suka bayar was paid by hadiza dake she be oga wife,
ita batama aiki duk tafisu rike kudin banza sabida matsayin mijinta na petroleum minister

Lcki guda aka contacting social media monitoring commision aka saka takunkumi wa youtube
twitter tiktok instagram da sauran wajeje already wanda suka soma yadata anbi duk an goge an
kulle acct dinsu. Some few bloggers ke da hard copy na videos dinta da aka dauka a church sai
nemansu akeyi amma ba aci nasara ba.
Zunzurutun Kudi na fine mai yawa akasa akan duk wanda ya yaɗa labarin scandal na auren
halisa mansa zaijishi a kotu wanda hakan yasaka Abun ya dawo abun hayaniya da cece kuce
wajen jama'a a social media musammn ma wajen yan mata da sukejin tsananin kishinta da
masu mata hassada sabida cigaban data samu da rayuwarta batare da tayi karuwanci ba. Babu
wani mahalukin dayasan pastlife dinta sosai kamar meenal talba sauran kawayen dik basusan
labarinta deep deep hakanan ba.

Mafi yawan Mutanen gari duk sunsan halisarne a matsayin mace me kamun kai da neman
nakanta cikin jajircewa.

Aynzu Kusan Kowa so yake yaji asalin dalilin dayasaka wann famous weding na halisa mansa
ya ruguje domin a fito da aibunta idon duniya wanda makiyanta na fili dana boye suka dade
suna jiran fitowarsa.
Ayi sharing please...
08060712446 chat surayyahms.


_*CHEATERS CLUB...*_
_(Babban goro sai Magogin ƙarfe...)_


#ROMANCE
#FICTION
#ADULTHOOD
#SEXADDICTS

#WOMENPOWER

BY
_SURAYYAHMS_
_08060712446_


⏯️5️⃣

Jita jita da Hayaniya akan labarin rugujewar auren halisa sai dada sanyi yakeyi a media saboda
babu wani sabon abu dazai assashi domin kuwa tsananin tsarone da takunkumi kawayenta
suka kakama atakota ina wanda yasaka kusan kowani tantirin blogger Da ɗan jarida yake
tsoron shigewa trap dinsu.
Bayan kwana biyu kacal da faruwar komi iyakarsu din ne suke mamaye aganganta cikin bata
kulawa duk da ma bata farka ba, bayansu sai kuma uztaz dake kwana a asibitin a daf abakin
kofar dakin da halisa take kwance yanamai gadinta shima,a tare da security police men guda
biyu da aka kawo musu masu basu tsaro wanda har sun fara sabawa da uztas din sosai.
Baqin ciki da takaicin zach haryau bai kaurace a zuciyan kawayen nan ba,shema'u marafa data
dau mugun zafi sai zuga sauran kawayen takeyi akan su daukar wa halisa fansa akan zach
koda shima zai dandana yaji abunda halisa taji amma haka meenal taki sam ta dinga kawo
musu tauhidi dan kawai bata son garin daukar fansa aje asirinta ya tonu.
Duk sanda suka tada maganar itace zata nuna masu tafi kowacce cikin su damuwa da rayuwar
halisa.

A kalamanta takanyi amfani da rauni wajen cusa musu tunanin cewa halisar yanzu tana bukatar
samun sauki da kwanciyar hankli ne ba daukar fansa ba.

Shema'u kuwa gani take kamar insuka bar zach ahakan ai tamkar yaci dasune abanza, snn su
kansu basuyi wa halisar halaccci ba, hadiza da vicky suma sun karfafa wann lafuzan abakinsu
amma haka fir meenal ta tubure tace musu hakan ba dede bane kawai abarsa da ALLAH a rife
maganan sabida lfya da kuma kwanciyar hanklin halisa.
Hakan ya jawo kowa yake dan shan qamshi da ita,tun bayan data kushe lamarin daukar fansa
wa halisa sauran kawayen sukayi sanyi suka dena yawan kula hirarta sosai aganinsu sunada
kudi me dumbin yawa da kuma ikon da zasu iya yin hakan acikin sauki sann abun kunyane
agaresu duka ace basu tsayawa halisa wajen yaqi da zaluncin da zach yay mata ba aduk irin
shakuwansun nan. daga haka suka zamto saidai suyi magana daddaya da meenal amma badai
su sake mata fuska sosai ba.

A kwana na ukun ake tsammanin halisa zata farka kamar yadda likita yace musu dan haka
yaune kowaccensu ta wuce gidanta domin samun karamin hutu da kuma dedetuwar hanklin
fuskartar halisar agobe.

Kusan dolensu ne su zamto masu kara mata karfin gwiwa a shawarce hadiza tace musu karda
kowacce acikinsu tazo da baqinciki ko ta nuna rauninta da tausayinta agaban halisa inta farfado
inba haka ba bazasu iya fizgeta acikin halin deprssion datake ciki ba.

Sai can Wajajen karfe hudu na yamma snn suka fito izuwa harabar asibitin dayaji wani irin
greeny soft landscaping da kuma adon fulawowi yay kyau sosai.

Hanklin mutane atake ya koma kansu babu wani halitta dake harabar da bai juyo ya zuba musu
idanu ba.

Gasu da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0