Showing 21001 words to 24000 words out of 42194 words
cikakken dirin kuguna ga kuma manyan nonowa wanda sukaji gyara,fatar jikinsu yana
sheqi yawani cika fam fam Kana ganinsu dai kaga irin matan nan masu son gyara jikinsu,
matane kalar hutu irinsu sai wane da wane masu cin duniyarsu da yar tsinke.
Atare dukkansu suke takowa gwanin ban sha'awa takunsu me cikeda Aji da salona sassnyar
kamiya, vicky ta sake albarkatun gashin kanta na asali daya wani zubo mata yabi kan kafadarta
sauran suka kwanta har gadon bayan ta tana tafiya tana dan yarfashi da hannu a fakaice.
Dumbin mutanen dake harabar asibitin sai satar kallonsu suke wasu har na cin karo da juna,
atare suka nufi inda tsadaddun motocin su na manyan jeepa jepai sukenan a parke kowacce ta
shiga nata personal driverta ya hau tukata izuwa gida.
Adede marabar hanyarsu kowace acikinsu ta doshi anguwar da mansion dinta yake..
Nan hadixa meitama ta wuce hamshakin gidan da mijinta ya gina mata a no:305 Victoria
Arobieke street a anguwr lekki gidan tamkar aljannar duniya haka yake an narka nera wajen
kerashi da kayan kyale kyale saidai cike yake da duhu da baqin ciki da takaici da rauni
musammn daya kasance kamar ita daya take rayuwanta acikinshi.
hadiza tana cikin wani irin narkakken daula mai lullube da kewa da tashin hankli na rashin
samun gamsuwar zaman aure daga wajen mijinta Alhaj Yusuf Kyari.
mijinta babban ministan man fetur ne na kasa sam baida lkcin kansa ma bare na matarsa
arayuwa,dan sai hadiza taci tsawon wata daya ko biyu koma fiye da hakan agidan itakadai,
daga ita sai dumbin masu aikinta batare data hade ido da mijinta ba tsabar shige da fice da
harkan siyasa daya saka agaba.
At age of 26 already hadiza har ta kamu da cutar hawan jini da ciwon damuwa, musammn da
bata samun cikakken kulawar mijinta sosai akanta, shiyasa abu kadan na tashin hankli inyazo
mata zakaga ta rude sosai tana kuka fiyeda kowa sabida wann rauni daya cikke fadar zuciyarta,
gashi tanada wani irin tsananin kishi, snn a duniya babu abunda hadiza ta mugun tsana kamar
kalmar kishiya.
Daga dayan bangaren Vicky ta wuce nata gidan mijin dake cikin anguwar Oba akinjobo Avenue
ikeja wato asalin cikin garin lagos. Dake vicky din sananniyar senior lecturer of economics ce a
hadadden exclusive private university din nan wato pan Athlantic university dake anguwar lekki
tayi karatu sosai shiyasa tafisu duka a shekaru cos she is curently a 33 years old lady .
Ita yar asalin garin edo ce, tana jin yaren yarbanci snn tanajin yarensu na edo state din sosai,
Ta auri mijinta dan oyo state, cikakken bayarbe ne dake da alak da historical obaseki kingdom
of edo amma mahaifyarsa inyamurace cibiyar Anambra state irin jan inyamurai din nan ne masu
kalar fatarsu so fresh and yellowish a kuma murmure dan haka danta ya fito farisol dashi
kyakkwa sosai na fitan hankali. Wanda Tsabar Kyan sa da iya nuna bajintarsa wajen saka
sutura da hawa motoci nagani na faɗa dayake tukawa agari yasaka akecemai prince of all time.
Cikakken sunanshi shine "femi falana". Amma duniya da masoyansa sunfi cemai "prince femi
falana". Tsabar Kyaunsa da ajinsa yasaka yake da ruwan farijinin mutane dan haka yana yawan
yin harkansa ne big and rich international companies da kuma manya manyan kusosin kasa
bana wasa ba.
Irin manya manyan multi million nera contract na alfarma dayake samu a hannun yan siyasan
lagos har saiya baka makurar mamaki saika rasa ta ina yake cin karo da irin wann sa'ar
arayuwan shi. Ya iya kashe kudi ne kamar baisan zafinsu ba.
shiyasa Daya tashi yin aure yaje ta can edo state inda ake masa ikirarin sunfi kowanne kabila a
nigeria mata masu fasalin kyau da albarkattun diri na gani na fada, anan ma saida ya durje
sann ya zakwalo matarsa wato victoria williams baltimore Sabida aganinsa itace tay daidai da ta
zamo matarsa a duniya sabida ilimi kyau aji da sauran qualities dinta da ya tabbata kowanne ɗa
namiji zaiso ace ya samu irinsa ajikin macen daya aura.
Liver pool estate apapa anan shema'u marafa take da zama, mahaifinta Alhaj marafa tsohon
ministan Aviation ne mahaifyarta kuma hajya hajara retired chief judge ce a adamawa state dan
nan ne asalin garinsu dake su fulani ne. Karatu da aure ya kawosu zama a garin lagos, shemau
bada wuri tay aure ba saida takai age of 30 sabida ta riga da ta rantse cewa itadai bazata aure
talaka ba sai hamshakin me kudi.
Shekara biyu kenan da aurenta, tana auren wani shahararren building contractor irin babban
civil engineer din nan ne dayay karatunsa a china ya fito da first class, babu lefi suma sun tara
millions of nera snn suna rayuwarsu ne cikin arxiki da wadata sosai duk dama shema'u wani bin
takan kalli matsayinsa dana sauran hamshakan mazajen kawayenta duk sai taji aranta ta
rainashi musammn inta dubi irin duniyar daular da hadiza take zaune aciki.
Shikuwa mijin nata mai suna alhaj engr mahmud Bello a kullum kkrin sakata a aljannar duniya
yakeyi da kulawarsa da soyayyarsa dan bakaramin masifar sonta yakeyi aransa ba.
Iya wann makahuwar soyayyar dayake nuna mata shine yasaka haryau shema'u bata fito fili ta
asalin nunamai cewa ta raina arzikinsa ba, dan komin tsadar abu a duniyan nan inta nema
awajen sa bata rasashi godewa Allah ne kawai bata iyayi aranta..
itade arayuwa kullum ciwon zucyarta nagakan rayuwar hadiza ce, gani take kamar rayuwa cikin
narkakken daula data gama tsarawa kanta shine ayanxu hadiza ta sameshi a memekonta.
Hakan yasaka shema'u marafa tafi kowa raɓuwa da kuma kusantar hadiza fiye da kowa acikin
sauran kawayen,irin shakuwa da Amanar dake tsakaninsu kamr na meenal da halisa ce
Izuwa ynxu shemau tasan dukkan wani sirri da matsalan aure dake tafe da rayuwar auren Adiza
dan sun shaku da juna bana wasa ba.
"A nan Herbert marculay way dake anguwar mainland na lagos state Hadadden Gidan Amina
Ali talba wato meenal talba yake.
A first street kyafaffen gidan nata yake, daura da Gidan Wata shahararriyr fashion Celebrity ana
ace mata jasmine tacha,ita model ce na kayayyakin sakawa ajiki,both cikin kasa da waje. dan
haka ne ma suka san juna da Halisa mansa sosai, dake dacan sana'ar da halisar tafarayi kenan
bayan ta kammala karatunta na jamia da zimman saita samu wasu yan kudade snn tafara
neman aiki dan tanada gudun kaskanci da walankaci.
Halisa mansa tana fara modeling kuwa Allah ya saka mata albarka aciki, modelling shine silar
dayasaka halisa tasamu daukaka da shahara da kuma suna kafin ta fito ta gina kamfanin kanta
tana handling busineses dinta batare da kowa ya rainata ba..halisa tayi huzzling da fadi tashi
arayuwa sosai,tay aiki kala kala har Allah yazo ya bata arziki mai yawa da temakon saurayin ta
zach.
Seda Halisa tay kudin kanta sann ta siya ma kantan wani white luxurious mansion a anguwar
masu kudin gaske da bakowa yake samun kasancewa ciki ba wato victoria island.
tana rayuwarta ne acikin makeken gidan nata na nan a Akin Adesola street dake anguwar
victoria island din tare da uztaz da sauran security men dinta da basu fi su biyu ba dan bata
debe tarukucen mutane agidan nata ba.
Ata dayan bangaren kuwa Wannan gida na meenal talba ya shahara ne sabida tsantsar
kyaunsa da yadda aka kawata gaban sa da shuke shuken fulawowi masu ratsa hasken
idanu,sai kuma uban tashen kima da mutunci da mijinta Dr Alhaj khaleel Abubukar yake dashi.
He is a 35yr old millonaire and a medical Doctor. Vibrant, Young and handsome gashi sam
baison hayaniya arayuwarshi. Shidin cikakken dan garin maiduguri ne yaren kanuri.
A jikin babban whitish gate din shiga cikin gidan nasu aka manna silver bell plate mai bala'in
dauke ido anrubuta 4033 residence.
Yadda tawaje yake a kawace da shuke shuke hakama cikin gidan yake koina an tsarasa ne
cikin tsafta da kwarewa dan haka mikakkiyar hanya guda daya ne zai kaika har cikin harabar
gidan dake dauke da wata wadatacceyiyar parking space da aka jera kala kalan motoci na
zamani.
Asalin main building din yana tsaye cur a tsakiya ne, gidan akwai filli sosai dan zaka iya
zagayeshi gabaki daya hartacan bayansa batare da kakai bangon sa ba,sai ya kasance filin
daketa bayan gidan yafi na gaban gidan yawa alaman su mutane ne da ke bukatar sirri a
personal life dinsu.
Dik wani kele kelen Swimming pools da karamin relaxation outdoor palors da main garage da
Duk Wani abu na shakatawarsu Duk anan abaya suka zuba bata gaban gidan ba..
Cikin gidan kuwa bangare hudu kacal yake dashi.
Shashe na farko na dauke da 2 rooms and a big palor masu kyau fadi da kuma yelwa.
anan shashin farko Meenal talba take da zama, Dayan bangaren shima iri dayane da nata
Sedei mijinta Dr khaleel ne ke zama aciki kowa dai acikin su na da personal space nasa da
room dinsa, dan meenal talba din wata iriyar murdaddiyar mace ce agidanta sam bata taɓa
amincewa wai suyi sharing room da mijinta ba.
sai sauran rooms guda biyu din da suka rage ake barsu kamar quest rooms dayan room din
anyishi tsarin dakin mai aiki ne amma mjinta yaki sam akawo mata me aikin sabida yasan tana
da mummnan zargi aranta sosai.
Dayan room din kuma anyishi ne a design din dakin bacci da falo mai kyau musammn dan in
baqo na jini ne ko na kusa da su sosai yazo.
Main palon su an kerasa ne da set din kujeru uku guda shida bakwai given a total of 18
luxurious chairs, bangare guda na wasu mahaukatan milk colour turkish royal chairs ne masu
golden crown,dayan bangaren kuma wasu mahaukatan cozy lush sofas ne wanda aka kera
design dinsu da silk nd velvet sai Italian sofas masu kalar brizzle brown throw pillows.
kujerun nasu sunyi matukar kawata gidan sabida da bold colours aka tsarasu, komi na cikin
gidan tsaddade ne me daraja,wani irin sanyi mai dadi dake fitowa daga airmores din falon
wanda shine ya kame jikin bangon falon ya sakamai yanayi me kwance gajiya sosai ajikin dan
adam.
Meenal talɓa ce ta siya gidan gabaki dayansa da kudinta dan gidan da halisa ta siya a victoria
island ya mugun tsaya mata arai,.tay hakan ne danta kwaco kanta daga boyayyar kishin
kawarta halisa dataji ya kamata na irin daukakar datake cin karo dashi, tunda suka taso aranta
sam batay tsammanin har halisa zata miƙe ta zamo cikakkeyr mace me sa'a a duniya ba, Duk
dama siyan gidan datayin shiyayi silar da haryau surukunanta suke samun matsala da ita.
Hasalima a dangin mijinta babu wanda yake zuwa gidan ko ya mata magana hatta iyayenshi.
Matsalar ya soma ne ayayin da suke shirye shiryen aurensu da mijinta Dr khaleel, wann
shahararren gidan nasu ya zaɓa ne zai siya da kudinshi domin ya sakata aciki, sede girman kai,
hassada da son nuna isa yasaka meenal talba taje ta rigashi siyen gidan at a double price
domin kawai cikar burinta da kuma son asaka gidan nasu a sunanta bana mijinta ba.
Meenal tana wani irin jiji dakanta tana kuma baza alfahari sosai da dumbin dukiyarta na gado
hadi da cewa mahaifiyarta ta tarbiyantar da ita ne awani siga na sakalci da nuna mata ita
watace a duniyan nan.
Meenal ta taso ne acikin narkakken daula dan haka tarbiya da iya girmama dan adam yay
karanci a kwakwlwarta, arayuwarta ita kanta kawai tasani bata son wani mutum yay wani abu
arayuwarsa face saida amincewarta.
She is a very controling lady, And an Emotional blackmailer. Meenal Kwararriyar Macijiyar sari
ka noke ce, Zata iya tsula maka mugunta abayan idonka amma sai tazo gabanka tayi maka
kuka ta nuna a duniyar Allah nan tana dare dakai dari bisa dari.
Itade muddin rayuwanka bai tsaya a iya matsayin data ajeka ba toh tabbas sai tasan hanyar da
zatayi ta rabaka da Abun da bataso aranta din.
Tanada wani irin boyayyar mugun hali najin cewa duk wanda yake tare da ita dolene yakasance
a kasan ta karde a fita da wani abu sann kowama yay rayuwarsa akan bisa tsarinta ba akan
nashi ba.
Duk wani abun farinciki ko daukaka idan ya sameka inhar abun bai gamsheta ba toh komin
shakuwarrku saitay kkri ta ruguza abun a boye. Snn haryau bbu wanda ya fahimci wann hali
nata sabida yadda ta mugun kwarancewa a wajen saka fuska biyu، iyakar mahaifyarta datake
dora ta akan komi itake ke lura da wann mugun halin nata.
Gidan da suke ciki da mijinta a yanzu haka nata ne, koda khaleel ya nuna bacin ransa lkcin
dataje ta siye gidan sai tanuna mishi tsabar sonshi datakeyine yasa ta siya musu amma bada
wani manufa ba, iyayen mijin nata kuwa sun ji baqin cikin hakan da tayi dan mahaifiyarsa ta riga
ta fahimce kamr meenal din so take ta zamo itace me controlling din gidan khaleel amma bashi
ba.
Anyi tashin hankli sosai kafin aurensu, da chan ma kamar za'a fasa auren amma abune da
Allah ya qaddara.
Haka iyayensa sukayi hakuri suka amshe karereyin ta na cewa so ne ya jawo ta siye gidan
dansu zauna aciki..
Sedai ba awani jima da yin aurensun ba Doc khaleel ya fahimce komi daga cikin munanan
halayyar meenal talba.
Domin kuwa karamin sabani in ya shiga tsakaninsu haka zata bushe idonta ta soma masa gori
tanamai cewa in bazai bi abunda take so ba ya fita mata agida ai bada kudinshi ta siya ba. Tay
masa munanan gori irin haka a farkon aurensu yafi sau a kirga.
Intaga yay fushi zai fice sai kuma sauya kalar tausayi harta kame kafafunshi tayi ta kukan fitan
rai tana wani irin rikitaccen birgima akasa tanamai bashi hakuri tana cewa sharrin shedan ne.
Haka Doc khaleel yayita fama da ita musmmn a farko farkon aurensu har abun yazo yabi
jikinshi ya soma danne zuciyarsa akanta yana hakuri da ita sosai.
Sosai ya fahimce cewa Baida cikakken iko akan matarsa meenal iyakar abunda tayi niyya shi
takeyi agidan bata damu da hakkinshi na aure ko wasu abubuwan da yake so aransa ba.
Iya abunda ke cusa mai tausayi aransa shine sanin cewa meenal tana mutuwar sonshi aranta
bana wasa ba, inkomai zai kasance masa karya a duniya amma son da meenal take masa
shikansa yasan na gaskiya ne, duk sanda yace su rabu koda a wasu ne to babu shakka
abubuwa mumunana ne yake biyowa baya. Sau tarin yawa yaso ya rabu da ita din tunma kafin
aurensu amma meenal intaji hakaan rikicewa takeyi, takaiga hatta poison saida tasha dan ta
mutu akansa. Tabbas Zata iyayin komi domin mijinta amma saukar da kai da biyayya ne kawai
bazata taɓa iya mashi ba.
*********
Tun barinsu asibiti meenal take juya tunani dayawa aranta, 4:30pm dede driver ya iso da ita
bakin gate ya danna horn mai gadi ya taho a guje yana kkrin budewa, dagata glass din windon
motar ta hango motar mijinta Dr khaleel atake fuskarta ya sauya tahau yamtsusahi acan kasar
wuyarta taja wani irin takurarren tsaki.
"Barka da zuwa hajiya
Allah ya temakeki.Allah ya tsareki..."
Mai gadi ne ke miƙo gaisuwa cikin rusunawa da girmamawa amma ko kallo bai isheta bare ta
amsashi.
Saida driver yy daf da zai shiga ciki snn tace stop a dakilance cak ya tsaya awajen.
Glass taja ta wurga wa me gadin wani irin kaskantacce kallo baisan lkcin daya sunkuyar da
kansa kasa ba.
Dauke kai tay sann tace
"Kai me gadi..Yaushe Doctor ya dawo gidan nan??
Bakinsa na bari bari ya budi baki yace Allah ya temaki ki hajiya ai Baima fi mintina 20 da
shigowarsa ba.
Daga nan batacemai komi ba ta maida glass din motar ta rufe sann ta umarce driver daya juya
yakaita office dinta kawai
Dan aranta tasan dolene in tashiga ciki zasu samu matsala dashi aranta tasani sarai dolene
mijinta yanemi ya bukaceta duba da kwananta goma sha bakwai kenan tana can gidan halisa
suna shirye shiryen biki hade da kwana biyu da sukayi a asibiti..
and if ders one thing she hates very much shi ne sex a aure. A nata ra'ayin
Gani take kamar yawan bawa namiji sex shiyake kawo raini tsakanin miji da matarsa. Besides
tafison ana kwana da itane ayayin da take bukatar hakan bawai idan mijinta yana bukace ba.
Meenal is a chronic feminist at heart dan bata fotowa fili ta fada amma kuma tsarin rayuwartan
bisa akan haka yake tafiya ba karya .
Itadin irin matayen nan ne da suke da ra'ayin cewa mace da namiji have equal right, in zatay
girki shima dole yayi, in zai gaisheta zata gaishe shi, in zata kwana dashi dolene sai tayi ra'ayi.
Awajen ta namiji ba shugabanta bane bare kuma tay jagora da shi, yadda zaiyi yadda yakeso
da rayuwarsa haka itama zatayi da nata rayuwar but deep down inside her heart she still
expects him shidin ya kasance tamkar wani bawanta, as handsome and rich as he is awajenta
babbanabun alfaharine agareta taga tana juyashi sosai, so take ya saukar mata da kai ta
mulkeshi while he humble down and worship her needs and desires as his wife a duk lkcin
datake son haka...
Atayani sharing izuwa grps grps da kuke ciki please.
08060712446 chat surayyahms direct.
_*CHEATERS CLUB...*_
_(Babban goro sai Magogin ƙarfe...)_
#ROMANCE
#FICTION
#ADULTHOOD
#SEXADDICTS
#WOMENPOWER
BY
_SURAYYAHMS_
_08060712446_
⏯️6️⃣
Kananan tsaki mai tafe da takaici meenal ta dinga jerowa akan hanyarsu ta barin herbert
marculay street na anguwar nasu,duk tagaji jikinta nayi mata nauyi nauyi amma batajin tana
bukatar wani hutu,nan da nan ta umarce driverta ya wuce da ita inda babban