Showing 54001 words to 57000 words out of 101517 words

Chapter 19 - DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVELS BY MAMUHGEE.pdf

Mamughe   

22 Nov 2025

2773

ta
nufa fridge ta bude ta dauko Mata ruwan roba masu sanyi sosai ta kawo Mata ta miqa Mata.

Karba tayi ta bude Kai tsaye takai bakinta tana Sha Sarah na kallonta da mamaki.

Ajiyar zuciya kadan ta sauke bayan tagama sha ta ajiye sauran ruwan tana cewa"

Sarah zanje gida yanzu kaina na ciwo Ina buqatan hutawa ko zai sake.

Tare suka fito da Sarah din itace take tuqin takaita gida suka nufa cikin gidan tare.

A Palo suka tararda Hanifa zaune tareda anty Amina data kawo Mata sabuwar Awarar da
Umma ta Aiko Mata wadda akaiwa sauce din kayan miya dasu carrots da kwai.

Kallo daya Naj tayiwa Awarar taji tana son ci abinda Bata taba yiba shine ko dakinta Bata
shigaba ta qaraso gefen Hanifan ta zauna ahankali tana cewa"

Yunwa nakeji sosai har kaina Yana ciwo.
Ta dauka plate tana miqawa Hanifan tana cewa"

Samun zanci.

Zuba Mata Hanifa tayi tana cewa"

Lallai yau 'yar gaban goshin hajjo yunwa takeji tunda ko daki bazaki iya qarasawaba.

Batace kalaba saidataci Awarar a bakinta taji kanta dake sarawa ya daina ta dago ta kalli
Hanifan ahankali tace"

Thanks.

Sai alokacin ta kalla anty Amina tana cigaba daci suna gaisawa anty Amina na kallonta dakyau
cikin nazari tace"

Naj bakida lafiyane Naga kamar kin fada.

Kallonta Hanifa tayi tana cewa"

Ramar aikice Amma duk da hakan Ni Banga ramarba haske dai Naga tayi sosai kodai bakida
jini ne Naj?" Taqarasa fada tana Dan zare ido.

Batareda ta dagoba tace"

Lafiyata kalau stress ne kawai amma zanshiga hutu sbd komai yakoma yanda yake a office din
Inshallah.

Saidata qoshi kafin ta qarasa dakinta tabarsu a palon ta tube ta shiga toilet wanka.
Sai datai wankan taji jikinta ya sake sosai ta fito daureda towel ta nufa jikin mirror kenan taji
wayarta na ringing ta juyo ta nufa wayar dake Kan gado ta dauka sai kawai taga No din qasar
waje destination id dinta ya nuna Mata United States of America.

Kai tsaye ta dauka batareda ta tsaye tantance kiranba Wanda yake Vidcall sai ganin mutum tayi
ya bayyana kan screen din wayarta Yana zaune cikin lafiyayyan palonsa sanyeda uniform dinsa
na sojojin America dasukai Masa wani irin kyau uwa uba hutu da nutsuwar daya samu ta
bayyana ataredashi Ya zuba Mata fararen idanuwansa har zuwa kirjinta dake daureda towel
Tsananin hasken data qara yasashi sake zuba Mata idanuwansa,
wannan ne Karo na farko data gansa cikin uniform ta dauke kainta ganin irin kallon dayake
Mata sai alokacin ta tuna da towel ne jikinta ta kashe wayar tana jefarwa Kan gado ta tafi tahau
shirinta.

Baccin maraice yayi sai magriba ta tashi ta fito bayan tayi sallar magriba sbd yunwa me tsanani
datake ji.
Kicin ta nufa sbd sanin lokacin cin abincin Daren baiyiba tasan Hanifa na kicin sbd Bata jimawa
bataci ba shiyasa take zuwa kicin taci ta koshi Kuma ahau dining aci da ita.

Tana Shiga kicin din ba kowa sai ruqayyat dake qarasa aikin abincin Daren ta nufa fridge ta
bude ta dauko milk drink tasha sosai ta dauko cake guda hudu ta cinye ta qara da apple biyu
kafin taji ta dan samu nutsuwa ta fito suna hadewa da Hanifa dazata Shiga kicin din neman
abinda zataci itama tace"
Naj yunwa nakeji cake zanci da Madara tunda kin cunyemun awarar da Umma takawo min
dazu.

Batace komaiba Takoma Palo ta zauna tana duba wayarta tana jiran agama abincin akawo
dining.

Sallar ishai taje tayi tana fitowa hajjo na fitowa suka dunguma dining Hanifa tuni ta riga kowa
Isa.

Naj din ita tazubawa hajjo abinci takawo Mata ruwa da komai ta kalli Hanifa da Bata harta zuba
abincinta tafara kaiwa Baki.

Zama tayi itama tareda zubawa ta zauna suna binta da ido ta dago ta kallesu ganin irin kallon
dasukewa abincinta yasata kallon abincin sai alokacin taga ta zuba da yawa ba kamar yanda ta
Saba ba dama kwanakin gabaki daya cin abincinta ya sauya ta Dan fuske tana cewa"

Yunwa nakeji sosai duk yau banci wani abincin kirkiba.
##MAMUH#

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107





*_DM 34_*
Hajjo kallon abincin takuma Yi kafin ta kalli Naj din cikin kulawa da nutsuwa tace"

Najma ki daina zama da yunwa Haka sbd zata iya Miki illa yanzu wannan abincin zai iya qulle
Miki ciki,Kisha tea kafin ki ci abincin cikinki ya sake tukuna.
Kallon Hanifa tayi tana cewa"

Miqa Mata tea din ta zuba ta Sha.

Qaramin flask din dake cikeda black tea dinda yaji kayan qamshi da hadinsu lemon da Zuma
wanda koyaushe dashi ake jere abincin safe Rana da dare Wanda qaidar hajjo ne wadda ta
Saba da Shansa Kuma al'ada da dabi'ar Shan nasa ya Kama duk Wanda yake gidan ko baqi
akai idan za'a kawo musu ruwa sai an tambayesa ko akawo Masa tea din.
Miqawa Naj Hanifa tayi tana cewa"

Kin riga kinfara cin abincin kinsha tea din daga baya" ta aje tana daukan spoon tafara cin nata
abincin.

Kamar yanda tasaba cin abinci a natse ta cinye abincin tas tasha ruwa kadan ta zuba tea din
Wanda kurba daya Tai Masa ta ajiye tana cewa Alhmdlh ahankali.

Kallonta hajjo tayi tana sake cewa"

Idan Zaki ringa zama da yunwa irin Haka Zaki sa ciwofa ya kamaki karki sake hakan daga yau.

Guntun murmushi tasaki ahankali tana kallon Hanifa da har lokacin abincin takeci tace"

Yaune kawai hakan bazai Kara faruwa Inshallah hajjo.

Barin gurin tayi ahankali tanajin nutsuwarta ta dawo ta dawo palo ta zauna sai alokacin ta dauka
wayarta tana dubawa har Hanifa da hajjon suka Gama suka baro dining din hajjo tayi dakinta
sbd qafafunta da ruqayyat zata gasa Mata da ruwan dumi.
Hanifa Kuma gefenta ta zauna tana daukan tata wayar itama tace"

Naj gobe umma zata faramun sabon gyara Isma'eel zai dawo next week fa.

Juyowa Naj din tayi ta kalleta tana sake maida hankali kan abinda take dubawa a wayar tace"

Shine kike Zillo Haka?
Cemasa zanyi yayi zamansa sai zaki haihu yadawo muga qarshen gyaran.

Dariya Hanifan tasake tana cewa"

Zillo ma ai kadan ne zille zille zanyi ma idan ya dawo tunda bansan kalar zille zillen da matan
duniya ke can suna Masa ba tunda bana kusa Dana Haka idan yazo nawa lokacin ne nayi
haukama idan Zan iya,
Hannah kina ganin duk ranarda tasamu auren Marshal wannan rawar kan datake ai uwar
ubansa zamu gani akan wannan datakeyi Yan.......

Hade sauran maganar tayi tana rufe bakinta Jin Naj din tayi shiru sbd gabaki daya ta manta da
Naj take maganar,ta Dan kalli fuskar Naj din data juyo itama ta kalleta tareda sake wani irin
guntun murmushi tana basarwa da cewa"

Ashe kinada qarfin yiwa miji zille zillen Kike makure Mana fuska ki nade muna dawainiya da
matarsa.

Haba sirikita idan bakiyi hidima daniba waye zaiyi....

Dan kame fuska Naj din tayi Hanifan tasaki dariya tana cewa"

Sorry my Naj.

Wayar Hanifan ce tayi ringing ta waiwayo tana kallon wayar ta maida kallonta kan Naj da kallo
daya tayiwa wayar taga sunan me Kira ta dauke tana maida hankali akan tata wayar.

Dauka Hanifa tayi cikin murmushin ganin video call ne ta dauka Kai tsaye tana cewa"

Hey Deen Marshal,ya kake?

Kallonta yayi Yana Dan gyara crossing qafafunsa da yayi wayar na ajiye saiti dashi a gabansa
Yana zaune acikin office dinsa sbd sun safiyace har hantsi ma yafara,
Ya bude Baki ahankali yace"

Lafiya kalau,ya baby?
Kinje scanning din kuwa?
Nayi mgna da Dr sa'id,ki turamun scanning din I want to see it.

Ok,ok,Baby is fine,and iam fine also" satar kallon Naj tayi tana cewa"

And Naj ma tana Lafiya.

Jingina yayi baya Yana folding hannuwansa fararen idanuwansa akan wayar cikin muryarsa
data Gama Isa cikin kunnuwanta yace"

Bata wayan.

Kallonsa Hanifa tayi tana Dan kame fuska da murmushi akan fuskarta tace"

JALAL karka damu qawata da wannan kamewan naka,
Wani irin kallo yayi Maya Wanda yasata harararsa tana cewa"

Kome ka zama karka manta dai Ni yayarkace.

Dan rufe idanuwansa yayi ya bude da wata muryar yace"

Matan auren dake gefenki Zaki bawa wayar.

Naj dake zaune duk takasa ma qarasa abinda take a waya sbd zancen a bayyane yake fita ta
miqe zata bar gurin lokacinda Hanifa ke kokarin miqa Mata wayar Kai tsaye taji muryarsa ba
Wasa aciki yace"

Kika bar gurin Zakiyi mamakin hukuncin hakan.

Dakatawa tayi tareda waiwayowa ta kallesa ta cikin wayar zatai magana saita kasa ta fuske
tana kokarin wucewa tabar Hanifa ta riqota tareda maidata zaune tana cewa"

Dawo ki zauna Bari Ni natashi kicin zanima.

Miqewa tayi tabar gurin bayan ta aje wayar saiti da Naj din.

Dauke Kai Naj din tayi tana cigaba da duba wayarta tanajin idanuwansa na yawo akanta duk sai
hakan yasata kasa nutsuwa ta dago ahankali fuskarta a hade suka hada idanuwa ta dauke Kai
kafin tayi wani motsi a natse yace"

You look sexy in that dress.

Da wani irin yanayi na kunya da takaicin kayan dake jikin nata ta motsa zata kashe wayar
yasakar Mata wani kallon daya sata hadiye wani yawun dake neman sarqeta yace"

Ok goodnight jeki kwanta.

Kashe wayar yayi sai alokacin ta sake daure fuska tana dauke idanuwanta daga gefen wayar
tana kallon kayan jikinta da gaban rigar take a Dan bude Ana hango tsakiyar kirjinta da condom
bra Dinta ta rabasu ta miqe tabar gurin ta nufa dakinta.
Tana shiga tubewa tayi Bata sake wankaba sbd Dan sanyi datakeji ta saka kayan bacci tayi
kwanciyarta take bacci ya dauketa.

Washe gari sallar asuba kawai ta Gama ta fito taje kitchen Tasha tea me zafi tana lumshe ido
sbd rashin shansa a Daren jiyan yasa takejin yunwa Kamar hakan.

Da cake Tasha tea din ruqayyat data fara ayyukanta tana binta da satar kallo sbd sanin gabaki
daya Naj din batada ciye ciyen abinci qaidarta taci lokacin cin abinci tagama takuma shikenan.
Har tagama tafito Hanifa Bata zoba Dan Haka Takoma daki ta kwanta wani sabon baccin me
nauyi yakuma dauketa.


Sai qarfe goma da mintuna ta farka tana kallon agogo ta saki wani qaramin numfashi tana dafe
Kai sbd ganin irin lattin datai Wanda Bata Saba lattin ba irin Haka.
Zuro qafafunta tayi ta sauko gadon tana nufar toilet Kai tsaye tayo wanka ta fito.

Babu Bata lokaci ta shirya cikin doguwar jallabiya Maroon da qaramin mayafin data nade kanta
dashi Wanda kalar abayar ta fitarda tsananin hasken data qara ta fito qamshin khumrah kadan
Yana Dan tashi a jikinta..

Kai tsaye gurin hajjo dake zaune palon ta qarasa ta zauna gefenta cikin kulawa tace"

Good morning hajjo, muntashi lafiya?

Kallonta hajjo tayi cikin kulawa tana cewa"

Lfy kalau,yau kinyi lattine?

Eh,zanci abinci na wuce.

Dining ta nufa ta zauna tareda Kiran ruqayyat takawo Mata ruwan sanyi tafara cin abincin kenan
saiga Zainab din Anty Amina tashigo da sallama ruqayyat data bude Mata kofar palon tana
biyeda ita zuwa dining din.

Anty Naj Ina kwana?

Lafiya kalau zainab yasu umma da anty Amina suka tashi da Dadah?

Lafiya kalau,ga wainar Anty Hanifa Nan Zan koma aikin su daughnuts mukeyi da ummana da
aka kawo Mata na wani bikin idan Anty Hanifa ta fito Ina Mata Ina kwana.

Juyawa tayi ta qarasa gurin hajjo tana gaidata har hajjon na Bata sako gurin umma kafin ta
wuce.

Qamshin wainar ya ringa Shiga hancinta Amma dayake Sam waina Bata dametaba saita dauke
Kai tana daukan hakan amatsayin rashin damuwa da bataiba da waina
Amma qamshin sai sake Shiga hancinta yakeyi Yana sata Jin wani iri ba shiri ta miqe tabar
gurin tana goge bakinta da yawunta keyi Kamar zasu tsinke Dan Haka Kai tsaye handbag dinta
ta dauka tana cewa"

Hajjo na tafi office saina dawo.

Ok ki kula,saikin dawo.

Sai data Shiga motarta ta sauke wata irin Ajiyar zuciya tana sauke numfashi ahankali.

Sai data samu nutsuwa kafin ta tayarda motar ta fice daga gidan ta nufi office.

Isarta office taji abinda take no yakuma taso Mata da qyar ta daure ta iya kaiwa office dinta tana
Shiga ta nufa toilet da sauri wani irin amai me qarfi da wahala na kufce Mata.

Da sauri Sarah tabiyo bayanta ganin irin yunqurin Aman datake me wuya da qarfi.

Daqyar Aman ya tsaya ta wanke fuskarta tareda dagowa ahankali tana miqewa dukkanin Rabin
qarfinta ya tafi ta kalli Sarah tana cewa"

Bani ruwan sanyi zansha.

Cikin kulawa da damuwa Sarah tace"

Naj kinci wani Abu ne?
Ko Zan Kira Dr sa'id ne yazo ya dubaki idan bakyajin Dadi.

Girgiza Mata Kai Naj din tayi tana fitowa toilet ta zauna a kujera tana karban ruwan sanyin ta
bude Tasha ahankali tana ajewa tace"

Basai kinkira Dr sa'id ba inaga naci abinci da yawane kawai zanji sauki yanzu tunda na same na
rage kawai dai karki Bari a dameni banajin Dadi Kuma.
Lumshe idanuwa tayi tana dafe kanta dake Dan juyawa sbd Aman, Sarah ta fice tana sake
Mata sannu.

Wunin kasa gane kanta tayi gabaki daya a office din Haka dai ta tattara Takoma gida wani Dan
zazzabi na damunta.

Ko a gidan data Isa abinci kawai tasamu taci ta kwanta saikuma taji daughnuts din dazu da
Zainab tafada Mata takeson ci Dan Haka ta daga wayarta takira anty Amina tace"

Anty Amina kibawa zainab daughnuts takawomin nakasa cin abinci cikina ya qulle.

Kash wlh wainda akaiwa harsun Aiko an karba duka saidai ko samosa akwai sauranta Bari
akawo Miki.

No ki barshi banasonta zanci cake kawai.

Tana kashe wayar taji zazzabinta na neman qaruwa Haka dai ta lallaba har dare shima tanacin
abincin dare ta kwanta gabaki daya Aman ya sakar Mata da mutuwar jiki da guntun zazzabi.

Ko washe gari wani sabon uban latti ta buga dayasa fita ko abinci bataciba
Sai data Isa office Tasha milk drink aikuwa tana gamasha Amai ya biyo bayansa Wanda yafi na
jiya take hankalin Sarah ya tashi ta zubawa Naj din data Gama galabaita tana cewa"

Naj please kibari nakira Dr sa'id.

No tattara min kayana gida zankoma jiri nake gani.

Tsayawa Sarah tayi tana kallonta cikin tsananin shakkun tunanin daya shigeta da mamaki me
tsananin qarfi tareda kasa gasgata tambayar dazatayin tace"

Naj are you pregnant?

Wani kallon mamaki da takaici tayiwa Sarah din duk da tana Dan jin jiri ta yamutsa fuska a hade
tace"

Are you stupid?
Ta Yaya zakimun wannan tambayar inada Wanda zaimun cikine?
Sarah please karki karamun ciwon Kai just leave,kije ki dauki key din motar muje ki kaini bazan
iya tuqin ba.
##MAMUH#


*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*


*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

*_DM 35_*


Albishirinku mata💃shin Ina ma'abota ado da kwalliya🗣�Ina team no makeup🗣�Mata gareku
inamai tabbatar muku dacewa duk wnd takeneman kayan gyaranjiki walau matsalan fata kike
fama dashi kamarsu pimples, tabo, sunburn,nankarwa, knuckle ko Mai Kika shafa yabatamiki
jiki Dama sauransu walau Kuma kawai kinasan kigyara fatarki kizamto tauraruwa abarso abar
marari agurin kowa�Mata inamai tabbatar muku dacewa kujaraba kayan mg's skincare Koda
gudane dg cikin kayansu kuga abun mamaki🧚🏻�♀� domin kayansu kankat ne Koda iya sabulunsu
Kika Dana saikinfita zarra cikin Mata domin ynd fatarki zaikoma Shar kamar Madara kidinga
kyalli kina haskakawa duk inda kikayi se ankalleki😘Kuma wani abun jindadin ma shine duka

kayansu organic ne Babu na bleaching kawai zaigyaramiki jikine yafiddomiki d ainihin natural
beauty dinki inma NASA haske kikasiya natural ne kawai bn bleaching b��♀�mekike jira hjy maza
garzayo kinemi naki acikin farashi merahusa kigyara jiki kiyi fes abinki baruwanki da sekinyi
kwalliya inzaki fita�kifita aganki da zallar kyawunki hjy�kanawa mutanenmu ina godiya Kuna
nunama mg's one luv tnx for ur patronage dama Yan sauran state mg's na godiya may your
pocket never lck azo asiya Kaya hilis karnakoma kauyenmu🥺Yar shawarmannan karta
gagareni🤧�
Henajiku lvs🤭
Meso should chat
08062991549
07046881166
Call 08064532391
Soap:3k, beauty kit:11k,bridal kit 18k
Instagram:glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare

Team glow✅

Masu buqatan makeup ma duk mgs skincare suna kulawa da wannan ko a makeup studio dinsu
kokuma a gidanka.
08062991549



************
Sarah binta tayi da ido tana sake qure kallonta akanta Dan kuwa duk da ita ba likita bace Amma
ta taba aure harma da bari na ciki harso biyu kafin suka rabu da mijin Dan Haka tana iya
ganewa ko hasashen ciki ajikin mace Amma Kuma Kamar yanda Naj din tafara batada Wanda
zai Mata ciki bayan mijinta Dan kuwa tare sukai karatu da Naj qawartace ita din cikakkiyar
sheda daga Nan har koina zata iya bayarwa akan nutsuwa da kamun Kai irin na Naj din to
Kuma Marshal Wanda yake matsayin mijinta kowa ya iya yanda ya tabbata Babu ko gaisuwa a
tsakaninsu bare su Aminta da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0