Showing 63001 words to 66000 words out of 101517 words

Chapter 22 - DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVELS BY MAMUHGEE.pdf

Mamughe   

22 Nov 2025

2777

tanajin idanuwansa
na yawo jikinta.

Takowa yayi ahankali ya qaraso bakin gadon
Ta qarasa kwanciya tana rufewa batareda ta kallesa ba sai zuciyarta dake Dan bugawa da sauri
sauri.
Ahankali ya zauna bakin gadon ya kamo hannunta ya riqe cikin nasa hannun tareda sauke
qaramin numfashi yayi shiru ahakan dumin tafukan hannayensu suna shiga cikin na juna.

Dan rintse idanuwa tayi tareda budewa sbd yanda dumin tafin hannun nasa ke saka jikinta
kokarin sanyi ta Dan motsa tana kokarin zare hannun nata sai alokacin ya Dan waiwayo
ahankali ya zuba Mata idanuwansa dasuka sata dagowa ta kallesa.
Wani kallo yake Mata ta dauke idonta tana sake kokarin zare hannunta
Ya riqe hannun tareda tayarda zaune Yana janyota jikinsa ya rungume,
Bayason hayaniya nutsuwa kawai yakeson Yi sbd kansa na Dan Masa ciwo kadan sbd
damuwar ciwonta daya zo dashi dakuma kukanta daya qarasa damar da nutsuwar cikin kansa.

Qwacewa take kokarin tana turasa ahankali ya kalleta Yana sake yimata kyakkyawar runguma
ya bude Baki a natse cikin yanayi na rashin son hayaniyar yace"

Ki nutsu banason hayaniya,

Kema bakida lafiya,idan Kika qi nutsuwa Zan saki baccin gajiya.
Daure fuska tayi tareda son sake qwacewar amma Bai Bata damar hakan ba sbd irin rungumar
da yayi Mata idanuwansa a rufe.

Qarfe biyu da Rabin dare ta farka ahankali tareda bude idanuwanta sbd yunwa da qishurwan
daya tada ita
Ta motsa ahankali jinta cikin jikin mutum ta dago da sauri ta kalli fuskarsa sbd ta manta gabaki
daya da zuwansa dakin da daddaren.

Fuskarsa ta kalla da qaramin hasken wutar gefen gadon tana Dan dauke Kai daga kan fuskar
tasa bugun zuciyarta na qaruwa ta zare jikinta daga nasa tana kokarin saukowa gadon ya bude
idanuwansa Yana kallonta a Dan kasalance kafin ya tashi zaune Yana kallonta yace"

Lafiyanki kuwa?

Ko kallonsa bataiba ta miqe ta nufi kofa tana kokarin fita ya tashi a natse ya riqota Yana kallon
idanuwanta da bacci yagama sakinsu yasake tambayarta cikin kulawa Yana kallon cikin idonta
dasukai laushi.

Dan rintse ido tayi tana rasa abin Yi Kai tsaye ta sake zamewa tana nufar kofa ta bude ahankali
ta fice Yana binta a gefe da mamakin Ina zata cikin Daren.
Kicin suka nufa Yana sake kallonta da mamaki Yana kallon kitchen din sbd bazai iya tuna
ranarda ya taba shigowa kicin din ba sai yau.

Fridge ta nufa ta dauko orange juice me sanyi ta zuba a cup ta maida sauran ta nufa inda cake
yake ta dauko guda biyu ta fito Yana biyeda ita Yana kallonta da mamakin cin Abu cikin tsakiyar
dare.

Karban cup din yayi daga hannunta sbd sanyin juice din Yana kallonta da ido yayi Mata alamar
sanyin zai qara Mata zazzabi.

Zaunar da ita yayi a palon tagama ci da kansa yakawo Mata ruwa Tasha tana qin kallonsa
tagama ta miqe ta nufa daki ta shige.

Tsayawa tayi tsakiyar dakin cikeda mamaki da tsoro ta kallesa bayan yashigo da ido shima yaka
Mata wani irin kallo sbd gabaki daya kayan baccinta daketa damunsa da wani irin qamshi tuni
Tana bude Baki da niyar nuna Masa kofa ya ranqwafo ya hade bakinsa da nata Yana fara Bata
wani kiss me sanyi da nutsuwa ta rintse ido da qarfi tana son qwacewa Amma takasa sbd jikinta
dake mutuwa ahankali ahankali.
Ahankali hannuwansa suka sauka cikin rigarta ta dauke numfashi tana qanqame hannuwansa
da qarfi sbd yanda tsikar jikinsa suka miqe ta bude idanuwa daqyar zata kallesa ko zata iya
hanasa da idanuwanta Amma kallon dayake Mata yasa idanuwanta neman makancewa jikinta
na saki

Ya dauketa gabaki dayanta Yana dorawa Kan gado bakinsa cikin nata har lokacin sai
hannuwansa dake yawo cikin jikinta suna barazanar rabata da numfashinta.
##MAMUH#


*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*


*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

*_DM 39_*
Qarfe shida tayi wanka tayi sallah daqyar sbd tsamin jiki da bacci me nauyi dake cikeda
idanuwanta tareda kasala Takoma ta kwanta wani bacci me nauyi ya dauketa sbd tun asuba
daya fita sallah Bai dawoba Yana sashensa shima baccin yakeyi me nauyi sbd tunda ya iso Bai
samu hutuba da nutsuwa sai bayan asubar.
Hannah tunda uwar safiya ta tashi tana aiki hada Masa kayan breakfast a sashensu duk da
gabaki daya hankalinta na Kan yanda zatai tasan meye manufar Naj akan Marshal dinta Dan
kuwa wlh bazata yardaba Naj ta cike gurbanta a rayuwarsa.

Sai guraren goma tagama ta nufi dakinta tayi wanka tafito ta zauna gaban madubi tana
shiryawa cikin adon kwalliya da turare masu qarfi da tsada ta nufi kayanta ta fidda wata
doguwar riga me fadin wuya da roba roba ajikin yadin dayasa ta Dan lafe jikinta ta sake saka
wasu turarukan ta daura qaramin scarf daya Gama fitarda gashinta me Dan tsayi ba laifi sbd
itama kyakkyawar ce ta fito daukeda basket ta nufi sashen hajjo sbd tafi saka ran zuwa yanzu
Yana can din sbd kusan Sha daya tayi.

Tana shiga hajjo na daki Babu kowa a palon bayan ruqayyat dake sake jere abincin Rana da
aka fara gamawa.
Aje basket din hannunta tayi a dining ta juya ta nufi dakin Naj datake Jin shedan na ayyana
Mata taje tunda Naj din Bata Nan zuwa yanzu tasan tana office.
Tana Isa jikin kofar ta Murda ta bude ahankali zata shiga taji Naj din na waya da Sarah cikin
damuwa da rashin sukunin data tashi dashi akan cikin,gabaki daya hankalinta ya juye Tama
rasa Ina zata saka ranta da tunaninta komai nata ya tsaya cak
A yanda ta yau din ta ringa Jin abubuwan da jalal yake Mata har cikin ranta ta tabbatarda aikin
cikin jinintane sbd abinda yafaru a Daren yau din sosai jikinta ya karba hakan Wanda ta
tabbatarda hakan yaci gaba tozarcin datake gudarwa kantane zai sameta sbd yanayi na cikin
Wanda shima dakansa ya fahimci a Daren jikinta ya karba saqonsa tako Ina, ta rintse ido tanajin wani irin kunya da takaicin kanta da ma na cikin Kai tsaye cikin damuwa
tace"

Sarah ki shirya kizo yanzu Zaki daukeni muje wani asibitin ayi scanning Zan biya ko nawane a
ciremun cikin Nan,
Kunyar zancen Nan ma yafita nakeji,kizo yanzu,gani Zan fara shiri.

Kashe wayar tayi tana kokarin saukowa daga gadon da gabaki daya qamshinsa yakeyi ta
yamutsa fuska tareda miqewa tana gyara zaman towel din dake daure ajikinta Wanda Takoma
bacci dashi bayan tayi sallah
Ta inda ta ajiye takardar jiyan ta dauko tasake budewa ta karanta zuciyarta na tsalle da quncin

rashin sanin Yaya zatai da wanann qaddara ta cikin data sameta Kuma tsoron cirewar na Dan
shigarta Dan Bata taba kwatanta hakan akantaba.
Shafa cikinta dake shafe ahankali tayi tana sauke numfashin dayake sake shigar da ita damuwa
ta maida takardar cikin envelope dinta ta saka cikin handbag dinda zata fita da ita kafin ta daga
qafafu ahankali ta nufi toilet yashige tareda rufo kofar.

Wani irin tsalle zuciyar Hannah keyi na shiga cikin wani razanannen yanayi na kaduwa da tsoro
tsoro dakuma farin cikin Jin wannan muguwar tonuwar asirin dazai samu Naj Wanda zai
taimaka Mata shikenan qarshen Naj da Marshal yazo,
Bama Marshal ba ko iyayenta saisun tsaneta bare familyn Alfa Dan kuwa ba tantama idan har
yanda taji Naj nada ciki to cikin tsohon saurayinta dasuke aiki guri dayane Abaas lamido.

Da sauri ta bude kofar ahankali ta shige dakin ta isar jakar da Naj tasaka result din ta bude
ahankali tana kallon kofar toilet din ta dauki envelope din tareda rufe jakar ta silale ta fice tareda
rufe kofar ta bar sashen gabaki daya da sauri.

Sashensu ta qarasa hannuwanta na rawa da jikinta tun a Palo ta tsaya hannuwanta na rawa
tafara kokarin Ciro takardar daga envelope din
Mum Malika dake zaune ta miqe itama ta matso cikin mamaki da son ganin menene take cewa"

Menene kiketa rawar jiki haka kina zare idanu.

Bude result din tayi dakyau tana karantawa zuciyarta na tsallen wasi wasi duk da shedan na
saka Mata tabbacin cikin wani guri ta samosa
Saidai Kuma tunanin sanin wacece Naj da girman kamun kanta da sanin darajar kai nasata
tunanin ba cikin kowa bane saina Marshal.
Cikin wani mummunan yanayi na fita hayyaci tace"

Uban waye yayi Mata ciki?Dan kuwa Babu wani kusanci a tsakaninta da Marshal bare ace
cikinsa ne,
Wannan cikin bana Marshal dina bane,Sam Sam,
Zan nuna Masa wannan Dan yasan wacece Naj da irin rayuwar datake da wasu mazan...

Da sauri mum Malika ta qwace takardar tana karanta cikeda mamaki da firgici itama,
Ta dago tana jinjina Kai cikin Shiga tunani tace"

Tun kwanaki Naga alamar ciki ajikin yarinyar Nan Amma ban kawo hakanba araina sbd sanin
Babu wani kusanci ko mu'amalar kusa dake Shiga tsakaninta da Marshal Kuma banajinma
kowa yasan sunada kusanci kowa yasan Babu wata mu'amalar kusa tsakaninsu to Ina wannan
cikin ya fito???
Qwace takardar Hannah tayi idanuwanta na sauyawa da tsananin baqin ciki da tashin hankalin
rashin sanin taqamaimai cikin Ina ya fita cikin tsananin baqin ciki da zafin Zuciya tace"

Koma Ina ya fito nasan bana Marshal bane,
Ko Ni Marshal Bai taba yiwa kallon sha'awa ba nida nake Masa shigar daukan hankali kala kala
tareda bayyanar Masa da duk wasu sigar daukan hankalin maza Amma Bai taba Bina da kallon
sha'awa ko so dayaba bare ita da Bai taba ganin wani kayan daukan hankaliba ko jikinta a
bayyane bare har ya iya kusantarta Dan Haka Marshal bayada alaqa da wannan cikin shiyasa
Dole Zan nuna Masa Dan yasan waye Naj da halinta ko zai sawwaqe Mata taqara gaba.

Zama mum Malika tayi tana janyota ta zauna itama cikin nata baqin cikin tace"

Ba kince tace abortion zataiba?
Kibari saimun samun tabbacin abortion din saimu samu hanyar sanar dashi ta yanda idan yaji
tayi wannan abun qyamar Kuma tana kokarin zubarwa Dan Kar wani yasani zaifi daukan zafi
mukuma mu samu abinda mukeso,
Amma dai yanzu ki Adana takardar Nan ba yanzu zamuyi amfani da itaba karki Bari zafin
Zuciya da rashin hakurinki ya Bata Mana aiki nasan halinki bakida dangana ko kadan.

Zafin da zuciyar Hannah ke Mata yasata miqewa tana maida takardar cikin envelope ta nufi daki
ta dauko mukullin motarta ta fito ta fice zuciyarta na wani irin nauyi Dan dai ita tarasa yadda da
zancen inda zata saka cikin.

Motarta ta nufa ta bude tashiga tana kokarin tayarwa Naj ta fito Sarah na tareda ita tana
sanyeda doguwar rigar jallabiya ash da gyale black datai rolling Jakarta na hannunta Sarah ta
karba key suka Shiga motar suna kokarin tadawa ta fito Tata motar zuciyarta na sake tafasa ta
nufi sashen Marshal da tashinsa bacci kenan yayo wanka Yana sanyeda qananun Kaya ash da
sukai Masa kyau ya dauki wayarsa zai saka Kira Hannah Tai knocking kofar.

Kallon kofar yayi tareda Dan dauke Kai sbd baya buqatan damuwar kowa yau shiyasama yau
zai tafi gidansa dake anguwarsu ta sojoji zai Kira Dr sa'id can ya samesu ya duba Masa Naj din
acan yanason sanin menene matsalarta Dan ko yau da asuba tayi Amai kafin yafita sallah.

Bude kofar yayi tareda zuba Mata idanuwansa fuskarsa a kame ta kallesa tanajin zuciyarta na
qara mamayuwa koina da sonsa,
Bazata rasashiba Kota halin Yaya, Marshal natane Dan bazata iya rayuwa babusaba.

Juyawa yayi yakoma ciki ganin irin kallon datake Masa da dukkanin idanuwanta abinda yafi
tsana kenen agurin Mata yawan kallo.

Idanuwanta rufewa sukai da takaici da baqin ciki da tsananin kishinsa ta fitarda envelope din
hannunta ta qaraso ta ajiye Masa a gabansa ta juya zata fice saikuma ta dakata tareda juyowa
ta dawo cikin marairaice fuska hawayen data Dade tana dannewa tun dazu na radadin da
zuciyarta keyi zuciyarta na zafi tace"

Marshal ina maka son da bazan iya cin Amanarka ba Kamar Naj sbd Haka nakasa boyewa
abinda naji nakuma ga tana kokarin Yi,
Abortion take kokarin........

Wani kallon daya dago Yana Mata yasa maganarta maqalewa tana kallonsa zuciyarta na
harbawa da fatan yayi mummunar fusatar dazata tashi kowama ayi duk abinda za'ai.

Idanuwansa ya maida Kan takardar data aje yakai hannu Kai tsaye ya dauka ya bude.
Sunan asibitin yafara kalla yaga asibitinsu Dr sa'id ne ya gangaro da idanuwansa zuwa cikin
takardar Yana karantawa.

Shiru yayi idanuwansa zube akan takardar wani irin yanayi na rashin tabbaci da Kuma abinda
Hannah tafada yasashi aje takardar tareda miqewa ya nufi dakinsa ya dauko key din motarsa
ya fito lokacin Hannah tuni ta fice ta nufi motarta itama ta fice Suma su Naj tuni suka fice daga
gidan suka nufi wata private hospital dinda wata yayar Sarah ke aiki.
Scanning aka fara yimata bayan sister farida Tai Mata dogon bayanin illar abinda takeson ayi
din na cire Mata cikin tana sake cewa"

Ki koma gida kiyi tunani wannan abune me girma ba'ason gaggawa.

Sarah da duk hankalinta yake atashe tanajin zuciyarta na turata data Kira Marshal ko Hanifa ta
sanar musu tunda takasa Hana Naj din da idanuwanta suka rufe da kunyar aji zancen cikin
bayan itama din tana iya ganin hankalinta ba akwance yakeba da al'amarin.

Ahankali tace"

Naj Dan Allah mukoma gida ki sake zaunawa kiyi shawara akan hakan.

Cikowa idanuwanta sukai da hawayen dake bayyanarda tsananin damuwar da zuciyarta ke ciki
ta girgiza Kai ahankali tana kallon takardar scanning din dake nuni da cikin watansa biyu da sati
biyu harda kwana uku ahankali tace"

Sister nagama yanke shawaran Yi din kawai.

Da kansa yake tuqa motar zuwa asibitin Dr sa'id sbd Yana buqatan mgn dashi bazai iya jiran
saiya tashi aikiba yazo gidan Dan Haka Kai tsaye can ya nufa.
Kirane yashigo wayarsa ya Dan kalli wayar Yana ganin sunan Hanifa ya share Kiran Dan baya
cikin mood na magana da kowa yanzu sai zuwa anjima.

Ko daya Isa asibitin sai alokacin ya nema wayar Dr sa'id cikin sa'a Yana office zaune Dan Haka
koda yashigo cikin mutuntawa Dr sa'id ya nuna Masa kujera Yana cewa"

Barka da zuwa Marshal,
Hope lafiya Naga kazo da kanka asibitin Kai tsaye?
Badai jikin Naj ko Hanifa bane ko?

Dan rufe fararen idanuwansa yayi ya bude Yana kallon Dr sa'id fuksarsa a kame kamar
koyaushe Kai tsaye yace"

Dr ka duba Najma akan ciwon dake damunta inason sanin taqamaimai menene matsalar,Ina
nufin akwai abin daya kamata nasani?

Kallonsa Dr sa'id yayi Yana sauke ajiyar zuciya a fili tareda gyara zama cikin nutsuwa yace"

Ciwonta ba komai bane face laulayi na ciki datake dauke dashi Wanda dama Dole zata ringa
irin wainnan qananun ciwon kafin cikin yafara qwari.

Rufe idanuwa yasake Yi ya bude ahankali yanajin wani irin yanayi na shigarsa ya sake kallon Dr
sa'id zaiyi mgna text din Sarah yashigo wayarsa Kamar hakan"

_please kana buqatan zuwa wannan address din Naj tanason aikata abinda yake hadari ga
rayuwarta._

Sake karanta saqon yayi zuciyarsa na kasa fahimtar zancenta duka ya dago ya kalli Dr sa'id
cikin yanayi na ransa dake neman baci yace"

Tasan cewa tana daukeda ciki ne?

Eh munyi mganar da ita saidai gskia zancen cikin kamar Bai kwanta Mata.

Ta maka maganar cire cikin kenan????"" Yafada Yana kafe kallonsa kan Dr sa'id din daya fara
kame kamen boye zancen da yayi.

No,yes I mean ta nuna bataso Amma ai na Mata mgn Kuma inaga tabar zancen.....

Miqewa yayi idanuwansa na sauyawa ya fice daga office din ya nufi motarsa Yana kokarin shiga
idanuwansa a juye da wani irin mummunan yanayi saiga motar Isma'eel yashigo asibitin da
gudu Yana Kiran nurses saiga dr sa'id yafito take sukai kansu sbd Hanifa da ake kokarin fitarwa
motar jini ya balle Mata gabaki daya Bata hayyacinta.
Wayar Isma'eel dayaketa Kiran Marshal Bai dagaba itace tashigo wayarta daidai lokacinda zata
saka hannu a takardar abortion din tana dauka cikin tsananin tashin hankali yafada Mata mugun
labarin dayasata sakin takardar tana miqewa cikin tsananin tashin hankali ta fice da sauri Sarah
tabita tana tambayar lafiya Amma Bata tsayaba ta karba keys din motar da kanta taja cikin
tsananin gudu sukabar asibitin zuwa asibitin su Dr sa'id.

Suna parking taga motar marshal agurin Bata tsayaba sukai ciki da sauri tana Jin qafafuwanta
na neman sagewa da tunanin halinda kowa zai Shiga idan Hanifa ta rasa cikinta.
##MAMUH#



*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107



*_DM 40_*
Isarta bakin gurin yayi daidai da isowar anty Amina itama hankalinta tashe,
Idanuwanta na cikowa da hawayen tsananin damuwa da tsoron halinda Hanifa zata shiga ta
juyo ahankali tana kallon Isma'eel da duk yagama ficewa hayyacinsa sbd damuwa saidai
tawakkalinsa yasa yaketa kokarin natsar da kansa ya kalli Naj din kafin ya juya ya kalli Marshal
dake magana da Dr sa'id cikin wani irin yanayi na tsananin zafi biyu daya hadu akansa fuskarsa
amatuqar hade Babu rahama ko daya akai.

Shigewa Dr sa'id yayi da sauri yana cewa su Dan kwantar da hankalinsu Inshallah zasuyi iya
kokarinsu.
Kasa zama tayi sbd tsananin tsalle da bugawar da zuciyarta keyi ta rintse ido cikin yanayi na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0