Showing 90001 words to 93000 words out of 101517 words
Chapter 31 - DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVELS BY MAMUHGEE.pdf
Kan cinyarsa Yana cin abincin da ita ahaka ta ringa binsa da idanuwa tako Ina Yana sake
cikata da mamakinsa da girman abubuwan dayake Wanda basa boyuwa.
Koda yagama suka Gama samun bakinta tayi da kasa tambayarsa akan komawan datakeson Yi
takama hannunta suka koma daki da kansa yakaita har toilet sukai brush suka fito ya hau gado
ya kwanta tareda miqa Mata hannu da ido yace Mata zo Nan Kamar wadda aka daga hannunta
aka miqa Masa Haka tasamu kanta da hannun nata akan nasa ya jawota ya kwantar gefensa
Yana Dora kanta kan pillon da kansa yake suna fuskantar juna ahankali ya lumshe idanuwansa
Yana rungume hannunta daya a kirjinsa yace"
Goodnight Mrs DEEN.
Lumshe nata idanuwan tayi itama tana sauke qaramin numfashi Dan baccin ya dauketa itama.
Bacci Sosai sukai musamman bayan sallar asuba dasukai sallah suka koma Dan kuwa yau Kai
tsaye ya hanata guduwa sashen hajjo Kamar yanda take data nacewa komawan sai kawai ya
sake yayi Making love da ita Wanda yadaukesu lokacin har gari yagama wayewa sukai wanka
sbd tsananin gajiyan datai Dole tana kwantawa baccin wuya ya dauketa.
Bata Farkaba saida wata yunwa me qarfi ta tasheta,ta Dan motsa tana bude Idanuwanta
ahankali tana Dan kallon gabanta ta tuno a inda take sai kawai taji jikinta yakuma sakewa da
mutuwa sbd tariga tasan yanzu Kam hajjo tagama gane Bata Kwana acan ba.
Dan Haka yaye bargon datake rufe dashi tayi tana tashi zaune tareda zuro qafafunta qasa tana
son sanin menene time.
Baya dakin ita kadaice
Ta Dan kalli wayarsa dake aje Kan drawer na gefen gadon ahankali takai hannunta ta taba
screen din yayi haske Dan taduba time sai kawai tayi arba da hotonta akan wayar dayayi kyau
sosai tana sanye da riga da wando da wula qarama dukkaninsu fararene Banda gashin kanta
daya fito shikadaine baqi yayi kyau sosai da Dan boyayyan murmushi a fuskarta da tsananin
mamaki take kallon hoton tanason tuna yaushe tayisa Amma takasa tunawa saidai tanada
tabbacin koma dai yaushene ba yanzu bane Kuma a qasar turawane duba da yanayin shigarta
dakuma mutanen dasuka fito bayan hoton,
A iya saninta kafin aurenta duka duka zuwanta qasashen waje baifi so uku suma duk sbd
issues na ciwon Hanifa ne sai Wanda suka tafi kwanaki na dashen last cikin Nan nata daya
bare Wanda shikuma bayan aurenta ne,
A dukkanin tafiyar Nan dasukai nataredashi sukajeba bayan wannan ta qarshen wadda Kuma
tanada tabbacin Bata saka kayan nanba saidai idan ta mantane,
A Ina yasamu wannan hoton????
Koma dai a inane hakan yasaka zuciyarta cikin wani irin hali na kasa danne abinda yake
ranta,fuskarta na bayyanarda sirrin ciki wanda yake saukarda wata walwala farin ciki akan
fuskar.
Qarfe goma da mintuna ashirin da bakwai Kai tsaye ta miqe tana nufar toilet tabude tashige
hankalinta nakan tunanin ko harya fita.
Brush din tayi tareda sake shiga ruwan zafi bayan tayi fitsari ta Danyi mintuna aciki kafin tafito
tana gyara wuyan rigarta da har lokacin maballanta suke abude wasuma sun fincike sun fita sbd
yanda ya ciresu bayan sallar asuba dazai rabata da rigar.
Tana fitowa ta hangosa zaune a palon Yana duba sako a laptop gabaki daya hankalinsa nakan
laptop din ya aiki da ita Jin rufo kofar bedroom dinsa yasashi sanin ta farka Amma Bai tashiba
baikuma dauke idanuwansa da hankalinsa Dake kan aikin gabansa ba saidai ya Dan bude Baki
cikin kulawa da kwarjini tareda Kamala yace"
Good morning Mah lady,
Xo nan naji Yaya Kika tashi.
Ba musu ta qaraso tana kokarin zama gefensa ya kamo hannunta ya jawota ya Dora Kan
cinyarsa Yana barin aikin dayakeyi ya maida hankalinsa kanta Yana shinshina gashinta daya
tayata drying dake qamshin _Elvive extraordinary oil_ na _L'Oreal Paris_ ya gangaro da
hannunsa ya Kama nata hannun ya Dora Kan cikinta natane aqasa sai nashi asaman natan
cikin kulawa da tsananin son cikin dama ita dake daukeda cikin yace"
Hey little Alfa,good morning.
Bakinsa dake maganar take kalla kafin yasake mgna akai knocking ta waiwaya ta kalla kofar
tana kokarin sauka daga jikinsa ya riqeta Yana hanata damar hakan sbd yasan haniface yayi
waya da ita kafin yabaro bedroom cewan takawowa Naj din abincin Dan yasan takusa tashi
baccin.
Ahankali ya 'dan daga murya kadan yace tashigo kawai.
Hanifa najin hakan ta saki numfashi Dan kuwa tasan da wuya idan ba ajikinsa Naj takeba tunda
taga Bai taso ya bude Mata kofarba da kansa,
Marshal bayajin kunyarta,ta kowama bayaji kila Banda iyayen Naj din Suma Babu ruwansu da
yanayin rayuwarsa Amma Naj din dayake neman zararwa da kunya yakamata ya ringa raga
Mata.
Murda kofar tayi taturo tareda shigowa ta maida ta rufe tana kallon Naj da tun tanajin kunyar
Hanifan yanzu ta rage tunda ta fahimci shikuma Haka Allah yayisa da sakewar fuska batareda
ta nuna taga zaman dasukaiba tace"
Barka da safiya sirikita.
Da wani irin kallo yabita Yana sakin boyayyan numfashin daya sakata sake baje idonta akansa
Jin sunan da Hanifa takirata dashi yace"
Da gaske ke sirikartace?
Na dauka qawartace,
Hanifa sirikata na nufin matan dana right?
Aje kayan da Hanifan ta shigo dasu tayi a dining tana cewa"
Eh matan Dana ko matan qanin ko Matan yayana duka suna nufin sirikata.
Wani murmushin yakuma saki Yana Kai bakinsa kunnenta ahankali yace"
Kin zama sirikatanta kenan no more my qawa ko my aminya right?
Wani kallon daya kusan kashesa da mamaki Tai Masa ta bude Baki cikin taushin muryarta tace"
Zata cigaba da zama qawata Aminiyata har abada,
A alaqana da ita bandauketa sirika....
Murmushin dayan sakarwa zancen yasata kasa qarasawa tana miqewa da sauri tabar jikinsa ta
nufi gurin Hanifa wadda ta juyo zata baro gurin ta nufi kofa tana cewa"
Inada abin Yi natafi.
Hajjo Kuma na gaidaki...
Ko tsayawa Jin abinda Naj zata fada bataiba ta nufi kofa tafice tareda rufowa.
Tasowa yayi yaqarasa janta zuwa dining din sbd sandarewan datai a tsayen Jin gaisuwar hajjo
data Aiko Mata idan ba tsokanarta Hanifa keyiba da gaske ne tashiga uku da kunyar Hajjo.
Batasan lokacin data kallesaba cikin damuwa tace"
Yanzu shikenan hajjo tasan inda nakwana?
Zama yayi yana zaunar da ita yayi kissing hannunta Yana cewa"
Harma da Wanda Kika kwana taredashi tasani da......
Rufe Masa Baki tayi da sauri tana kallon idonsa Dan tasan zai iya fadar komai batareda shakka
ba.
Zame hannunta yayi daga bakin nasa Yana nuna Mata abinci da ido.
Kusan shine yaciyar da ita abincin a baki duk da tana Dan kaucewa har Dole ta ringa ci daga
hannun nasa suka gama yajata suka koma daki.
Cikin black _Balenciaga_ short sleeve da wando,
Sai agogon _Emporio Armani_ dake hannunsa Wanda yakeda tsananin tsada yafito Kai tsaye
ya nufeta tana tsaye gaban mirror tana sake busar da kanta daya sakata Kuma jiqawa ya Dan
kamota ta baya yayi kissing wuyanta ta lumshe ido Yana shaqar qamshin turensa daya shigeta
sosai yace"
Zanfita saina dawo ki shirya gobene tafiyanmu da qarfe goma na safe.
Juyawa yayi yafice yabarta tsaye tana kallon fuskarta dake blushing ta cikin madubi kafin taci
gaba da busar da kanta da dryer.
Riga da skirt na lace maroon tasaka Wanda hanifa takawo mata tayi sai turarensa datai amfani
dashi tuna nata basa Nan din ta fito tana Jin kunyar kanta sbd yau kayan data saka din Kamar
sun bayyanarda Dan kumburin cikin nata.
Palon tafara gyarawa kafin tadawo bedroom dinsa din tagyara takira Hanifa aka Aiko Mata
ruqayyat ta taimaka Mata da gyaran kicin ita Kuma tayi sauran.
Qamshi koina ya dauka ta ragewa AC din palon qarfi ta dangana ta rungumi kunyarta ta fito
bayan ta rufo ta zaro key din tayo cikin gida tunda dai Dole ta taho din komai kunya.
Cikin tsananin rashin sa'arta hajjo na Palo tareda Dadah datazo bankwanar tafiyar tasu gobe
Dan shi Marshal din yashiga kafin ya fita zuwa inda zashi Dan zai iya dawowa kurarren lokaci
shiyasa yashiga yayi musu sallama ya wuce shine Dadahn tazo sallama wa mutuniyar tata.
Tana ganin Dadah ta dauke Kai tana saddaqarwa da abinda zai biyo baya tafara qarasowa jiki
amatuqar sanyaye.,
Cikin mamaki Dadah ke kallonta lokacinda ta bude Baki ahankali tace"
Hajjo Ina wuni?
Dadah sannu da zuwa.
Dadah da bakinta baya shiru da barin zance tace"
Wannan daga ita take cikin uwar ranar nan?
Badai haryanxu tana zuwa aikinba da sabon ciki?
Cikin kulawa hajjo take kallon Naj din tace"
Aa tadaina zuwa,
Aiki Kuma Kam yanzu ai saidai kila acan Qasar idan mijin zai Bari,
Yanzu daga sashen mijinta take...
Wata dariyar tsufa Dadah tayi tana maida kallonta kan Naj din tace"
ALLAH me iko,
Yanzu agaban hajjon bayan kalolin rashin arzikin dakika shimfida kala kala akan bakyason mijin
shine tun kafin ayi tarewa ke harkin tare abinki,
Ai kuwa kin hutar da hajjo da afake sashenta Ana Mata Dan wake zagaye Bata saniba kuje can
ku qarata Allah yasa yaqara dirko Miki wani cikin daga can....
Dariya Hanifa tayi tana cewa"
Dadah Ana samun wani cikin bayan akwai wani dama?
Hajjo kuwa dariyar zancen kawai tayi tana cewa"
Najma zoki zauna kusa Dani muyi firar bankawana kinji.
Qarasowa tayi tana Dan hararar gefen Dadah ta zauna.
Dadah tace"
Eh nagani kina hararata,Dattijo kikawai baniba.
Sai alokacin Naj ta kalleta tace"
Shikuma me yayi Miki?
Haihuwarki yayi.
Fira suke atsakaninsu ganin Haka itada hanifa suka bar palon suka nufa dakinta inda Hanifa
tahau hada Mata kayanta cikin 'daya daga cikin sabbin set din akwatinan da hajjo tasa Marshal
din ya biya na gurin Haj nafisat da aka siyo.
Hanifa na hada Mata kayan it's Kuma tana waya da Sarah akan takawo dukkanin takardun
dazata sakawa hannu na damqawa sabon president dinsu aikin.
Sai kusan yamma suka fito tareda Dadah suka tafi gidansu Dan yimusu sallama.
A dakin umma habiba suka fara tsayawa suka Dan Jima acan tana Mata Yan nasihunta duk da
kusan duk da Gori acikinsu kafin suka fito suka nufi sashen ummansu suka yada zango acan
tareda umman da anty Amina suka hau nasu bakin.
Umma Tai Mata nasiha sosai tareda Yan maganganu na rayuwar aure da Kama miji kafin su
anty Amina suka Dora da nasu Wanda suke hadawa na tsokana dakuma tunatar da ita hadarin
kusancin Hannah da mijinta tunda aure zai iya shiga tsakaninsu.
Sai dare suka baro gidan bayan sunyi sallama da kowa umma ta hadota da tsaraba,suna
dawowa gidan Kai tsaye a palon ta zauna tana fuskantar Sarah Dake jiranta ta zauna tana
cewa"
Sorry Sarah nabarki jirana.
Karban files din hannunta tayi tana daukar pen tafara budewa tana kallon kayan drinks da aka
kawowa Sarah da snacks tace"
Kici wani Abu Bari naduba nayi signing din sai driver ya maidaki gida tunda dare yayi.
Fira sukeyi sama sama tana duba takardun tana signing Sarah nafada Mata yanda abubuwan
office din ke tafiya saita Dora da cewa"
Naj Abbas fa yanata yawon son adawo Masa da aikinsa anyi zama yafiso hudu Marshal ya
tsaya akan hukuncinsa ya takura akan saina basa sabuwar number dinki Wai yanason magana
dake Akan Marshal din kozaki Masa mgn dashi.
Bata dagoba abinda ke gabanta takeyi cikin rashin kulawa da zancen tace"
Duk indama zai samu Number na ki tabbatarda Baki Bari yasamuba
Maganar aikinsa Kuma bana tunanin ko hajjo zata sauya ra'ayin Wanda yake maganar akai
bare Ni.
Qarasa signings din tayi tarufe file din qarshe tana hadawa ta miqawa Sarah tana cewa"
Thank you Sarah.
Naj zanyi kewarki gskia Amma Kuma hakan shine fatanmu ki kasance tareda mijinki kisamu
hutawar gidan aure,Ina Miki fatan alkhairi a rayuwar aurenku.
Nagode Sarah,muje Naga Wanda zansa ya kaiki gida.
Miqewa sukai suka fara zuwa dakin hajjo sarah Tai Mata sallama suka fito suna kawowa
harabar gidan Yana dawowa daga masallaci sallar ishai sanye cikin riga da wandon _Nike_ ash
kala
Sarah ce ta gaidasa cikin mutuntawa da girmamawa matsayinsa name Companynsu.
Da kansa yasaka drivernsa yakai Sarah din gida da motarsa kafin suka nufo sashen hajjo
tareda mutuniyar tasa tana gefensa Yana amsa wayar da aka kirasa lokacin har suka Isa ya
wuce dakin hajjo Kai tsaye ita Kuma ta wuce dakinta.
Ya Jima sosai a sashen kafin ya tafi
Itama ta fito taje kicin ta dauko drink da snacks tadawo dakinta ta aje kafin ta Haye gado ta
kwanta Dan tuni dama tayi Shirin bacci tana kwantawa bacci ya dauketa.
Washe gari qarfe Tara aka fito da kayanta aka Kai mota tafito sanye cikin doguwar English
chiffon gown me Dan transparent sai blue skinny jeans daya lafe jikin cinyoyinta daga saman
kuwa rigar ba transparent bace.
Handbag din _Calvin clein_ ce qarama a hannunta wadda wasu abubuwanta ke ciki qafarta
kuwa loafers ne D&G.
Rungume hajjo tayi idanuwanta na Dan cikowa da hawaye ahankali ta furta" I will miss you
hajjo.
Murmushi hajjo tayi tana shafa kanta tace"
Rayuwa mai albarka Najma,
Ki kula da kanki Kuma Kinga kinada ciki,munada buri da fata akan cikin Nan idan Allah yasa
yazo lafiya yakuma Raya manashi.
Ahankali ta gyada Kai tana cewa"
Inshallah hajjo.
Fitowa sukai tareda Hanifa suka Isa sashensu Dad Alfa Wanda ke jiranta shima.
Yan bayanai da nasihu yai Mata kafin ya Dora da cewan yasaka Mata kudi a account din
_CPB_ account na qasar da aka bude Mata kafin yayi Mata adduar fatan alkhairi suka fito jikinta
duk a sanyaye.
Koda suka fito tareda Hanifa da Anty Amina data kalli Dad Alfa daya fito shima zai fita cikin
girmamawa ta gaidasa tana matsawa daga hanyar dazai wuce din ya amsa tareda kallonta
Yana cewa"
Aminah Yaya ummanku da Dadah Ina gaidasu.
Zasuji" tace kafin suka wuce mum Malika na Bin su ukun da muguwar harara tana cewa" tsofin
munafukai acikin ranta.
Suna Isa mota Yana zaune cikin bayan motar Yana waya a natse fuskarsa sanyeda _American
optical_ goggles dayayi Masa wani irin kyau Dan gabaki daya tun anan din yakoma shigarsa ta
can turai.
Hango Hannah sukai tafe a shirye cikin riga da wandon jeans na _Valentino_ tayi kyau sosai
itama fuskarta sanyeda _Bulgari flora_ glasses dinta dama tuni aka saka akwatinta a mota.,
Baki sake Hanifa ke kallonta Anty Amina ma kusan kasa riqe mamakinta tayi Banda Naj dataji
wani Abu yataso Mata ta juyo ta kallesa ta cikin glass din motar taga ko gefenda Hannah din ke
tahowa Bai kallaba sbd hankalinsa nakan wayar dayake Yana Dan Yi Yana dagowa ya kalleta
cikin kasa gajiya da kallonta.
Maida kallon nata takuma Yi Kan Hannah da kayan jikinta dasuka bayyanarda rayuwar turai
gabaki daya atareda ita Allah yasama dad ya fice da kila shi zai iya Mata mgna Amma mum
Malika Kam rungumeta tayi tana washe Baki tace"
My baby I will miss you, please ki kula da kanki karki wahalarda kanki akan program dinnan
Amma kiyi kokari ki dawo min ta abinda zanyi alfahari dake, Allah yasamu abinda kikaje yi,
Dan qasa qasa tayi da muryarta yanda bazasujiba tace"
Idan kungama kwanakin program din kibar masaukinki kikoma gidan Marshal din kema kafin
kidawo.
Gyadawa mum din Kai tayi tana murmushi tace"
I love you mum, muntafi saimun dawo.
Baya gefen Marshal su Anty Amina suka saka Naj dataji Kamar tafiyar tafita ranta Amma Kuma
ayanda takeji ko cewa akai anfasa da ita ta zauna bazata zauna din ba matuqar da Hannah
za'ai tafiyar.
Tana zama ya Kama hannunta ya sarqe da nasa Yana Dan kashe Mata ido daya har lokacin
Yana waya.
Gaba Hannah tashiga badan tasoba aka tada motar suka fice daga gidan su anty Amina na bin
motar da ido.
Ciki suka dawo bayan tafiyansu Naj din suka zauna palon jiki a mace sbd sunsan sai wani ikon
Allah ne zai Hana qura tabiyo bayan wannan tafiyar tasu da Hannah tunda sunsan Naj din ita
Kuma kayan haushinta sunfi na kirkin yawa zata tsaya fushi da basarwa har Hannah ta ringa
Mata shishiginda zai iya kawo damuwa.
A airport suna Isa Babu Bata lokaci sbd time yayi akai duk abinda za'ai suka wuce.
Ticket din Economy class aka siyawa Hannah sabanin shida Naj dake first-class sbd Daman
yanason sakewa da Naj din yanda zata sake Masa hannunta kuwa dama Yana cikin nata tunda
suka zo airport din har suka Shiga jirgin suka zauna Wanda Hannah tayi zagi,tayi Allah ya tsine
yafi so a qirga. ##MAMUH#
************************
*_ZAFAFA BIYAR 2022í ½í´¥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*í ½í±‡í ½í±‡
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*í ½í±‡í ½í±‡í ½í±‡
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*í ½í±‡í ½í±‡
09134848107
*_DM 51_*
*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE_*
08067558902
Manyan Mata,manyan yara dasukasan sunsan kansu afagen zagewa suyi gyara me kyau na
musamman suzo ga gwanarmu wadda muka tabbatarda aikinta da kyawun kayanta,
*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE_* nada kayan gyaran Amare da masu
haihuwa,gyaran jiki Dana cikin jiki harma dana fata Wanda take aikawa koina a fadin Nigeria.
Ta bangaren kayan Mata ma kuwa dukkanin kayan gyaran dakike buqata tanadasu kala kala
masu kyau da tsafta tareda inganci da qarfi,
Mun tabbatarda aikinta shiyasa muka kawo muku tallarta.
*_AMARYAR KB GLOBAL ENTERPRISE_*
08067558902
******************************
*_51_*
Saida asuba jirginsu ya sauka lokacin Naj tayi matuqar gajiya sbd yanayi na ciki ga Kuma
yunwar datake damunta duk da snacks din dataita ci Basu Mata maganin yunwartaba abincin
gske take buqata shiyasa duk jikin yake a sanyaye bawani qwari Koda suka fito