Showing 66001 words to 69000 words out of 101517 words
Chapter 23 - DEEN MARSHALL COMPLETE HAUSA NOVELS BY MAMUHGEE.pdf
sagewa Dan Bata fatan wani Abu ya samu Hanifa ko babyn,
Tana roqon Allah yasa Hanifa cikin Nan rabonta ne Dan tafi shaidar yanda take tsananin son
haihuwa da samun baby Amma wannan ne karo na uku Wanda dagashi idan har ta rasa batajin
za'a Kuma yimata wani dashen.
Matsowa Sarah tayi qafafunta a sanyaye ta kalli Naj cikin kulawa da Dan qaramin sauti tace"
Naj ki zauna Kuma ki Dan kwantar da hankalinki kema kinsan ba'a son kishiga damuwa sbd
yanayinki please.
Satar kallon Marshal Sarah tayi taji gabanta yasake bugawa cikinta na Dan kadawa ta dauke
Kai sbd ganin wani irin mummunan hadewar fuska da wani boyayyan fushi dayake cikin
idanuwansa Yana zaune ya harde qafa Babu Wanda yacewa kala sai jiran tsammani dasukeyi.
Qin zama Naj tayi tana Dan kaida kawo ahankali idanuwanta na neman kuka Amma yaqi zuwa
sbd tashin hankalinta biyu ya kasu tanajin tashin hankalin halinda Hanifa ke ciki ga nata tashin
hankalin sbd sosai take sake jin tsoro da shakkar cire cikinta dayake neman mamayarta Wanda
ke sake cusar Mata da kai gabaki daya ta rasa wane tunani zatai,ta rintse ido tana dafa bango
sbd sarawar da kanta ke dauka Yana neman sakar Mata da jiri.
Anty Amina dake kallonta cikin kulawa tace"
Naj ki zauna Mana tunda kema zazzabin da kikai Ba gama sakinki duka yayiba karki qara Mana
wata damuwa Anan idan Kika shiga cikin wani hali.
Sai alokacin ta kalli Anty Amina tanason fashewa da kuka yaqi zuwa ta Dan sake dafa bango
Sarah na kamata ahankali ta qarasa kujerar kusada Marshal ta zauna tana sunkuyar da Kai har
lokacin hankalinta duka baya jikinta.
Gabaki daya Babu wata alamar data nuna Marshal dake gurin yasan da wanzuwar dukkaninsu
a gurin bayan anty Amina data Dan basa bakin komai zai daidaita inshallah Akan Hanifa itama
bayan Kai daya gyada Mata ahankali bai samu cewa komaiba sbd a yanayinda yake ciki idan
ya fitarda fushinsa da tsananin bacin ran dayake ciki kowa bazai iya tsayawa agurinba.
Ismail ma miqewa yayi yafara safa da marwa yana Dan bubbuga hannayensa dake nade a
kirjinsa,
Yanason Kiran Yan gidansu ya sanar musu Amma bayason tayar musu da hankali tukuna sai
ansamu Kan matsalar.
Hannuwan Naj rawa suke ta damqesu tana Dan rintse idonta daketa cikowa da hawaye Amma
kuka da hawayen sun kasa saukowa tsoro ne fal aranta,
Hannu ta daga ahankali takai Kan cikinta ta dafe tana sake Shiga wani sabon yanayi,anty
Amina dake lure da ita ta matso ta dafata Anatse tana kallon fuskarta da duk take bayyanarda
damuwarta a natse tace"
Naj,kina Lafiya dai?
Kasa mgn tayi ta sauke Kai ahankali tana sake dafe cikin ta gyadawa anty Aminan Kai.
Dr sa'id ne ya bude kofa yafito ahankali tareda wani Dr Adebayo
Dukkaninsu suka kallesa suna kallon idonsa da bakinsa jiran Jin abinda zai fada Dr Adebayo
kuwa wucewa yayi zuwa office dinsa.
Kallon Marshal Dr Sa'id yayi Yana sauke numfashi tareda ajiyar zuciya ahankali kafin ya maida
kallonsa kan Isma'eel a natse yace"
Hanifa ta rasa cikin sbd ta haifi babyn da Bai Isa haihuwaba kwata kwata hakan ne yasa babyn
baizo da raiba sbd baima Gama zama cikakkiyar halittaba,
Jinin ya tsaya duk da ta zubarda jini sosai Amma bama buqatan qara Mata wani jinin sbd
munduba pcv dinta is normal,
ayi hakuri Haka Allah ya nufa,wannan jarabawa ce idan anyi tawakkali za'a cinyeta Kuma za'a
ga ribar hakan, Allah yabata lafiya,an bi kofar baya anfita da ita zuwa dakin hutawa zaku iya
samunta acan.
Sake kallon Isma'eel yayi Yana cewa"
Zaka jira mu hado maka babyn sai aje a rufe ko.
Kallon Marshal da idanuwansa suka qarasa sauyawa gabaki yayi cikin kulawa yace"
Sorry Marshal,Allah yabada hakuri yabada rayayye,
Ita Hanifan kwata kwata Babu wata matsala atareda ita yanzu saidai damuwa Dan Haka tana
buqatan ku dukan.
Juyawa yayi ciki yakoma Dan hado gawar 'dan babyn yakawo.
Kowa agurin kasa kuka yayi sai Naj dakejin kukan nason taso Mata Amma yaqi fitowa ta dago
jajayen idanuwanta ta kalli Isma'eel da qarfin imaninsa yasa ya daurewa zancen sosai Yana
jiran fitowar Dr sa'id
Kasa kallon gefen Marshal tayi tanajin nauyin zuciyarta na qaruwa ta miqe Kai tsaye ta bar
gurin ta nufi hanyar dakin datasan can za'a Kai Hanifan a Amenity Sarah na bayanta anty
Amina kuwa matsowa tayi cikin kulawa da tsananin tausayawa tana sake bawa Marshal hakurin
wannan rashin shida Isma'eel dake gyada Kai cikin wani yanayi Yana cewa"
Bakomai anty Amina nagode.
Marshal kuwa Kai kawai ya gyada Mata har lokacin Yana zaune a inda yake idanuwan Nan
tamkar zasuyi Aman wuta sbd baqin ciki,bacin Rai dakuma damuwar Hanifa.
Tsayawa tayi itama har akawo babyn.
Da tsananin sanyin qafa Naj ta tura dakin tashiga fuskarta na narkewa da ganin hanifar wadda
tana ganin Naj din ta sauke Kai wani irin gigitaccen kuka na zuwar Mata da sauri Naj din ta
qaraso ta zauna tana rungumeta itama Bata hawayen na gangarowa alokacin.
Kuka Hanifa keyi Sosai Wanda yake fitowa daga tsakiyar ranta tareda dibbin 'daci da ciwon
rashi na cikinta,
Sosai takejin wani irin radadi da zafi dama ciwo Wanda takeson kokesa idan zai fito shiyasa
take kukan sosai zafin zuciyar Amma yakasa raguwa saima tsananta da quncin keyi.
Kukan Hanifan har cikin zuciyarta Naj ke jinsa sbd kukane da Bata taba irinsaba,kukane me cin
Rai na Shiga zuciya,tanason Bata hakuri Amma takasa bude Baki sbd tanajin ciwon da Hanifan
keji,tasake rungumeta nata hawayen na sake gudu.
Kukan datakeyi tuni yafara daga hankalin Naj din ta dago tana kallonta ta bude Baki murya a
yamutse taka cewa"
Hanifa Dan Allah kiyi hkr ki daina kuka Haka Inshallah Zaki samu wani babyn,
Dan Allah ki daina kuka Haka Kinga Baki Gama warwarewa kada wata damuwar ta shigeki.......
Wani kukan me qaramin sauti yakuma zuwar Mata tana girgiza Kai cikin dasashiyar murya tace"
Naj Ina tsananin son babyna Amma Allah baiyi Zan zama uwaba.
Hanifa karki cire Rai daga rahamar ubangiji Dan Allah..."Naj tafada hawaye na gangarowa
idanuwanta dasukai jajir.
Naj bakowane yakeda rabo da Sa'ar zamowa uwa ba kila Ina cikinsu duk da na dandana
zamowa uwa me renon ciki ko ahakan na godewa Allah
Amma zafi nakeji da qunci cikin zuciyata sosai......kakane yaci qarfinta ta sunkuyar da Kai
tanayi.
Gabaki daya jikin Naj mutuwa yayi da Tsananin tausayin Hanifan Dan kuwa ko Hanifan Bata
fadaba kowa yasan zatai qunci sbd tsananin soyayyarta da son haihuwa Amma Allah ya
qaddara hakan,
Sake mutuwa jikinta yayi da wannan yanayin na Hanifa ta dafa cikinta tanajin shin idan ta cire
cikinta zata iya Shiga irin wannan halin na Hanifa na kuka da baqin cikin rasa nata babyn¿
Dafata Sarah tayi ahankali,Bata dagoba ta rufe idanuwanta hawayenta na gangarowa akaro na
farko taji kamar qaunar cikinta ta motsa aranta tasake kallon yanayin quncin dake Kan fuskar
Hanifa ta rufe ido tanajin qaunar cikinta amatsayinta na uwa,
Uwa mahaifiya zata zama,idan ta cire cikin tazo kukanta yafi na Hanifa.
Dafe kanta tayi tana rasa tunanin Yi sai tazama kamar Hanifan ta zuru zuru da ita sbd rashin
sukunin zuci Dana fili ga na Hanifa.
Bude Baki takuma Yi a kasalance tana son rarrashin Hanifan Amma takasa sai shafa Mata
bayanta take tana gyada Mata Kai alamar tausayawa har lokacin hannunta daya na Kan cikinta
datakejin Kamar zai zube sbd tsoro da firgicin datake ciki,
Tunanin hakan Kuma shiyafi komai sakata rudu a daidai yanzu a wannan lokacin.
Shigowan marshal ne yasata dagowa ahankali ta kalli kofar sbd Jin qamshinsa daya fara Shiga
hancinta ta sauke idanuwanta akansa zuciyarta na harbawa da wani irin bugu tana qure
kallonta akansa akaro na farko tunanin wannan shine mahaifin cikin jikinta,
Shine uban 'da ko yarta,
Wasu irin zafafan hawayene suka gangaro Mata,ita tata qaddarar kenan kuma ta abun kunya
cikin qanin qawarta ajikinta,
Tayaya zata iya kallon kowa da wannan cikin bayan kullum cikin tashin hankalin ta qi Aminta da
auren ake,
Duniya ta shaida rashin yardarta da Aminta da auren ta Yaya zata iya kallonsu da cikinsa
ajikinta bayan ko tarewa bataiba, ta ina?ta Yaya suka samu kebewar data samu cikin?
Da wane ido zata kalla hajjo da ma Dadah datasan bazatai shiru ba,harma ummanta da Hanifa
duk batasan ta Yaya zata iya kallonsu da wannan cikinba gashi Kuma yanzu bazata iya cutatar
da kantaba ta cire cikin sbd jinsa data farayi ayau akuma Nan asibitin sbd gani ga wane datai.
Yanayin fuskarsa da Babu wani sauki acikinta kamar dai ayanda yake kame koyaushe saidai
yau muguwar kamewar tafi ta kullum Wanda takewa kallon yanayinda Hanifa take ciki ta dauke
idanuwanta ahankali daga kansa din ta sauke Kai tana miqewa daga gefen hanifar ya qaraso
Yana kallon Hanifa da ganinsa keson dawo da kukanta Wanda yafi komai cin ransa ganin
hawayenta Dana wadda yanzu yafi komai takaicin kansa daya Bata lokacinsa.
Riqeda hannun Hanifa yake Yana kallonta da idanuwansa cikin kulawa yace"
Soon Zaki Kuma samun wani Inshallah just have faith ki dauka wannan jarabawa Allah zai duba
zuciyanki ya Baki wani ok????stop this tears now.
Handkerchief dinsa yaciro daga aljihun wandonsa ahankali ya fara share Mata hawaye Yana
Dan kokarin sake kwantar Mata da hankali fuska kame.
Anty Amina ce ta qaraso itama tana sake Bata nata rarrashin suna cikin hakan saigasu umma
da hajjo sun iso motarsu daban ta dad Alfa da mum Malika dabam sai 'yan gidansu Isma'eel
dasuka iso mum dinsa da qannanesu biyu sai qaninsa namiji daya na dakin ya cike da Yan uwa
kowa Yana fidda kalar jimaminsa sbd Babu wanda abun Bai taba zuciyarsa Dan dukkaninsu sun
qwallafa Rai a cikin bama kamar hajjo da Dad Alfa sbd rashin 'yaya a familyn Alfa din sunason
'yaya su hayayyafa a cikin zuriar ko Dan a morewa dukiyar da aketa tarawa.
##MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR 2022í ½í´¥_*
*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)_*
_SO DA ZUCIYA_
*_SAFIYYA HUGUMA_*
_DABI'AR ZUCIYA_
*_MAMUH GEE_*
_DEEN MARSHALL_
*_HAFSAT RANO_*
_HALIN GIRMA_
*_BILLYN ABDULL_*
_TAKUN SAKA_
*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*í ½í±‡í ½í±‡
D’aya 300
Biyu 400
Uku 500
Hudu 700
Biyar 1k
*_Zaku tura kudin a_*
6019473875
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai shedar payment dinki a*í ½í±‡í ½í±‡í ½í±‡
08184017082
*Kokuma katin waya na MTN anan*í ½í±‡í ½í±‡
09134848107
*_DM 41_*
Yanda kowa ya damu yake Kuma bayyanarda damuwarsa yasa Hanifa daina kukan saidai
fuskarta Kam Bata dubuwa ta kumbura sosai tayi jajir daqyar mumyn Isma'eel tasata Dole
lallabata Tasha tea dasu magani aka hada ruwan zafi sosai anty Amina ta taimaka Mata tayi
wanka ta gasa Mata jikinta suka fito tasaka doguwar riga Mara nauyi lokacin maraice yayi sosai
kusan kowa ya tafi sai anty Aminah da Naj din sai Sarah Yar hannun damar Naj Isma'eel ma
lokacin yasake dawowa daga gida dayaje ya sake kintsowa cikin wasu kayan sbd waincan sun
baci.
Kallon Naj da idanuwanta sukai laushi Sarah tayi ta kalli Anty Amina tace"
Anty Amina kice tazo na maidata gida Mana ko abinci taci itama ba isashiyar lafiya ne da itaba
gashi idanuwanta sun nuna ta galabaita Amma taqi zuwa
Hanifan ma gatanan alhmdlh taji sauki ki daure muje gidan kici abinci kiyi wanka ki Dan nutsu
saiki dawo asibitin.
Kallonta Hanifa tayi da idanuwanta dasukai mugun nauyin kumburi ta bude Baki ahankali cikin
kulawa a natse tace"
Naj kije gida Mana ki huta gaba daya kinyi na kyan gani sbd damuwa da gajiya,naji sauki
banajin komai yanxu kije banson ganinki ahaka zanji ba dadi.
Dagowa Naj din tayi tana kallon Hanifa jikinta na sake sanyi ta dauke idanuwanta daga kanta
tun yanzu tanajin kunyar hada Idanuwa da kowama kafin aji aikin dake jikinta cikin sanyin
murya tace"
No banajin yunwa ko naje gidan bazan samu nutsuwaba zan zauna din anan...
Naj karki kamanta fa tunda safe Kika fita ba daga gida kikayo Nan ba Dole kina buqatan samun
hutawa....
Sarah please nace Zan zaunsa Anan...
Anty Amina ce ta katseta da cewa"
Akace kije ki dawo mana.
Marshal ne ya shigo dakin tareda Isma'eel da Dr sa'id lokacin har anyi sallar magriba
kowannensu Yana zuba nasa kalar qamshin turaren Amma gabaki daya nasa ya take nasu
qamshin ya cika dakin Yana sanyeda jallabiya fara qal da alama wankan maraice yayi ya nufa
masallaci dagacan yayo asibitin idanuwansa na Kan Hanifa datake zaune Kan gado duk jikinta
a mace tayi sanyi.
Wasu maganunan Dr sa'id yakuma rubutawa cikin folder dinta tareda Masa wasu tambayoyin
yana rubutawa cikin folder din yayi signing ya rufe Yana ajiyewa ya kalleta cikin kulawa da Bata
qwarin gwiwa yace"
Ki sake Inshallah rabo na zuwa agaba,ki qara hakurine Hanifa okay???
Gyada Masa Kai tayi ahankali tana cewa"
Thank you Dr sa'id.
Dan murmushi yayi Mata kafin ya maida kallonsa kan Naj datai mugun laushi sbd har wani irin
jiri me qarfi take gani daga zaunen cikin kulawa da mamaki yace"
Naj yakamata fa kije gida kisamu hutawa da abinci,you don't you look good kinsan Kuma
yanayinki kema masu ciki ba'a son suna saka damuwa irin haka,"""kallon Marshal yayi Yana
cewa"
Inaga yakamata ka kaita gida yanayinta ya nuna ta galabaitu sosai.
Tsit dakin sukai kowa wuta na dauke Masa musamman Hanifa da anty Amina dasu kadaine
Basu San da cikinba sai Isma'eel Amma shi me cikin yasani yau din sai Sarah datafi kowa sanin
komai.
Batareda anty Amina tasaniba tace"
Waye me cikin??
Kallonta Dr sa'id yayi sai alokacin ya lura da yanayin kowa yake fahimtar ba kowane kenan
yasan da maganar cikin ba ya Dan juyo Yana kallon Naj datai zuru takasa dagowa jikinta
amatuqar sake yayi Dan gyaran murya Yana kallon Anty Amina yace"
Tana buqatan zuwa gida koma yayane."ya juya ya nufi kofa zai fice Marshal ya dago sai
alokacin ya kalleta lokacinda take bude Baki jiki ba nauyi tace"
Lafiyata kalau banajin komai Zan zaun.....
Akaro na farko da kowa yaji tsawar Marshal Da ba Naj din kawaiba Hanifa ma da anty Amina
Saida suka Sha jinin jikinsu suna kallonsa cikin tsananin mamakin ganin bacin ransa shima
akaro na farko da wani irin kallo dake sake saka Mata shakkar halinda take ciki Yana dauke Kai
daga kallonta yace"
Kitashi ki koma gida yanzu,
Anty Amina ku maidata gida karta sake dawowa asibitin ta zauna gida.
Yana fadar hakan ya miqe ya nufi kofa ta dago tanabin bayansa da kallo zuciyarta na tsalle
ahankali ta bude Baki zatai mgana Anty Amina ta tareta da cewa"
Tashi muje kinji abinda yace.
Hanifa kuwa kasa shiru tayi ta kalli Naj din data miqe Tasha gabansa zatai magana jiri ya dibeta
tayi baya zata Fadi anty Amina da Sarah suka zaburo zasu tareta Amma yariga ya tareta ta
hanyar riqota yana Mata wani kallon Yana sake boye fushinsa akanta yace"
Ke kanki baya daukan magana daya me sauki?
Ki aje wannan shirmen kije gida idan kuma kina shirin komawane gurin cire cikin daganan toh
let me be very clear with you,
Idan wani Abu yasamu cikin Nan zakisan wayeni,nayi tunanin banzan tunaninki baikai kiyi
tunanin cire ciko ajikinki ba Amma har Zaki iya zuwa wani asibitin daban tunda Nan Dr sa'id yaqi
yarda da manufarki sbd kece Kika fi kowa shekara a duniyan Dan Haka kisa aranki wani Abu
yasamu cikin Nan zakiga abinda bakyaso now get out of my sight.
Cikin rudu da mamaki Anty Amina take kallon Naj data Gama jiqa fuskarta da hawayen baqin
cikin tayaya yasan da cikin har yasan tayi niyar zubar a hasale anty Amina tace"
Naj cikine dake kike son zubarwa?????
Cikin tsananin hawaye ta dago tana kallon fuskarsa dake a hade Babu sauki tako Ina ta bude
Baki tace"
Ban aikata......wani wanan Mari ne ya sauka fuskarta Wanda yasata faduwa zaune da sauri
hanifa ta sauko gado ta qaraso ta riqe ummu da basusan da isowarta ba Saida tayi Marin.
Dr sa'id ma da Isma'eel matsowa sukai suna bawa umman hakuri duk da kowa yashiga
mamakin jin abinda Naj din taso aikatawa.
Wasu sabbin hawayene suka tsinkewa Naj takasa dagowa tana sake qaramin kuka ahankali
Ya rintse idanuwansa tareda Dan sake kame fuska ya kamo hannuta daya ya damqa cikin na
anty Amina Yana cewa"
Ki kaita gida kawai.
Baiso zancen yafita Haka ba yaso yabarshi a tsakaninsu Amma taja zancen yafita sbd rashin
Jin ta.
Umma kallonta take zuciyarta na zafi ta tiriri Tama kasa cewa komai sbd zuciya data Gama
cinta
Hanifa ta Kama hannun umman suka Isa bakin gadonta ta zauna tana bude Baki ahankali tace"
Umma Dan Allah kiyi hkr karkiyi irin wannan fushin addua zamu taru muyi Mata,tayi lafi babba
Kam wannan karon Amma Dan Allah Kar ayi fushi da ita tashiga damuwa kuma wani ciwon
yashigeta tunda har dai akwai cikin.
Fuzgarta anty Amina tayi Dr sa'id da Isma'eel yabita Yana cewa"
Kibita ahankali sbd yanayinta Mana.
Kala Bata samu cewa ko wannnensuba sbd zuciya data Gama cinyeta itama.
Sarah da duk tagama Shiga rikita rikita ita ta Isa motar Naj dasuka zo da ita da sauri,
Anty Amina ta bude baya ta tura Naj din da lokacin take kuka sosai na abun duniya daya rufto
mata tonon asiri cikin dare guda.
A mota Babu abinda Anty Amina keyi sai tsokin baqin ciki akai akai
Tanajin badan cikin ba Kamar ta rufe Naj din da mugun duka da zagi.
Suna Isa gida Sarah na parking suka fito Naj tayi gaba tashige gidansu tanajin bazata iya Shiga
gidaba ta hada ido da hajjo da maganar cikin.
Bayanta anty Amina tabi Sarah Kuma da motar ta nufi gidan Alfa tashige tayi parking tafito
itama jiki duk a mace da yunwa da damuwar halinda Naj take ciki.
Sashen hajjo ta nufa Kai tsaye