Showing 318001 words to 319356 words out of 319356 words
Chapter 107 - ZINARE Book 1 Complete Hausa Novels by Nafisa Aliyu Salsal.txt
ba, da taimakon shaidar da yayi ma kabarin ya ci sa'ar gano shi, bayan da suka kammala yi mata addu'o'in, suka yanke shawarar shiga cikin dajin don su yi yawon buɗe ido, babu tsoro ko fargaba atare da su, saboda akwai sojojin dake tsaron su, su kansu suna da bindigunsu na kansu da suka mallaka bayan sun zama jami'an Isod, cikin nishadi suke kutsawa cikin dajin suna tafiya sunayin fira yayin da su ke tuna rayuwar da su ka ta6a yi a cikin shi saida su ka yi nisa a tafiyar tasu suka lura babu Mutun biyu a cikin su, aruɗe suka ci burki hankulan su atashe suka soma ƙwala masu kira da karfi"Sister Unaisah! Big bro! Garkuwa! Kuna ina ne! ina ku ka shiga ne"? Yadda suke ƙwala masu kira kamar maƙoshinsu zai 6alle, raba kansu sukayi gida uku wasu suka miƙi hannun dama wasu sukayi hagu yayin da wasu suka miki hanya, Gaba ɗaya suka bazama neman su a cikin dajin..
Duk Kiran da suke ƙwala masu kwata kwata ba su ji ba, suna acan saman Wata gabjejiyar Bishiya mai girma da faɗi, tana da yalwar rassa da Ganyayyakin da su ka yi mata rumfa, ba zaka taba gane akwai mutane asamanta ba, saboda rassan bishiyar da ganyayyakinta sun lullu6e su hasken rana ne kadai ya ke hasko su, wata irin ni'imtacciyar iskace ke ratsa fatarsu mai dadin gaske.
yana a kishingiɗe saman wani ƙaton reshe na bishiyar mai faɗi, yayin da ta ke akwance saman jikin shi, ta ɗaura kanta a kirjin shi.
Gaba daya tafukan hannayensa suna a daddafe da matashin cikin ta, wanda baifi wata biyar ba, sunyi kyau a cikin fararen kayan su fiye da ko da yaushe ga dukkan alamu bacci ne ya yi awon gaba da su, sunyi nisan kiwon da basa jin kira a cikin kunnan su.
kwatsam wani giant snake Ya biyo jikin reshen da suke a kai, Ya durfafe su gadan gadan, Yana gab da zai hau kafar Unaisah, Omair ya farka daga bacci, nan take idanunsa suka gane mashi macijin, wani irin faduwar gaba Yaji, Yasan muddin Ya hau jikin Unaisah zata iya firgitar da zaisa ta fado daga kan reshen.
Yana tsaka da tunanin yadda zaiyi da macijin, Yaji ta ambaci sunan shi "My Man.." hankali atashe ya dubeta a lokacin da take kokarin buɗe idanunta, kaitsaye suka shiga cikin nashi, murmushi tasakar mashi, kwata kwata bata lura da halin da yake a ciki ba, abun dayake ma zullumi kartayi motsin da zaisa macijin Ya sareta, Hamma tayi kafin ta rufe bakin yayi saurin hade bakinta da nashi, gaba daya ya kashe mata jiki ta kasa motsawa, kissing dinta ya shiga yi yayin da yake zare pistol daga waist dinsa a hankali, idanunsa akan macijin Ya saita kanshi, Ya daddage Ya sakar mashi alburushi a tsakiyar kan shi, ji ka ke daramm!!! Tsabar firgitar da ƙarar harbin da kunnuwana suka jiyo min ne yasa na gigice har bansan sa'adda Na saki alƙalamin da nake rubutu da shi ba.
Alhamdulillah 🤩 🥳🥳subhanallah🤩, Masha'Allah🤩 La'ilaha Ilallah🤲, Allahu Akhbar 💖
THIS IS THE END OF KURKUKUN ƘADDARA 😭😭😭
All praise is due to Allah, the Most Merciful and Benevolent, for granting me the strength and perseverance to complete my novel, "THE PRISON OF DESTINY"
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah mai rahama mai jin kai, Tsira Da Amincin Allah Su Kara Tabbata Ga Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S.A.W)
Ina Godiya ga Ubangijinmu Allah subhanahu wata'ala, da ya bani tsawaicin kwana da lafiya da karfin gwiwa da juriyar kammala rubuta littafina na biyu mai suna 'KURKUKUN ƘADDARA" wanda na shafe tsawon shekara ɗaya da watanni ina rubuta shi, da daɗi da ba daɗi amma Alhamdulillah yanzu komai ya wuce, na ƙara shaidawa cewa sannu bata hana zuwa, kuma komai mai wuce wa ne arayuwar mu indai mu ka yi hakuri, Tabbas Ina Alfahari da baiwar da Allah ya bani ta rubuta littafin kurkukun kaddara fiye da littafina na farko kuma fiye da sauran littattafan da zanyi agaba saboda ya fita daban babu tamkar shi ko dan darussan dake a cikin labarin wanda ni kaina dana rubuta shi, na ilmantu, na fadakantu, na kuma nishadantu, nayi kuka tamkar raina zai bar gangar jikina saboda yadda labarin ya ta6a zuciyata inajin shi kamar True life story, bani ba hatta makarantar littafin sun shaida hakan.
Ina fata littafin Kurkukun ƙaddara Ya zama Alkhairi a gare ni, Allah Yasa kowa ya amfana da littafin Kurkukun ƙaddara burina ne, 😍Darussan dake ciki Allah ubangiji yasa mu amfana dasu🙏 ya sadar da ladan gareni da mahaifana da yan'uwana da dukkan masoyana a duk inda suke a faɗin duniya🥰 kura kuren ciki Allah ubangiji ya yafe man🙏_
_*Gaisuwar ban girma da karramawa ga mahaifiyata Hajiya Rabi'atu Yahaya, she is my first luv and my everything, kin gama min komai arayuwa, Allah ya ƙara maki lafiya da nisan kwana, bazan iya misalta kyautatawar da kikayi min ba, Allah ne kaɗai zai iya biyanki, kin gama min komai, Allah yasa Aljanna ta zama makoma agare ki💘, 🤲✍️*_
_*Jinjina Ta Musamman Da Ban Girma Ga Uwar Masu Uba Hadda Marayu, HAJIYA KUBRAH, kada Ku manta gaba ɗaya Littafin Kurkukun Ƙaddara tun daga farko har ƙarshen shi sadaukarwa ne ga Mommy Kubra, Jarumar mace, mai daraja da ƙima, saboda Ita yasa na jajirce na tsara labarin ya yi daɗi yayi ma'ana saboda inaso ya zama abun tunawa da ni da alfahari a gare ta, kin gama min komai arayuwa Mommy, goyan bayanki, tallafawarki, shawarwarin ki, da ƙwarin gwiwar da kike bani sun kasance ƙarfin kuzari na, Ina alfahari dake a koda yaushe kuma bazan ta6a mantawa da halaccin da kika yi mana arayuwa ba, Allah ya Kara Daukaka Darajarki Fiye Da Tunanin Mai Tunani da ke da Ahlin ku, Allah Ya kare ku daga sharrin makiya da mahassada, Allah ya shirya maki zuri'a, Allah yasa ku gama da duniya lafiya Allahumma Amin 🤲*_
_*YABON GWANAYE YA ZAMA DOLE🤩JINJINA TA MUSAMMAN DA BAN GIRMA A GAREKU YAYYE NA NA KAINA DA BABU KAMARKU, ABUN ALFAHARI NA 🥺🥳🤩*_
AUNTY ZEE DA MUNAH BATURE MY P.E.
haƙiƙa kunyi namijin ƙoƙari gurin gyaramin rubutuna tun daga farko har ƙarshe baku ta6a gajiyawa ba, kun nuna min kauna, kun bani goyan bayanku da karfafamin gwiwa aduk lokacin dana nuna na sare, kun bani shawarwari masu muhimmanci da suka amfane ni agurin rubuta littafina, Kun tsaya min tsayin daka don ganin rubutuna ya yi kyau, wallahi ni bazan iya biyanku kokarin da ku ka yi min ba, sai dai in cigaba da yi ma ku addu'a Ina son ku ina kaunar ku 🥺🤲
_*JINJINA DA BAN GIRMA 🤩🥳😍 ga masoyana na asali masu sayan book dina, Dumbin gaisuwa da fatan Alkhairi zuwa gareku a duk inda kuke a fadin duniya, members Na Paid grps ɗina*_
_*Kurkukun Ƙaddara paid
Takun Karshe Posting section
Prison Of Destiny
kurkukun Kaddara Facebook
Prisoners Posting section*_
_*bayin Allahn nan kunyi hakuri dani, kun jure bibiyana har zuwa karshen littafina, kun jure kar6ar uzururrukana, nasan kun wahaltu gurin bibiyar littafina musamman wadanda na fara da su tun farko, don haka ina mai ƙara baku hakuri ga duk wanda na 6ata ma rai yayi haƙuri ya dubi girman Allah da manzonsa ya ya fe mun, badan komai ba sai don mu rabu lafiya, ba lallai mu sa ke haɗuwa a wani littafin ba, tun da rayuwar mu a hannun Allah ta ke, bansan ko zan kai lokacin da zan ƙara rubuta wani littafin ba, ina sonku ina kaunarku, ina jin dadin Comments dinku, ina rokon Allah daya saka maku da mafificin Alkhairinsa, Allah Ya sada fuskokin mu gaba daya agidan Aljanna, Alfarmar Annabi Muhammad SAW🤲✍️*_
Special Thanks To My Teammates
Aunty Zee Lalu, the Writer Of Asanadin Makwabtaka
Oum Arwan, Writer Of Auren Katin ƙasa and Matar Taj
Hafsat Amjad writer of Captain Janan da sauran su
_*Karku bari abaku labari, ga wadanda basu karanta books dinsu ba, Ina baku shawarar ku hanzarta mallakar naku, saboda Labaraine da babu kamar su, kunsan Team dinmu akwai baiwar tsara labari, kuma salon mu na daban ne, we're new writers but da ƙwarewar mu muka fara rubutu, Readers sun shida hakan 🤩🔥✍️*_
_*DAGA ALƘALAMIN HAFSAT BATURE MUHAMMAD (BOSS BATURE) WRITER OF ABBAN SOJOJI AND KURKUKUN ƘADDARA🔥✍️*_
*SINCE 2023 TO MON, JAN 20, 2025*