Showing 30001 words to 33000 words out of 110493 words
Chapter 11 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa
Tayi shiru hakan yasa na mike tsam na koma daki sarka dai guda ukkune banga dalilin aje wanan kayan ba ga bukatansu ya taso mutumin nan yana iya kokarinsa wajen ganin ya ban kula da karfinsa da abinda Allah ya hore masa amma kamar Ammah bata duban hakan ita.
Irin wanan tunanen na kwana dashi a raina da safe da Abbu zai fita rakani na dauko maganan inda na kara bashi shawara yace zai duba insha Allahu.
Don sam baison kan abin duniya ya samu matsala da uwayena Allah zai bashi mafita insha Allahu duk da hakan ban dadara ba na daiyi shirune a lokacin.
Bayan na dawo kuma na kara tuntuban Ammah kan zancen sai cewa da tayi dani ta gane ina son hadata da mijintane da yar uwarta.
Nakan zauna inyi mamakin irin tsoron da Ammah ke ji akan nana wani lokaci Abbu dai bai taba kayansu ba kuma bansam yadda akayi ya samu kudi ya saida gidan nan da muke ciki ya cika ba duk a cikin dan kakanin lokaci.
Sai ji nake ana fadin wai zamu tashi daga unguwar nan da muke ciki hakan yasa muka kara matsa kusa da unguwar yan uwansu Abbu don zan iya cewa a unguwa dayama muke yanzu dasu.
Abbu sam bai iya mikani daya daga cikin gidajen yan uwansa in zauna yace don yan uwansane shiya san halaiyan kowa da ace ni yarsane ta cikinsa da zai iya yin hakan gareni.
Da dai wasu dalilai daya barwa kansa sani ya sayar da gidan nasa muka koma sabon wuri amma Ammah kance wai akan dalilin karatuna da baida amfani karatun mace da yake ragage gareta tunda aure zatayi.
Sai gashi dawowan mu nan sabon wajen a yanzu Ammah din tafi kowa jin dadin hakan saboda sana,anta takeyi sosai a unguwar kuma ya karbu don tana saida kayan miya.
Tana dahon taliya tunda safe kuma tayi na rana haka na marance yara harda manya suna shigowa sosai saye sai ya kasance kamar mun shigo da sa,anmune cikin unguwar.
Karatuna yanzu kuma yana cigaba sosai don kaina a kullum kara budewa yakeyi don banda wasa haka nake raba dare ina karatu sosai don kare mutuncina.
Nan yan uwa suka fara dan kus kus akan dawowan mu nan din don sunyi mamakin yadda za ace Abbune ya sayi wanan gidan da kudinsa wai kullum yana yawo akan keke.
Shi dai Abbu din yakayi murmushi kawai idan suna zancen a gabanshi don ba huruminsu bane da dole sai ya zauna ya fada masu illa iyaka shidai ya barwa Allah sani don baiwane daga Allah hakan gareshi.
Cikin haka mukai hutu makaranta don dama koda naje an danyi nisa ga karatu lokacin don hakane nayi dan watani muka samu hutu.
Sai lokacin na fara tunanen wani makaranta zan jona islamiya don ci gaban karatuna a lokacin akwai gidan wani tsohon mai kudi dake da wani babban islamiya can nacewa Abbu ina son a kaini naci gaba.
Inda Abbu yaji dadi sosai da wanan shawaran tawa baiyi sanyi a gwiwa ba ya kaini saidai irin kalubalin dana samu a wacan unguwar shina samu a nan din na yawan kallon da nake sha gun mutane balle a yanzu dana zamo yar matshiyar budurwa.
Ko a jami,a hakan nake samun wanan matsalan dasu wasuma a gabana zasu dinga gulmana saukin abin banda abokiya ko wani kungiya ni kadai nake karatuna da komai .
Gashi ko wani malami yayi aiki zan haye don maida kai da nakeyi har sauran yan uwan karatuna suka fara zargi waiko dai suna banine wani malamin mu dan dattijone ranan da yai muna aiki na samu yace bai yarda ba saina fito na wanke kaina gareshi .
Haka na fito din nayi solving a gaban kowa tun daga wanan ranan suka daina zargina ga malamai na samu saukin hakan garesu.
ZAINAB IDRIS MAKAWA[8/14, 10:55 PM] Zainab Idris Makawa Writer: M/C COLLECTION MAKAWA COLLELECTION ONLINE BUSINESS FASHION & BEAUTY ITEMS SUCH AS LAGOS LACES, SHOES, BAG, COTONO KAMFALA COTONO ATAMFA, LAGOS GOWN DONGUWAN RIGA, TABLE FAN,HAND DRYER KIDS,FASHIONS etc
LAGOS NATIONWIDE DELIVERY SAI KUNZO A CIKIN SAUKI INSHA ALLAHU,,,,,,,,
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
2️⃣1️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
Gurfane nake gaban Abbu dan nisa kadan da India yai shimfidansa daidai shigowa gidan don haka ba kowane zai iya jin mu ba a lokacin.
Ban boyewa Abbu komai ba saidai na danyi gyaran zancen yadda zai fahinceni har zuwa photona dana samu anzana da case din da akayi da wayan da aka kawo min da yamma na mika mashi.
Nisawa naji yayi kafin ya ce to Nanata ai aikon gama ya gama saidai kiyi hankali gaba kuma din mutane yanzu ba abin yarda bane shiya kike ganin taimako yayi karanci a yanzu Allah ya kyauta ya tsare gaba.
Ki dai kara kula da rayuwanki Nana donke amanace a wajen my yanzu don haka ki kara kulawa kinji ba komai mutum zai jefa kansa a yanzu da sunan taimako don sai abin ya rufta dakai a karshe kazo kana da ansani kuma don haka kibi a hankali da kowa nana.
Shikuma wanan alherin daya aiko muna Allah saka da alheri garesa don ba kowa zai tuna kamai halarci ba haka alamu sun nuna shi din mutumin arzikine tunda yasan kiyi masa har ya iya tunanen me zai saka maki dashi ya fito muna ta nan to mun gode Allah ya tsare gaba tashi kije ki .
Bayan nabar wajen naji yasawa Ammah kira dams suna zaune da yayan anty har anty ana hayaniyar cin abincin dare.
Wanda hayaniyar ya batawa Aimana da task taji tataunawan mu da Abbu din amma bataji komai ba son hayaniyar tasu donsu basu iya abu cikin hankali ba.
Nan na zauna wajen su na debi abinci na fara ci kafin yaron anty yace min anty ban nuna making takalman dana sayo ba ya mike naji uwar na fadin takalman da yai ma kadan ya matse da yawa yaushe zaka more mai ?
Ina ruwan su anty ba anty ba anta samira ta fada daga gefen uwar sai ta biyun mai bi mata tace kedai samira na rasa mi tayi maki baki son zancen ta mama hwa tace itama zaman uwa take garemu.
Nan ta hayayoko kanwar da fadin a,a wallah Allah ya tsari gatari da saran kashi wa a uwata can dai gasu gada uwata kan gata nan kowa ya Santa.
Ke ke manta tace haushi taka bata inta ganta waka kallonta in Aeesha na waje kwab naji uwar ta buge bakin karamar yarinya lokaci guda.
Haba anty ki barta mana ya da duka haka kuma don suna shirmensu tsiya a bani so yanzu fisabillahi ya dace su hwadi wanga magana a gabaki Aeesha ?
Kukan data saka yasa Abbu da Ammah tambayan meke faruwa uwar tace ba komai nan ta biyun saratu tace in an mu ta bugeta don' tace samira tace haushin anty Aeesha takaji ranan wai ta hwaye kyau da tsiwa.
To ai sai ta yankata kafira mai mugun aniya samiran nan ba samiran arziki bace ina fadi ina kari Ammah ke fadan haka .
Taci gaba da fadin banda yar banza mai baki kamar bakin zunubi Aeesha ba kanwar uwarki bace like fadan haka gareta ina nan da safe kudinta ta dauka taba kanin ki inba nakaba wa zaima haka ?
Ta nuna ita nakune ta sadaukar da kanta ga Dan uwarku dan abindake gareta ta dauka ta mika masa ai naga ga uwar naku nan gida ta kasa bashi kwandala ya cika.
Abincin nake ci yayin da nake jinsa kamar madaci a bakina haka nake kokarin turawa don kada in kwana da yunwa don sam ban yarda da inci abinda Aimana ke dafawa daki ba don a sani dai gidansu baifi gidan mu arziki ba da zata kawo min rainin wayau.
Yo rainin wayau mana haka kawai zata zo gidan mu cin arziki ta nemi ta rainawa mutane hankali don wullakanci wanan yasa tunda ta fara hakan make bar mata dakin ga baki daya.
Yau ace nice nake gudun abincin gidan mu duo kokarin iyayyena akaina tunda na taso har kawo yau Abbu bai taba kasawa damu ba wurin ciyar damu abinci koda ba dadi kuwa zamu daici ba za a kwana da yunwa ba.
Saidana daidaici ta gama na mike zuwa daki don har lokacin duo muna tsakar gida ana shan iska kodana shiga akwance na sameta saidai batayi barci ba.
Shirin kwanciya na soma kafin naji muryanta tana fadin dadin abindai mutum yasan asalinsa hakan yasa na dan juyo na kalleta kafin nace wanda baisan asalinsa ba sai a hanasa rayuwa ko ?
Aida sauki tunda ba icce ya kawo mutum duniya ba iyayye suka kawoshi kuma ba a yanke kauna a zuciyan mumuni.
Waike malama daga jin magana kin zake haka kina ta zuba nace wai tayaki nakeyi naga kinayi me kadaine dama mutum daya ai bai magana shi kadai data haka kowa yaja bakinsa yai shiru.
Na kula da Aimana a yan kwanakin nan da take ikirarin cewa tayi saurayi dan kasan wake uwarsa tayiwa mamanta magana zata hadasu sure sai wani jiji da kai da daukan kanta so higher ya taso mata.
Tana ganin tafi kowa tana jin ita wani tsiyace a yanzu don dan kudin da take ganin ta fara rikewa a hannunta abu kadan zatace hjy tace hjy tayi kaza.
Dama nasanta da kyashi da hassada mai karatu inbaki manta ba tunda na fara Jami,a ta matsa saida tazo itama tafara haka kuma da muka taso unguwarsu suka matsa suma zasu taso da hakan bai samu ba lokacin shine ta dawo gidan mu da zama.
Sai gashi kuma tana son zama min wani kaddara a cikin rayuwata a yanzu don hakane datayi min nake bata amsa a take kamar yadda tayi min din.
Washegari kafin in gama shiri har ta fice gidan ita bata tsaya mun fita yadda muka saba fita ba a tare saidana gama na sallami Ammah don't Abbu na waje lokacin.
A nan na sameshi nake fadin Abbu zan tafi Sam na manta da zancen man bashir a raina munyi sallama yana kokarin miko min kudi mota ta tsaya kofar gidan mu.
Dani dashi muka bi motar da kallo don ganin wanene acikin motar har ya bude motar ya fito matashine dan karfafa dashi haka ya nufo inda muke yanawa Abbu sallama tare da gaidashi.
Kafin ya kalloni yace nine aka turo in dinga kaiki makaranta da safe in dawo dake da gamma jiya nazo don jiya ya kamata in fara aikina saina samu bakya nan a lokacin.
Kallon juna mukayi nida Abbu kafin nayi kasa da kaina sai naji Abbu yace amma bawan Allah waya turoka haka yana tambayan matashin ?
Dan murmushi ya sake a fuskanshi cikin ladabi yana fadin baba ni aikinane amma ita tasan da zancen ai don kamar hakan kariyane da gata a gareta wajen ogan mu.
Waye ogan naku Abbu ya tambaya cikin kafesa da ido sai naji yace man bashir jika a wajen mai martaba sarkin gabas maici yanzu.
Kai Abbu ya fara dan kadawa yana fadin na,am na,am shike nan ya turoka ka dinga yiwa yata wanan hidimar koda yaushe?
Kwarai baba ko ina take son zuwa nine zan diga kaita in har ta sanar min insha Allahu zanzo in kaita don shine aikina a yanzu.
Don haka baba don Allah karkuce a,a ga hakan don idan kunyi hakan tankar kun hanani hanyar samunane saboda aikin nan ba karamin dadin samunsa nayi ba kasan iyayye suna bukatan hutu a yanzu tunda mun kawo karfi.
Kallon Abbu nasakeyi don inji ya koresa da fada amma sai naji Abbu din yace cikin mutuwar jiki jeki Nana ya saukeki ban fatan sanadin mu ka rasa abin farautawa iyayyenka rai yarona saidai amana don Allah duk da bansanka ba amma lafazinka ya kwanta min a rai daka fada min gaskiya akanka .
To nima ga amanan yata nan a yanzu na danka a hannunka ka dinga sa ido a motsinta da komai ka kula min da ita bisa ga amana son Allah.
Insha Allahu baba zan rike nakuma kula kamar yadda ka bani amana in Allah ya yarda addu,an kudai muke nema ko yaushe garemu.
Hakane Allah yai maku albarka dakai da sauran diyan musulmin Allah ga baki daya ya amsa da amin ya kalloni yana fadin muje ko ?
Sake kallon Abbu nayi naji yace jeki Nana ta Allah yana tare dake aduk Indi kike Allah ya tsare muna ke ya kare yakai lafiya a dawo lafiya kuma.
Amin Abbu na fada tare da mike nabi bayan mutumin kafin na iso ya bude min bayan mota nashiga na zauna ina mai runtse idanuna a hankali don bakon yanayin da yazo min a bazata.
Tunda muka kama hanya dashi ba wanda yai magana a cikin mu har muka kawo ejection din da muke hawa mota da zai karasa damu school Aimana na hango cikin dandazon dalibai dake jiran abin hawa har lokacin bata karasa school ba ashe .
Har ciki ya shiga dani ya aje nayi mai nagode ba yawa hjy aikinane a fito lafiya ya fada hakan baisa na juyo ba na shiga ciki.
Ashe a gaban wanan Hindu ce da kawayenta mota ya ajeni nan suke tambaya wai wacece ni saidai ba wanda zai basu amsa har shiga aji akan idonsu nashiga suna tsaye suna gulma akaina lokacin.
Masu zugata na zugata masu cewa tunda taga haka tafi harkata kawai zaifi amma tana tsaye bakin ciki ya hana tama magana taimakona dana kara batar masu dakoni wacece sai irin rigunan nan da nake sakawa da bai bari taga tufafina na asali da tunanen ta ya bata sanin ni din ba kowa bace a lokacin.
Yayin da Aimana ta shigo school wata kawarta data ga fitana a motar take fada mata yau ba tare muka shigo bane ai taga mota ya ajeni sai hakan ya bata mamaki da har na rigata shigowa makaranta a lokacin.
Sam na manta da zancen sabon wayan da akace in kunna za ayi magana dani a lokacin sai Dana zauna zancen wayan ya fado min a rai a hankali na mika hannu na dauko wayan daga cikin jakata dake gefena.
Cikin hikima na kunna tayi karan da har ya jawo hankalin wasu a kaina amma na fuske don duk zamana dasu basu taba ganin wayata ba dama balle su dauka wani abune.
Sakone har ukku ya shigo min na farko daga mtn suna min tallan mono dinsu sai na biyu bangane number maishi ba an rubuta call me back when you are online.
Na kara maimaita sakon kafin naje na yaya sulaiman da tafiya ya kamashi zuwa Kaduna tsawon kwana hudu ke nan baya gari.
Ya rubuto yana tambayana lafiyan mu tare da nuna yadda yayi kewan rashin mu a lokacin wanda hakan yasa na dan saki gutun murmushi .
Ba laifi gaskiya kinsan yadda saurayin farko ake ji dashi hakane ya kasance tsakanina da ya Suleiman din don tun muna daukan abin matsayin wa da kanwa har yanzu mukai muna nunawa juna matukar kauna a tsakanin saidai a waya hakan yafi kasancewa a fili har yanzu muna da nauyin juna don muna da sauran yarinta gaba dayan mu a lokacin soyayyan dai akeyi hakana.
Shigowan malam Lawal yasa ni natsuwa kamar yadda ya saba muna lecture yauma hakan ne rabi da rabi hira a haka kuma yana gamawa zai iya cewa test zaiwa mutane.
Don haka wanda ya gane halinsa zai maida hankali kada ya shamace mu yau ma dai hiran wata batutiya a inda yai karatu yai muna a harkan computer inda a cikin hiran nasa ya bada labarin yadda ta hada wani waya by mistake saidai bai kai karshe ba yace ya bamu assignment akan labarin nan kan kowa ya daure da zancen.
Yana fita wayan nan sabuwa da shaf na manta dashi yana daukan kara sai can na tuna ai tawace na dauka da sauri Man bashir nagani rubuce.
Dakyat nagane received na dauka ina kaiwa a kunnena saidai anyi shiru ba magana nima kuma banyi magana ba kamar yadda maishi bai min ba.
Still wayan na a hannuna hakana kuma ba a