Showing 48001 words to 51000 words out of 110493 words

Chapter 17 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa

30 May 2026

1448

Dadi kin kama jinsa ke nan a rayuwanki tunda kina tare da MB a yanzu sai kince yayi maki yawa zan daina.

Kada kasa iyayyenka suyi kuka dani a yanzu fa kan hakan suce ina kwashewa dansu kudi ina kaiwa gidan mu mb yana ciyar damu da komai nasa.

Ki sani MB ki ba rago bane daya dogara ga a bin iyayyensa nashi yake nema ta hanyar halakan irin ku dubu Mb zai iya kula dasu yarinya a yanzu.

Niba kudi ko kyalkyal banza nake son gani ba mb nake son gani gaba da gaba naga halinda yake ciki a idanuwana .

Karki damu da hakan gone Auwal zai kawoki nan har wajen mb sai ki shirya haduwa da mb din shine na mayar masa da amsa da yasashi dariya har salman din ya fahinci dani yake online a lokacin.

Wanan ya kawo badakala a tsakaninsu har mami ta shigo ta samresu saidai bata fahinci kan musayar bakimsu ba lokacin harshi salman din ya fita

Babu komai a zuciyana ranan sai farin ciki kusan duk wanda ke gidan mu ranan da abinda ke cikin zuciyarshi a lokacin musan man nida iyayyena da abin ya shafa kowa da abindake yawo a zuciyarsa.

Ni dai a bangarena ina ganin nayi dace a lokacin don ba kowace mace bace zatayi sa,an dace irin wanda nayi na haduwa da MB a lokacin.

Sai har na kasa hango matsalan dake akwai a tsakaninmu wanda zai iya haifar mana da matsalolin da ba a so masu muni daga baya saboda idona ya rufe a lokacin na fada tarkon soyayya lokaci guda nake ganin ba abinda zai iya kawo muna tsaiko a rayuwa.

Yayin da Abbu da Ammah su kuma da zullumin hakan suka kwana don sunsan yana da wuya iyayyen Man Bashir su yarda da auren mu ba tare da sunsan waye takamaimai din mahaifina ba.

Abu daine idan rabon mutum ya ratsa a jikinka sai kaci rabonka don haka wanan abubuwan da yake min a yanzu yana yin sune akan rabonane naci dani dasu daga gareshi kawai.

Don sun dade a daren jiya suna tataunawa a tsakaninsu karshe dai sukai min adduan fatan alheri da samun sauki a rayuwa na mafita mai kyau.

Washegari kan ban fadawa kowa komai ba na shirya tsab da zuman fita school amma a zahiri kwaliyan zuwa wajen MB nayi in dubashi idan mun fito break kafin mu koma Auwal zaizo ya kaini ingaidashi.

Anty safiya kasa daurewa tayi saida tayi magana nace kinsan yau Monday ce anty ko bature yana girmama ranan ai.

Yan aji dai sai satan kallona sukeyi ban kula kowa ba ina Allah Allah lokaci yayi in ware saima naga lokacin yai tsawo a ranan daya da wani Abu kuwa Auwal yazo ya daukeni shima sai sheri yake min bandaiyi magana ba na kyaleshi.

Komai na jikina marching color ne shigar ya tafi daidai nasan gidan wancan zuwan da mukayi in group da sauran course mate dina don haka wanan karon ban tsaya mamakin mansion din ba saboda nayi a wacan karon da mukazo a cikin taro.

Saidai motocin da muka ganine a haraban gidan yasa Auwal fadin akwai baki a gidan bari na kirashi muji saidai yayi kira bai dauka ba yasa yace mu shiga kawai ciki kai tsaye.

Wani hanya muka bi ba wancan da muka shiga wacan karon ba wanan ta baya yake wajen lanbunsu muka bi.

Sai gamu a katon falon dayake mallakinsa .

Falon daya sha kayan alatun zamani iri iri farare kal dasu ga kayan motsa jikinsa nan a gefe daya zube .

Yana bude kofan ya tura dariyansune ya shiga kunnuwan mu a lokacin yayin da su kuma suka juyo lokaci guda garemu.

Kasa hade dariyan dake fuskansa a lokacin yayi yana mai zubo muna idanusa yana bin mu da kallon a cikin mamaki fuskansa daya baiyana karara a lokacin.

Sannu a hankali duk suka juyo suna sauke kallonsu a kan mu suma don suga meya dauke masa hankali haka har ya sake kafan daya hana mami tabawa a lokacin.

Inda nima kallon kafan nasa nakeyi cikin tashin hankali don ban dauka har ciwon yakai haka ba ashe ban damu da duban ko suwaye tare dashi ba a lokacin ga damuwa karara a fuskata dana nuna lokaci guda ina bin kafar tasa da kallo.

Sai mahaifin nasane yace ku karaso daga ciki mana sannu ku da zuwa Aeesha ko dalibar man bashir ashe kin samu labarin abinda ya samesa ?

Lokacin naga matan dake falon tare dash cikin shiga ta alfarma duk sun sake kalloni da yar kunya na karasa dan takowa saidai har lokacin banyi nisa da kofan shigowan ba don girshin da mukai masu.

Au ko itace yar kwara din tasa data dauke masa hankali take kokarin hanasa yi muna biyyaya a,a lalai ?

Lokacin na dago ido daga kallon kafan nasa dana shagala dayi tun shigowan mu na sauke kan wace ke magana din bakace yar karfafa da ita ga kuma alaman hutu ya nuna a jikinta.

Amma hakan bai hana aga bakinta na asali daya baiyana ba a jikinta duk da gyaran da jikin ke samu na gata.

Dan tattara natsuwana nayi na fara gaidasu ina fadin ina wunin ku ya mai jiki kuma cikin jin kunya tare da girmamawa ?

Jiki Alhamdullahi ai da sauki gashima ana daga dashi ya taka yanzu yana shagwaba abu ga dan dangi dan asali.

Au ko kece Aeesha da nake jin labarinki a wajensu lalai tubarkallah masha Allah, ashe kuna tafe kin samu labarin gwarzon naki ba lafiya ke nan umman salman dake gefen kafadan shi zaune take fada na dan fadada murmushi nace jiya nake jin abinda ya faru cikin sanyin murya.

Karaso ciki mana ku zauna Auwal ka tsaya da ita daga kofa kuma tana nuna muna kujeran da ba kowa a sama dake gefe daya.

Wai hjy hafsat dama haka kuke barin ko wani banza na shigowa gidan yadda sukaga dama ko wani lokaci babu kwabo ko security a kansa?

Dayan matan da tunda muka shigo batayi magana ba sai bina da kallon banza tana watsarwa da takeyi run shigowan mu.

Wanan dai da gani kin san barbaran yanyayawace ba tarbiya garesu ba hjy kubura irin yayan nan ne na tsaraban saudiya saiko dai idan ubantane ya auro yar gantalin Arab yazo da ita oho ?

Dayan tace kinsan maza da son farar mace wanan inba fari ba meya gani a wajenta shi zamanta kwara din ne ya baka sha,awa kome ?

Dadin abin dai dan asali sai yar asali ko mutum yaki kuwa don mu da asali muke ado ka rike wanan kalman tawa ka aje.

Ta fada tana mikewa wanan dai matar dake magana a gadarance ta sake fadan hakan ta mike tsaye tana gyara gyalen jikinta.

Har zan kai zaune saina fasa da sauri ina mikewa sai naji umman salman na fadin haba dai da girmanki kuma kike wanan abin gaban yarinya karama hjy kura.

Nan daddysa ya dauka da fadin no bansan yaushe zakuyi girma da wanan halin naku na nunawa dan adam Shiba komai bane.

Common, come here, naji ya fada ba kuma kunyan hakan a gabansu yasa na danyi kasa da kaina lokaci guda son kunya.

Come closer, come and have you sit here ya sake fada wanan karon tare da dan dagowa yana nuns alaman dani take tare da nuna min wajen da mahaifiyarsa itama ta mike daga zaunen da take gabanshi saman Stoll.

Gashi ya tsureni da idonsa akaina alaman dai dani yake a lokacin kan in taho inda ya nuns min in zauna.

Kije Auwal ya rada min hakan yasa nabi umurninsa na taka zuwa garesa din na zauna a Inda ya nuna min ba tsoron komai a zuciyana lokacin.

She is my girl friend and this my aunt's ya nuna min su da hannu sai hjy my lovely umma and my mami too you already know Dad before na dan gyada kai alaman eeh sai kuma ya juya wajen umma din yana fadin.

Hjy wanan ce Aeesha daliban da tafi kowa hazaka a fanin mu kuma nake ji da it'a sosai a ,,,,,,,

Kai dakata da wanan iya shegen naka na banza kaji ni da kyau ke ki jini da kyau in kina jin hausa in kuma sai turanci ko larabci ki samu wanda zai fassara maki hakan.

Wanan da kike gani ke ba hadin kifi da kaska don yafi karfin ki wanan maimakon taga fushi a fuskana sai murmushi na sake cikin karfin hali a fuskata.

A cikin harshen larabacin dana matsa kaina na koya don bacin rana irin wanan tun ina karama na koyi larabci kuma na iya.

Umma since take magana tace na dauka duk abinda suke min a wasane don haka kada in damu dasu na gyada mata kai da na,am.

Sai naji suka mike fice da ita da mami din nasa ganin abinda yan uwan mijinta ke shirin aikatawa a lokacin.

Suna fita naji daddy din yayi wata tsawa tare da fadin hjy Amina bazan dauki cin zarafin kowa a gidana ba

Damage nasani ai yaya da saninka make komai dake faruwa ta juya ta fita tana sababi tana aibantani haka yar uwar ta watsa min kallon tsana itama ta fice daga falon.

Sai lokacin na kula da wanan hindatun da suke zaune ashe falon sums kamar basu cikin falon a lokacin .

Naji mamaki kwarai yadda yayi mata tsawa ta fice da sauri tare da yar uwar ta lokaci guda har suna hada kafa wajen fita.

Dan shirune ya biyo bayan fitansu kafin daddy nasa yace kada wanan abin ya dameku Ku barni dasu kawai zanyi maganin su shima ya fita.

Shi ko dan nasa sai faman murmushi da yakeyi a fuskansa baice komai ba har daddy din nasa dana ga alamun so karara yakewa dan nasa ya fita.

Sai can ya kalloni ina zaune na sada kaina kasa zuciyata tana min suya da kokarin rufewa lokaci guda kan abinda ya faru din.

Muryan shi yane naji ya ratsa min kunnena da fadin .

Are you OK hakan yasa na dago naga yana kallona na daga masa kai alaman eeh iam OK din kamar yadda ya tambaya .

Sai naji yace right yana kokarin daga kafar ya sauke ta kasa yacewa Auwal ya dauko min abin sha lokacin nace dashi.

No iam going dama nazo naga jikin nakane kuma Alhamdullahi naga da sauki so ni zan koma don ina da lectures three .

So yanzu kin gani hankaliki ya kwanta ko na dan kara murmushin karfin hali ina fadin gaskiya hakane na mike tsaye ina karasa fadin hakan.

It's means kin dauki zancen su da zafi ke nan ko na ji ya jefo min tambayan a bazata.

Da Saudi na girgiza masa kaina cikin alaman dakewa nace ba komai ai Allah ya kara lafiya na juya ta hanyar da muka shigo na fita da sauri Auwal ma ya biyoni yana kirana saidai ban kara juyowa ba.

Saida na fita na hango fitar matan tare da yaran nasu gidan sai lokaci naji hawayen bakin ciki yana sauka min a fuskata lokaci guda



ZAINAB IDRIS MAKAWA

[8/19, 9:03 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [8/15, 07:30] Seenabu Makawa: M/C COLLECTION MAKAWA COLLELECTION ONLINE BUSINESS FASHION & BEAUTY ITEMS SUCH AS LAGOS LACES, SHOES, BAG, COTONO KAMFALA COTONO ATAMFA, LAGOS GOWN DONGUWAN RIGA, TABLE FAN,HAND DRYER KIDS,FASHIONS etc

LAGOS NATIONWIDE DELIVERY SAI KUNZO A CIKIN SAUKI INSHA ALLAHU,,,,,,,,

JA YA FADO,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

2️⃣6️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

[8/15, 07:30] Seenabu Makawa: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1ftp

Hjy kura dake tuki a haukace cikin tashin hankalin abinda idonta ya gano mata ta juyo tana fadin watau hjy Nasare matukar ba rabashi da yarinyar nan akayi ba babu yadda yaron nan zai lankwasu muna a yanzu matukar wanan tana cikin rayuwansa.

Abune mai wuya hjy kura rabashi da ita yadda like nufi farat daya haka don ni kaina badon na daure ba ba zan iya ciwa yar nan mutunci haka a gabanta ba don' yarinyar nada kwarjini matuka a idon mutum.

Gumi taji ya zubo mata kamar wace aka watsawa ruwan zafi ta dankai hannu ta share kafin Dan juyo kallo year uwar nata tana fadin .

Nasare ki duba fa yaron nan tunda ya kyala ido yaga yarinyar nan gaba daya lokaci guda ya birkice har ya manta ko suwaye a tare dashi hankalinsa gaba daya ya koma gareta.

Amma aisu iyayyen nasa basu kula da hakan ba basu san babban illa bace jefo iron su a cikin zuria don a karshe gaba daya zata jaye masa hankalinne ga kowa sai ita da yan uwanta ai mugun abin a cikin jini yake masu rabu da mace maikyau kinji hjy balle wanan din da idonta ya bude haka lokaci guda .

Ki duba sai wani nuna yakeyi tankar baisa damu a wajen ba tunda tazo fara,a ya sauka a fuskanshi danice ke kawai hakkura zanyi da zancen hadin nan yaje ya karata da ita shi zai yabawa aya zaki ai akarshe.

Wasa kokeyi ko ba,a hjy Nasare ai tunda nayi niyar hadashi da Hindu kuma na dace itama tana sonsa angama in baki labari yayi kuskure data fado a komata don ko wayayi masa tsaye a duniyan nan sai ya auri Hindu.

Shi kuma yaya nasan yadda zanbi dash har ita hjy mami din don saina dasa kiyayya da gaba a tsakaninsu da dan in raba tsakaninsu muga ta tsiya son da kuma.

A,a yaya kura ki bar masu dansu don Allah kada kiyi hakan tunda kema nakine yaron nan yaya bai cancanci hakan agareki ba yanzu gaskiya karki manta alherinsa garemu fiye da sauran yan uwa.

Wani kina ganin zan jaye a niyatace Nasare ai yanzu aka soma ina ganin baki san baiwa da arzikin yaron nan bane har like ban shawara a yanzu injaye .

Da wata ta shigo gidan nan taci banza mu kara komawa yan amshi gara ina ganin tawa gidan duk hanyan da zabin a yanzu na shirya sai ya dawo yana bin Hindu da kafarshi wallahi.

Wanan fa ba yakina ni kadai bane Nasare yakin kan mune ga baki daya nake muna harsu iyayyen nasa haka kawai in zauna kallon ruwa ,,,,

Shiru hjy Nasare din tayi tana tunane a zuciya kafin ta furta a fili yanzu na fahinciki yaya tace koke fa kin tsaya ana baki kina roko.

Ido rufe na nufi get da zumar fita daga gidan yayinda Auwal ke bina a baya yana kwala min kira har ya cin min ja nayi na tsaya yake fadin kar kiyi haka man's Aeesha ki tsaya in dauko mota mu tafi.

Yadda ya marairaice yana magana yasa naja na tsaya din ina bin bayansa da kallon yadda yake wani sauri a lokacin

Atake naji zuciyana yana wani irin bugawa da karfin gaske lokaci guda sai wani abu nake jin yana yawo ajikina wanda na rasa meye wanan din don yafi gaban damuwa a lokacin.

Tambayan kaina nayi meya kawoni irin gidan nan meye hadina dasu dama kome suka fada a kaina aigaskiya suka fada din don bankai matsayin bin dasu ba ai.

Daidai nan Auwal ya karaso ya bude min mota don in shiga banyi musu ba son inaki ko tafiya ya isheni kafin nakai bskin titi nan da get ma na kasa kai kaina balle inda zan samu mota da zai karasani.

Ina zama ya rufe ya shigo ya soma ja dagani har shi ba wanda yai magana na dan lokaci sai can naji yace hjy kura ke nan itace kebiwa daddyn oga wajen haihuwa.

Amma tafi kowa fitina da izza a dakinsu fitinaniyace ta gaske komai nata a gadarance takeyisa da mijinta mai kudine sosai amma tunda ya mutu ta kama dukiyan ta kumushe ita da babban danta yanzu sai yan dabaru .

Duk kuma wanan bai isheta darasi ba kowa a wullakance take kallonsa har gobe ko mu nan saboda ita saida muka dauke kafan mu wani lokaci gidan nan saboda cin mutuncin da tayi muna.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0