Showing 84001 words to 87000 words out of 110493 words
Chapter 29 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa
daura aure muna dakin don yaya habib sun tafi daurin auren yaya kabir shiyasa matar nasa ta lake min tunda safe muke tare da ita ashe.
Su Aimanan nan suka samemu sukaci abincin da muka aje masu Ammah tazo da anty safiya da yaranta biyu da suke zaman gida tare duk muna gidan an rufe gidan namu a ranan don yinin bukin.
Sun kafa wasa kofan gida a nan zasuyi wasan karshe tare da dj kafin akai amare dakinsu muna nan dakin umma yan gidan ango sukazo muka shiga gyara masu wajen zama.
Wanan ce ai naji wata na fada a bayana hakan yasa na juyo don ganin mai magana a lokacin aiko tubarkallah wallahi wata ta fada.
Kaina ya daure ban gane me suke fada ba a kaina saida tace min ga hjy ummi can tana neman ki ai a waje.
Zan fita saiga anty ummi din sun shigo wuri ya matse dole na fito muka gaisa dasu wajen tun daga wanan lokacin muna tare da kharat saida zasu tafi muka fito masu rakiya nan suke tambayana nan ne unguwar mu wai ?
Asmau tace ga gidan mu can na ukun can shine namu ai ashe har nan kuke ta kara fada zo muje gun motan anty abin bukinki yana ciki tazo maki dashi khairat ta fada.
Hakan yasa na bisu har bakin motar buhune cike da abubuwa khairat din ta bude boot din motan ta fito min dashi tana fadin kinsan anty ummi da yaya Bash akwai alkawarin amana donshi take haba haba dake nayi murmushi.
Yaushe zata koma na samu kaina da tambaya tace da gobe ne amma yaya A Dabo yace su bari sai friday jibi su koma Ok zanzo har gida in gaida ita nagode .
Asmau ce ta dauka zuwa gidan mu da sauri don kada a taruwa kayan tasan halina tace zan rabawa mutane.
Ji nayi an dafani hakan yasa na juyo da sauri daga kallon Asmau din anty ummi dince a bayan mu dan dukar da kai nayi ina fadin sannu anty nagode naga sako jiya yau kuma ga wani an kawo min.
Kece next fa daga wanan sai kuma munzo naki a wanan unguwa waima kuna waya da kanin nawa koda yake yaki yarda yace shine yayana.
Murmushi nayi mata ina noke kai ta kara kamuni tana fadin mu zamu tafi wata kila ba zamu kara haduwa ba daga wanan karon ?
Ai tace zatazo gida ta gaida ke hjy a sayi kaya harkafa daga bayan mu aka fadi hakan duk muka juya anty safiyace a bayan mu take fadan hakan ga anty ummin din.
Hjy Allah ki gwada zaki nemeni daga baya kayan mu ba irin nasu bane mu kayan el,sutra muke saidawa hadi hadin gida na ainihi babu surki ba algus babu cutarwa idan baki yarda dani ba ki tambayeta gidan mu daya da ita ai ta nunani wajen matar.
Kasa ka bude inshige naji a wajeb saboda kunya itako taci gaba da fadin kyautama zan baki hjy tunda naganki tare da wanan bari zan hado yanzu don Allah kada ku tafi ku tsaya ku karba.
Anty ummi din ta juyo gareni tana fadin wai da gaske gidan ku daya nace yayatace gidan mu daya da ita sai ta bita da kallo tana murmushi.
Sai kuma wata tazo ta dauke mata hankalli garemu wai ance akawo kudin wankin amarya ta danja tsuki tana fadin su duk me suke a wajen nan oya lanti kibi kowa daya dace saiya bada ki dawo na cika akara maza jeki don Allah akwai inda nake son zuwane daga nan.
Bayan matar ta tafine ta juyo tana cewa dani zamu gun mai babban dakine yau tunda safe ta aiko min da zagin cin mutunci zan tafi mu kwasa da ita.
Ai bana jin tasan da itama anty khairat ta fadi hakan tace oh haba dai kinko huta da bakinsan wainar da ake toyawa bama nikan yau ai nasha zagi tunda safe.
Ban fahinci komai a zancenta ba saiga anty safiya din ta dawo tana fadin zanba Aeesha ta baki kan ku tafi don ido yayi yawa anan yanzu.
Na hada maki da matar minister, izzar mowa, gumban ukku bala,i amma don Allah hjy in kina da kishiya wanan izzar mowa din kiyisa sau daya please ?
Kai matar na very funny wallahi kwantar ni banda kishiya zan iya yin amfani dashi gaba daya kwarai kuwa ta fada tare da fadin don girman Allah kiyi amfani dashi ke kadai a wajen na sayarwa shi kaya mu talla da ikone sai mun soyema muke zaba maka da mun kalli mace musan meya dace da ita.
Dan tsuki naja yasa ta kalloni tana fadin kin gani ko ke yarinyace baki san komai ba ja bamu waje don Allah kinji nan zancen manyan mata ake a yanzu.
Abinda nake so ke nan kuwa anty khairat ta rigani jan hannuna muka dan gusa zuwa jikin motarsu sai muna kallonsu suna ta zuba kamar sunsan juna saboda dadin bakin anty safiya din wajen sana,anta.
Bayan sun gama ta miko min leda cikin dabara tace ki saka mata a mota na karba kamar yadda tace nace gashi tace in saka a mota na anty ummice wai khairat ta karba.
Ni dai nasan ta karba kawai don kawaici ne don irin matan nan hamshakai me suke nema kuma a yanzu banda shirmen anty dai.
Za a tafi da amaryane a lokacin don haka bamu saka kanmu binsu ba don kowa na fadin zai tafi sun kawo irin manya bus bus din nan na kwasan mutane har guda ukku na yan kai amarya.
Anty basira ma bata tafi ba muna tare da ita sai lokacin take min hira wai ai anty fati din da mijin nata dataje wajensu tayi hutune suka hadu a can Abuja.
Nikan ina mamaki ina ta hadu da Dan Nadabo family ashe mafari ke nan a in mamaki wai sai gata tana ce min muje gidan mu tana son sayen abu wajen anty safiya.
Mamakina ragagene saboda yadda nake ganin manyan mata na zuwa saye wajen anty safiya din kayan da take kira da El,sutura ingantace a fadan ta.
Saidai anty safiya din mun samu tabi gayyan yan kai amarya a lokacin mun kirata a ways sai cewa tayi Asmau ta fitar mata da kayan ta nuns mata hakan akayi kuwa ta barni da mamakin yadda Asmau ke bayanin kayan.
Karshe ma mikewa nayi na bar wajen sai gashi a karshe ma dai nake ji a bakinsu wai tasayi kaya yakai na dubu ashirin gunsu.
Har karfe goma na dare tana gidan kafin mijinta ya dawo ya dauketa su taxi suna ta hira da anty safiya data dawo kai amarya.
Sai wajajen sha dayan dare su yaya suka iso da amaryan yaya kabir din daga katsina yace matar ta fito shi a gajiye yake ta fito suka wuce masaukin su.
Nikan nagaji dama wanna nayi na kwanta sai barci washe gari kowa ya tashi ya barni gashi kwana biyu ban samun ganin Abbu don barcin safen da nake kwanci yi da safen har ya fita ban falkaba.
Wai mamaki anty Basira da mijinta ya kirata ya azzalzaleta kan ta fito shi ya gaji itace ta tayar dani daga barci tana fadin bayan mun gaisa da ita Aysha don Allah ki fadawa anty nan kada ta fita ta jirani zanzo in kara kaya.
Tau kawai na amsa mata dashi tare da tambayanta Amira yarsu tace gata a wajen daddy na katse kiran cikin jin haushin tayar dani da tayi din a lokacin.
MATA KU SAI KAYAN EL,SUTURA BA KARYA KO SON KAI KEDA KIKA DAURE KIKA SAYA KE ZAKI BA WASU LABARINSA INSHA ALLAH SAI KUNZO
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[8/29, 9:52 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [8/15, 07:30] Seenabu Makawa: M/C COLLECTION MAKAWA COLLELECTION ONLINE BUSINESS FASHION & BEAUTY ITEMS SUCH AS LAGOS LACES, SHOES, BAG, COTONO KAMFALA COTONO ATAMFA, LAGOS GOWN DONGUWAN RIGA, TABLE FAN,HAND DRYER KIDS,FASHIONS etc
LAGOS NATIONWIDE DELIVERY SAI KUNZO A CIKIN SAUKI INSHA ALLAHU,,,,,,,,
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
3️⃣5️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
[8/15, 07:30] Seenabu Makawa: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1ftp
Ranan an barni da mamaki don sai gashi anty ummi ta aiko aje mata da anty safiya itama wai akwai wash da zasu tafi kawaiyenta da zasu tafi a ranan nason su ganta da kayanta.
Na fada mata ta shirya za azo a dauketa zuwa gidan hjyn nan na jiya nan anty safiya ta fara rawan jikin had a kaya ba,a jima ba saiga driver yazo daukata din suka tafi .
Wanan yasa koda anty Basira matar yaya Habib tazo anty safiya din ta fita a lokacin amma haka ta zauna zaman jiranta saida ta dawo wajajen karfe dayan rana.
Nikan ina mamaki a raina me sukeji a wanan kayan shiriritan na anty safiyane wai suke rawan jiki saya haka ?
Tunda suka shige daki sun jima a dakin sai dai dariyansu akeji jefi jefi Ina nan kwance naji sako ya shigo min wayata .
Daga classrep din mune yana sanar min da Monday zamuyi resuming school naji dadin jin wanan sakon don zaman gida ya isheni a lokacin har yana son juya min rayuwata a yanzu.
Don haka tun a lokacin na fara jawo takarduna Ina hadawa a waje daya Aimana dake kwance tana charting ta dan dago tana fadin ya akayi don jin tsukin dana dan ja a lokacin.
Ya akayine na juyo ina fadin kinga waifa takardana da zanyi submitting ashe na barshe hannun Joe kuma ita bata maida min dashi ba gashi dashi zamu tafi IT dashi.
Wai kina nufin har zaku tafi IT ke nan nace to kinki karatun nan Aimana da yanzu dake za a tafi nina rasa dalilinki na dakatar da school dinki a yanzu tunda auren ba tashi yayi ba.
Naga tayi min wani irin kallo kafin naci gaba da fadin kyawo ya kasance koda zaki shiga gidansa kina da iliminki ko kina kanyi kinga,,,,,
Dakata don Allah Aeesha don me mace ke dagewa da karatu wani lokaci badon saboda ta karewa kanta matsalolin rayuwa na gidan miji dana yan uwa bane nan gaba ?
Ehh kamar hakan ne dai amma ban dauka hakan bane kadai zaisa mace ta dage da karatu a sali a bangarena mace na karatune don abubuwa da dama na rayuwa fiye da wanda kika lissafa a yanzu.
Toni a yanzu banda matsala a wanan tunda kinsan wanda zan aure yana iya tsare min komai na rayuwata dana iyayyena had yan uwa.
To don me zan tsaya wani bata wa kaina lokaci da karatu can damage karatun nan don kawai neman na kai na shigesa kar ingani ga wani .
Don haka barin karatuna matsalatace don ni ya shafa ni kadai kije Allah yabada sa,an karatu ke koke don kina da wanda ya tsaya makine ai kikake .
Da badon hakan ba ba zaki kai wanan lokacin kina wanan wahalan banzan ba wai karatu kuma yanzu shima ya tafi kinga dole ki dage ai a yanzu tunda Abbu nason kiyi karatun aikya dage dashi.
Ooh really haka zakice Aimana na dauka dani dake mun zama daya a yanzu ta yadda daya zai iya tsayawa ya fadawa dan uwa gaskiya kai tsaye.
Amma tunda kin dauka haka Allah ya baki hakkuri tace amin tana wani fisge fisge kafin can inga ta mike tana shiri wai gida zata tafi a wanan lokacin samira ta shigo dakin ta sameta tana shiri.
Tace a,a Aimana badai tafiya zakiyi ba a yanzu kin fasa zuwa gidan amaryam ne muga kwam nafasa ta fada a fusace .
Samira ta kalloni tace wani abu ya farune kuma mummy nace ba komai daga dan magana tayi fushi haka dani wai zata tafi gida.
Zakice dan magana mana Aeesha tunda ke naganeki baki son kowa yakai matsayin dake kika kai kinfi bukatan koda yaushe a gani a wajen ki ke kadai .
Mu ko muna faman binki kamar wasu sakarkaru a kullum baki encourage dina akan auren nan da zanyi sai kin samu wani sukan da kikayi kan hakan .
Dagani har Samira sororo mukayi muna kallonta na wani lokaci kafin Asmau ta fado dakin kamar an jefota taji kalaminta ta cabe zancen da fadin .
Wanan magana kuma haka anty Aimana kamar dama kana jirace da mutum aiko bai kamata aji hakan ba a bakinki yadda mummy ta dauke a yar uwa.
Dama aina fada maki mummy Aimana najin zafi akan ki tun kalamin da tayi shekaran jiya akanki ni naji ta zube min inbashi ba daga dan maganan fatan baki zata tsaya tana wanan maganganu haka ?
Tsakaninsu ya koma da aimana din har Ammah taji ta shigo dakin tana tambaya duk su anty safiya suka task ake maida magana.
Keko Aimana ai wanga magana bai kai na zafi ba fadin gaskiyane kawai tsakanin ku ai dake da Aeesha a yanzu fatan alheri mukewa kowan ku a rayuwa.
Nan sai tayi mata fadan rashin kyautawa tunda banice na kawota gidan ba ai hakan yasa ta fasa tafiya a ranan da gamma suka kwasa zuwa gidan amarya anty fati ni dai banje ba tunda nasan abinda zai kaisu.
Karfe goma agogon can nan ya nuna tara takwas da rabi yasan lokacin fitan kakanshi bai ba hakan yasa ya danna masa kira a lokacin akai sa,a ya shiga kuma har yaji an daga.
Sallaman da yayine ya sheda muryan jikin nasa don shi kadai ke masa hakan saida yai murmushi ya amsa masa tare da fadin aina zata tunda naja auren kane zuwa wani lokaci kake fushi dani kaki kirana ?
Aure kuma ya tambaya cikin mamaki kakan nasa yace ba ka turo min da zancen ka yarda a hadaka da yar gidan Amina ba a yanzu har na yarda na turo ayi komai.
Ni kuma grandfather yaushe na turo idan zan fada aida kaina zan sameka da zancen in baka zabina ba wani zan turo ma ba wait waima wana turo wajen kane ?
Gaskiya ban sanda wanan zacen ba grandpa saidai idan tsufa ya fara kama ka magaji yaji tsohon ya ambaci sunan sa ya amsa da yes grandpa .
Kada kace min baka da masaniya akan zancen nan kakan ka iya yazo min da maganan har nan falona da dare saidai nayi mamaki don yadda mukayi dakai a baya.
Ke nan hakan na nufin shirine hakan kai baka da masaniya akan hakan so suke sujawa kansu tonon asiri kome da ba zasu hakkura da wanan zance ba wai ?
Grandfather nasan shirin matarkace wanan amma badon kai ba da nayi maganin duk mai baki a ciki zan turo a kwashe min su baki daya in kaisu human right abi min hakkin bata min suna da suke son yi.
Kai dakata nan ba turai bane don Allah aiba kai akaiwa laifi ba yanzu nida suka zo min da zancen banza a gabana na tara mutane aka shede hakan ?
Yace what I am telling you grandpa zanyi maganin matar nan very soon ya kashe wayarshi yayi kiransa hakan bai samu ba yasa ya hakkura dashi din.
Gudun kada ya jawo masu abin kunya yasa akaiwa kowa daya dace kiran gagawa a cikinsu sam basu dauka wanan zance bane saida suka tarune ya fito masu da zancen da basu zata ba ya fara da.
Iya ya amsa da rankaidade yana daga mai hannu cikin ban girma saida ya ja iska irin na sarakuna yace ban dauka har dakai za a iya tukarana da zancen banza ba irin wanan.
Tuba nake ranka ya dade a yafe min idan munyi ba daidai ba yace rufa min baki mutumin banza kawai .
Hakan da sukaji duk wanda ke wajen ya shiga hankalinsa don sun san koma meye ba zancen wasa bane don mai martaba baya irin hakan da kowa.
Yallabai a gafarceni iya ya kara fada cikin ban girma ya dan motsa hakan yasa da sauri bafaden dake kusa dashi yayi sauri gyara masa kimtsin shi.
Ina zancen auren yaron nan magaji ya fito ka sameni dashi da sauri suka fara kallon kallo a tsakaninsu a take ya gano bakin zaren inda zancen ya fito a