Showing 27001 words to 30000 words out of 110493 words

Chapter 10 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa

30 May 2026

1426

na gama sulala taliyan nawa saidai bankai ga ciba dole na kwanta don kaina dake min ciwo.

Ammah data zaci nagama bataji nayi magana ba ta dauka don ta kishingidane lokacin ina zaton barci takeyi ta fito tana fadin kin gamane Aeesha ?

Taji shiru hakan yasa ta nufi wajen da ta hago tukuyar aje na sauke na aje budewa tayi taga ban taba ba yana yadda na dafashi aje.

Hakan ya bata mamaki ta taka zuwa kofana tana magana sai ranta ya bata ina bayi kila kamar zata tafi ta dan leka hangoni tayi a kwance nayi rub da ciki kwance din.

Salati ta soma tana fadin yau ga tsiya ki gama abinci makin ki zauna kici sai ki dawo daki ki kwanta kuma don shashanci.

Ke Aeesha fa ta ambaci sunana da dan karfi hakan yasa na dago na dan kalleta da idanuwana da suka kade sukai jawur a lokacin.

Subbahanallahi badai kitson bane yaja maki ciwon kai kuma yanzu kasa magana nayi sai kai dana kada mata kawai.

Ikon Allah ta fada hankali tashe ta koma ta shiga dakinta sauran magani ta dauko min kwara biyu na panadol daya rage ta debo ruwa a randa ta tsureni saida taga na shanye ta juya tana fadin .

Daga ciran kaya sai ya zamo kari ni tunda nagane hakan na daina damuwa da zancen kitsonki Aeesha ayi mace ace ba gyara ni na taba ganin hakan inba gareki ba ?

Allah sarki duhun kai da jahilci ya hana Ammah ta gane cewa har yanzu jikina da nasu halittansa akwai bambamci sai take ganin hakan kamar wani surface kawai jikina keyi don ko nan din akwai ai wace bakace amma hakan yana faruwa dasu sai ya kasance mace bata son abinda zai taba lafiyan kanta din.

Shan maganin a sannu kan ya fara lafa min jin yadda Ammah ta matsa min ne kan in tashi inci abinci yasa na dan fito na tsankwara zuwa dakina ina dan loma biyu bakina ba dadi don haka na koma na kwanta.

Koda salman ya shigo office din kai ya dago ya dan kallesa sau daya yaci gaba da aikin da yakeyi ba tare da yai mashi magana ba.

Basket din abincin da ya shigo dashi ya aje a gefe yana kallon wanda ke tsaye gabanshi a lokacin kafin yaji ya furta mai zaka iya tafiya amma ka maida hankali sosai don Allah ga aikinka .

Don kasan mutumin nan ya iya takon saka sosai da mutane ta yadda zai bat da kamanshi yayi aikinsa ba tare da an gane hakan ba yace yes sir ya sara mashi ya fita.

Sai lokacin salman din yakai zaune yana fadin good morning bai damu da amsawanshi ba yace a zuba breakfast ne yana dan kallonshi.

Kasa yaga yakai yana dan kwantar da kansa saman hannayesa da yayi makari kamar filo dasu don yaji taushi alokacin.

Ganin yadda ya kwanta yasa ya dan zuba masa ido kadan kafin yace dashi akwai matsalane yana mai kafeshi da idanuwansa.

Hannu ya karkada masa kafin ya gane nufinsa ya mike tsaye yana shirin fita jin dan uwan nasa yaja tsuki yana dagowa yasa ya dan juyo garesa yana fadin ka zauna kayi break din ka niba yanzu ba kasani.

Barin dawo akwai abinda zanyi a waje yanzun nan bai iya amsa mashi ba don kansa dake damunsa da ciwo ya kara kaiwa kwance din yadda yake da farko din.

Salman din yana fita yabi wani dogon corridor dake wajen da yake weekend ne yasa ba mutane da yawa a cikin school din .

Dan nisa kadan ya zauna yana fuskantar wani waje kafin can da sauri ya tura hannunsa a cikin alhijihunsa ya ciro wayansa kiran iPhone yana daukan wani photo ya mayar da wayan a aljihunsa.

Yakai wani lokaci a zaune wajen kafin ya mike ya bar wajen bai koma office din dan uwan nasa ba kai tsaye ya nufi cikin haraban makaranta tafiya ya danyi mai nisa zuwa wani lungu yayi abinda zaiyi a can ya juyo koda ya dawo har lokacin dan uwan nasa na a yadda ya barshi dan barci ya samu a lokacin da har yai mai nisa kadan jin an shigo masa office din yasa ya dago ksi yana kallon maishi.

Nan salman din ke fadin lafiya dai ko ya nuna masa kansa alamun shike damunsa dan shiru a lokacin hakan yasa ya zauna yana fadin ko zamu gidane don ina ganin ai kamar mun gama da yau.

Saida ya dago da kyau ya tsurawa dan uwan nasa ido kafin yace dashi akwai wani abinda ka samu ne a yau yace ba za a rasa ba amma sai nan gaba kadan zakaji komai.

Bai yarda da shirmen dan uwan nasa ba a yanzu don hakane ya kawar da kansa gefe daya kawai donshi baya son ma ya sako shi a zancen aikinsa ya dai fi barinsa a matsayin yaronsa kawai anan din.

Basu jima ba ya mike don tafiya gida har yakai kofa ya juyo yana fadin kazo da mota ke nan yace ehh ko dai na kaika gidane sai in dawo in dauki motar tawa.

No muje dai kawai ya fada dan haka daga shi har dan uwan ba wanda yaci abincin saida ya kai get yaba wanan yaron nasa ya karba yana godiya.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[8/3, 9:28 PM] Zainab Idris Makawa Writer: ELSUTRA HOME OF FASHION & BEAUTY ACCESSORIES AND BEYOND

MAMAN BIBO KAYAN MATA

08068871330 KOKO ROAD SOKOTO

JA YA FADO,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

1️⃣0️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

Murna yaran suka soma hanin tarin raken daya kwaso masu shi a zatonshima zasuce basa son rake din sai gashi suna zanga masa godiya.

Yake tambayan su ko Bashir ya shigo don baiga motarshi a waje ba kuma yana gabanshi don shi ya tsaya yayi dan tsaye tsaye hanya.

Ya dawo dayan ta fada part din nasu ya nufa kai tsaye duk da kofan yana rufe a lokacin hakan bai hanasa shiga ba ya murda kofan ya hangoshi kwance haka yasa ya juya shima tare da mamakin dan uwar nasa.

Sai lokacin ya tuna da bai karya ba fa nan ya fito neman abinda zaici yayi sa,a sun gama abincin rana shiya zauna yaci ya koshi fita ya sakeyi .

Don shi ba irin dan uwarsa bane da kullum daga wajen aiki sai gida yana da abokai da yake yawan hurda dasu a cikin gari.

Wasa wasa har washegari ina fama da ciwon kai dole zuwa yamma na gyagije don kada Ammah tace banda lafiya ba inda zanje washe gari don na fahinci ita karatun ma bai kwanta mata a rai ba.

Dole cikin dakiya na samu jikin ya dan kara warware mun washe gari ko Abbu na dukan kofana na fito waje da sauri nayi haraman sallah.

Bayan na idar na hau murhu don banson bari Ammah da aiki da yawa don haka nice nayi muna abin karyawan safe.

Karfe bakwai saura har na shirya kamar yadda aka sanar min kuma yana a jikin timetable din da na saya ina tsaye kofan Abbu ina fadin Ammah na shirya.

Jin hakan yasa ta fito tana fadin yanzu yar kan bokon nan kike rawan jiki haka don Allah kamar wace akaiwa wahayin wani alheri.

Dan murmushi nayi ina fadin banson in fara da makarane Ammah gyara muryan da Abbu yayi yasa ta kauce mashi a hanya ta dan karasa fitowa wajen.

Ya dan kalloni yana fadin kin shirya ke nan nanata zakiko iya shiga yau ko a bari sai gobe tunda jikin naki bai karasa warware ba.

Da sauri nake fadin zan iya Abbu insha Allah shike nan aikin kare zance ya fada tare da fadin muje nayiwa sale dan gidan wazan magana zai kaiki har school din naku inyaso sai ki dawo da kanki garin dawowa don iya kaikine kawai mukai magana dashi.

Na juyo don inyiwa Ammah sallama na samu ta rike haba tana kallona don cikin tufafin da Abbu ya dinko min ne na saka kuma kayan sun min daidai kamar an aunani matsala dai wrapper tayi min da atamfan yasa nake dan hardewa tunda ban saba sakashi ba.

A kofansu muka hangoshi yana goge babur din nasa har can muka taka Abbu na gaba ina biye dashi a bayanshi muka kai ya dago yana gaida Abbu din.

Kafin naji Abbu yace to gata nan sale don Allah ka tabbatar da ka kaita har ciki don Allah ya amsa da to baba insha Allahu.

Daga bayan baba na dan leko ina masa ina wuni ya amsa min cikin fara,a tare da fadin yau za,a fara shiga ke nan nace ehh Abbu yana tsaye kofan gidan nasu saida yaga tashin mu ya juya zuwa gida.

Yana mai min adduan fatan alheri da neman kariya daga Allah shiko nan Sale sai yan faman gyare gyare yakeyi a cikin motansa kafin yace yi hakkuri fa kinsan ban gama gugabane kuka fito kada baba yaga na dan tsaya nawa gashi tsaye na amsa da babu komai Allah dai ya kaimu lafiya.

Cikin yardan Allah muka shiga lafiya har inda madakatar mu yake nan ya fita yana dan waige waige har ya hango wanda yake nema a wajen ya yafitoshi tare da kiran sunarsa ya juyo.

Ya iso inda muke yace dama nasan zuwa yanzu kafito don Allah wanan kanwatace unguwar mu daya ina son in nuna maka itane idan tana neman wani taimako.

Kai sale kanwarka ina wanan ai da ganinta yar haure ce saidai da yake ka gyara zancen ka fadi gaskiya zan yarda to yaya zan karasa da itane yace kaima ka sani ai yana zaro yan canji ya bashi yace barshi kawai mu samu ciko mu karasa ciki.

Jeki kanwa ga mota can ki shiga ya nuna min motarshi din don akwai tazara daga inda sale ya ajeni zuwa cikin haraban school din don bako wani mai mashin ake bari ya shiga ba har ciki ba.

Da yake safiyane saiga wasu mutum uku sunzo tare nan muka garzaya zuwa cikin school din dasu har kofan science department ya kaini ya aje zan fita yake fadin to kanwa ko zan anshi lambarkine idan kun tashi inji ?

Banda waya na bashi amsa kai tsaye a zatonsa gatse nayi masa don budurwa kamata za ace banda waya hakan yaba sauran daliban dariya sai lokacin nasan na kwafsa ma son dariyan da sukayi din.

Ya juya yana fadin to idan kin fito anyi dace na shigo na karasa dake waje ai ina nan ko yaushe sai yamma nake barin nan din.

Godiya nayi mai na juya nacigaba da tafiya gabana sai faduwa yakeyi a lokacin kai tsaye na kusa kai ajin yan tsirarun dalibaine zaune maza da mata don lokacin ba a gama registration ba.

Kuma gashi safiyane ba a taru ba hakan yasa na danyi siririyar sallama ina rabon ido mm a hango gefen wani taga can baya ba kowa na nufi can na zauna a takure.

Ni ba waya ba balle in kalla kuma ni ba littafai ba balle nace zan danyi karatu a lokacin hakan yasa na duka kawai kamar mai tunane.

Ina a haka naji ajin yayi wani tsit lokaci guda da sauri na dago kai dan ganin meye yake faruwa wanda nagani a gaban aji tsayene ya sa gabana faduwa lokaci guda.

Yana saye cikin suith din maza dark blue tayi masa kyau sosai ko wancan ranan a cikin irinsu na gansa saidai wancan bakakene suna da kuma bambanci da wanan.

Lalai ya tabbata magana Ammah ya fito ashe shi din malamine dama a wajen da farko ban fahintar me yake fada saida na kwantar da hankalina na fara gane bayani yakeyi wai zaiyi test idan ya gama.

Don turancinsa zaki rantse da baturen gaskiyane shi yadda yake kara harshen shi a lokacin don hakane idan baka natsu ba baka iya fahintar shi.

Kalon kalo naga daliban sun fara a tsakaninsu don ban gane me hakan ke nufi ba yasa ban wani damuwa ba abunda da dai na sani zan rubuta ai in mika mai.

Yawancin abinda akai muna ne a secondry ya maimaita muna kafin ya fara rubutu da dan sauri sauri lokaci guda nida ko pepper banda na fara tunane sai gashi ya raba muna pepper's da kanshi .

Har answer wanda zamu rubuta fasahan mu tunda na duka ina karatu question pepper din ban dago ba sai da zan fara rubutu na tsaya dauko biro dina ba tare da wani fargaba ba na duka na fara rubutu yana tsaye kyam yana rabon idonsa ga kowan mu a gaban aji fuska murtuk a lokacin.

Badai nice ta dayan kaiwa ba amma zan iya cewa ina cikin na farko da muka mika kowa kuma ya mika zai fita wajene kai tsaye.

Fita nayi na samu sauran wa yanda suka fara fitowa din na samu can dan nisa dasu na tsaya ina bin ko ina da kallo don dai ni sabon shiga ce zance ga komai.

Allah ya rufa min asiri yawancin abinda ya tambayemu na dan sansu don yawan bitan littatafai da nakeyi nawa textbook hakan ne ya taimaka min.

Nan nake jin halaiyansa wajen su daga inda nake zaune din kamar ban tare dasu sunan malamin dai yakai ukku ko hudu shine malam bash ko malam dan kwalisa ko bakin bature mai wuyar sha,ani duk dai naji sunan ne a dan tsayin da nayi a nan a takure nake zaune naji kamshin turarensa ya daki hancina ashe shine ya fito zai tafi hakan yasa na dago kai in kallesa caraf idon mu ya sarke dana juna nayi saurin sauke kaina kasa da sauri.

Har yazo da dan saurinsa ya shige wani lungu nan kan ranan yasha zagi kowa da abinda yake fadi a kansa lokacin son sun fahinci makyatacine shi daga zuwa sai test haka don Allah ?

In turanci yake ji ko wani abu meyasa ya buge ga koyarwa yana abu kamar wani boss can wata mace ta fada a bayana.

Shigowan wani malamin yasa aka nutsu don daukan darasi lissafine tsatsanta bayan na wacan da muka buga don haka koda muka fito kaina ya gama daurewa a lokacin.

Don yanzu nasan na shiga karatu wanda bana secondry ba balle primary don haka na dawo gida a matukat gajiya sai da dan huta na mike na fito taya Ammah aikin gidan har zuwa lokacin da Abbu ya dawo daga kasuwa.

Ranan zaune yayi ina bashi labarin abinda ya faru a school din yake fasin dama karatu sai an dake Nanata Allah yasa kina da himma da kwazo kan hakan saiki kara maida hankali sosai don Allah.

Matsalan da yanzu naga Abbu yana fuskanta shine na yawan cacan kudin abun hauwa da yake min inda har ya fara korafin hakan naji.

Ba wai Abbu ya nuna ya gaji da hakan bane a kaina neman mafita dai yakeyi yadda abin zaizo masa da saukin Allah saboda yana korafin wurin yayi nisa damu sosai don ma wanan dan abokin nasa ya tausaya masa ya dan rage masa kudi yadda sukai ciniki.

Allah yasa ina zaune a wajen da yake magana ba kasafai nake yawan tsoma masu baki ba bansan ya akayi ba ranan nayi subul da baka ina fadin Abbu ka fitar da sarkokin nan mana ka cika kudin gidan da kayi magana kwanaki.

Kafin in rufe baki naji Ammah na fadin ji mun yarinya akan karatun naki za a sa sarka a kasuwa aje sayen gida dashi ?

Kai naga Abbu ya dan girgiza kafin yace da ita mayar da yukanki kube Ammamatan nima ba zanyi hakan ba ai don nasan abinda nake yi karatu kuma yarki ta fara ke nan sai ta zamo wani abu a rayuwanta insha Allah hakan nake fata ko bayan raina.

Nauyi da kunyar abinda Ammah tayi taji ta koma fadin ni malam aiba nace wani abu bane kada dai ita nana din ta dawo kuma babu kayanta an batar dasu kaga hakan ba zataji dadi ba ta bamu amana munci ke nan.

Din wa take turo wanan kayan a nan yanzu ina dai don yarinyar nance amfanin karatunta baifi na ajiyan sarkokin nan ba ashe Ammah?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0