Showing 39001 words to 42000 words out of 110493 words

Chapter 14 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa

30 May 2026

1429

mami dinsune yaji sabanin na salman din da yake saka ranji a lokacin tana fadin dama nasan zaka iya fita da safen nan bamu gaisa ba dakai.

Yasa na hana idona barcin safe yau don in ganka tunda kai baka damu damu ba a yanzu sai kai ficewanka ba tare da mun gaisa ba .

Dan murmushi ya saki yana fadin mami ba haka bane wallahi koda nake fita lokacin baku tashi daga barci ba haka kuma in nace zan kara lokaci sai in makara.

Tsuki taja tana zama race na rasa dadin me kakeji a wanan koyarwan da kasa kanka a yanzu wallahi me zaka tsunta a rayuwanka cikin koyarwan kasan nan magaji ?

Kai ya dago yana murmushi kafin yace mami ba zaki gane bane ko nayi maki bayani amma ai kinsan bawai koyarwan bace manufata dole akwai dalilin hakan gareni.

Kwarai kuwa ina zan gane kuwa magaji tunda yar kwara din da ta dauke maka hankali har kake son muzanta yar uwarka tana wajen inako zan gane komai a yanzu.

Cikin mamaki ya maimaita sunan yar kwara din da Mamin ta fada yace wacece hakan kuma mami ban fahinceki bane fa ?

Ina kuwa zaka fahinceni tunda kana son dauko min magana wajen hjy dake ganin nice ummul,aba,isin daurema gindi kakeyin komai.

Saidai ka sani shi sure wani lokaci akan yisane don't nasaba ko asali ba wai abinda zuciya ta nace was so ba karka manta da gidan da kafito shine fadakarwana a gareka.

Yau koda yarinyar nan yar wani hamshakine ko wani kusan gwaunati idan ita din ba jinin sarauta bace hakan ya zamo ragage a cikin family din nan .

Duk da naga mahaifinku ya kamama ya hana ayi ma magana toni dolene in tunasar dakai hakan magaji son abinda ka iya ye ya komo gareka wata rana.

Idan har kana son kanka da arziki kayi biyayya ga hjy ku shirya da yarinyar nan da tace zabitace gareka ka zauna lafiya kamar kowa da ita.

Sai lokacin ya gane inda zancen Mami din nasa ya dosa akan hjy mai isa take magana da Hindu watau ke nan har yanzu suna nan kan bakarsu na sai ya auri Hindu din shida ba zancen aure yanzu a zuciyarsa.

Wanan tsohuwar bata sanni bane wallahi dare guda zan turo a sace min ita in koya mata hankalin da gobe bata kara shiga min hanci ko wani yace tayi hakan gareni.

Don't dare try that noses in your life don nasan ba hankali gareka ba zaka iya nan ba turai bane kada ka jawo muna la,anta don Allah a wajen mutane.

To ku fada mata ta fita harkata wallahi tunda ba haihuwana tayi ba tsohuwar nan ta fara isata a rayuwa wallahi why zata sani a ido hakane ?

Ido uwar ta rufe ta haushi da fada sosai don kada ya dauko masu magana saboda sanin halinsa da tayi sam baida dabi,um malam bashe a rayuwansa sai ya aikata abinda ya fada din yaja masu zagi a banza wajen yan uwa.

Haka salman ya samesa rai bace saidai baiyi magana ba don yasan shigowan Mami din ne sanadin hakan daya samu dan uwar nasa din.

Har suka kai school baiyi maganan komai da kowa ba duk kwarin gwiwan days dawo dashi sai yaji komai ya tsaya masa cak mami ta dagula mashi lissafinsa.

Kan son sai yabi umurnin hjy don kawai a zauna lafiya akan me zai bi ra,ayin abinda baiso bai kauna a rayuwansa shi don kawai wasu suji dadi zai batawa kansa lokacinsa a banza.

Tunda Salman ya fahinci hakan baiyi kokarin yi masa maganan komai a lokacin ba don hakama ya fice ya barshi office din don ya dan sarara shi kadai.

Baka jin komai a office din sai karan na,Iran sanyaya waje dake aiki sai kuma na fridge dake nasa aiki saiki dauka ba kowa a office din lokacin.

Murda kofan nayi na shigo office din cikin mamaki duk da banji alaman wani a ciki ba haka kuma yasa nake mamakin fitarsu subar kofansu a bude ranan don koda wasa basa hakan tsakaninsu saboda muhinmancin kayan dake cikin office din.

Hangosa nayi ya kifa kansa saman table din kamar yana barci a wajen yasa na dan Dade tsaye ina kurawa sumar kanshi idanu dake sheki tsakiya yayi dan wani round dashi ya kwanta mai gwanin sha,awa kamar anzana mai su hakan.

Saida na kare masa kallo na dan lokaci na juya ina kokarin fita daga office din lokacin naji muryan shi kasa kasa yana fadin come here.

Tare da dagowa daga yadda taken yana bina da wani irin kallo kamar ranan ya fara ganina a duniya kasa nayi da kaina da sauri ina fadin sannu da dawowa.

Is that the way da zakiyi welcoming dina haka kerere dake come and have your seat ya fada tare da dora takardan dake hannusa saman table din.

Na turo baki ina zagayo ga kujeran dake kusa dashi na zauna idona saman takardan daya aje din a lokacin wanda heading din takardan an rubuta in vestige on MADINA SALIU.

Takardan da yaga na tsurawa ido kamar ina nazari yakai hannu ya jaye daga gani yana turawa a drawer table din kafin ya dago yana fadin ya karatu ?

Dan farrr nayi da gwala gwalan idanuna kafin na nisa ina fadi kasa kasa da karatun ba dadi wallahi yanzu tunda baka nan ban samun karin haske.

Au tunda ban nan sai karatun ya zamo maki wasa ke nan a yanzu baki mayar da hankaliki ga karatu ke nan a yanzu don kawai ban nan Aeesha ?

You're not serious ke nan ga karatun a haka kika zabi wanan course dama an fada maki software engineering course din wasane ?

Ni ban zaba ba bani dai sukayi law nakeso a rayuwata ko doctoring amma suka laka min wanan dole na karba da yanzune ba zan karbeshi ba wallahi .

Dariya na bashi sosai saidai shi ba mutum bane ma,abucin darawa da yawa hakan yasa ya murmusa yana juyawa saman kujeran da yake kai aka turo kofan.

Salman ne ganin mu hakan yasa ya dan tsaya data kofa yana fadin sorry to interrupter please bansan kina ciki ba ai.

Haba ya salman ko ina ciki meye kamar wasu munafukai da basa son a shigo kuma no haba dai ba haka nake nufi ba kanwata kawai dai banjo dadin katse maku da nayi bane ya dan saci kallon Bashir din ta gefen idanunsa.

Wani ta kardan ya ajema man bashir din a gabansa dake dauke da sunan Madina din kamar na farko yana fadin she attended this school before but a karshe aka nemeta aka rasa kuma.

Kallonsa yayi ya kalloni hakan yasa na mike ina fadin barin barku kuyi aikinku don naga kamar kuna son tataunawa tsakanin Ku kan wanan madina din.

Kallon juna sukayi kafin salman yace No ki zauna abinki ko har kinyi break ne da zaki taxi na girgiza masa kai ina fadin ina rike yau Monday ne na fada ina mikewa tsaye.

Kafin ku tafi kizo ki sameni ya fada ya mike tsaye shima na amsa da insha Allahu sir don yanzu ba sauran nauyi ko kunya su don yadda suke jana a jikinsu din ko yaushe tundai shi salman shi ya saba min da magana a gabansu yanzu.

Ina fita salman din yace she is so cute a yanzu da saidai zancen umma da inna tuna yakan Dan sare min gwiwa datace wanan dattijon ba mahaifinta bane dole akwai dai.

Hindu takai case din yarinyar nan gaban hjy don akansa yau Mami ta sameni daki da safe she is trying to a spoil this innocent girl a wajena har tana kiranta da wani suna a gabana.

Mami zatayi kuskure idan tace zata rabaku a yanzu da shakuwa ya shiga tsakanin ku haka da ita kun dace sosai da juna saboda yarinyar bata da hayani ta samu tarbiya yadda akeson mace ta samu ko yanzun nan da nasameku haka abin ba karamin burgeni yayi ba wallahi.

Saboda na fita na barka cikin bacin rai na dawo kuma na samu kana dariya haka a cikin sauki sai abin ya burgeni don tasan kanta tunda har ta sakaka yin dariya ke nan.

Salman ya fada da dan karfi salman din ya amsa da na,am ya Bash kona fadi wani abinda ba daidai bane a yanzu.

Kofa ya nuna mashi da hannu alaman ya fita ba mussu ya fita yana mashi dariya, shima murmusawa yayi yana shafa fuskansa don ya rasa abinda zaice da dan uwan nasa.

Sakone ya shigo mai a waya ya dan jima bai duba sakon ba har saida salman ya dawo yana karyawa bayan ya zuba masu ruwan shayi suna sha ya mika hannu ya dauki wayan nasa dake nuna alaman sako ya shigo masa a lokacin.

STAR GIRL yaga ta turo sakon yadda yayi serving sunan a wayar shi hakan yasa ya bude sakon guntun rubutune aka turo masa dashi kamar haka .

Who is she Madina Saliu ?

Cup din dake hannusa ya aje saman table ya fara rubutu yana murmushi ya rubuta kamar haka Do you want now about her ?

Fuskan salman yana kansa don ranan abin mamaki yake gani a gun dan uwan nasa kuma ba daman yayi magana ko yanzu bai iya raba dayan biyun cewa bada Aeesha yake charting ba a lokacin.

Shiko ya mayar da hankalinsa sosai a wayan yana murmushi tare da bani amsa danace eeh ina son sanin wacece ita.

Sai ya rubutu min idan kin sani zancenta zai shafeki kin yarda da hakan na turo masa da ehmana indai ya shafeku nima ai ya shafeni .

Sai ya turo min da kizo office kiji koyewa ita yanzun nan na turo mashi da gani tafe insha Allah don ina son sanin ta din a karshe ya turo me wai.

Are you jealous on me ?

Alaman dariya na turo mashi kafin kuma in rubuta mai akan wani dalili zanyi kishinka ?

Zoki fadi hakan a gabana da salman in baki amsa ya kashe wayan yana murmushi ya dago kai salman dake zaune ya zuba mashi ido suka hada ido dashi sai ya basar yana fadin.

Har ka gamane koka tsaya gulma dole inyi gulma yau ina ganin abin mamaki a wajen dan uwana da alama dai tarko ya kama mutum biyu yau din nan.

Wayar nasa ya garo masa zuwa gabashi ya cabe yake fadin meye na tarko acikin nan salman din yana dariya ya mayar da wayan yana fadin ai bance a wayanka ba yallabai.

Kawai dai magana nakeyi ya dan shako iska kafin ya furzar yana fadin na rasa meyesa mata duk suke haka now ita wanan tana tambayana akan madina who is she to me ?

Cab zancen ashe bana wasa bane har ta gano hakan yace the girl is talent tana da saurin fahinta yana daga cikin abinda yasa nake sonta a raina.

Nima na fahinci hakan don nasan baka hurda da dakiki abinda na fara dauka ke nan yanzu kuma sai wasan yake son ya sauya a ganina.

Bai sauya ba yana nan yadda yake kawai dai yanayine hakan zancen umma da lafazinta kan yarinyar nan yasa na fara tausayawa rayuwanta har naji ina son in taimaka matan.

Sai gashi itace ta rigamu hakan ta fara taimakon mu lokacin da bamu zata ba a hannun makiya wanan yasa na kara jinta a raina sosai har zuwa yanzu.

Sun dauki lokaci kafin sufita sallah don ya fahinci ba zai shiga ajiba ranan saidai kasan zuciyarsa ya rasa meyasa naki zuwa din bayan kuma da zan fita ya sanar min da in dawo.

Daga wajen sallah suka bar school din don sakon Moses daya shigo masa hakan yasa suka fita zuwa inda Moses din yayo masu kwantace.

Ga azumi ga rikemu da Mrs Naomi's tayi cikin aji har zuwa wani lokaci wanan yasa na fito a galabaice department din su Aimana na nufa nake fada mata zanje gida banjin dadin jikina.

Tace mu tafi ita bata tashiba tukunna Auwal na kira yazo ya daukeni muka bar school din wajenshi nake jin basu cikin haraban school din a lokacin.

Har ya saukeni na tuna ban sayo lemu ba yasa nake fada mashi ko zai sayo min yace in bari anjima idan gamma tayi masu kayan fruit sunfi fitowa a lokacin.

Kodana shiga gida alwala nayi nayi sallolin dake kaina na samu wuri na kwanta duk da gamma yayi a lokacin amma abu ga mai azumi sai barci ya daukeni.

Auwal ya kira yana tambayanshi ka dauko tane yace tun dazun na mayar da ita gida ai naga kamar azumine ko bata jin dadi saidai zan koma tace tana son lemun buda baki.

Kafin ka koma ka sameni a gida ya fada mashi salman ya lumshe idanunsa don suna tarene had lokacin bayan ya gama yake fadin sai kaje da kanka salman kaji meke damunta kafin nan Ku biya ka said mata abubuwan shan ruwa.

Kamar me ke nan ya tambayeshi shiru yayi bai bashi amsa ba ba,a jima ba kuma Auwal din ya iso nan salman ke masa sheri da Auwal driver hjy.

Auwal din yakai zaune yana fadin ai aikin nan ina jin dadinsa sosai salman saidai yau din nan na daukosu da wata bakar yarinya da ita Aeesha din tace min wai yar uwartace ita.

Amma ina suspecting din yarinyar kamar akwai yar tsama a tsakaninsu da Aeesha din irin kallon da take mata na daban be gaskiya.

Zaka sa ido akantane ka fahinci ko wacece ita ina tsoron kada su cutawa yar mutane saboda dani don ko INA yanzu zasuyi kokarin kawo min hari akaina .

Angama yallabai zanje na kai mata kada akira sallah don yamma ya soma tare da salman zakuje zai saya mata abubuwa zaije ya ganta yaji meke damunta din.

Ina gida kwance Ammah tasa min kira da natashi magariba ya soma karatowa hakan yasa na fito waje da zumar na aika Asmau ta amso min kankara da multina don' ni na manta da zancen Auwal ma a lokacin.

Yaro ya shigo yana sallama dauke da kaya niki niki cikin manyan ledoji yana fadin ance nashigowa Aeesha dashi na shan ruwa.

Ledane cike tab da lemun danace sai daya da shima abarbane sai kwalayen watermillos zasu kai biyar ko fiye da hakan sai wasu bakaken ledoji dake dauke da kayan sanyi na kwali dayan ledan kuma ke mai karatu kin canka.

Nan nabar su anty safiya ana fadin kaga masuyi don jalla komai a gadarance akeyinsa a raina nace yau ba habaicin ke nan kuma ba zancen kwaraya tabi kwaraya da ake fadi.

Ina fita naga salman ne da Auwal hakan yasa na kako murmushi a fuskana ina fadin Sir kaine ashe da kanka ?

Murmushi yayi tare da fadin kin hana min yaya zaman lafiya hjy Aeesha ai dole mu taso mu duba shine ko ya ya kike yace sai nazo na duba masa ke ko lafiya kike ?

Haba dai shima ai yasan lafiyata kalau tunda dazun muka rabu dashi Aimana dake tafe har tana tuntube wajen kallon mu kanta ya kara daurewa sosai batace damu kallaba ta shige gida suma sallama sukai min suka shiga mota suka tafi.

Ammah dakewa Aimana sannu da zuwa tayi tsaye tana bin kayan da suka zageye din da kallo kafin Samira tace duk garan azumine haka aka kawowa mummy Aeesha su.

Wai waye wanan ta samu cikin lokaci guda haka yake wanan kashe kai kamar baisan zafin kudi ba ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA

[8/17, 9:01 PM] Zainab Idris Makawa Writer: [8/15, 07:30] Seenabu Makawa: M/C COLLECTION MAKAWA COLLELECTION ONLINE BUSINESS FASHION & BEAUTY ITEMS SUCH AS LAGOS LACES, SHOES, BAG, COTONO KAMFALA COTONO ATAMFA, LAGOS GOWN DONGUWAN RIGA, TABLE FAN,HAND DRYER KIDS,FASHIONS etc

LAGOS NATIONWIDE DELIVERY SAI KUNZO A CIKIN SAUKI INSHA ALLAHU,,,,,,,,

JA YA FADO,,,,,,,,,,,,

ZAINAB IDRIS MAKAWA

BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,

2️⃣4️⃣

GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,

YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,

HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,

[8/15, 07:30] Seenabu Makawa: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1ftp

Abbu ne ya dubi kayan ya girgiza kai yana nisawa yace anya Ammamatan bamuyi sakaci ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0