Showing 87001 words to 90000 words out of 110493 words

Chapter 30 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa

lokacin.

Hauwa na fahinci kuna son ku mayar damu kananun mutane a idon duniya yanzu lokacin ya juya zamani yazo da wani sauyi an bar wancan akidan hadin na baya a yanzu.

Lokaci muke ciki na yancin kai dakai koda kuwa baka son abin nan kamar me dole kasa ido hakan ya faru ga maishi.

Naja kunnenki a falon nan ki sakawa yaron nan ido a lamarinsa wayewansa da akidunsa ba data bane da namu a yanzu da yake ganuwan wanan shekarun nasa kinki.

Yau gashi kina son ki kaini ga abin kunya mutuncina ya zube a sanadin jikana Dan da Dana ya haifa da cikinsa like son zubar muna da kimarmu dan ra,ayin kanki.

Shi magaji yafi kowa be yallabai ina haihuwansa akayi kamar kowa don haka dole a juyasa kuma yadda akeso tsawa ya daka mata abinda ya jima bai mata ba yana fadin duo abinda suka aikata su kuka da kansu ayanzu bayan ya gama masu fada son ransa.

Yayi gyaran murya ya mike don shirin fita fada duk da ya makara a ranan amma saida ya fita don sauraren matsalan al,ummanshi.

An tashi fada karfe daya aka cafke iya a hanyasa ta komawa gida wasu Jami,ai da ba,ansan ko suwaye ba.

Wanan yasa na tare dashi sukayi saurin sanar da maimartaba halinda iya ke ciki gashi ba a san inda suka nufa dashi ba a lokacin.

Maimartaba yasan aikin hatsabibin jikansane don haka ya fara neman layinsa baya shiga a lokacin hakan yasa aka kira masa mahaifinsa dagashi sai shi suka tatauna zancen nan ma shima din yayi trying layinsa bai shiga ba a lokacin.

Damuwana shine bansan iya wa yanda zaisa akama masa ba a wanan zancen hakance yasa nake son a dakatar dashi ga komai.

An kira masa mai babban daki hjy hauwa ya sanar da ita duo wanda ke cikin zancen nan ta sanar dashi yayi gagawan kawo kansa nan gidan sarauta don mafaka saboda yanzu iya yana hannun wa yanda ba asan ko suwaye ba.

Yaron nan ashe yaron banzane daga ana son yi masa gata zai fitowa mutane da haukansa a fili shine matsalan da run farko na guda gashi kuwa.

Ban fahinci inda zancen ki ya dosa ba yallabai ba zancen yanzu bane anjima zan maka bayani yanzu dai bari mu nemo kura tazo nan don nasan tana cikin maharansa.

Anyi kiran layin ta baya shiga hakan yasa ta fita da sauri don tura yarta ta sanar da ita halin da ake ciki saidai Hindu din bata gida a lokacin ance ta fita bayan an kira layinta.

Ga zance bana fitowa a fada ba duk da sunsan gaskiya hankalin iyalin iya ya tashi sunyo tawaga zuwa gidan maimartaba.

Na gamawa Abbu bayanin zancen komawan mu school ke nan na daga akai sallamawa Abbu waje.

Ya fita ya dan jima a can naji yana kwala min kira na fito sako hijjabinki muje ya fada kawai da sauri na koma daki na saka hijjab dina karami nafito.

Muna fita kofan gida naga mutane da manyan kaya naji Abbu yace gata nan yallabai jin hakan yasa nakai kasa cikin girmamawa ina gaidasu.

Suka amsa cikon sakewa tare da fadin sakone daga mai marta don Allah ki natsu ki bamu amsa kan abinda mukazo nema a wajanki.

Na gyada kai yace tambayan lamban wayan yallabai Bashir mukeyi don kakansa sarki ya kira duk layukansa basa shiga a yanzu.

Shine ya turo mu wajen ki mu samo masa numbersa dakeyi a yanzu a wajenki a hankali na dago kai na dubeshi na dukar ina fadin.

Wallahi bamu taba waya dashi ba tunda ya tafi asalima ni banda labarinsa a yanzu don ya fada min cewa mun rabu ke nan ba zan kara ji daga garesa ba kuma.

Kallon juna naga sunyi na dan lokaci kafin suce damu shike nan malam dama shine kawai tambayan kuma ta fada muna gaskiya mun gode.

Har zan mike sai kuma na koma na gurfana ina fadin baba badai wani abin bane ya sameshi ko na fada cikin damuwa da nuna kula.

Da sauri yace wallahi yana lafiya yana dai son suyi magana dashine kuma layinsa baya shiga a yanzu yasa ya turo mu nan.

Wallahi ni banda ko wani masaniya akansa yanzu tunda ya bar wajen mu din sukaiwa Abbu godiya suka tafi su Aimana da suka dawo har tana cin karo da samira wajen kallo.

Sun tafi na shigo gida suka fara tambayana su waye meya faru mukaga an kiraki nace wallahi nima ban san su ba ba kuma abinda ya faru na shige dakina.

Ko a daki saida ta kara tambayana nace mata daga gidan su man bash suke a takaice ban fada mata komai ba sai ajiyan zuciya naji tanayi.

Sai darene anty safiya ta kirani dakinta tana fada min irin alherin data samu wajen hjy ummi da anty basira tana fadin ke irin su ko biyar sukazo ai harka ya budu ke nan wajen mutum .

Ta amshi layin wayana wai zata kira idan ta koma, kema na saka mata naki ta karba a wajena na bata tana ta fatan wai Allah yasa dan uwata ya aureki .

Ashe dan uwanta yana neman ki ne shine yasa na ga ta damu dake kala bance mata ba don hankalina baya wurin ta a lokacin.

Nidai har lokacin hankalina ba a kwance yake ba don nasan dole akwai matsala don haka kawai ba zaisa suzo har gida a banza ba.

Don kawai tambayan layin waya dole kawai wani abu da suka boye muna da yake faruwa da man bash din a lokacin zuciyana ta raya min hakan.

Sai kuma tsoro da fargaba akan hakan yakamani lokaci guda sai gashi na tsunci kaina da danna layinsa na nan daya saba amfani dashi ake fada min bai shiga layin a yanzu.

Washegari kusan tare da Aimana muka bar gida mun rabu da ita akan zatayi min waya tayi min bayanin halinda ake ciki akan komai.

Sunan na daije school ne duk da kowa na farin cikin dawowa amma ni yanayina kawai zai nuna maka ban cikin good mood a lokacin.

Muna fitowa break na nufi office din nan nasu saidai alama ya nuna an dade ba,a amfani dashi kuma ko don ba,a gama dawowa bane oho ?

Tunda ba kowane ya dawo daga hutun dole da mukaje din ba a lokacin gashi kuma examation zamu fara wai har an mana time table a ranan kuma.

Ji kawai nayi inbar school din hakan yasa na fito zuwa parking place na shiga mota da niyar barin wajen horn naji anyi min na juya ta cikin glass ina kallon maishi salman ne a cikin motarsa wace man bash yake shiga a baya.

Saida gabana ya fadi don ganin motar ya tuna min abubuwa da dama a lokaci guda a hankali na sauke glass tare da kokarin budewa in fito.

Sai dai Ya rigani karasowa wajen da nake don haka ban fito ba yake fadin Aeesha ce long time no see aina dauka baki garin nan kema gaba daya ?

Saida na dan saki guntun murmushi mai kama da yake nake fadin Ina zanje sir kawai dai yanayine ya boyeni yanzun daga office dinku nake na duba yana rufe.

Ohh wancan side din dama saboda mutumin ki aka bamu wancan din don aikinsa yana son siri yanzu kuma na koma office din department din mu da zama dama a can nake .

Can nake zama wanan din an rufeshi ai sai abin ya dan daure min kai kafin naji yace dani i hope lafiya kike nemana ?

No lafiya kalau sir dama dai tambayanka zanyi kan ,,,,, sai naji ya katseni da fadin akan Bashir kike nufin zakiyi tambaya ?

Kinyi kuskure babba tun a wancan lokacin Aisha idan kin fada son bashirne ma ki daina don zaki wahal da kanki ne kawaine a yanzu a banza.

Don kema tun farko ya kamata ki gane hakan tun sanin koshi waye da kikayi don haka ya tafi ke nan you nerve see him again in your life .

Ko a kaddarama ya shigo kasan nan baki da daman da zaki gansa kuma a yanzu don haka ina shawartan ki daki debeshi a cikin zuciya ki ga baki daya ki kama gabanki zai fi maki sauki.

He only used you to achieved his goal ya kuma samu ya kuma samu hakan yanzu ba sauran wani abu daya saura a tsakanin ku yanzu dashi ina gani ?

Pardon sir ban fa fahinci zancenka ba inda ya dosa na yayi amfani dani ya tafi kome kake nufi da fadan hakan ?

Ban fahinci wani amfani yayi dani ya cinma bukatarsa a kaina ba yayi nasara ?

Wuri da dama Aisha ya amfana dake da ba zaki gane hakan ba a lokacin don idanuki yana rufe, bansan meyasa ku mata you only depend on love da kowa ba.

Ke kin dauka sonki Bash keyi da gaske in har haka kike dauka ki cire hakan a zuciyanki yanzu please ba wanan zancen a nasa .

Kyau ko kudi ko wani ilimi naki baya taba damunshi ga mace ko ya rudeshi don mutum ne shi mai wani irin ra,ayi na daban aikinsa kawai ya sawa gaba shi.

Don haka ina shawaratan ki da ki fitar da zancensa gaba daya a zuciyarki dama ranki kada ki kara zuwa nemanshi a guna kin masa amfani ya biyaki a lokacin final the game is over now.

Jin zancesa na karshe gareni yasa na dago na kalleshi cikin mamaki daga inda nake zaune don in tabbatar da salman ne kuwa kodai wanine.

Mutuwan zaune nayi ina kallon salman din don ban taba tsamani ko zaton irin hakan daga bakinshi ba gareni sai gashi gaba da gaba ya tsaya yana fada min zance haka mara dadin saurare da bakinsa ido da ido kuma.

Haka ya juya ya barni da baki sake cikin mamaki ina binsa da kallo ya tafi ya barni zaune a wajen na kasa wani kwakwaran motsi.

A hankali na iya maida kaina na saita saida na dade zaune a wajen kafin na tayar da motan na fice daga cikin school din.

A haukace nakai gida cikin bacin rai ina maimaita maganansa a kaina wanda banyi zaton ko taba tsamani jin hakan daga wurin mutumin da sam ban taba zaton hakan a gareshi ba .

Kalman daya fada na yayi amfani dani wurin cin ma manufarsa ya kuma samu ya biyaki ya tsaya min a raina yaki fita kuma kaina.

Babu kowa sai anty safiya na samu tsakar gidan mu tana aikin taliyanta sauran suna daki suna barcin gajiya a lokacin da mukasha.

Ko ita wai yaran anty ummi takewa shi don ta fada mata tana sana,anshi shine tace ayiwa yaranta suna sonsa sosai dalilin yin aikin nata ke nan lokacin.

Sama sama na gaisheta da aiki na nufi dakina naji tana fadin har kun daya Aeesha yau kan baku dade ba kamar kullum ?

Ban tsaya amsata ba na fada dakina saman gado na haye na saki wani irin kukan da rabona dashi tun bayan sanin iyayyena na asali da nayi a wancam lokaci.

Sai kuma ranan nayi makamancisa banda yar uwar shakikiya ko wata kawa ta dindin da zanyi sharing din zancen nan da ita inji sanyi da shawaran da zata bani.

Sai nake jin wai meyasa akai haifoni cikin duniyan nan gaba daya ?

Some times nakanyi wanan wanan wawan tunanen a zuciya amma naji wani malami ranan yana wa,azin hakan baida kyau ga musulmi na daina.

Amma yanzu sam bani wanan tunane ko girmane ya kawo hakan ko kuma samun kwanciyan hankalin dana samu daga sanadin man bash yasa wanan ya gushe min sai a wanan ranan na dawo fadin hakan a zuciyana

Yau a duniyan nan banda kowa da zance na yarda da shi har in fada mai cikina irin haka babu banda shi sai Abbu Abbu kuma namijine ba abokin irin zancen nan bane gareni.

Dole don haka ni kadai zanyi kida da rawana a yanzu har in samowa kaina mafita kan wanan tarkon da bansan manufarsu ba da suka dana min.

Ina jin Asmau ta tashi tana tambaya mummy ta dawone naga kofanta a bude mana sai naji anty safiya tace ta dawo dazun nan tana ciki.

Hakan yasa ta shigo ta samu na idar da sallah la,asar ina ninke sallayata tace mummy ashe har kun dawo yau kan baki dade ba kwarai.

Samun kaina nayi da fadin kinsan yau aka koma farko ba wasu mutane da yawa sosai a school din.

Sai takai zaune tana bina da kallo kafin naji tana fadin gashi ko ba muyi abincin rana ba yau, don saura tuwon jiya ya rage da yawa jiya shi mukaci dazun da rana.

Ba komai Asmau bana jin yunwa a yanzu tayi shiru na dan lokaci kafin can kuma tace dani mummy wani abu ya faru dake idon ki ya nuna kinyi kuka sosai wallahi ?

Saida na juyo na dan dubeta kafin murmushi yake ya biyo baya ina fadin wani abune ya bata min rai Asmau amma ba komai akwai Allah .

Sai naji tace dani kodai wani ya zageki inci ubanai wallahi yadda tayi maganan ya dan ban dariya nace ?

Haba dai ba komai ai ya wuce ta zauna shiru kamar tana tunane kafin ta nisa tace ina mamakin mutane wallahi mummy yanzu..

Da basu da tunane sai ka dauki laifin wani ka dorawa wani ba zaka barshi yaji da abinda ke damunsa ba ka dauko wani ka dagwara masa kuma.

Asmau ba hakana bane idan Allah ya hanemu da abu mu nisanci abin nan komai kankantar shi kuwa kada mu raina don fitinan yinsa yafi yinsa yawa .

Mutane nada gaskiya wani lokaci saidai suna abin ne ba bisa ka,ida ba kamar yadda hadisi ya koyar ayi, kamata yayi su fuskanci mai laifin a lokaci da ya aikata abin amma ba daga baya ba ka dabawa mutun zafin laifin bayan ya aikata hakan.

Nikin daure min kaina wallahi mummy ta fada nace ba zancen daure kai bane Asmau yau nima kaina din a daure yake wallahi.

Don Salman ne ya ban mamaki matuka don ban taba zaton haka a gareshi ba wallahi sai gashi yayi min abinda ya daure min kaina?

Salman dai da nake jin kina fada mummy nace shifa Asmau shidai dan uwan wanan matan da muka hadu shekaran jiya dasu a bukin nan.

Mutumin da nake wa kallon daraja da yan uwan taka yau shi ya kalleni ya fada min maganan da ya daure min kai iya son ransa a gabana Asmau.

Ni Salman yau zai fadawa Man Bash yayi amfani dani don cinwa manufarsa kuma ya biyani a fakaice yayi tafiyasa .

Kada kuma in kara gigin nemansa ta hanyar shi mu matsalan mu ke nan mata idon mu a rufe da mutum ya nuna kulawansa akan mu sai mu dauka hakan sone ?

Bamu la,akari da irin mutanen da level din mu ya dace muyi mu,amula dasu da farko duk wanda yazo gun mu sai mu dauka so ne a garemu Asmau ?

Ni Man Bash bai taba nuna min wani abinda zan fada son shi ba yadda yake nufi haka kuma ya fada min da bakinsa kwarai don wani manufa yasa ya tsaya ya taimakawa rayuwata shi salman ya sani .

Amma me zaisa yau ya fada min hakan kamar da wani manufa ko kuma na sani na yarda da plan dinshi aikin banza naji ta fada kai tsaye.

Wai man bash dai wanan naki mai mutunci saukin abin cikin zancensa bai sa kinyi sha shanci da man bash din ba ai.

Nace haba dai Asmau yace shine dai yau abin bakin ciki ko ba komai bane walle kishina nace kishin me kuma ?

Rabu da kurman kishi mummy kurman kishi kamar mahauka yake saka mutum ai kada ki dada karki kara wata kila baiso zaman ki da wacan din bane.

A shekarun Asmau da nake gani tayi kankanta da rike manyan magana a bakinta amma idan kinji ta zaro magana ko tsohuwa saita kaucewa Asmau kuma shigen duk haka da bi,ansu yake da manyan magana.

Sam banyi wanan tunanen da tayi ba cikin dan lokaci guda haka don ba zan kawo wanan tunanen kan salman ba amma in har ba hakan bane data fada meya kawo wana maganan haka a bakinsa cikin hasala dani yau ?

Kamar nayi masa laifi a baya kan mu,amulana da Bash ko kuma a sanadina wani abu ya taba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login