Showing 60001 words to 63000 words out of 110493 words
Chapter 21 - Ja Ya Fado Ja Ya Dauka Complete Hausa Novels By Zainab Makawa
yanzu wani zakuyi ciki nidai in son samu ne kuyi duka don Allah.
Gaskiya kam wata ta fada saratu din ta kara fadin wai barnan baki Allah yasa ko kala daya dai ayi din.
Asmau cire muna Iowa kala guda kala ukku harda Samira lokaci daya naga sun kalloni tana cirewa na mike na hada kaf din mu na juya wajen amaryan ina fadin bamu leda mu saka anty.
Nifa inji wars kudi a hannu ba barazana ba wai isan baka isa ba galadiman tusa inji kudi a hannu kawai ta fada tana miko hannu ki bimu ki karbo kudin ki.
Don isan galadiman yan Adam ai in ba a isa ba ayi saratu isance ya kawo hakan yanzun ma nan ko amaryan ta hauta da fada har iyayyen sukaji suka shigo.
Daya daga cikin yan matan nan ta mayar masu da abindake faruwa ta kare da fadin ba a haka saratu ai komu nan mukai zuciya nesa da ita wallahi da bamu zo gidan nan ba.
Mukan zamu zo tunda mun gane nufinta ai da ace bukintane idan munzo duk abinda taga dama tayi muna amma anty Fati ba tai muna komai ba kuma har gida ta bimu taci muna mutunci yasa mukazo.
Iyayyen na magana tanayi muka dauki kayan zuwa gida Asmau ce ta dauko a kai kowa da abinda yake fadi ina jinsu ban daiyi magana ba saida muka kawo kofan gidansu muka tsaya.
Yanzu Aeesha dan kalula kinsa mun dauko anko din nan ta yaya zamu biya ke nan nace Ku dauki naku ku bar muna namu zuwa gobe kwaji komai .
Ina baki labarin nan nan ne tiryan tiryan zeey don abinda zai biyo baya gaba saboda ku fahinta karfe takwas na baiwa Asmau kudinsu takai masu karfe tara alheri ya shigo min daga Man bashir galleleyar Montana ta tsaya a kofan gidan mu.
Inda gidan rabakaya kuma ke alhinin kudin kayan da Asmau ta tattara ta kai masu cash babu kwandala da yai ciwon kai ciki.
Auwalne yazo da motan tare da sauran alherin data biyo baya ya dade tare da Abbu suna magana kafin Abbu ya aika na fito nazo muka gaisa ya dan yi min bayani a gurguje tare da mika min key din motar a hannu na.
Ban tambayeshi komai kan man bashir din ba illa yana lafiya ko nayi hakanne don in nusa masa tunda yace including me wanan kalman ya tsaya min a rai lokacin.
Alheri kuma yayi niyar min ne yasa ya aiko dashi donshi mai kaikayin hannu kullum a cikin susan hannu yake ga wanda rabosa ya koka gareshi dama.
Munyi murnan mota yayin da Abbu ke murnan sabon shagonsa da za a gyara wanda Auwal yai masa albishir lokacin.
Motar tazo min a bazata don na debe rai ga zancen malam Bashir yanzu gaba daya tundai da banjo komai daga garesu ba na tsawon kwanakin da aka diba ko Auwal ya dauke kafa banji komai a wajensa ba,
A ranan Abbu ya kira masu aiki suka gyara min tsohon get din gidan mu dake rufe shekara da shekaru aka budeshi aikai masa siminti .
Saida yamma muna zaune tsakar gida muna hira Asmau ke muna zancen gidan Rabakaya wanan saratun abinda tace data kai masu kudi wai hakan yafi sauki ita ko ina yarinya zata fito da kudi aibai dameta ba ita kuma Asmau tace da ita balls kowa yasan muba cima zaune bane ai muna neman na kanmu da karfin mu basai mun jira an muna ba.
Ammah ke tambaya Asmau ta fara bata labarin abinda ya faru tun farko nan naji amma tace ai dole tayi hakan uwarta ba can Alh ya aurota Okene ba yana raba kayanshi lokacin.
Kinshin yan uba takeyiwa Fati a fakaice ita ta biyo ku gida kunzo mata kara hassadan hakan takeyi a fakaice ai.
Ammah don dai Farida ta matsa da wanan bukin ne in bashi ba sam nawa baizo daya da yaran gidan nan ba don rashin mutuncinsu yayi yawa wallahi.
Ku daije mata tunda ta biyoku balle yan mata na son suga bukinki ya haska kowa ya hallara an cika waje hakan sai ace bukin wance ya haska har dasu wance sunje balle ku da kuke yan gida anty safiya ta fada.
Washegari muka kai dinki don su farida da maryam sunzo wanan shagon da khairat ta kaini wanan karon ma can nakai dinki ya fada muna ranan da zamuzo mu s karba.
Mun dawo gidane muka samu maman Aimana tazo muna wuni nayi mamakin hakan don yana da wuya sana,anta na kitso ya bari ta fito don kullum cikin yan kitso take ita.
Nan na zauna falo muka gaisa take ta yabon yadda na girma na koma kafin tace Aimana yanzu fafir taki bokon nan bayan wahalan da tasha a baya nasa tasa wanan aure a zuciyarta.
Aure kuma na tambaya cikin mamaki tace wait baku wayane nace a,a mama mun kwana biyu gaskiya bamuyi waya ba.
Ashe baki san da zancen auren ba ke nan nace bata fada min ko dai wanda tun tana nan take zancensa wanda ke zaune a turai amma tace zancen a gurinki ya fito mama ?
Kwarai kuwa zance shine dai har yanzu ita da ubanta sun hau sun zauna basu taba ganin mutumi ba ko sanin waye shi alma wai haka suke son ayi aure.
Sai naji Ammah tace hakan na yuyuwa kuwa ai aure ba wasa bane wajibine abi ka,idojisa kafin a aura mashi ita.
Ni a yaddama nake ji shine wai kowa fa baisan dan hjy ba an daiga tazo ta tare a gidan daga bays data fara sabawa da mutane take fadin ai danta dake kasan wajene ya gina mata gidan amma har yau din nan ba wanda ya sanshi gaakiya.
Amma haka baban Aimana yayi tsaye wait sai shi don kawai hjy na masu wasa da kudi abin takaici yanzuma suke sintirin binta ko yaushe kan zancen.
Amma ko Aimana batayi dabara ba shine zata bar karatunta tun yanzu kan zancen da baida tushe baida dalili haba dai.
Bari inna koma zan turo maku ita ai yar gandoki muje bukine da taji zancen buki yanzune zaku ganta gidan nan ni dai na barsu nan da Ammah tana fada mata irin halinda suke ciki yanzu gidan.
Banji dadin jin zancen Aimana na barin school ba don zatayi aure saita bar karatunta ina hankalin Aimana ya shigane wai ?
Sunje kitso da kumshi duk akan bukin da nake gani ba wani muhinmancin halartan mu wajen duk da a yanzu kan hidimar bukin zuwan anty Fati biyu gidan mu kan bukin.
Duk da dai ni ba gwanan zuwa bukin kowa bane amma wanan yanzu dole na halarta tunda ya zama kamar na family din mune.
Kaina na wanke kawai sai mai dana shafa mai ya kwanta banyi kumshi ba ko wani iri amma dai na gyara jikina don in fito fes kamar kowa.
Ranan saka lalle ban samu zuwaba su samira sukaje sun dawo suna hira abubuwan da akayi saboda Ammah ne banje ba don zata fita ga anty ma tace zataje kamun yasa na zauna gida.
Sai washegarine da za ai kamu zan je sai gasu maryam da farida sunzo akan muje gidan Rabakaya din anty Fati tana neman mu wai .
Banso zuwa ba amma dole na shirya muka tafi wani dan dogon rigane a jikina mara nauyi marron colour sai gyale dana dora na rufe kaina dashi sai kuma wayata a dayan hannu tare da keys din dakina dana rufo.
Banyi zaton bukin ya kankama ba haka da banzo da wanan shigar ba haka don sai najini kamar sakayau wajen duk idanuwa a kaina.
Saboda tufafin basu wani rufe min jiki ba sosai duk da a yanzu na rage saka manyan hijjab yadda nakeyi da can don dokan da aka saka muna har na fara sabawa da fita haka kuma.
Motocine a kofan gidan da dan yawa sai mutanen da suka cika wajen naji maryam na fadin ango ya iso ke nan don gashi can na hango .
Ai tunda kikaji ya sulaiman yace yau zai iso ango yazone gabana naji ya fadi lokaci guda don ambatan sunan sulaiman din da tayi a lokacin.
Wai wai wai ke duba can ya Habbib ma yazo ashe inda take nunawa din na kalla a take na tuno da murde min kunnen da yayi lokacin ina karama yana sabon zuwa sojanshi yazo hutu ban sake ganinsa ba sai wanan ranan kuma.
ZAINAB IDRIS MAKAWA
[8/23, 10:13 PM] Zainab Idris Makawa Writer: https://www.facebook.com/groups/293543855250655/permalink/1171299937475038/[8/15, 07:30] Seenabu Makawa: M/C COLLECTION MAKAWA COLLELECTION ONLINE BUSINESS FASHION & BEAUTY ITEMS SUCH AS LAGOS LACES, SHOES, BAG, COTONO KAMFALA COTONO ATAMFA, LAGOS GOWN DONGUWAN RIGA, TABLE FAN,HAND DRYER KIDS,FASHIONS etc
LAGOS NATIONWIDE DELIVERY SAI KUNZO A CIKIN SAUKI INSHA ALLAHU,,,,,,,,
JA YA FADO,,,,,,,,,,,,
ZAINAB IDRIS MAKAWA
BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM,,,
2️⃣9️⃣
GA MAI SON BANI HAKKINA ZAI IYA TURA KUDI DUBU DAYA KACAL A WANAN LAMBAN 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO A KIRA WANAN LAYIN WAYAN 08036959257 NAGODE ALLAH YA BADA IKON BIYA MUN GODE NAKU HAR KULLUN YAR MAKAWA, , , , , ,
YAR UWA KADA KI RAINA NAUYIN HAKKIN WANI A WURIN ALLAH DOMIN AMANACE HAKKI,WANI A WAJENKA , , , , , ,
HAKKIN MALLAKAN JUYAWA AUDIOVISUAL S ZARIA TV KEDA WANAN HAKKIN KADA WANI KO WATA YAYI GANGANCIN JUYASHI ZUWA AUDIO PLEASE,,,,,,,,,,,,,
[8/15, 07:30] Seenabu Makawa: https://chat.whatsapp.com/CDBG34xpZRZ5dZR86m1ftP
Yana nan yadda nasan shi a baya saidai dan murjewan da yanzu yayi ya kara jiki da haske sosai yadda na hango ya zama wani abu yanzu da har mutane ke biye dashi a baya haka.
Cikin ladabi a bazata naga su maryam na gaidashi hakan yasa na dauke kaina da sauri zuwa cikin gidan inda mukai karo da wata mace yar bakar mace tana waya a kunyace nace sorry please ta daga hannu alaman ba komai.
Nayi mamakin ganin kwana daya amma gidan a cike yake da jama,a fam a lokacin ga manyan tukwane an dora ana motsa yar gwaunati wasu a zaune.
Ban tsaya gaida kowa ba kai tsaye dakin yan matan na nufa Asmau na biye dani a baya saidai bamu shiga ba muka tsaya a kofa harsu farida da maryam su karaso.
Jefi jefi hiran yan dakin da yan wajen yake shigowa kunne a wajen da muke tsaye din na waje na bayani kan yayan gidanne wance ta haifi wani da wani ai .
Na daki kuma ina jin suna gardama kan kudi da angonne zasu basune bansan anty fati na da layina ba sai ga kiranta ya shigo wayana lokacin ganin hakan yasa na leka dakin ina fadin gani a waje anty fati.
Wai dama kun shigo ashe ina farida da maryam nace tare muke suna waje mun barsu zasu shigo yanzun nan.
Zakice a ranan wasunsu suka fara ganina nida wayar hannuna suke kallo suna tambayan wacece ni ?
Naji lokacin da anty Fati din ta juya tana fadin sister din muce diyar brother din babane wanan din wata ta tambaya.
Hangosu da nayi tafe yasa nakarasa shiga daga cikin dakin ina gaidasu a jam,i suka karaso amaryan ke fadin maryam kinsan zakuje amsan kudi kuma kun tsaya bata lokaci haka don Allah.
Zaune nakai don ba zanje ba kudin ne har sai an wani binsu in suna da niyar bayawa kalloni tayi tana fadin kin zauna mana Aessha kai na gyada ina fadin suje kawai anty su karbo.
Yau ga tsiya keba zaki bane nace ban fito da shirin fita ba ai kinga yadda na fito na dauka iyakarmu nan ne ai.
Amma dai na fada maku tun jiya ai to dolene saida ita Saratu ta fada dolene ai kinji abinda baba dai ya fada ko to kimatsa tunda fitina kikeso ke .
Fitinan me anty tace bata zuwa ba sai mu mutafi ba ku kuke daukanta wata tsiya wallahi har take ganin wani abune ita haka kawai wanda bai fika asali ba zai nanuwa mutum daukan kan banza.
Dadin abinda dai yan asalin basu sukace hakan ba ai na fada daga inda nake ta juyo tana fadin me kikace dakin yayi tsit ana jiran jin amsan kowan mu.
Nace ke kinyi kadan in sake maimaita abinda na fada dan tsugunnin nan naki dai saratu duk da ta gime min sosai ga haihuwa banjin zan iya bata girman a yanzu.
Fitsararace ta gaske wai kamu na zagin koko a yau nace ashe koko yasan asalinsu daya ke munsan diyan sunna da yayan dore fa duk munsan komai ba wani zancen asali a nan kam uba naji shaka a bayana kafin ai haka Asmau takaiwa wace ta kama min kai duga kamar mahaukaciya.
Fada sosai Allah ya bamu sa,a mukai masu kaye a wajen ga zaki duk abinda yazo muna a baki mun fada masu ido rufe cikin dan lokaci guda.
Lalai yan sokoto bala,i ne kinji iyayyen suka zo ana tambaya take kuma Asmau ta lauye zancen ta zaro ido tana fadin ku koba haka akayi ba ai gara da mummy kowa yasan tana da uba ku da ake tantama akan ku fa ?
Abu ga taron mata nan da nan zance ya fara tafiya masu cewa ashe ma ina da ubana tunda ga Asmau ta fada kuma ashe shike min aike akai akai kuma komai dadewa zaku ganshi nan.
Uwar gidan rabakaya maman su ya habib ta kiramu tayi muna fada tare da ja muna kunne kan wanan tonon asirin na raba zumunci da mukeyi idan iyayyen mu maza sukaji sai rayukan mu ya baci sosai kafin ta juyo kan mu nida Asmau tana fadin keku Aeesha kada wanan abin ya dakatar dake cikin sha,anin nan ki shigo kuyi komai tare da yan uwanki kada wanan zance yasa kice zaku dauke kafanku badon saratu ko wani kuke gidan nan ba abu dayane ya hadaku a nan din.
Nagode mama na fada na mike ina cewa saratu muje zuwa lokacin har anty safiya ta iso gidan cikin tashin hankali saita samu an kashe maganan ko ince ya lafa a lokacin dai.
Koda muka koma gida banyi niyar komawa gidan ba amma anty safiya ta matsa min da na shirya muje din dole na tashi nayi wanka.
Wurine na kure adaka kowa ka gani yaci kwalliya masu anko kuma sun zuba anko dinsu inda bangaren gidan amarya suke daban na angoma haka.
Bamu samu zuwa wajen ba sai da akai nisa da shagali muka shigo daga can baya kadan na samu wuri na zauna nida su Aimana da zuwanta ke nan muka dungumo zuwa wajen bukin ban jima da zama ba akace yan uwan amarya su shigo suyi mata liki.
Dole na taso sai lokacin ma wasu suka sanda muna wajen kayan wasu material ne an min dinki mai combination dinkin yayi kyau sosai sai shara sharan hannu daya zuba min inda na daure sumana da ribon daurin dan kwalin dake kaina zaisa ki hango gashin nawa baki wulk da yake walkiya a daure.
Tun a mota munyi canji duk da ba kudi masu yawa ba a hannun mu amma sai ki dauka wasu kudine can.
Liki mu kaiwa yar uwarmu nafada daji da yan canjin hannun mu muka dawo mc din yana ta wasa mu kowa ya fada masa sunayen mu oho ?
Ban saba zuwa irin wanan wajen ba don haka nake jin kaina wani iri hakan yasa na mike na dan taka don barin wajen taron zuwa inda motoci suka faka.
Nida samira da maryam da itama tace hayaniya yayi mata yawa a lokacin muka bar Aimana da Asmau tare da farida suna kallon abinda akeyi.
Mun karaso wajen wata mota zamu gitta a daidai lokacin waya ta dauki kara na dauko ina duba wanda ke kirana Auwal ne a lokacin.
A daidai lokacin kuma wata bakar mota mai kyau ta tsaya gaban mu kadan saidai na ciki basuyi saurin fitowa ba a lokacin.
Can kofan motan ya bude ya habib din nan nasune ya fito cikin motan tare da matarshi da yarsu mace yar kimanin shekara uku ko hudu da haihuwa .
Haka kawai ganinsu ya sanya kirjina bugawa don rabona dashi tun ina shekara tara ko goma tunda yai min munguntan dana kasa mantawa dashi a raina
Kaina kawar gefe daya ina cigaba da waya don har ranan ina jin kamar a ranan yai min wani hikunci cikin muguntan daba zan taba mantawa dashi ba a rayuwata.
Akan munyi wasa da ruwan fanfo ya murde min kunne saida nayi zazzabi a lokacin sosai har asibiti aka kaini a lokacin muna tsohon unguwarmu.
Tun ranan ban kara yarda mun hadu dashi ba sai