Showing 3001 words to 6000 words out of 39491 words

Chapter 2 - Zinariya Book Compelet Novels By Aysha JB

tana ƙwala mini kira. Ɗan dakatawa na yi ina sake sauraro don sake tabbatar da ni ɗin ce ake kira ko kuwa, "Zinariya... "Na'am madam Salima ga ni zuwa." Bayan na je ta kalle ni tare da faɗin. "Ki shirya gobe ƙarfe shida za mu yi tafiya." Zaro ido na yi waje ina faɗin. "Tafiya ina? O'o ni dai a kaini gidanmu ba ni zuwa ko'ina wallahi." Banza ta yi da ita tare da haurawa sama, "Ni wallahi kar aje a sayar da ni ma a sa na daina ganin Innarmu... Cak Salima ta tsaya tare da juyowa ta yi mata wani irin kallo tana faɗin. "An ce miki ko na sayar da ke kuɗi zan yi? 'Yar talaka da ke har kina da bakin da za ki ce kar a je a sayar da ke? Ke ba abin farincikinki ba ne a ce za a keta hazo da ke? Karki kawo mini shashanci." Tana kawowa nan ta yi shigewarta.
cikin ɓacin rai na gama gyaran kitchen na koma ɗaki na ɗau waya zan kira Innarmu na ga ba ni da kati kamar na fashe da kuka saboda baƙinciki ga shi dare ya yi babu ta inda zan fita a gidan bare har in samu kati. Haka na kwana cikin ɓacin rai ina idar da sallar subahi na ji wani mugun ƙararrawa na ƙara kamar za a ta shi kaina, saboda neman fitina kaya kala uku kawai na saka a leda sai himar ɗina guda biyu, shi kayan ma doguwar riga ce kawai na saka guda biyu sai fallen zani ɗaya da T-shert ina isowa ta yi mini nuni da wata mota gidan baya na buɗe na shiga nan na ga drive ne sai wannan baƙuwar, ita kuma tare da mijinta suke a mota ɗaya.

Gaisuwa ce kawai ya haɗa ni da matar dan ita ma na ga alamar irin madam Salima ce ba ta da sakewar fuska, haka har muka iso airport nan muka iske wata babbar mata dan za ta iya kai wa sa'ar Innarmu duk sai na ga suna gaisheta, har shi mijin madam Salima wanda iya bayan rigar shi kawai nake iya kallo, ni kam ina rakuɓe a gefe rumgume da 'yar leda ta ina kallon su, haka na ga madam ta shiga jirgi da mijinta baƙuwarta ma ta shiga, ya saura daga ni sai matar nan. Ai tsayawa na yi na ce yau zan ga ikon Allah da gaske ne matar nan so take lallai sai ta sayar da ni, zaman 'yan bori na yi tare da kurma ihu ina faɗin. "Wayyo Allah Innarmu! Wayyo na shiga tara na lalace... "Subhanallah! Ƙalau kike kuwa 'yar nan?" Wannan babbar matar ta faɗa tare da ɗago ne. "Wayyo ni ku bar ni, ni wurin Innarmu zan tafi ni a kaini gidanmu." Kururuwata ya sa security suka nufo wurin suna tambayar ba'asi, nan take sanar musu da babu komai. "Yarinya ki nutsu babu wanda zai sayar da ke. Mu je jirgin zai ta shi."
"Wallahi ba zan je ko'ina ba..." Jama'ar da ke wurin suka tsaya kallon ikon Allah, da ƙyar aka ja ni zuwa cikin jirgi ina ihu ina fisgewa, duk na haɗa gumi da majina. Zaunar da ni ta yi a kujera ta jikin window kafin ita ma ta zauna kusa da ni ta saka min makari, lokacin da jirgin zai ta shi na kuma kurma ihun da ya sa mutanen toshe kunnuwansu ita kanta sai ta ta ce. "Kai ohooo! Wacce irin yarinya ce ke da babu nutsuwa tattare da ke haka?" Ajiyan zuciya na dinga saukewa ina jan sheshsheka. A haka barci ya yi awon gaba da ni, yaya B kuwa sai jinjina yarinta irin na Zinariya take yi. Har jirginmu ya sauka a Egypt ina barcina sai da matar nan ta taɓa ni don ta tashe ni nan ta ji jikina da zafi alamun zazzaɓi. Buɗe idanuwana da suka yi mini nauyi na yi da ƙyar ina jin jikina na rawa saboda sanyi-sanyi. Motar da zai kai mu masauki ne ya zo ya kwashe mu duka cikin motar kuwa ina kwance jikin matar nan don na lura duk ta fisu kirki so ɗaya muka haɗa ido da madam Salima shi ma ba wani kallon arziki ta yi mini ba. Hotel ɗin da muka je a ɗakin matar da na ji suna kiranta da Aunty B, na zauna ita kuma madam tana tare da mijinta baƙuwarta kuma ɗakinta daban. Ko abinci ban iya ci ba, ruwan zafi na sha nan na dinga kwara amai, hankalin Aunty B ya tashi nan ta kira Salima ta shigo ɗakin. "Ko dai yarinyar ta kwaso ciki ne na zo ina yawo da ita?" Wannan mummunar kalmar ta yi mugun dukar zuciyata, duk da ƙarancin shekaruna na san kalmar cikin shege mummunar kalma ce, kallonta na yi da jajayen idanuna da suka rine dan bala’i na ce mata. "Ni ba 'yar iska ba ce." Salima ta ce. "In ke ba 'yar iska ba ce amaye-amayen mene ne kike yi wa mutane? Ke ni ba za ki saka ni a masifa ba akwai jirgin da zai juya wallahi zan saka ki mayar da ke inda kika fito." Aunty B ta ce. "Haba ya isa Salima wacce irin magana kike faɗa haka? Yarinyar nan dai mai aikin ki ce, a gidan ki take zaune ta yaya za ta yi ciki bayan kuna cikin gida ɗaya?"

"Na sani ko tana biye-biye da dare?" Ni tun da uwata ta haife ni ba'a taɓa faɗa mini mummunar kalma irin wanda madam Salima take yaɓa mini yanzu ba. "Ni ba 'yar iska ba ce wallahi, ni ba 'yar iska ba ce. Allah sai ya saka min... Ko rufe baki ban yi ba wani aman ya sake ƙwace min salati da sallallami suka ɗauka. "Kin gani ko Aunty B? Ni dai wallahi ba za a saka ni a uku ba, gwara tun wuri ta koma inda ta fito." Ni dai tun da na miƙe da niyar barin ɗakin hajijiya ta ɗibe ni ban sake sanin inda kaina yake ba sai farkawa na yi na ganni kwance gadon asibiti.


Littafin Zinariya na kuɗi ne, za ku tuntuɓi wannan Number ta WhatsApp domin mallakar naku. ₦500.
09079740079

Maman Faruk.
[30/11, 3:49 pm] ༺𝐀𝐘𝐒𝐇𝐀 𝐉𝐁༻: *...ZINARIYA*
_Romantic🌹_

®
AYSHA JB

Farin Jini Writer's Asso..
5&6
Yunƙurawa na yi da niyar tashi nan na ji ni shakaf, zaro idanuwa na yi da sauri ina ƙoƙarin miƙewa da ƙarfi dan na ji wani abu mai ɗumi yana bin tsakanin cinyoyina. "Na shiga uku na! Me zan gani? Wayyo Allah an yanka ni! Wayyo Innarmu an sayar miki da Zinariya." Ihu nake kurmawa da iya ƙarfi na, dukkaninsu suka shigo ɗakin a rikice A'isha tana faɗin. "Ke dalla rufewa mutane baki duk kin cika mana kunne... "An yanka mutum sannan a ce kar ya yi kuka? Na rantse da Allah sai an dawo min da jinin jikina tare da naman da aka ɓantala a cinyata, na rantse ba zan yarda da wannan muguntar da ake shirin yi mini ba." Na ƙarasa maganar ina hararan su tare da murguɗa baki. "Iko sai lillahi, ke kuma Salima wacce aka ɗauko miki kenan? Allah shi kyauta." Cewar Aunty B, Salima da shigowarta kenan ta ce. "Ba naman cinya ba, kanki za a cire mayya da idanuwa kamar na mujiya, yarinya duk ta ishi mutane, ni da na san haka kike da hauka ina zan ɗauke ki aiki? Ai wallahi ki sauko ki zo ki wuce dan daga nan za a mayar da ke inda aka ɗauko ki."

"Na rantse da Allah babu me ƙarfin halin da ya isa ya cire mini kai, kuma sai an biya ni kuɗin albashina na wannan watan dan Innata ta ce ba a tura musu kuɗi ba. Ko a ba ni kud’ina ko kuma wallahi na hana mutum sukuni." Tsaki ta yi tare da barin ɗakin, Aunty B, ta ce. "Ke da'alla bar shashancin nan, girma ne ya zo miki... "Girma? Wane irin girma ne bayan kuma wannan girman da nake da shi? Ke ki kalleni ɓakutuwa na ciko ta ko'ina... Tagumi Aunty B ta yi tana kallon Zinariya, ga abin dariya amma takaicin halinta ya hanata darawa. Hannun Zinariya ta kama suka shiga toilet ta ba ta auduga tare da nuna mata yadda za ta yi, da yatsu biyu ta ɗaga audugar tana mishi kallon mamaki. "Eyye! Iko sai Rabbu! Wannan bala'in kuma daga ina? Ni ce zan saka wannan a jikina kalan aje a mini satan kayan hanjina? O'o wallahi ba ni iya wa da wannan abar." Riƙe da haɓa Aunty B ta ce. "In ba ki saka ba haka za ki yi ta yoyo... "Yo me ye a ciki? Ba gwara jinin ya yoye ba da in tara da wannan abar a zo a yi mini warwason kayan hanji."

"Ke fa da kanki za ki yi floshing ɗin shi idan kin gama.. "Fulo me? Eh lallai yadda za a ji daɗin kwashe 'yan hanjin kenan." Da Aunty B, ta ga ji da shirmen Zinariya fita ta yi daga toilet ɗin. "Ni na rantse ba zan saka wannan abar ba." Ta ƙarasa maganar tare da yin wurgi da shi. Ɗankwalin kanta ta cire tare da rabawa biyu ta cusa ɗaya tare da mayar da ɗayan kanta, tana murguɗe-murguɗen baki ta fito. Ko da ta yi arba da abinci ba ta tsaya tambayar na waye ba ta ɗauka ta fara ci, Aunty B, ta miƙo mata magani tana gamawa suka bar asibitin zuwa masaukinsu. Da yamma suka ɗunguma zuwa asibitin da za a yi wa Salima aiki inda likita ya yi mata gwaje-gwaje tare da ɗora ta a kan maganin kafin nan da kwana biyar za a yi mata aiki. Ita dai Zinariya an barta da yatsine-yatsine saboda warin asibitin ya ishe hancinta. Da lokacin sallar magariba ta yi ta je ta yi za ta yi sallah, Aunty B ta ce. "Babu fa halin yin sallah 'yar nan." Sheƙeƙe Zinariya ta kalleta tare da haɗa kai da wuya tana faɗin. “Kamar ya babu halin yin sallah? Kafurta ni kike son yi?" Aunty B ta ce. "Ai ba maraba, duk wanda yake cikin wannan yanayin bambancin shi da kafiri kaɗan ne... "Yanzu kina nufin na fita daga musulunci ko?"

"Shakka babu." Riƙe haɓa Zinariya ta yi tana faɗin. "Taɓɗijam! Lallai sai na yi shari'a da duk wanda ya yanka min cinya." Zama ta yi shuru tare da rafka tagumi da hannuwa biyu tana tunanin hanyar da za ta bi don ta koma gida, ita gaskiya ba za ta iya ci-gaba da zaman wannan wurin da aka kawota ba. Tana zaune tana mita cikin ranta har ta fara barci a zaune, Aunty B ce ta tashe ta ganin yadda take gyangyaɗi. Bayan kwana biyu ta samu tsarki a cewarta ba za ta fara sallah ba sai ta yi wankan shiga musulunci, haka kuwa aka yi domin sai da ta yi wankan kafin ta fara sallah. Yanzu ta tsiri fita farfajiyar hotel ɗin ne don ta ce ba ta iya zaman wuri ɗaya, saboda baƙin hali irin na madan Salima haka take saka ta wanke musu toilet da gyaran ɗaki bayan kuma akwai ma'aikatan da suke gyarawa, amma haka ta hana su ta ce ita tana da mai aikinta.

"Dan baƙin hali a yi ta saka mutum aiki bayan ga su nan da ma'aikatan su, ko abinci ta ci sai dai ta saka mutum ya zo ya kwashe kwanuka ya fito da shi." Zinariya ke magana tana tafiya har ta fito wajen hotel ɗin, lokacin ƙarfe tara na dare ta tsaya gaban wani shago tare da harɗe hannuwa tana kallon yanda mutane ke ta harkokinsu ba mai shiga sabgar wani.

Gefen shagon ta je ta tsaya tana kallon wuta mai launi da ke juyawa yana haskawa ilahirin kayan shagon, tsawon minti uku tana nan tsaye ba ta ankare ba sai ji ta yi an fisgota da ƙarfi tare da toshe mata baki aka tura ta cikin mota, mutsu-mutsu take yi tana ƙoƙarin ƙwacewa daga riƙon da aka yi mata amma ina, ji ta yi an shaƙa mata abu a hanci wanda tun da ta shaƙa ba ta sake sanin inda kanta yake ba sai bayan kwana uku da aka watsa mata ruwa masu sanyi ta buɗe idanuwa a firgice da ihu, na tsinci kaina cikin wani ɗaki mai girma da faɗin gaske. A lokacin da na yi arba da yara tsarata da waɗanda ba su kaini ba cikin mummunar shiga hankali na ya yi mugun tashi, ina kallon yanda ake yage kayan jikinsu ana duba halittar su, nan na ji cikina ya sake ɗurar ruwa, "Shi kenan ta faru ta ƙare! Ta tabbata dai wannan matar sayar da ni ta yi, wayyo Innata..." Gabaɗaya sai suka juyo suna kallona, matar da na ga tana duba ƙirjin yaran na ga ta nufo inda nake tana ɗaga hannu alamar me ya faru? Kafin ta fara magana da harshen da ba zan iya cewa ga abin da na tsinta cikin maganganunta ba. Mannewa na yi jikin bango yayin da jikina ɗauki mugun kakkarwa.


"Innalillahi ina aka kawo ni? Ina ne nan?" Tambayar da nake ta yi kenan cikin ihu da hayagaga, amma duk cikin waɗannan matan babu wacce ta yi zarrar ba ni amsar da nake son ji, ita tana nan tana wasu yarukan da ban gane kansu ba, yayin da ni ma nake yaren da na fi ƙwarewa akanta, ina kallon yanda ake yi wa yara 'yan ƙananu yara alluran da ban san ko na mene ne ba.

Ɗirka-ɗirkan mata ne guda biyar masu ji da ƙarfi suke finciko yara tare da danna musu allurori, idan kuwa ka ƙi ba da haɗin kai da duka ake haɗawa, yau ni na ga bala’in da ban taɓa gani ba tun da nake a rayuwata. Ina kallo da zaran an gama tsikara musu allura zubewa suke yi a ƙasa suna ihu da birgima wanda daga ƙarshe sai su ɓingire da barci daga haka sai a ɗauki yaran a fita da su zuwa wani ɗaki inda nan ne za a kula da su a dinga ba su cimar da zai ƙara musu lafiya ya sake fitowa da halittar jikinsu. Cikin sati biyu, kafin a fita da su zuwa wani gida inda a nan ne za a baje kolinsu kowa ya zaɓi wacce ranshi ya yi masa.

Cewar matashiyar da ke zaune a gefe na, cike da razani mai haɗe da ɗumbin mamaki nake kallonta sannan na matso kusa da ita ina faɗin. "Ke Bahaushiya ce?" Ture ni ta yi da hannunta tare ta sunkuyar da kanta ƙasa tana faɗin. "Idan kina son kanki da lafiya karki yarda ki zo kusa da 'yar'uwarki ko ki nuna jin ƙai da tausayinki gare ta." Idan kuwa aka fahimci mun san yaren juna ko wata shaƙuwa ta fara shiga tsakaninmu shi ma wannan wani hukunci ne mai zaman kansa. Dan haka za a wurga ki a ɗakin gardawan maza su yi miki wulaƙancin da sai kin kai wata kina jinyar kanki, gwara ki ci gaba da yi musu yaren da kika iya kafin ki fahimci nasu yaren." Shuru na yi ina juya wannan mugun lamarin cikin zuciyata. Sai da mata suka fita kafin ta ɗago kai, nan na ƙare mata kallo, ita ma dai yarinya ce amma za ta kai 19 zuwa 20. Ga ta fara tass kyakkyawar Bafulata, saɓanin ni da nake nan baƙa.

"Yau kwananki biyar kina cikin barcin da aka saka ki, ke kuwa wane ganganci ne ya kawo ki wannan duniyar da take cike da zalunci haɗe da son zuciya? Kin san rashin imanin da ake nunawa 'ya'ya mata kuwa musamman mu da muka fito daga Nigeria? Me ya kawo ki Japan har da za ki faɗa harkan karuwanci... "Ya Subhanallah! Karuwanci? Ni da nake Egypt me ya kuma nake yi a nan? Ni fa daga tsayawa a bakin shago na ji an toshe min baki tare da fisgoni ban sake fahimtar komai ba sai yanzu da na buɗe idanuwana na tsince ni a nan."

Wani irin dariya ta yi tare da faɗin. "Sayar da ke fa aka yi, kamar yadda ake safara daga Nigeria haka ke ma aka yi miki... "Ba shakka wannan muguwar matar za ta aikata kamar yanda ta faɗa."

"Wace ce?"

"Madam Salima, matar da nake yi wa aiki, mun zo ne da sunan za ta karɓi magani ne ko za a mata aiki ne ni ban sani ba, wato shi ne wannan matar za ta yi safarata zuwa nan, shi ne za ta buga mini tambarin da har na mutu na bar wa dangina da zuri'ata mummunar tabon da ba zai taɓa goguwa ba kenan? Wai mai ya sa imani ya yi wa mutane ƙaranci ne?"

"Ba ki da iyayen da za su tsaya miki ne?"

"Ni da nake 'yar talaka, daga dangin uwa har na uba, Innarmu ke ɗawainiya da mu domin babanmu ba ruwan shi da sauke nauyin iyali, Innarmu ke fita ta nemo mana abin da za mu ci a haka ta saka mu makaranta mu huɗu, kin san hannu ɗaya ba ya ɗaukar jinka, dole dukanmu karatun ya tsaya daga Firamare, yayuna mata kowa na neman kuɗi don a taru a ruwafa juna asiri wannan dalilin ya sa ni ma na fara aiki fa duk don abin ya yi wa Innarmu sauƙi, Innarmu na son mu, haka ma babanmu ba ya ƙaunar wani abu ya taɓa mu amma hakan fa ba shi zai sa ya saya miki ko da takalmi ba ne idan sallah ta zo, duk ya bar ɗawainiyar kan Innarmu. Ban san halin da za su shiga ba idan suka fahimci ba na nan."

Numfasawa na yi kafin na ci gaba da faɗin. "Babanmu ba zai taɓa barin madam Salima ba muddin ya ji labarin ta sayar da ni, domin kuwa za ta sha terere dan duk inda ya zauna sai ya yi wannan batun."

Kallon matashiyar na yi jin ta tuntsure da dariya. "Ba fa zai iya shari'a da masu kuɗin nan ba, ƙarshe ma za ta iya cewa ita ba ta ma san

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login