Showing 6001 words to 9000 words out of 39491 words
Chapter 3 - Zinariya Book Compelet Novels By Aysha JB
wata mai aiki ba ke dai ki yi addu'ar Allah ya fitar da ke.
Littafin Zinariya na kuɗi ne akan ₦500. Za ku tuntuɓi wannan Number ta WhatsApp domin mallakar naku.
09079740079
Maman Faruk.
[30/11, 3:49 pm] ༺𝐀𝐘𝐒𝐇𝐀 𝐉𝐁༻: *...ZINARIYA*
Romantic🌹
®
AYSHA JB
Farin Jini Writer's Asso..
7&8
Gyara zama na yi ina kallonta sanan na ce. "To ke yaya sunanki? Me ya kawo ki nan? Su kuwa waɗannan azzaluman babu hukumar da za ta dakatar da su ne ko ta kama su? Oh ni na shiga uku, shi kenan ba zan sake ganin Innarmu da babanmu ba? Allah sarki yaya Fadila, Allah sarki yaya Radiya shi kenan an ɗauke muku 'yar auta... "Kina da abin dariya wallahi, bari na ba ki labarin wannan ƙasar da ta yi ƙaurin suna. A Japan, ana fataucin mutane ne da nufin yin lalata da bautar da su kamar bayi a ƙasar, Japan ƙasa ce ta asali, wadda ake yawan ziyarta, haka kuma ƙasa ce da ake safarar 'yammata musamman masu ƙananan shekaru don mai da su karuwai a yi lalata da su ba bisa son ran su ba.
'Yan ƙasar Japan, musamman mata da ake yin safarar su ta hanyar mai da su karuwai da ƙarfi da yaji a cikin Japan da kuma zuwa wasu ƙananan ƙasashen waje. Ana safarar waɗanda suke daga ƙasashen waje zuwa cikin ƙasar japan. Yara kanana, da mutanen da suka fito daga dangi marasa ƙarfi wato waɗanda talauci ya musu katutu sun fi fuskantar matsalar fatauci. Ana yaudarar waɗanda aka yi fataucinsu da manufar kasuwanci, ana yi musu barazana da tilasta musu yin karuwanci. Masu safarar mutane
waɗanda suka kamasu suna ƙwace fasfo ɗinsu da takardun banki da duk wasu muhimman takardun da suka shafe su, ana yawan ɗaura musu basussuka don su biya su fanshi kansu daga halin da suke ciki. Ana raunata su idan suka ƙi amincewa, kina kallon yanda ake dukan waɗannan yaran, to haka suma manyan ake musu, sannan ana yi musu barazanar kisa kuma da yawa daga cikin waɗanda aka yi safarar su suna kamuwa da cututtukan da ake ɗauka ta hanyar jima'i, da fyaɗe, kuma suna rayuwa a cikin yanayi mara kyau rayuwar ƙunci da wahalhalu. Wasu idan suka samu ceto ma'ana idan suka tsira suka gudu suna fuskantar wariya, daga jama'a a dinga ƙyamar su. A irin wannan yanayin baƙinciki kan sa har suna yunƙurin kashe kansu. Akan ɗauke su hotuna a lokacin da suke tsirara sai a watsa hotuna a yanar gizo don muzanta su". Riƙe haɓa Zinariya ta yi tana faɗin. "Bala'i! Lallai ana shege a duniya, abin da muke ji a labarai yau dai gamu cikin yanayin, to su kuma masu fataucin daga ina suke?"
" Masu fataucin maza da mata a Japan sun fito ne daga wurare dabn-daban. Masu safarar mutane galibin su membobi ne na ƙungiyoyin masu aikata miyagun laifuka, suna haɗuwa ne su cure waje ɗaya don samun sauƙi wajen aikata miyagun Laifuka. suna da alaƙa da ƙungiyoyi da dama, suna da ɗaurin gidi daga fannin manya 'yan ƙasan, domin suna ba su kaso mai tsoka daga abin da suke samu. Wannan dalilin ya sa suke gudanar da harkokinsu hankali kwance ba su da haufin komai domin babu wanda zai yi musu shamaki ko karan-tsaye bisa kasuwancinsu. Hatta gwamnatin ƙasar muryarta ba ta isa ta yi amo ba... "To amma ke mai ya fito da ke? Ki ba ni labarin ki, yaya sunanki?"
"Hinduu, sanin labari na kuma ba zai ƙare ki da komai ba. Don gudu na yi daga gida na shigo duniya saboda za a tilasta ni yin rayuwa da wanda ba shi ne zaɓin zuciyata ba, ba nan na fara zama ba. Sai da na yi rayuwa a Thailand kafin ni ma aka sayo ni zuwa nan." Jinjina lamarin Zinariya ta yi cikin zuciyarta kana ta ce. "Kuma kema an yi miki allurar ne?"
"Ba ki ji na ce miki sai da na fara rayuwa a Thailand kafin na zo nan ba? Ai tun a can an riga da an yi mini komai, har ciki na yi aka cire, daga ƙarshe aka yi mini tsarin iyali.. "Aka cire ciki kuma? Ta yaya? Mene ne kuma tsarin iyali?" Zinariya ta faɗa cike da zallar yarinta. "Ina nufin ni na yi mu'amula da maza ba so ɗaya ba ba so biyu ba har na samu ciki na haihuwa, sai aka zubar da shi, aka kuma yi mini allurar da zai hanani ɗaukar wani cikin." Shuru Zinariya ta yi domin duk ba ta fahimci abin da Hindu ke magana akai ba. "Aka yi miki ciki haka na haihuwar yarinya, kuma se aka zubar da cikin?" Ta faɗa tana dafe cikinta tare da ɗago hannu tana kwatanta yadda ciki yake idan ya yi girma ya fito. "Oh ni Zinariya ko yaya ake yin cikin oho" Kallon Zinariya Hinduu ta yi sosai domin ta lura har yanzu ba ta ma gane kan maganar da take mata ba. "Ba ki san yanda mata da miji ke kwanciyar aure ba?" Girgiza kai Zinariya ta yi alamar a'a, "Kin je islamiyya kuwa?" Zinariya ta ce. "Wannan ai tambayar raini hankali ce, ni tun ina shekara sha biyu na yi saukar allo." Dariya Hindu ta yi sannan ta ce mata. "Okay."
Zinariya ta ce. "Yawwa na tuna."
Hinduu ta ce mata. "Me kika tuna?" Zinariya ta ce. "Kin ce an miki allura a can Telan yake ko ina? Kuma nan ɗin ma sai an yi miki wani allura?"
"Duk cikin maganar iya abin da kanki ya iya riƙewa kenan?" Gyaɗa mata kai na yi, "Ai nan za su duba kafin su yi min. Idan suka fahimci ni ba cikakkiyar budurwa ba ce, ma'ana na yi sex da wani na miji, za su kaini ɗakin 'yanci ne kawai a yi mini gyaran jiki sai su fita da ni zuwa inda za a zo a ɗauke ni... "Me ye six kuma? Idan aka ɗauke ki ina za a kaiki?"
Hinduu ta fahimci Zinariya ba ta san ma komai ba a harkar, wannan dalilin ya sa ta yi shuru zuciyarta cike da tausayin Zinariya, dan ta san muddin ta shiga hannun mazan garin Japan fasa ta za su yi, ba su iya bin mace da sauƙi ba.
"Kin yi shuru...
"Shh! Yanzu za a kawo mana abinci." Aikuwa tana rufe baki sai ga shi an buɗe ƙofar tare da shigowa da abinci, aka ajiye ma kowa na shi. Ga dai abinci lafiyayye amma ko burge ni bai yi ba. "Ki dai ci abinci, dan in kika ƙi ci haka za ki zauna da yunwa." Cewar Hinduu, kaɗan na tsakuri abincin na ture sauran.
Na so mu ci gaba da hira amma sai Hinduu ta ce barci za ta yi, haka na ƙyale ta, washegari ma haka wannan gardawan matan suka zo suka ɗibi yara kusan goma dan gaskiya muna da yawa. Ranar da na cika sati cikin yaran da aka ɗiba har da ni, lokacin da aka zo ɗaukar sunana zuciyata ta tsinke, hankalina ya yi mummunar tashi domin na tsani yanda suke yage rigar mutum suna duba ƙirjinshi, cike da tsoron na kalli Hindu kafin a zo ɗauka na murya na rawa na ce. "Na shiga uku ina za a kaini?"
"Za ki shaƙi iskar 'yanci mana, ke kam ki kwantar da hankali za mu haɗe ne in sha Allahu da zarar na fito." Daga haka Hinduu ta ɗauke kai ba ta sake min magana ba. Da suka zo ɗaukana na fara turjewa aikuwa matar ta ɗaga hannu da niyyar kwaɗa mini mari, nan na tsura mata idanuwa tare da tamke fuskata na tsuke baki ina jiran saukar mari, amma sai na ga saɓanin haka, cikin zuciyata na ce wallahi da kin mare ni kin ga yanda ake hauka. Yage himar ɗin jikina aka yi wanda tun da na zo da shi nake nanuƙe a jikina, ko wanka na yi ba na yarda na cire shi. Ina ji ina gani aka barke rigar jikina, nan suka ga ƙirjin sulum ba komai sai ɗan kan da ya fara tasowa. Kallon juna suka yi suna yare ga dukkan alamu sun yi mamakin ganin babu komai a ƙirjin. Haka suka danna mini allura har guda biyu, na daɗe ina jijjiga tare da jin gaɓɓai na suna sakewa kamar wanda ake kwance mini su kafin wani wani masifaffen barci ya yi awon gaba da ni. Sai tsakiyar dare sosai na farka nan na tsinci kaina cikin wani ƙayataccen ɗaki inda na ga 'yammata bila adadin suna ta harkokinsu, ina ta kallonsu ganin yadda suke ɗaure da ɗan ƙyallen ƙirjinsu yayin da suke sanye da wani ɗan mitsitsin siketi, tagumi na yi ina kallon galewar rayuwa dan wallahi ko gama saukowa cinyarsu siketin ba ta yi ba. Wani irin lafiyayyen abinci aka kawo min wanda tun da nake ban taɓa ganin irin shi ba, nutsuwa na yi na ci sosai ina karon 'yammatan ɗakin, wata mata ce ta zo ta riƙe hannuna zuwa toilet nan aka shiga wanke ni ba ji ba gani, kusan sati biyu ana min wani irin masifaffen gyaran jiki tare da wanke ni da ruwan turaruka. Gashi na da yake tufke aka warware shi, nan shi ma aka gyara min shi duk da ba wani yawa ne da shi ba amma yana da tsayi dan ya sauko har kafaɗata. Ƙirjina kuwa saboda fitinar shi da aka yi da shafe-shafen mayuka da magungunan dole ya fara fitowa har kana iya ganin shi ta cikin riga saɓanin da ba a iya ganin komai.
Ni kaina ƙaunar kaina nake yi wallahi ganin yanda na yi masifar kyau, jikina har wani sulɓi yake yi, sai kallon kaina nake ina sake latsa fatata da ta murje ta yi fresh sai ka ce baƙar baturiya. (Ni kuwa na ce su Zinariya an samu na yi, sai a yi ta latsa jiki) Da dare ina zaune bayan na gama cin abinci na ɗauki wani riga mai ɗan mutunci daga cikin kayan da aka ba ni na sakawa ina ƙoƙarin sakawa sai ga matar da take yi mini gyaran jiki ta shigo ta karɓe rigar tare da miƙo min wasu kaya, buɗe kayan na yi na kalla tare da kallonta. "Me ye wannan? Me zan yi da ita?" Da ta fahimci abin da nake faɗa sai ta karɓi kayan tana gwada mini yanda zan saka. Innalillahi na ce ganin irin mugun kayan da ke jikina wanda ba shi da maraba da gidan sauro. Tsirara ziryan, dafe ƙirji na yi tare da kallon madubi ina faɗin. "Na shiga uku ni Zinariya, yau kuma haka na zama?" Jan hannuna matar ta yi zuwa waje inda aka saka ni cikin wata mota.
****
Egypt.
Neman duniyar nan a yi wa Zinariya amma ina, babu ita babu labarinta. Hankalin Salima ya tashi sosai amma da ta tuna Zinariyar ba zaman Egypt ɗin take so ba sai ta lauya zancen tare da faɗin dama can ba son zaman take yi ba shi ya sa ta gudu. Da wannan kalaman ta share batun Zinariya. Aunty B kuwa cewa ta yi. "Amma Salima sai yau na sake tabbatar da ba ki da hankali da imani, ta yaya 'yar mutane za ta ɓata sannan ki zauna hankalin ki kwance? Me za ki cewa iyayenta?" Salima ta ce. "Me kuwa zan ce musu wanda ya wuce na faɗa musu 'yar su guduwa ta yi, ni na ɓatar da ita? Dan Allah Aunty B ki ƙyale ni da wannan maganar." Mamaki ya cika Aunty B ta kasa yin wata magana, daga ƙarshe haka suka dawo bayan gama aikin da za a yi wa Salima.
Dawowarta ba jimawa ta sa aka kawo mata 'yar aiki, amma ko wata ba a rufe ba ta kore ta saboda rashin kamun kan yarinyar, a haka ta dinga canja masu aiki ta kasa samun ƙwaƙƙwarar da za ta mata aiki ba tare da sun samu saɓani ba. Wani lokaci ta kan tuna Zinariya, duk da tana shiririta amma a hakan take mata aikin da ranta yake so, sai da babu ita take jin takaici, da zarar kuma ta tuna irin rashin kunyar da ta dinga yi musu sai ta ji gabaɗaya haushinta ya rufe ta, take kuma take kore tunanin Zinariyar daga zuciyarta.
****
Uwaisu Sadi, wanda ake yi wa laƙabi da Malam Uwaisu haifaffen garin alƙaleri ne da ke jihar Bauchi, wanda tun fitowarshi cin rani bai sake waiwayar gida ba, yana da ilimin addini da na zamani wannan dalilin ya sa ake kiran shi malam Uwaisu kasancewar wani lokaci har bugun ƙasa yake yi kafin ya yi aure, bayan auren shi da Mardiyya sai ya daina da ya fahimci ba ta son sana'ar. Nan ya shiga 'yan buge-buge yana samo musu abin da za su rufawa juna asiri kasancewar ita ma iyayenta ba masu ƙarfi ba ne, amma duk da haka suna tallafa mata musamman da suka lura da ba wani aiki Uwaisu yake yi ba. Ita ma ba ta zauna haka ba, inda take sai da kayan miya a gida, a haka suka fara tara iyali inda hidimar ta fara yin yawa wanda daga ƙarshe Uwaisu ya zare hannu ya barta da ɗawainiyar yaran. Tsakanin Fadila da Radiya tazarar shekara guda. Fadila shekararta 19, Radiya 18, sai mai bi mata Zinariya mai shekara 16, kafin Ahmad wanda suke kira Madu shi kuwa shekarar shi 12. Yaran sun taso da farin jinin jama'a.
Zinariya da Madu sune tsagerun gidan, hatta 'yan unguwa ba su bar su ba, ga shaƙiyanci da zolaya domin kuwa in suka saka mutum a gaba da zolaya haka za su mayar da shi mahaukaci, ga shegen kafiya da naci idan ka taɓo su. Malam Uwaisu na ƙaunar Zinariya sosai dan wani lokacin yakan saya mata abu ba tare da ya saya wa 'yan'uwanta ba. Wannan dalilin ya sa ba su jituwa da Madu, dan kishi yake muddin Baban su ya yi wa Zinariya abu bai yi mishi ba. Cikin haka watarana Zinariya ta ce lallai za ta fara aiki tun da su Radiya su ma suna gidan aiki, amma sai Innar su taƙi, tana ganin Zinariya ta yi ƙankanta da aiki, da ta dage lallai sai tana so ne ya sa Innar su amincewa.
Ajiye wayar Inna ta yi tare da ƙwalawa Madu kira. "Je ka duba in babanku ya dawo ku taho tare." Bai kai ga ƙarasa fita ba suka ci karo da juna. "Yawwa baba da ma Innarmu ce take neman ka."
"Ya labarin Zinariya? Ka je gidan ka duba ta?" Hannu Malam Uwaisu ya saka cikin aljihun rigar da ke jikinshi tare da tatare rigar ya zauna yana faɗin. "Ke kin ji maganar banzar da matar ta turo mai gadi ya faɗa min ne a lokacin da na je neman Zinariya?"
"Me ta ce?"
"Cewa ta yi wai wacce Zinariya ake nema? Shi ne na ce kamar yaya? Wai ai tun watanni uku da suka wuce Zinariya ta gudu daga gidan.... Zubur Inna ta miƙe dafe da kirji tana sallalami.
Littafin Zinariya na kuɗi ne akan ₦500. Za ku tuntuɓi wannan Number ta WhatsApp.
09079740079
Maman Faruk.
[30/11, 3:49 pm] ༺𝐀𝐘𝐒𝐇𝐀 𝐉𝐁༻: *_ZINARIYA...🌹_*
Farin Jini Writer's Asso..
*For you Ishaq Nasir Abdallah Nasrulla 💔🌺*
9&10
"Ai ki kwantar da hankalinki Mardiyya ƙariyar iskanci suke ji, ba taƙamar su dukiya ba? Na san matakin da zan ɗauka dan wallahi sai sun fito min da 'yata, in ma sun je sun sayar da ita ne duk za mu sani amma wallahi Zinariya sai ta fito ba za ta salwanta ba, ai mai kamfanin S.S ne uban gidan nata." Zama Innarmu ta yi tana yarfe hannuwa tare da fashewa da kuka tana faɗin. "Wayyo Zinariya, wayyo 'yata, Allah ka dawo min da ita lafiya, Allah ka tsare min 'yata." Fita malam Uwaisu ya yi yana kaɗe babbar rigar shi bai zarce ko'ina ba sai police station, bai tsaya ina nan ba ya nemi masu watsa labarai nan aka dinga ɗaukar shi yana jawabin abin da ya faru, take gari ya ɗauka lungu da saƙo zancen ɓatar Zinariya ya baza ko'ina, nan 'yan jaridu suka buga labarai tare da ɗora hoton Zinariya da S.S. Inda ake zargin shi da ɓatan mai aikin gidan shi. Iyayen Zinariya na cikin damuwa da ƙunci musamman da hukuma suka wanke S.S daga zargin da ake yi mishi saboda rashin ƙwaƙƙwarar hujja dan ya ce bai san batun ɓatan wata 'yar aiki ba.
*** **
Zare gilashin idanunshi ya yi tare da miƙewa da laptop a hannunshi ya nufi ɗakinta daidai ta fito daga wanka tana ɗaure da towel ta ji an turo ƙofar ɗakinta. Waigowa ta yi da murmushi tana faɗin. "Saifu yau kai ne a ɗakina... Shuru ta yi ba tare da ta ƙarasa sauran maganarta ba ganin ya nufi kan bed ɗinta tare da ajiye laptop ɗin ya harɗe hannuwa a ƙirji yana binta da kallo fuskarshi a haɗe. "Wani irin shashanci ne wannan Salima? Akan wani dalili ne za a dinga yaɗa hotona a social media ana faɗan wasu maganganu? Girma kike amma kullum cikin jawo min magana kike, kullum case ɗinki da masu aiki, abin bai tsaya ina nan ba har ya zo kaina yana shirin shafan kasuwanci ne? Ita yarinyar da ake maganar na ɓatar da ita yaushe ta yi aiki a gidan nan? Na santa ne da za a dinga alaƙanta ni da ita?" Matsowa ta yi kusa da shi tare da faɗin. "Duk fa ba abin ɗaga jijiyar wuya ba ne, wannan wata ƙaramar alhaki ce kawai ban ma san yanda aka yi har maganar ta je media ba amma zan yi wa abin tufkar hanci, bari na kira gidan jaridar... "Wait malama." Tana ƙoƙarin ɗaukar wayar ta ji furucinsa. "Saifu malama fa na ji kana cewa? Me ya shiga kanka ne yau da ka zo kana kiran sunana gatsau? Hakan bai maka ba har da kirana da wata malama... "Tambayar ki nake wata yarinya ce wannan?" Ya faɗa cikin ɗaurewan fuska alamun babu wasa. Dafe kai Salima ta yi cikin alamar gajiyawa da zancen sa kafin ta zo ta kamo shi da nufin su zauna saman bed ɗin tana faɗin. "Kana ji ne Saifu, ka bar wannan maganar na ce