Showing 1 words to 3000 words out of 82684 words
Chapter 1 - Sirrin Daukaka Book Complete by Aisha Jb Mrs Danshuwa
UMMI JB:
♡SIRRIN ƊAUKAKA...
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..*
_♡F.J.W.A
'''Wa sallallahu ala Akaramil Mursalina Aj'main Muhammadin wa'ala alihi wa Sahabihi
wa,sallam'''
PAGE ONE..
"Baba burina kasha kafini bukata dan Allah." kawar da kanshi ya yi gefe duk da jikinshi baya
motsi sakamakon ciwon dake tattare da shi bakin shi ma a karkace yake ƙwalla ne ya gangaro
masa da sauri ta ajiye kofin tana share mishi hawaye "Baba na ɓata maka rai ko? Toh kayi
hakuri ln Sha Allahu bazan ƙara ba." A hankali ya soma magana "Jiddah ni baki min komai ba,
hasalima bana buƙatar komai ya shiga bakina.. da sauri ta dakatar dashi "kar kace haka Baba
in baka shaba maganin fa? nafi son lafiyanka fiye da komai domin kai da mama kaɗai kuka
ragemin kune gata na! kunne bangon da in na jingina ajikinku nake jin daɗi ku kaɗai ne farin
cikina kayi hakuri kasha kaga jiya bakaci komai ba."
"Jiddah ina ganin gazawata! ni ya dace in fita in nimo muku abinci ni yadace na muku komai
keda mahaifiyarki Amma dubi halin da nake ciki kalla fa? jiddah na gaza muku wannan
abubuwan gashi dangina wanda ya kamata su tsaya su temakeni duk sun gujeni kowa guduna
yake sabida banida kuɗi ni talaka ne!.." kukane ya kwace mishi Mama da fitowarta kenan daga
banɗaki ta karaso tare da durkuwa a hankali ta ajiye butan hannunta dakyar ta miƙe sakamakon
cikin jikinta dayafara tsufa "Kayi hakuri Allah yana sane damu kuma wannan jarrabawace bawai
don baya sonmu bane a'a ya yi haƙan ne don ya gwada imaninmu kuma a kullin muna gode
masa Allah ya ubangiji Allah kai kayi Adamu kayi hawa'u Allah bamu da kowa bayan kai
Ubangiji ka sassauta mana Allah ka kawo mana agaji Alfarman wannan rana ta juma'a kabawa
Mijina Usama lafiya" jiddah dake jikin mahaifinta ta amsa da "Ameen mamana. "
Dafa cikinta tayi tare da girgiza kai rabonta da abinci tun jiya shima kanzone wanda jiddah taje
makota tayi wanke wanke ta samo musu Allah kenan! me yanda yaso da bawanshi "Asama'u
ɗauki kokon nan ki sha." mama tace. "a ah Usama kai yafi dacewa daka sha domin kasha
magani." Usama yace "Asma'u bana son jayayya kin fini bukata bani da burin da yawuce ganin
farin cikin iyalina daga shi se bashin Mu'azzan dake kaina inna roƙon ka Allah ka billomin da
hanyar da zan cika wannan burin nawa kafin mutuwata.. "kabarmu dawa usama?. "Akwai
Allah.."
Juyo da kanshi yayi ga Jiddah "ɗauki ki baiwa mahaifiyar ki Allah ya miki Albarka ubangiji ya
tsaremin ke da mutuncinki Allah ya rabaki da sharrin samarin zamani!." ɗaukan kunnun tayi ta
nufo mahaifiyarta dashi "buɗe bakinki nabaki mamana." ba musu ta buɗe bakinta domi Ɗan
cikinta harya fara motsi tsaban yunwan dake cinta cokali kurɓa uku taman kokon ya kare cire
kofin jiddah tayi a bakinta Ahankali Asma'u ta lumshe idonta hawaye na gangaro mata wani irin
yunwane ya taso mata.
Wurgar da kofin Jiddah tayi tana kiran sunanta "Mama mamana meya sameki?." cizewa tayi
tare da faɗin "bakomai Jiddah..."
Shuru suka zauna chan Jidda ta miƙe butan da mahaifiyarta ,ta ajiye ta ɗauka roban fentin da
take zuba ruwa ta nufa shuru tayi sakamakon ganin bokitin ba ruwa "Sauran ruwan na zaga
dashi." cewan Mama bokitin ta ɗauka "bari inje in samo ruwan" fatan Alkhairi suka mata bayan
ta fita Asma'u ta matso jikin mijinta kwantar da kanta tayi a jikin taburman da yake kwance "lna
son shafa fisƙanki babu halin haka ko zaki temaka ki ɗauki hannuna zuwa ƙan fusƙan taki?"
wani irin marayan kuka tasa a hankali sautin kuƙan nata yake fita hannunshi ta kama takai
saman fisƙanta amma lna ko motsi bayayi dalilin haka yasa ta kara sautin kuƙan nata "meyasa
haka! meyasa wasu mutanen basa duba gobensu! meyasa wasu mutanen suke manta alkhairi
? yanzun sakamakon temakon kenan? usama duk kai kajawo mana wannan masifar meyasa ka
Auro mana masifa jubeni da yarintata na koma tsohuwa kalleni... kalli cikina wai yau mune
abinda zamuci yake gagarar mu? me muka mata?, takwashe komai Allah kana gani ƴata ba
makaranta ko ɗaya Ƴar da zamu ciyar amma i'ta take fita tasmo mana abinda zamuci Yarinyar
da bata huci wanka ba amma wai yau i'ta ke ɗawainiya damu Allah ka kawo mana agaji..
"Asma'u kiyi hakuri tausayinta naji gani nayi kowa ya gujeta gani nayi ta fara fusƙantar tsana da
tsangwaman mutane kowa ya gujeta bansan haka ze kasance ba na nufeta da Alkhairi amma ta
saka min da sharri ta rabani da Ɗana ta ruguzamin komai nawa kalli yanda ta mayar dani,
*LAIFINA NE"* (Shima sabon buk ɗina ne yana nan tafe da yardan Allah),
"Asma'u." ɗagowa tayi taga shima yana hawaye share mishi tayi sannan i'tama ta share na
fisƙanta "Jin yanayin da ka kira sunana kaɗai ya shedamun magana kakeso kayi dani me
muhimmanci koma menene in na Addu'ar Allah yasa kunnuwana suji Alkhairi.." "Tabbas
maganace zamuyi wanda nake so kiyi mata kyakkyawan fahimta ki hangi nesa karki juyawa
akalan maganata zuwa baya , ina nufin karki tuna baya domin inhar kikayi haka sheɗan ne ze
rinjayeki ki bijiremin wanda inhar haƙan ta kasance bazanci daɗi ba nayi iya tunani da hange
hange Asma'u bani da hanyar da zan biya Mu'azzan dubu talatin dalilin haka na yanke
shawarar.. "shuru yayi yana nazarin yanayin da zata ɗauki maganan bezata ba, yaji tana faɗin
"Ka yanke shawarar bashi Auren Hauwa'u koba abinda kakeson cewa ba kenan kayi shuru
kanajin tsoron faɗa domin bazan amince bako? shifa mutumin nan baka sanshi ba, babu abinda
kuka haɗa matarsa uku kasuwancine ya haɗaku gani nake kuma be damu da kuɗinsa ba domin
yanada wanda sukaci uban dubu talatin Hauwa bazata iya ratsa mata uku ta zauna ba wallahi
na tabbata zata ci baƙar wahala yarinyar da bata san menene rayuwa ba watan gobe fa Hauwa
zata shiga sha-huɗu.." katseta yayi "wake sama da wani cikin neda ke?." sunkuyar da ƙanta tayi
kasa "wakeda ikon zab'arwa Jiddah mijin Aure? cikin nida ke wake da iko da Me-Jiddah? akwai
wani bayan ni akwai abinda uba shine adon ƴar sa, mutumcin ƴa mace Gidan mijinta.."
......."Tabbas Da Uba ake Ado, amma ka gane man, Hauwa bazata iya ɗauƙan nauyin da kake
shirin ɗaura mata ba, kayi hakuri mijina bawai inna jayayya dakai bane a'ah halin da zata tsinci
kanta nake tunani Ya zanyi? Na amince..." bata rufe bakinta ba taga mutane suna shigowa
"Lafiya? ya zaku shigo mana har ɗaki ba niman izini?.." maƙalewa sauran maganan yai
sakamakon ganin Maigidan dasuke zaune a ciki hannu ya miko mata cikin rawan murya tace
"Kayi hakuri Ado.. "Ke Dakata bashi ya kawoni ba kud'i zaku bani banja da tsayi ba, shekara ta
zagayo kunce na muku uziri nabarku kun sake wata biyar Kai! Gaskiya ina bukatar kud'i ko
abarmin Gidana, domin zan zuba sabbi 'Yan haya"
"Ado kasake Kara Mana lokaci wallahi a halin yanzun ko ficika bazaka samu ba abincin da
zamuci ma ya gagaremu.." Ado yace abincin da zakaci ma ya gagareka bare dubu takwas ku
kwashe komatsansu ku watsar su fita min daga Gida wannan ai zance banzane! 'yan
kayayyakinsu suka shiga kwashewa suna watsar dasu a kofan Gida "Dan Allah kiyi hakuri karku
tozartamu ka dubi Allah ka dubi Halin rashin lafiyan da Mijina yake ciki... "Ku jasu ku fitar mun
dasu daga Gida bana son Kara ganinsu Kona sak'an d'ayane" (Nayi Alkawari insha Allahu babu
turanci a littafina sede in ya zama dole ne, dolenma me k'arfi).
Tafiya take riƙe da bokiti Gurin d'iban ruwansu na tuka tuka, ta nufa nan ta tarar da Gurin cike
da mutane Fam shuru ta tsaya tana tunanin yanda zata tsaya har layi yazo k'anta ga Halin da
iyayenta suke ciki matsowa tayi Kusa da Yarinyar da layi yazo k'anta "Ayya 'yar uwa dan Allah ki
temaka ki zuba min nabar Gida IYAYENA duka babu me gamsheshshen lafiyan jiki." Cikin
tausayawa Yarinyar ta karb'i bakitinta ta Tara mata cik'e da murna Jiddah ta Mata godiya
sannan ta shiga kok'arin d'agawa har ta d'aura a k'anta "Chabd'i jan ai wallahi Baki isa ba Taya
zakiso a Bayan mu sannan kije kid'iba ruwa ai wallahi kinyi kad'an.." yarinyar data zubawa
Jiddah ruwa tace "haba Baraka ki dubi Halin da take ciki dan Allah ki rage niman fitina Hauwace
fa wanda Da, muke makarantar Allo tare kafin daga baya Allah ya jarrabe mahaifinta da rashi
karatunta ya tsaya a halin yanzun ma Yana kwance baya motsi ai ko don Haka kya barta taje
Gida." tsalle baraka tayi "Ke Zubaida ban tambayeki ba, surutu chaaa kaman wani kanari Ina
ruwana da jarabta waya jawomusu ba ubanta ba ruwan Nan Kuma wallahi bazaki tafi dashi ba."
Ture bokitin K'an Jiddah tayi take ya fashe ruwan ya zube a kasa Durkusawa Jiddah tayi tare da
fashewa da wani i'rin marayan kuka taga samu taga rashi, wannan tozarcin dame yayi Kama?
D'agowa tayi ta kalli Baraka ga mutanen gurin Kowa na tur DA abinda tayiwa Jiddah "Ku barta
daman haka rayuwa take wannan d'inma yana dagacikin jarrabawan DA Allah ya rubuto mana
kije bazan ce Miki komai ba Allahn dayayimu shi kad'ai yasan huk'uncin daze miki ni ban i'sa
namiki Abinda Allah be miki ba." Tana kuka ta karasa maganan tattara bokitin tayi tasoma tafiya
Zubaida tace "Hauwa kiyi hakuri dan Allah ga ruwana ki d'auki D'aya." Carab Baraka tace
"Wallahi bazata d'auka ba aje a Haka gayyar tsiya Wanda talauci ya Kare musu..." Juyowa
Jiddah tayi tare da fad'in "Me kud'i da talaka duk Allah ne yayisu! Kuma babu Wanda yafi wani a
Gurin Ubangiji Bayan Wanda yafi jin tsoronsa da kiyaye dokokinsa Alhamdulillah mu
talakawane Kuma bamu dogara da kowa ba se Allahn dayayimu bawai bayason mu bane
yayimu a talakawa sedon ya gwada yanda karfin imaninmu yake kefa? Uban naki karkashin
mace yake mijin tace! Se abinda uwarki take so yake Mata jikinsa na b'ari ban fad'i hak'an dan
ranki ya b'aci ba, in kinji zafin maganata kiyi hakuri Zubaida nagode sosai da tausayawanki
gareni." Tafiyarta tayi Baraka ta kudunduma wata uwar ashar Wanda ni Aysha bazaku jishi
abakina ba, domin yafi k'arfi na.
"Meye abin damuwa da zagi data Miki ,Bayan ke Kika fara? Ai wallahi Nan gaba duka zakisha
Allah ya temakeki Hauwa yarinyace me hakuri wallahi na tabbata da watace Sekin kwashi
kashinki a hannu kai lna amfanin fitina?." Jiddah tana tafiya rumgume da fasassun bikitinta, tana
kuka a Haka har ta karaso anguwarsu tun daga nesa ta fara ganin mutane a kofar gidan da
sauri ta karaso Mama ta gani Kusa da Mahaifinta tana kuka Bata San lokacin da tayi watsi da
bokitin ta karaso gurinsu ba "Baba Mama lafiya meya samu samu baba naganshi a kasa ya
kuka fito waje.." kafin mamarta tayi magana Ado yace "Nina sa aka watsar min dasu a waje
domin na gaji da ganinku cikin Gidana Dan Haka wallahi ku tattara ku barmin kofar gida Kona
Kira muku jami'an tsaro" Wani i'rin kuka Jiddah tasa "Dan girman Allah Baba Ado kayi hakuri
wallahi bamuda Gurin Zuwa kan dubi Halin DA muke ciki ka barmu mu zauna Wallahi nayi
Alkawari zan biyaka kud'inka." Tsaf yake kallonta tare da shafa Tunbinsa "I'dan zaki ringa Zuwa
D'akina muna kwana tare Har Gidan zan bar muku." Sunkuyar da kai Jiddah tayi kasa Asma'u
tace "Wa'iyazu billahi 'yar tawa kakeson lalatawa Insha Allahu Allah baze ta'ba baka nasara ba
D'an i'ska la'ananne..." Haureta yayi da kafarsa take ta kifu da cikin jikin wani i'rin kara tasa tare
da Kiran sunan mijinTa "USAMA.. wayyo cikina mutuwa zanyi" daga Haka Bata karacewa komai
ba Da sauri Jiddah ta matso gurinta d'agota tayi tare da d'orata jikinta Kumatunta ta shiga
tabawa "Mamana dan Allah ki tashi mama karki tafi ki barmu a wannan duniyan da take cik'e da
azzalumai mama Kinga babana banida wasu Bayan ku ki tashi mama karki min haka...
"JIDDAH." DA k'arfi ya Kira sunanta kallon mamarta tayi tare da kallon mahaifinta Ajiye
mahaifiyarta tayi tare da rarrafawa gurinshi "Baba kana ganin Abinda sukayiwa mama baba
baka iya d'aukan mataki ba? Matarkace fa Wanda nauyinta yake rataye a wiyanka Baba kana
kallo sunci mutumcinta sun tafi..."Jiddah Jiddah Jiddah ki kula da k'anki ki tsare mutumcinki duk
runtsi karki d'auki d'abi'ar bezo cikin addini ba karkiyi abinda Al'uman musulmi zasuyi tur dake
daga karshe Jiddah nayi biyan bashi dake , ki bishi duk inda ya Sanya kafafunsa.." Wani i'rin
kunfane ke bin bakinsa Amma duk da Haka be Dena k'okarin mata magana ba, "Allah ya Miki
Albarka Allah ya tsare ki.." Baba me kake cewa haka Ya mahaifina! Ka tashi ka motsa
gab'ob'inka Muje mu kwaci hakkin mu... A hankali ya sauk'e wani i'rin ajiyan zuciya...
Maman Faruq
12/26/23, 8:58 AM - UMMI JB: ♡SIRRIN ƊAUKAKA..!♡
_Wattpad@ayshajb_
®️
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..*
[Kungiya Domin wayar da kan mata, Farin jini writer's domin ci gaban Mata.]
_♡F.J.W.A♡_
Page2 .
Tab'ashi take tana kiran Sunanshi Amma shuru baya motsi kwantar da Kanta tayi a jikinshi
tana kuka "Yanzun Baba kaima i'rin barcin mama kayi yanzun saura ni d'aya , ku tashi mana
kun barni ni kad'ai , nifa bana jin wannan barcin" Limamin anguwarsu ne yazo gurin sakamakon
ganin mutane da yayi sun kewayesu "a a lafiya naga kun taru anan meke faruwa?" Ganin
Hauwa kwance jikin mahaifinta yasashi faɗin "Hauwa ya kuke zaune a waje?" ɗagowa tayi da
sauri tana kuka ta fara labarta mishi abinda yafaru. durkusawa yayi tare da faɗin "Hasbunallahu
wani'imal wakeel khai khai! wannan zaluncin har i'na yanzun duk acikin ku babu wanda ze
temaka musu kun tsaya ne kawai kuna kallonsu haba! wannan wacce i'rin rayuwace Sekace ba
musulmai ba, nasan da 'Yan uwanku ne Dole nasan se inda karfin ku yakare amma duba
Usama ne da matarsa mutum me kirki dason jama'a mutumin da babu ruwanshi da kowa meye
amfanin tsayuwarku , Dan Allah ku watse anan!".
d'aya bayan d'aya suka shiga tafiya ya saura mutum uku d'ago Usama yayi yanayinsa kaɗai ya
sheda masa rai yayi halinsa Rai bakon DUNIYA girgiza kai yayi yana tunanin rayuwarsu na
baya lokacin yana cikin wadata kafin zuwan wannan bak'ar Kaddaran kai wasu mutanen basuyi
ba , rufe mishi idanuwa yayi tare da fad'in "Allah yaji k'anka Usama ubangiji yasa halayyarka
nagari subika Allah seya saka muku ka mutu da baƙincikin Ado kuma insha Allahu seyaga
karshen sa" Da sauri na ɗago duk da kasancewata yarinya amma ai nasan kalman mutuwa
kallon liman nayi ina zare mishi ido "Baban nawa ne ya mutu! Mahifina me sona Babana me
K'aunata Babana meson Farin cikina Babana meson ganin dariyata ka duba liman da kyau
mahaifina yana raye taya ma ze mutu ya barni ? kullun Babana seyace min Jiddah Allah ya miki
Albarka Allah yakare min ke daga sharrin duniya da abinda ke cikinta kullun seya shafa kaina
yana faɗin Jiddah burina ki samu ilimi burina kiyi karatun Addini Jidda Ki kasance 'Ya me biyaya
gana sama dake Allah ya bani lafiya nabiya bashin mu'azzan Baralabe anya kuwa babana ze
mutu dan Allah liman ka duba wallahi yana barci ne mama kinaji. ki tashi dan Allah baba
katashi..!" wani i'rin kuka mecin rai take tana juya kai seda liman ya zubda kwalla tsaban
tausayinta da yamamaye zuciyarsa "Kiyi hakuri Hauwa usama k'an ya rigamu gidan Gaskiya"
Kan mahaifiyata na ɗago ina kuka duk na haɗa majina da hawaye na ɗaurata asaman cinyata,
hannunta na kama ina matsewa "Shi kenan Liman Babana yace indena Jayayya da nagaba
dani, Allah yaji ƙanshi Allah ya kafarta mishi mama ki tashi dan Allah kema karki mutu ki dubeni
nayi k'ank'anta da zaman maraici"
Da temakon sauran mutanen dake gurin Liman suka D'auki gawan mahaifina bayan an mishi
wanka an suturtashi suka mishi sallah lokacin muna ɗakin matar liman Mama har yanzun bata
farka ba sun dubata wai dogon suma tayi har zuwa lokacin da liman yazo yace inje inma
mahaifina bankwana amma nadena kuka inhar inna son mahaifina sede na kasa domin ina tuno
halin da zamu shiga nan gaba nida mamana haka na daure na mayar da sautin kukan sede
hawaye yaki barin fiskata hannu nasa a zanin da aka rufeshi hawaye masu zafine sukaci gaba
da biyo k'uncina dakayar na i'ya masa addu'a shima cikin zuciyata domin muddin nace zan fito
dashi fili ba shakka kuka zanyi haka innaji inna gani aka ɗauki mahaifina Babana me sona da
son farin cikina aka tafi dashi gidanshi na gaskiya shi kenan babu shi an rufe babinsa ya tafi ya
barmu bazan sake ganinshi ba ya zanyi da raina ranan haka na wuni kuka sallah ma yinsa
kawai nakeyi abinda ya kara ɗagamin hankali har yamma mama bata farka ba, ga zuciyarta na
bugawa fisƙanta yayi fayau, gashi mu ba wanda yazo daga dangin mahaifina duk da anje an
faɗamusu amma sunki zuwa kirin kirin suka ware mahaifina sabida shi mahaifina shi ɗaya
mahaifiyarshi ta haifa ko gurinsu naje se su ringa kyarata basa so na raɓu da ƴaƴansu dalilin
haka nadena zuwa suna sane da halin rashi da muke ciki amma cikinsu babu me temakon mu..
mahaifiyata kuma marainiyace matar liman ta kawo min abinci amma na kasaci domin nariga na
saba da zaman yunwa a halin da nake ciki ma wallahi ko nace zanci bazan iya ba,
Seda mama tayi kwana biyu kafin Allah ya farkar da i'ta lokacin ina saman sallaya ina sallan
la'asar juyawan da zanyi naga tana motsi kafin nace wani abu ta rigani magana abinda ya fito
bakinta shine "USAMA cikina ciwo yake min" mezanyi in banda kuka Domin akwai so kauna da
Fahimtar juna a tsakaninsu gurinta nazo "Mama kin tashi?" kallona tayi tare da faɗin "Hauwa
i'nane nan ina Usama?" kafin na mata bayani matar liman ta shigo "Masha Allah sannu Asma'u
kin farka?" kallonta mama tayi kafin tace "Larai.. Ke Hauwa magana nake dake kina min kuka
ina