Showing 75001 words to 78000 words out of 82684 words

Chapter 26 - Sirrin Daukaka Book Complete by Aisha Jb Mrs Danshuwa

mata Abinci bata sake zuwa ba,
Wayan Nabil ta shiga kira, amma no answer, komawa part ɗin iyayensu tayi tana sanar dasu
halin da ake ciki na rashin dawowan Jiddah Abban Nabil yace “Shi Nabil ɗin fa?” Nuwairah tace
“Abba nayita kiran wayanshi baya ɗauka tun safe daya fita bai dawo ba..” Inna tace “Bai dawo
ba kuma? Ina ya tsaya har wai haka? Shida ta gota ace bai dawo gida ba?” “Wallahi Inna Haka
yake fita ya daɗe wani lokaci ma in ya dawo baya zama da zaran yayi wanka sake fitan yake sai
Shaɗayan dare..” Alhj Abdallah yace “Har shaɗayan dare?..” kafin tace wani abu suka tsinkayo
muryanshi yana sallama “Wa'alaikumu Salam Yaya baka ga kira na bane? Since inata kiran
wayarka No answer Jiddah Bata dawo gida ba...” “Bata dawo gida ba? Ina taje?” ya faɗa yana
kallonta “Dama ɗazun tare muka fita tace zata siya...” ai bai tsaya jin ƙarshen zancen nata ba ya
fita da sauri suna masa magana ma ko sauraronsu bai yi ba, Saƙon Location ɗin asibiti ne ya
shigo wayarshi ya rasa Number waya, bai tsaya wani bincike ba ya nufi Location ɗin.
Ya sameta zaune jingine da bango hannunta da alluran ƙarin ruwa Da sauri ya ƙarasa Kusa da
ita yana faɗin “Jiddah...” ɗauke shi tayi da wani lafiyayyen mari zai sake magana ta kuma ɗauke
shi da wani mari hannu biyu dafe da kumatunsa bude jajayen idanunta tayi tana kallonshi “Kika
mare ni?” “Na mare ka..!”
“Akan wani dalili?”
“Dalilai masu yawa da ƙwararan hujjoji Ashe kai fasiƙi ne ban sani...” ɗauke ta yayi da mari cikin
ɓacin rai yace “Karki yarda...”
“Dakata Nabil ai ba ƙariya tayi ba” Juyowa yayi yana kallon Nuwairah dake bayanshi ta harɗe
hannuwa tana kallonsu “Ƙwarai kuwa kuma kin min dai-dai da kika masa wannan hukuncin Duk

wasu abubuwan da kake aikatawa kallonka kawai nake, munsha fita da Jiddah tana ganin
Motar ka, Amma saina ƙaryatata saboda bana so wani matsala ya shiga tsakaninku last fitan da
mukayi wanda kace zaka kaimu shopping daga baya kaƙi amma a shop mall ɗin na ganka da
Farkanka...” “Ya isa!”
“Meye abin jin Zafi anan? Gaskiyace kasan da zafi kake aikatawa? Baka san mutumcin mu
dana iyayenmu kake zubarwa ba? Why Nabil? Ka ɗauki ƙazamin riga ka sanyawa kanka wai kai
ne da ajiye Karuwa a waje..” runtsa ido Jiddah tayi da ƙarfi tare da fashewa da Kuka me sauti
ƙarasowa Gurinta Nuwairah tayi tana lallashin ta “Haba Aunty Nuwairah maiyasa tun farko kika
rufe Ni? Bai yasa baki fayyace min Halin Mijin da nake Aure ba? Yanzun a haka zamuci gaba
da rayuwa da Miji irin sa? Gaskiya bazan iya ba! Wallahi bazan iya cigaba da zama da Nabil
cikin wannan ƙazamin rayuwar daya jefa kanshi ba” Kallon Dr dake koro mishi bayanin sallama
yayi tare da duban takardan Ganin an biya komai ne yasa shi kallonta “Waye ya kawo ki asibiti?
Meya sameki? Wa ya biya kuɗin?”
“Me kuwa zai kawo ni asibiti bayan baƙin ciki da takaicin Ɗa Namiji, akan meyasa kake
tuhumata da tambayar waye ya kawo ni asibiti Kana can tare da Karuwanka kana sheƙe ayar
ka meyasa Nima bazan fita in shaƙi iska ba....” a zabure ya matso yana shirin Marinta Nuwairah
ta riƙe mishi Hannu tana faɗin “Dalla can dubi yanda kake ta wani ɗaga jijiyar wuya, dan kawai
ta faɗa maka abinda ba haka bane”
“Da kin ƙyale shi, kayi abinda ranka ya maka amma Zamana da kai ya ƙare bazan iya zama da
ƙazami irinka ba”
“Kinga Jiddah ya isa haka tashi muje gida tunda an sallameki”
“Babu inda za'a tafi har sai ta faɗa min uban daya biya kuɗin Asibitin nan!”
“Au haba? To ko zargina kake saboda kana da Karuwa a waje nima kana zargin zanyi abinda
kake aikatawa ne?”

_Afuwan bana jin daɗi ne_


Maman Faruq
12/26/23, 9:03 AM - UMMI JB: ♡SIRRIN ƊAUKAKA..!♡*

®AYSHA JB

FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION

*Wannan page ɗin naku ne, AYSHA JB CLUB tare da Wattpad Fan's Much Love Guysí ¾íµ°í ½í¸�
kuyi yanda kuke so dashi..*
34Shuru kawai Nuwairah tayi tana kallon yanda suke cacar baki, ba irin haƙurin da bata basu
ba amma Ina koma zuciyarshi yai sama Cikin gajiyawa da haniyarsu ta ɗauki wayanta tana
faɗin. “Tunda bakwa jin haƙuri bari na kira Gida wataƙil in suka zo zaku ƙyale wannan maganar”
ta ƙarasa maganar tare da kai wayan kunninta karɓe wayan yayi tare da jan ƙwafa ya fita waje
kallon Jiddah tayi tare da ɗaukan jakarta dake gefe sannan tace. “Oya Malama zaki tashi ne ko
nayi tafiyata dan naga ke da mijin naki kun ɗau zafi sosai in Kuma daga nan akwai inda zaki tafi

ne sai ki sanar min” Saukowa Jiddah tayi daga gadon tare da saka takalmin suka fito motan
Nuwairah ta shiga suka nufo gida dai-dai ana kiran Sallar magariba ɗaki Jiddah ta nufa tayi
alaula tare da sauke sallolin dake kanta, Nuwairah ce ta shigo mata da jakanta tare da
magungunan da aka bata a asibiti Abincin dake kitchen ɗin ta ɗumama tare da kawo ma jiddah
tana idar da Sallah ta koma bayi tayi wanka riga mara nauyi ta saka sannan ta tsakuri Abincin
kana tasha magani lumshe ido tayi tana jin yanda kanta gefe ɗaya ke sarawa shigowa yayi tare
da tsayuwa yana ƙare mata kallo, ko ɗagowa batayi balle tace mishi wani abu, “lokaci na ƙarshe
kenan da zan sake tambayan abinda ya kaiki asibiti da ɗan iskan daya biya miki kuɗi” buɗe
jajayen idanunta tayi tare da watsawa cikin nashi kallon ƙwayar idonshi tayi sosai kafin ta ɗauke
kanta, miƙewa tayi tana shirin fita yasa mata ƙafa ta faɗi, zata tashi ya sake danneta “Wacece
ke da zan miki magana kisa kai ki wuce ba tare da kin bani amsata ba..?” cikin wani irin ƙarfin
hali tasa duka hannunta biyu ta tureshi, wanda sai da ya buga ƙeyarshi da bango, motsin da
tayi da ƙarfi ne yasa hannun da akayi mata ƙarin ruwa ya fara fitar da jini, nuna shi tayi da yatsa
cikin ɓacin rai tana faɗin “Karka yarda ka ƙara taɓa tsaftataccen jikina da ƙazamin hannunka..”
miƙewa Yayi da sauri yana shirin kamota fita tayi da sauri dan ta lura muddin ta tsaya zai iya
illatata domin wani ƙazamin kishi take hangowa a idanunsa, a main falo ta dakata tana kallon
yanda suka tsaya cirko cirko har Mahaifiyar Nuwairah “Meke faruwa anan? Kai Nabil meka
zaburo kake shirin yi? tun ɗazun kun cika mana gida da hayaniya, ke Jiddah Ina kika je tun
safe? Meya kai ki asibiti?” Mahaifinsa ne ya jero musu wannan tamabayoyin yana jiran Su bashi
amsa Kallon Jiddah Nuwairah tayi sannan ta juyo tana kallon Nabil wanda ya ɗauke wuta yana
jiran abinda Jiddah zatace tuni zuciyarshi ya fara lugude ga zufan rashin gaskiya dake karyo
masa Buɗe baki Nuwairah tayi zatayi musu bayani ganin haka yasa Jiddah taran numfashinta
gurin faɗin “Abba bafa wani abun ɗaga Hankali bane, zazzaɓi ne ya tare ni shine nayi saurin
zuwa Asibiti..” Kallon Nabil Inna tayi tare da faɗin “Kai kuma Meye kake binta kaman zaka
daketa?” da sauri Jiddah tace “Bafa wani abu bane, daman hannuna dana fama ne yake ta bina
in tsaya ya gani shine nake gudu...” fita sukayi ya saura su uku kallon Jiddah Nuwairah take
cike da mamaki ganin yanda ta rufa mishi asiri ba tare da ta faɗi ainihin abinda ya faru ba,
“Allah ya ƙwace ka dan wallahi da nice aka tambaya bazan taɓa rufa maka asiri ba, kana da
daman da zaka gyara kuskuren ka kafin lokaci ya ƙure maka” kallon Jiddah tayi tana cigaba da
faɗin “Kinyi Abu ne kyau da kika rufawa mijinki asiri lallai ba ko wacce mace bace zatayi abunda
kikayi Allah ya tashemu lafiya dan Allah ki ƙara Haƙuri akan na da”
Ɗaki Jiddah ta koma tana shirin kwanciya ya zauna yana faɗin “Hmmm tunda abun haka ne
ina ga zan ƙara Aure..” Ɗan Murmushin takaici da ɓakin ciki tayi tana tunanin anya kuwa
wannan Nabil ɗinta ne kuwa? Anya ba sauya mata shi akayi ba domin ta lura Gbɗy baya ma
cikin Nutsuwa bare ayi tunanin Hankali tattare dashi “Allah ya bada sa'a” daga haka tayi shuru
tana tunanin wacece i'ta da har mijinta ya manne mata yake kuma iƙirarin cewa zai Aure ta?
Humm koma wacece bazata barta haka ba, tunda Har Nabil ya fara taɓa lafiyan jikinta da sunan
Duka Wallahi sai ta Nimo ko wacece Yarinyar taci uban ta, kai har ma da uwar ta.
Ɗakin Nuwairah yaje kamar yadda ya sanar da Jiddah haka itama ya faɗa mata Aikuwa ko tutuf
bata ce masa ba, haka ya gama zaman shi ƙarshe fita yayi a gidan, Girgiza kai kawai Jiddah
tayi tare da sauke labulen window bayi ta nufa tayi Alwala tazo ta shimfiɗa sallaya nan ta fara
jero nafiffilu tana masa Addu'ar shiriya bata runtsa ba saboda damuwa da baƙin cikin dake
ƙunshe a zuciyarta kuka take sosai tana tunanin Nabil nacan gurin wata mace, macen ma
Karuwa, Sai bayan Asubahi ya shigo gidan lokacin ta gama ƴan aikace-aikacen data saba,

Nuwairah ce ta fito tana kallon yanda ta kammala komai “Kai Jiddah wannan aiki haka, kinsan
fa baki da lafiya ai da kin bari nayi komai” “Barka da Fitowa Aunty Nuwairah, ai ba komai
wallahi” Hannunta Nuwairah ta kalla tana faɗin “To ya ƙarfin jikin naki? Ina fatan kin ji sauƙi?”
Jiddah tace “Alhamdulillah da sauki sosai” Zama Nuwairah tayi tana faɗin “To Masha Allah jiya
Yaya yake min maganar da ban gane kansa ba, na fara tunanin gwara a kaishi asibitin
mahaukata a dubashi dan ga dukkan Alamu karen hauka ya cijeshi” Girgiza mata kai Jiddah
tayi tana dariyan zancen ta. “Kai! Nuwaih yana cikin hankalin shi nafi ɗaukar maganar da wasa
yake..” ajiye spoon ɗin tayi tana faɗin “Wasa fa kika ce? Allah da gaske yake kuma nasan zai
kai maganar gaba” Kallonta nayi domin wlh na ɗauka barazana yake “Allah ya kyauta” nace
sannan ya shiga ɗaki nayi shirin fita.
Jin motsin tura Get yasa ta gyara zama tana daɗe faɗaɗa fuskanta da yalwataccen murmushin
a tunanin ta Nabil ne, Amma jin wani ƙamshi na daban yasa ta shiga kokonto waye haka?
Jiddah kuwa tsayawa tayi tana ƙarema Gidan kallo sosai tana kallon ɓarnan da akayi da dukiya
musamman ma kyawawan kujerun Alfarman dake falon ga danƙareren tv bango “Waye Anan?”
Aaliyah dake fitowa ta faɗi haka tana mamakin ganin mace, Cikin nutsuwa Jiddah ta juyo tana
tuna mai muryan ja da baya Aaliyah tayi tana nunata “Meya kawo ki gida na?” harɗe hannuwa
Jiddah tayi a ƙirji tana matsowa tare da ƙare mata kallo “Aaliyah!! Ohh daman kece Karuwar
tasa? Kece kikayi kane kane a rayuwar mijina? Kice kika ɗauke wa mijina hankali oh Na tuna a
can baya kince zaki addabi rayuwata hakane Abun dama? To yau koni ko ke dan wallahi saina
Kashe ki yanzun! kuma anan!! Saina lalata duk wani halitta na jikinki..” ja da baya Aaliyah ta
shigayi tana faɗin “A'a Jiddah dakata nayi miki bayani wallahi Ina Son Nabil shima kuma yana
ƙaunata yanzun haka muna shirin Aure ne dan mu mallaki junanmu...” ɗauke ta tayi da
lafiyayyen marin da se da ta fitar da jini ta hancin ta, cakume wuyan riganta Jiddah tayi tana
jijjigata cikin ɓacin rai “Mijin nawa kike shirin Aura ko? Zaki Aure shi amma a lahira dan baki da
gurbin zama cikin matanshi na duniya” tana gama faɗin haka ta shiga kifa mata mari kukuwa
kawai Aaliyah ta shigayi da Numfashi saboda riƙon da Jiddah tayi mata Numfashinta na
barazanan ɗaukewa Dunƙule hannun Jiddah tayi da niyar kai mata naushi cikin tashin hankali
Aaliyah ta tare cikinta da hannu tana faɗin “Dan Allah karki kashe rai, Ciki gareni na sati shida
Please naci albarkacin sa...” ta ƙarasa maganar cikin kuka, cikin tashin hankali Jiddah tace
“What! CIKI!!! Innalillahi wainna ilaihi rajiun” Jiddah ta faɗa tana ja da baya tare da fashewa da
kuka “Ciki de na Haihuwa? Kina da ciki? No! Ƙariya ne!!” dawowa tayi da gudu takai mata wani
mummunan naushi a ciki, ƙara me ƙarfi Aaliyah ta saka tare da zubewa a ƙasa ɗif Numfashinta
ya ɗauke na wasu daƙiƙu, ruwa me sanyi Jiddah ta zuba mata a Fuska tare da ɗagota “Karki
yarda ki sake raɓan mijina ke ko Sunan mijina kikaji Ina so ki toshe kunnuwanki dan wallahi naji
Mijina yana tare dake kashe ki zanyi!!” Kaman mahaukaciya haka Jiddah ta shiga dukanta ba ji
ba gani, kafin ta shiga janta har ƙofan gida ta watsar da ita dawowa tayi cikin Gidan tare da
Zuba fetur ta cinnawa gidan wuta tana fitowa ta tarar da Nabil yana shirin ɗaga Aaliyah dake
ƙwance cikin jini Cikin wani irin mawuyacin halin Aaliyah ta Riƙe hannunshi tana faɗin “Yau nake
shirin sanar da kai amma matarka ta ɓata komai Nabil Baby Na ciki gareni shine tazo ta kashe
ni da Abinda ke ciki na” A zabure ya sa ke ta tare da nufo Jiddah nan ya shiga zuba mata mari
cikin ɓacin rai “Akan me? Me yasa kika zubar min da ciki...”
“Nabilllll” da gudu ya nufi gurin Aaliyah tare da ɗaukanta yasata a Mota suka nufi asibiti.
Gida ta nufo gbɗy bata cikin nutsuwarta “Jiddah Ina kika je?” Ina Jiddah bata ma san da ita ake
magana ba, riƙe ta Nuwairah tayi tana faɗin “Jiddah menene haka? Ya naga fuskan ki a

kunbure waya dake ki?” wani irin kuka ta fashe dashi tare da faɗin “Nuwairah Yarinyar da Nabil
ya ajiye har ciki gareka wannan Karuwar tasa nake faɗa miki ciki gareta saboda naje na dake ta
shine Nabil ya mayar min da fuska haka Akan karuwa Ya min haka!” Cikin tashin hankali Inna ta
ƙaraso gurin har zaninta na shirin faɗuwa kasa “Me nake ji haka? Ke! Jiddah me kike faɗa ne?” Girgiza kai Jiddah ta shigayi tana faɗin “Babu komai..” Rufe mata baki Nuwairah tayi itama cikin
kuka tana faɗin “Ƙwarai Abinda kunnuwanki suka jiye miki haka ne, Nabil ne ya ajiye Karuwa a
waje duk wannan rigingimun da muke duk akan maganar ne..." Rufe mata baki Jiddah tayi tana
girgiza mata kai alamar karta faɗa “ƙyale ni Jiddah Halin Nabil ya isheni gwara na fayyace
komai” tiriyan-tiriyan ta dinga faɗa musu komai Wani wawan burki Nabil yaja yana kallon
Nuwairah dake bayani Juyowa mahaifiyarshi tayi nan ta shiga zuba mishi mari tana faɗin
“Wannan ba tarbiyan dana baka bane, wannan ba Renon Asma'u bace, Nabil kaine da ajiye
mace a waje har da ciki?” sunkuyar da kanshi yayi ƙasa yana sake jin wani ɓacin rai, duk
abinda suke Mahaifinshi na kallonsu jinjina kai yayi yana mamakin Halayyar da Nabil ya ɗauko
“Da Girman ka, da ilimin ka, kana da iyali kasan Hukuncin zina kuwa? Anya Nabil baka fara
shaye-shaye ba kuwa? To wallahi ka buɗe kunninka kaji da kyau bazan ɗauki wannan ƙazantar
a cikin gidana ba, ban taɓa Zina ba, dan haka...” da sauri Jiddah tace “Dan Allah Abba karka
masa baki, dan girman Allah kuyi masa addu'a shine kawai abunda yake buƙata” gyaɗa kai
Mahaifinshi yayi tare da nuna shi da yatsa ransa a ɓace ya bar gurin haka ma mahaifiyarsa
Nuwairah kuwa hannun Jiddah ta kama suka dawo part ɗinsu.
yanke shawaran barin Gidan Jiddah tayi, nan da Nan ta shiga haɗa kayanta tare da buɗe wani
ƙaramin jaka ta ɗauko hoton Mahaifiyarta, rumgume hoton tayi tana hawaye sosai cikin kuka
take faɗin “Umma lna cikin Ahalinki yau nice matsayin matar ɗan da kikafi ƙauna yau gashi zan
barshi bazan iya cigaba da zama dashi a irin wannan rayuwar ba, bazan iya zama baƙin ciki da
damuwa su kashe ni ba, gwara na koma inda na fito gwara na tafi kuma tafiyar da bana jin zan
sake dawowa”
Zoben Azurfa da awarwaronsa ta ɗora kan hoton tare da ɗan shot note ta ajiye, ATM ta
ɗauka tare da Nufar part ɗin Mama-Sadin ganin tana barci ne yasa ta juyawa da niyar fita ɗan
gyaran murya taji mama tayi a hankali ta juyo tana kallon yanda Mama ke motsawa da sauri ta
fita a gidan kuɗi masu yawa ta cire kafin ta bar ƙasar direct Gidan Fadilah ta nufa dan bata so
kowa yasan tazo Nigeria daga dangin Ummi bata samu Fadilah a gida ba, me musu gadi ne
yake sanar da ita tafiyan da tayi tare da mijinta key ɗin cikin gidan ta karɓa daga gurinshi
kasancewar ya santa da Fadilah shiyasa bai wani damu ba, Ɗakin Fadilah ta shiga nan ta
adana kayanta tare da shiga bayi tayi wanka a gurguje tazo ta biya sallolin dake kanta
kasancewan dare yayi sosai bazata iya yin girki bane yasa ta haɗa tea kawai tasha ta kwanta.

Chadi....

Bana ganin Comment

Maman Faruq
12/26/23, 9:03 AM - UMMI JB: ♡SIRRIN ƊAUKAKA..!♡*

® AYSHA JB

FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION

Alhamdulilah jiki ya yi sauƙi sosai ina matuƙar godiya da addu'o'inkuí ¾íµ°í ¾í´�

35 Riƙe hannuwanshi tayi da ɗan ƙarfi tana kiran sunan shi, a hankali ya buɗe idanunsa tare da
faɗin. “Sannu Aaliyah ya kike jin jikin naki yanzun?” ya ƙarasa maganar tare da shafa fuskan ta.
“Da sauƙi Lover ai na ɗauka ka tafi..” Girgiza mata kai yayi sannan ya taimaka ma ta ta zauna,
shafa cikinta tayi tana kallon shi da murmushi. “Kana murna kuwa?” zama ya yi kusa da ita tare
da kwantar da kan shi bisa kafaɗarta shima ya ɗora hannunshi saman nata tare da sa kin
kyakkyawan murmushi yana lumshe ido, sun jima a haka na tsawon lokaci kafin ya janye
jikinshi daga gareta tare da nufan ofishin likita tattaunawa sukayi akan yanayin jikin na ta kafin
ya dawo ya samu har ta koma barci gyara tsayuwar sa ya yi yana ƙare ma ta kallo tare da
ƙurawa cikin jikinta ido, sosai yake jin farinciki mara misaltuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0