Showing 78001 words to 81000 words out of 82684 words

Chapter 27 - Sirrin Daukaka Book Complete by Aisha Jb Mrs Danshuwa

a ran shi kallon agogon da ke
ɗakin ya yi yana tunanin zuwa gida gashi dare ya yi sosai banɗaki ya shiga ya kama ruwa tare
da alwala ya dawo ya shimfiɗa sallaya ya fara nafila a saman sallayan ya kwana washe gari aka
basu sallama ya dawo da ita gida bayan ya sa an gyara komai na gidan da ƙyar ta ƙyaleshi ya
nufo gida.
Nuwairah ce kaɗai zaune a falon domin tun jiya suke niman Jiddah amma babu ita babu
labarin ta hankalin su ya yi matuƙar tashi sosai dalilin haka yasa mahaifin Nabil ɗaukan zafi
kasancewar ba irin kiran wayan da ba'ayi masa ba amma ya ƙi ɗagawa Mama-sadin ma da taji
labari hankalin ta ya tashi sosai inda ta shiga faɗa tana faɗin basu kyauta mata ba me yasa
basu faɗa mata tunda wuri tayiwa abun tufkar hanci ba, shiyasa kwanaki take ganin Jiddah cikin
yanayin damuwa ashe da walakin goro a miya domin Jiddah yarinyace me sakewa da mutane
duk da ita ba mace bace me yawan surutu da son hayaniya amma akwai ta da daɗi hira ga iya
tausasa lafuza duk maganar da zai fito daga bakinta me kyau ne da kuma ma'ana. tana da
haƙuri da kawaici, sau da dama tana tambayar ta yanayin zaman nasu ba ta taɓa gaya ma ta
wani abu da ake mata mara daɗi ba yawancin lokuta ma idan ta tambaye ta sai dai tayi
murmushi kawai daga haka zata shashantar da zancen ta wani siga yarinyar ta shiga ran ta
sosai tana jin ta kamar yadda take jin sauran jikokinta sai dai ƙaunar da take mata daban ne
dalilin da yasa ta ɗaga hankalinta kenan akan ɓatan nata.
“Lafiya kuwa Nuwaih naganki cikin wananan yanayin?” kallon shi tayi tana jin takaici da baƙin
cikin kasancewar shi ɗan'uwan ta wanda kuma yake matsayin miji a gareta ɗakin Jiddah ta
nuna mishi tare da ɗauke hawayen dake zubo mata kallon ta yayi zuciyar shi na dukan uku uku
a tunanin shi wani mugum abune ya samu Jiddan hankali a tashe ya nufi ɗakin cikin hanzari
nan yaga gabaɗaya ɗakin a hargitse ga dukkan alamu babu wanda ya kwana cikin ta kallon
inda akwatunanta suke yay nan yaga babu wasu daga cikin akwatunan zama yay gefen gadon
tare da dafe kanshi da hannuwanshi duka biyu yana jin wani irin tashin hankali tare da tunanin
Ina taje? Ina ta kwana? a wani hali ta ke? duk ba shi da me bashi wannan amsar kallon gaban
madubin ya yi nan yaga gabaɗaya babu kayan kwalliya da mayukan shafe shafenta miƙewa yay
yana zagaye ɗakin zuciyarshi na bashi lallai tana Nigeria yanzun haka, naushin iska ya yi yana
jin babu daɗi a ran shi, ta gefen gadonta yaga awarwaro da sarƙa ɗauka yay tare da bude hoton
dake gurin da wasiƙar da ta rubuta. “a lokacin da zaku iske wannan saƙon nasan nayi nisa Ina
so abar wata maganar dangantaka kayi gaggawan aikomin da takarda ta, domin bazan iya
cigaba da zama da mutum mara adalci irin ka ba, a yanzun na haƙura da aure da duk wani abu

daya shafi ɗa namiji nafi sha'awar zama ni kaɗai domin babu komai cikin rayuwar Aure daya
wuce baƙin ciki da damuwa. duka halin maza haka yake, duk yadda ka kai ga son gane halin
maza bazaka taɓa fahimta ba, domin kullum cikin canzawa suke baka gane gaban su balle
bayan su, Ina sake jaddada maka ka sauke min wannan ƙadararren Auren nake damin bazan
iya cigaba da zama da kai ba, karka ɓata lokaci gurin niman inda nake” wani irin gumi ne yake
tsattsafo masa tun daga tsakiyar kan sa zuwa wiyansa kalman Innalillahi wainna ilaihi rajiun
kawai yake maimaitawa kallon hoton yake hawaye na tarige rigen saukowa akan fuskansa,
Kenan Jiddah ɗiyar Ammah Asma'u ce? ita ɗin ƴar'uwa tace ta jini tasan da haka tsawon
wannan lokacin shine bata bani fuskan da zan fahimci hakan ba? Ya Salam me kenan na aikata
ban kyauta mata ba, juyowa yay da niyar zuwa shashin Mama-sadin nan yayi arba da Nuwairah
tsaye “Ashe akwai ran da zakayi kuka? tabbas nasan wacece ita shiyasa tun farko na watsar da
makaman yaƙina muke zaman lafiya nasan Jiddah ƴar'uwa tace Ƙanwa tace shiyasa nayi haƙuri
muke zaman lafiya..” dakatar da ita yay ta hanyar faɗin “Kinsan da waɗannan abubuwan shine
baki faɗa min ita ɗin Jinin mu ɗaya ba? maiyasa kika rufe ni? taya kika gano hakan? ni kaina
nayi mamakin yanda lokaci ɗaya kika watsar da wannan kishin naki kuke zaune lafiya taya haka
ta kasance?”
“Hanisa ita ta sanar min da komai ita ta sanar min da Jiddah ƴar'uwar mu ce, amma sai na
musanta daga ƙarshe se nasa aka bincika min har can Benue ɗin a nan ne na samu labarin
komai shiyasa na watsar da komai amman nace bazan faɗa ba, har sai ita da kanta ta fallasa
komai. Nabil baka kyauta ba, bai kamata ka taɓa Jiddah akan wata karuwa mara daraja ba, bai
kamata ka ɗagawa matarka ta Sunnah murya akan wata banza mara ƙima ba, Jiddah tana da
haƙuri ni shaida ce.
Jiddah macece me sauƙin kai da kwantar da kai dan a zauna lafiya macece da abin duniya bai
rufe ma ta ido ba, duk da tana kasuwanci amma haka tayi haƙuri tabar komai duk saboda tana
son zaman Aure amma sai kaƙi fahimtar haka, duk wani ƙoƙarin da muke maka da ƙoƙarin
sauke duk wasu haƙƙin ka dake rataye akan mu amma duk bamu ishe ka ba, meye a jikin
wancan yarinyar?” shuru yay yana sauraronta daga ƙarshe suka nufi part ɗin iyayensu nan suka
suka mishi faɗa sosai tare da nuna ɓacin rai akan abinda ya aikata mata shuru sukayi suna
sauraron bayanin da Nuwairah take koro musu game da Jiddah “Innalillahi kika ce Asma'u ta
rasu? Lahaula walakuwwata illabillah Allah sarki ashe babu rabon mu sake ganawa da Auta ta!
Allah ya gafarta muku Husnah Allah yaji ƙanku da rahama ashe Hauwa'u jikanya tace shiyasa
wani lokaci nake mata kallo kamar Asma'u ashe jininta ce to ka buɗe kunnuwanka da kyau ka
jini maza-maza ka tashi ka nimo min jikanya kai harda ɗanta dan baza'a bar shi can ba, bazai
yuwu mu danginta muna raye ita tana can wata uwa duniya ɗanta na tsakiyar kishiyoyi marasa
adalci ba. Karka yarda ka dawo batare da ka samo su ba” Mama saddika ta ƙarasa maganar
tare da fashewa da matsanancin kukan rashin ƴarta, nan suka fara lallashinta tare da kwantar
mata da hankali.
Miƙewa ya yi yana duba wayarshi da niyar kiran ummi nan ya tuna ya bar wayan a gidan
Aaliyah dole ya fito ya nufo gidan, sai dai ganin wata mota yasa shi shiga cikin mamaki fitowa
yay yana kallon motan tare da nufar ƙofan ɗakin ya kai hannu da niyar tura kofan Bedroom ɗin
nan yaji maganan daya kusan sumar dashi “Shi fa duk a tunaninsa cikin nan nashi ne bai san
ƙariya nake masa ba, wallahi ina baka labari susucewa yay yana faɗa min in kula mishi da Cikin
saboda yana tsananin son Haihuwa be san bayan shi Ina tare da kai ba...” da ƙafa ya taka
ƙofan a zabure ta ja zanin gadon tana rufe jikinta, wayarshi yaje ya ɗauka tare da tattara duk

wasu abubuwan da yasan nashi ne sannan ya nufi ƙofan fita yana faɗin “ki tattara duk wasu
tarkacen ki nan da minti talatin ki bar min gida idan kuma ba haka ba se nayi miki dukan da yafi
wanda Jiddah tayi miki shashasha wallahi nayi dana sanin haɗa jikina dake ƙazama! kariya!!
kiyi gaggawan barin Gidan nan!” “Nabil! dan Allah ka tsaya nayi maka bayani Nabil wallahi ina matuƙar ƙaunarka wallahi bazan
sake ba, dama ɗaya kawai..” wani mugun tsawan daya daka mata ne yasa ta kasa ƙarasa
sauran zancen nata fita yayi yana jin zuciyarshi na zafi, lallai ya aikata kuskure a tunaninshi
cikin nashi ne ashe ba haka bane bayan shi tana tarayya da wanin sa, yana dawowa gida ya
fara shirin tafiya washe gari kuwa sammako ya buga sai Nigeria ummi tayi mamakin ganinsa da
kuma abinda ya kawo shi ranta ba ƙaramin ɓaci yayi ba lokacin daya ce mata ya biyo sawun
Jiddah ne “To ai rabo na da Jiddah tun ranan da mukayi magana ta wayan ka bayan nan ban
sake jinta ba, daman ina tunanin kiran ka ganin kwana biyu shuru ba labari” miƙewa ya yi da
sauri yana faɗin “Innalillahi wainna ilaihi rajiun Allahuma ajirni fi musibati..”
“Amma bari na tuntuɓi Iyanmu in ji ko taje zaria” kiran Iyanmu tayi nan ma babu labari
hankalinta ya tashi matuƙa nan ta shiga kiransu Halimatu da Hanisa suma cikin tashin hankali
suke sanar ma ta lallai bata zo ba, babu ɓata lokaci suka iso gidan duk hankalinsu a tashi.
Ummi tace “To wai nikan meya haɗa ku da har tabar Chadi? anya Nabil ba wani mugun abu ka
aikata ba kuwa? domin nasan halin Jiddah nasan irin tarbiyan dana bata faɗa min abinda ya
haɗa ku”
Sunkuyar da kai ya yi yana jin girman maganan a ranshi “Bari na kira Fadilah ko Gurinta taje”
cewan Halimatu kiran Fadilah tayi tare da sanar mata halin da ake ciki , nan ita ma take sanar
mata cewan sunyi tafiya amma yanzun haka suna kan hanyar komawa gida in ta huta zata zo,
daga haka ta ajiye wayan jiki a sanyaye fita yayi a gidan yana tunanin Ina zaije nimanta yanzun. Kiran Arab Ummi tayi tana tare da sanar dashi halin da ake ciki sannan ta buƙaci ya kawo mata
Aakif shuru kawai yayi yana kallon wayar domin bata jira taji abinda zai faɗa ba ta kashe wayar
Kallon Nafisa ya yi kasancewar a ɗakinta yake nan ya sanar mata Halin da ake ciki “Masha
Allah kaga yanzun babu wata damuwa inaga ka basu yaron kawai Ita kuma duk inda take Allah
yasa tana hannu na gari” Jinjina kai kawai ya yi tare da miƙewa ya fita a ɗakin a falo ya samu
Aakif ɗin Yana karatu “Aakif dare fa yayi sosai kaje ka kwanta haka mana” ɗagowa yayi tare da
faɗin “To Abba” yana cikin tattara takardunshi hoton Jiddah ya faɗo kallon yaron yayi tare da
ɗaukan hoton kana yace mishi “Kana son ganin Jiddah?” da wani irin mugum sauri Zaina dake
fitowa daga ɗakinta ta ƙaraso gurin “Ji nayi kamar kace zaka kaishi gurin Jiddah Hahahaha!
Nace maka Jiddah bazata taɓa zama da wannan yaron ba, nice tayi asiri na rabaku nice nasa
aka tunzura zuciyarka har ka koreta sannan nice na hanaka Bata ɗanta duk wasu abubuwan da
suke faruwa nice na aikata Hahahaha! Nice silar mutuwar Mazkhura nice nayi karan tsaye a
rayuwar Jumana nice! Nice!!” miƙewa yayi ya shiga kifa mata mari ba gaggautawa da sauri
Aakif ya riƙe shi yana faɗin “Abba kayi hakuri ka dena dukanta bata cikin hayyacinta mu kaita
asibiti..” Nafisa dake fitowa tace “Babu wani asibiti Ishara ce Allah ya nuna mata, ai dama duk
wanda ya ɗebo da zafi bakinsa” dariya kawai Zaina take ba ƙaƙƙautawa duk tayi wani iri nan ta
shiga fisge kayan jikinta tare da watsar dasu, gashin kanta ta shiga fisgewa tana ihu da surutai
da wani irin gudu tayi waje wani irin sanyi jikinsu yayi nan take tsoron Allah ya sake ɗarsuwa a
zukatan su Fure'atu dake tsaye wani irin kakkarwa jikinta yake hankalin ta tashe, hakama
Nafisa da Arab jikinsu yayi matuƙar sanyi fita yayi domin duba yanayin da take ciki sai dai duk
yadda ya kai ga hanata fita Ina tafi ƙarfin sa Tafi take tana faɗin “Huhuhuuuu zan je gani nan

zuwa Jiddah zan zo bazaki taɓa ganin daidai ba tunda kika ɗauke hankalin mijina Ihuhhuuuu ja
muje ina tafe” a zabure tayi waje shi da mai gadi tare da me musu wanki suka mara mata baya,
gudu take akan titi tana ihu da surutai wani Babban gwangwaro ne yazo a guje tare da take ta,
gabaɗaya yanayin babu kyan gani baka iya ganin komai banda Ƙwaƙwaluwan kanta tare da
kayan cikinta wadda suke waje duk tayi daga daga, motan na wucewa suka nimi gawar suka
rasa zaman dirsham yayi yana faɗin “Innalillahi wainna ilaihi rajiun” kalman da yake ta
nanatawa kenan gabaɗaya ya tsorata ya firgice ya fita cikin hayyacinsa haka aka rirriƙoshi zuwa
gida wani irin mugun zazzaɓi ne ya rufe shi gabaɗaya jama'ar dake anguwar jikinsu ya mutu
tabbas mutuwa babban wa'azice Nan kowa ya dinga faɗan halayyar ta da irin abubuwan da
take aikatawa duk yadda Nafisa taso dubashi a gida kasawa tayi domin ita kanta tana buƙatar
me dubata haka duka ɗunguma asibiti har Fure'atu Jumana ce kawai aka bari a gida tare da
sauran yaran wadda suka rikita gida da koke koke.
** ** **
Buɗe ido nayi ina kallon Fadilah data zuba min marin a cinyata “Kai Amma Jiddah ke ba
ƙaraman ƴar iska bace daman nan kika zo kika maƙale gabaɗaya kin ɗagawa mutane hankali
kinga yanda ummi dasu Hanisa suka ɗaga hankali kuwa? yanzun fa daga can nake nace bari
nazo na ɗanyi gyare-gyare se na koma kawai ina shigowa me gadi yace nayi baƙuwa wallahi
take zuciyata ya bani kece Haba komai yayi zafi fa maganinsa Allah komai na duniya fa sai da
haƙuri domin itace jagaba kuma jagoran dake tafiyar da komai, wallahi yadda naga Nabil ya
bani tausayi sosai koma menene yayi miki tunda ɗan'uwan ki ne ya kamata ki ƙara Haƙuri akan
na baya wallahi baki kyauta min ba domin lokacin da Ummi ta take magana hawaye take..” da
sauri na tashi zaune ina faɗin “Ummin tawa ce ke hawaye wayyo Allah sarki Sorry ummi...”
“Allah ya shirye ki wallahi nayi tunanin zakice mu tafi ne yanda kika wani zaburo kika tashi
zaune” yatsina fuska nayi tare da nufan Toilet da niyar wanka kiran Ummi Fadilah tayi tare da
sanar mata Jiddah na gidanta jin haka yasa Nabil nufo gidan cikin gaggawa fitowa nayi ɗaure
da zani yayinda nake goge gashi na da towel kasancewar na wanke shi ganin mutum kawai
nayi a gabana take nasa ihu ina shirin zubewa saboda tsananin tsoron daya kamani da sauri ya
taryo ta cikin jikinsa yana shafa fuskanta domin da gaske de sumewa tayi ruwa ya shafa mata a
fuska tare da zubama kyakkyawan fuskanta ido yana kallon yadda take buɗe idanunta a
Hankali tureshi nayi ina niman zani na wani irin Kyakkyawan Murmushi yayi tare da danneta
yana faɗin “Im so sorry Jiddah nasan na aikata abubuwa da yawa Amma dan Allah kiyi Haƙuri
komai ya wuce wallahi nayi nadama kaina bisa wuyana ina mai bada haƙuri kodan albarkacin
Ammah da Ummi ayi haƙuri a yafe mini Please Sweetheart” ya faɗa cikin kashe murya tare da
zuba mata narkakkun idanunsa shuru kawai nayi domin bana jin zan sauko lokaci ɗaya a
bazata naji bakinshi cikin nawa da wani irin masifan na fara ƙoƙarin tureshi ina faɗin “Kawai
kace min kazo kaji daɗi dani ne, kazo na Buɗe maka ƙafa bayan irin cin mutuncin da kamin
akan wata karuwa..” haɗe bakinsu yayi tare da girgiza mata kai.
Wani irin lafiyayyen kissing ɗinta yake tare da shafo na shanunta laƙwas tayi tana jinshi domin
gabaɗaya yayi nasaran kashe mata gaɓoɓin jikinta kifa kanshi yayi yana wasa ƙirjinta sosai tare
da faɗa mata wasu irin kalamai masu wiyar ɗauka kuka ta saka tare da ƙanƙameshi tana faɗin
“Me yasa ka kasa fahimtar irin soyayyar da nake maka Sir Nabil! mai yasa! Wallahi ina ƙaunar
ka sosai, Yayana ina sonka soyayya mara iyaka amma ka kasa fahimtata duk wani kawaici da
kunyata na ajiyesu gefe na fito fili na fayyace maka Sirrin zuciyata kaine muradina tun lokacin
dana fara arba da kai, sai dai nayi ƙoƙarin nesanta kaina da kai ne saboda sanin matsayi da

kuma son kare mutunci da martaban Aure na..” shafa fuskanta yayi yana faɗin “Na sani nasan
kina sona nasan kuma kinyi haƙuri da halin ƙuncin rayuwa kinyi haƙuri akan komai lallai ke
macece da kowa zaiso ki zamo mallakinsa Ina miki nikin ba nikin ƙaunar da kike min. Ina so kiyi
Haƙuri kizo mu ƙarasa rayuwarmu kina da farinciki da jinin daɗi domin Ahalinki suna can suna
tsumayin zuwanki Kowa nason sake ganinki kowa na murna dajin cewa ke ɗin ɗiyar
Asma'ulhusnah ce ke ɗin fa Autar Ummanta ce shalelen Ummi Ƙanwar Nuwairah da Nabil
matar Nabil farinciki a gidana..” (tsakani da Allah wanga soyayyar ta tsumani..)
rufe mishi baki tayi da nata daga haka suka lula duniyar ma'aurata can ƙololuwan sararin
samaniya Cike shauƙin So da Ƙauna suke faranta ran junansu.
Bayan komai ya lafa ne ya kalleta tare da jan karan hancinta yana faɗin “Ki shirya sai mu wuce
gidan ummi tare ko?” Ajiyan zuciya ta sauke tare da gyaɗa mishi kai, tare sukayi wanka sannan
ya tayata shiryawa wanda gabaɗaya cikin shiririta aka gama shirin fita yayi yana jiranta a waje,
shigowa Fadilah tayi tana kallon Jiddah ta fashe da dariya “Taɓ lallai har an kammala soyewan
Allah yasa de ba'a ƙone ba..” da ɗankwalin hannunta ta jefi Fadilah tana dariya “Kinga bana
son sa ido fa” Fadilah tace “Babu wanin nan munafuka ana so ana kaiwa kasuwa, sai a cigaba
da haƙuri kisan lamarin rijalu sai ana haɗawa da batun haƙurin nan” rumgumeta Jiddah tayi
tana faɗin “Na gode sosai Bestie sai kin shigo kenan” daga haka sukayi sallama gidan Ummi ya
kawota sannan ya nufi hotel ɗin daya sauka domin yaƙi zama cikin gidan nan ummi ta shiga
faɗa kaman zata ari baki domin ranta yayi matuƙar ɓaci, “Kiyi haƙuri Ummin mu tunda tana cikin
ƙoshin lafiya ai Alhamdulilah koma dai menene ya wuce kema Jiddah baki kyauta ba domin kin
ɗaga mana hankali sosai” cewan Hanisa “I'm so sorry nasan ban kyauta ba amma in sha Allahu
hakan bazai sake faruwa ba ayi haƙuri Ummi na Please kiyi mun ɗan Murmushi mana haba
uwata kin san de bani da tamkar ki a yanzun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login