Showing 9001 words to 12000 words out of 82684 words
Chapter 4 - Sirrin Daukaka Book Complete by Aisha Jb Mrs Danshuwa
na ya fara barazanar barin ganagan jikina "Daka siya kace min
Hauwa'u gashi? ko kace naci ne da zan d'auka ? an fad'a maka ni mayunwaciya ce , to ban
bukata shi kenan! d'auki kayanka, Arab ka shafa min lafiya ka fita sab gata..." tureni yayi na
bugu da glass din motar me shegen karfi abin bakin ciki kainane ya fashe amma glass din ko
tsagewa beyi ba haka ya figi motar a guje ..
ajiyan zuciya kawai nake iyayi ga hawaye da yaki dena tsayawa kaina wani mugun ciwo yake
min azzalumin nan ko ya juyo yaga halin da nake ciki ajiyan zuciya na sauke me karfi domin
wani gargada muka shiga shi kuma yaki tafiya a sannu, seda na kara buga kaina daga nan
bansan meya faru ba tsaban a zaba se farkawa nayi na ganni kaina jikin wata dattijuwa fara sol,
ga kyau ga ,gayu jikinta mul-mul ajiyan zuciya ta sauke shi kuwa yana zaune fiskan ,kan da d'an
dama cikin tsamin hausarta tace "jeka kira likitan" yana fita ta dawo da dubanta gareni rufe ido
nayi itama bata takura min ba, ashe suma nayi koda muka iso zari'a ya tab'a ta yaji jikinta zafi
rau gashi bata motsi shine y ciccib'e ta a falo yaga iyammu "cikin takaicin halin d'an nata tace
koma kayi sallama domin ba d'akin kafura ka shigo ba, ai ko arnan suna konkon.."
"Dan allah iyanmu kiyi hakuri ki duba halin da ƴar nan take ciki.. "dakata! ince bakin halin naka
ne ka gwada mata, dukanta kayi ka fasa mata kai bayan rashin tarbiyan da ƴan boko suka nuna
mata (matan shi take nufi) kashe musu 'Ya kake son yi ba, kaje ni ba abinda zan muku na zare
hannun na zaga iyalanka.... "dan girman Allah ki gafarce ni wallahi ba abinda kike zato bane
iyanmu ba abinda na mata" share shi tayi taci gaba da karatun ta, ajiye jiddah yayi kaman ze
mata kuka da kyar ya shawo kanta shima da sharaɗin ze tsaya a gidanshi ya zama namiji, ya
amsa mata ne kawai amma bejin ze samu karfin gwiwar tsawatar musu domin suna haɗa mishi
zafi su gwara kanshi yanda suke so ne, daga karshe seda suka danganta da asibiti tare da likita
suka dawo ya cire min karin ruwan shayi ta had'a min kad'an nasha na shiga yun kurin amai
iska ta ringa hura min tare da watsamin ruwan sanyi har aman ya koma "sannu fa Allah yana
sane dake fatana ki zama haske a rayuwarshi Allah ya dubi lamuranki ya saukaka miki, ubangiji
ya ɗaukakaki" wani kuka ne ya kwacemin bata hanani ba seda nayi me isata kafin nayi shuru
lna sauke ajiyan zuciya sallama aka bamu muko koma gida kaman wani me aljanu mun isa
gidan ko cikakken min ashirin bamuyi ba ya mike lokacin lna kwance a doguwan kujera iyanmu
tana duba ishmawiy ya mike "Iyanmu zamu kaduna domin a gidan sawda zata zauna"
cikin gatse tace "tsawon shekara nawa?" gaba yayi tare da ɗaga kafaɗa "zuwa lokaci da allah
ya takaita zamanta a gidan... "kaci gidanku" murmushi yayi tare da fita kallo na tayi tare da juyar
da kai tausayin yarinyar take ji, i'ta kuma haka Allah ya kaddara mata shiga cikin iyalan lbrahimu
Gidan da ake rayuwa cike da bakar kishi, "tashi ki bishi Allah ya tsare, zanso ki mayar da
hankalinki kan karatu musammam ma, ta mahamadiya domin zata temaka miki qwarai wajen
inganta rayuwar aurenki zanso ki fita zakka wajen ilimin islama a cikinsu domin Allah ya jefoki
ne tsakiyar matan da suka jika da boko matan da basu bawa mijinsu mihimmanci kaman yanda
suka maida hankulansu kan ayyukansu ba, zance ma gwara Nafisah" nide ban bawa zanceta
muhimmamci ba domin na rasa inda ta dosa Allah ya temaka ma nayi wanka asibiti ..
Ga link Dan Allah idan kinsan ba karantawa zakiyi da comments ba karki shiga!
https://chat.whatsapp.com/HsMb0FG2FMMFCBLoDfHoyQ
*Maman Faruq*
12/26/23, 9:00 AM - UMMI JB: *♡SIRRIN ƊAUKAKA♡*
_Wattpad@ayshajb_
®️í ¼í¼�
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..*
FREE BOOK
Page6
Jingine da motarshi yake yana ganin fitowarta ya shigan tare da rufe murfin a hankali nake
tafiya har na karasa inna shiga yaja motar juyar da kaina nayi gefe har munyi nisa da tafiya
kafin ya waigo. "i'tace mahaifiyata iyanmu mu Shida ta haifa, Sawda ce babba tana aure a
kaduna malamace yarinyarta ɗaya tal, sai Musa shi kuma yana sudan da iyalanshi sai Abbas
shima yana sudan Aminu yana Bauchi nine na biyar se karaman mu Zaliya wanda take ABU
Mahaifin mu ya rasu shekara shida kenan" bance mishi komai ba har muka isa Kaduna
Gidanta baban gidane a gefe guda akwai makaranta wanda ake koyar da matan aure har da
na ƴan mata da yara megadi ne ya buɗe mana get yana de-deta tsayuwar motar muka fito yana
gaba inna biye dashi a baya Da sallama muka shiga falon ba kowa zama yayi tare da nuna min
kujera memakon nayi yanda yace sena zauna a kasa.
Shuru mukayi na yan mintuna kafin ya katse shurun ta hanyar fad'in, “na kawoki nan ne domin
ki zauna na d'an lokaci ki mayar da hankalinki kan karatun da zakiyi domin matana ba jahilai
bane , ko wacce da kika ganta da iliminta da sana'arta matsalar ki ne ki nutsu kinyi karatu domin
inganta rayuwarki domin mahaifinki Yana da burin kiyi karatu banda shirme... "Hmmm kasan
aiki nane shirme ai Daman nace matanka jahilai ne , daga zuwa na sun nuna min kalar tasu
ilimin, da kace na mayar da hankali ko karna mayar ince hankalin nawa ne? Kuma a jikina yake,
nagode insha allahu zanyi karatu zan nutsu kodan nacika burin Raina" Gyad'a Kai yayi kafin
yace. “yana da kyau.." "Daman ba kyau ne?" Na fad'i Haka inna lanƙwasa hannuwana..
"Ki kiyaye harshen ki, kisan abinda zaki ringa furta min karki bata min rai"
Sunkuyar da Kai nayi kasa.
"Kayi hakuri insha allahu zan kiyaye"
"Assalamu alaikum" tace kafin ta karaso cikin shigar kamala a nutse ta zauna kusa dashi.
"Amin wa'alaikis Salam barka sawda malama Sawda ummin halimatu"
Murmushi tayi kafin ta juyo gare ni "inna yini" nace mata murmushi tayi kafin tace "lafiya lau
hauwa ya gajiya da hakuri da k'anina?" Ta karasa maganar tana kallonshi bance Mata komai ba
had'e fiska yayi "haba! Dan Allah ai seki sa ta renani" a hankali yayi maganar,
Girgiza Kai tayi kafin tayi waya kichin "Yahgana ki kawo abinci" kashe wayar tayi , tare da
mikewa "Zo muje kiyi wanka da sallah kafin ta kammala"
Ɗakin Halima ta kaini tare da nuna min Banɗaki wanka da alwala nayi inna fitowa ta shigo da
bakar leda "Yanzun arab ya aiko kiyi amfani dashi. Bance Mata komai ba ta fita Dogayen
rigunane guda Shida se Himar da kananun tarkace a Raina nayi tsaki kafin na saka D'aya daga
cikin kayan sallahn dake kaina duka nayi kafin na kwanta saman salayan Nan da Nan barci ya
dauke ni cike da gajiya..
Yana ganin shigarsu shima ya mike masallacin dake wajen Gidan ya nufa anan yayi sallah ya
dawo abincin da aka jera ya zuba ya fara ci, Ummin halima ce ta shigo "Hauwan bata fito ba?"
Ba tare da ya D'ago ba ya Gyad'a mata Kai.
Dakin ta shiga Nan ta isketa kwance Girgiza kai tayi tare da dawowa "Ya naganki ke d'aya
Jiddan fa" "Barci take"
Shuru ne ya biyo baya na d'an lokaci kafin ta tsake shurun ta hanyar fad'in "Muazzan naga
Goshin yarinyar Nan da ciwo inna fatan ba matan ka bane suka sila?" Da sauri yace "a'a ba ko
d'aya me ruwan su da i'ta da zasu tab'a ta" Qurr ta masa da ido badan ta yarda ba tace shi
kenan.
"Wani shawara ka yanke game da rayuwarta?"
"Eh to in naga zan baki kudi kiyi yanda ya dace domin anan zata zauna inna tunanin inna
had'ata da matana Gaskiya Bazata ji dad'in zama cikin su ba, abin da ya dace kawai tayi zaman
ta Nan tunda Kinga Ga Halima naga Hanisa ma tana Nan (Yar Aminu tana karatu Gurinta).
Katse shi tayi "Ban ki maganarka ba, Amma har tsawo wani lokaci Zaka tsaya a Gidanka
yaushe zaka zama namiji me fad'a aji, haba! Wannan wacce irin rayuwa ce ace mutum bashi da
'Yanci shida gidanshi baka isa ka zauna na minti biyar ba tare da an tada hayaniya ba inna jin
zafin wannan abun Mata uku Amma duk ba me Hankali.." Mikewa yayi cikin Gajiya da jin
kalaman ta sosai suke tab'a zuciyarshi murya a dakile yace "Zan tura Miki kudi kiyi duk yanda
ya dace ni na tafi"
"Dole ka tafi tunda an tab'a maka Zinari Allah ya kyauta saura Kuma ka share Yar mutane dan
nasan halinka sarai... "Daman me zan Mata? bana tunanin zan zauna da yarinyar nan fa, domin
bata cikin tsarin matan da nake so Gata bak'a yar K'auye ba ilimi kai bata min ba ko kad'an
sallamarta tayi taje tayi rayuwarta..."
"Allah ya nunamin ranar da zaka zo kace in baka Hauwa Allah ya kaimu lokacin da har kasa
zaka rok'e ni in baka matar ka ni kuwa a lokacin zan gwada mata bade haka kace ba? Zaka ga
yanda Bak'a yar K'auye zata b'ata Lissafi da tunaninka a sauka lafiya"
D'aga kafad'a yayi alamar maganarta bai dameshi ba fita yayi yaje ya bawa motarshi wuta hotel
ya kama domin washe gari ze juya,
Tun lokacin data bar d'akin na farka Band'aki nashiga tare wanko fiskata nabi bayanta Amma
kafin na karasa na farajin maganar Arab da Hannun na rufe bakina domin wani i'rin kuka me
ciwone naji Yana shirin qwace min duk ni d'aya yake jifa da kalaman Nan, me namishi da zafi
silalewa nayi na zauna a qaka hawaye na bin fiskata bansan iya lokacin dana d'auka ba naji
sallaman mutane biyu da sauri na tashi na share hawaye na falon na shiga cikin fara'a tace
"harkin tashi bisimillah zoki ci abinci" Sunkuyar da Kai nayi kasa a hankali naji yaran da suka
shigo d'aya wacce nakega zamuyi sa'anni tace "Ummina wacece wannan Black beauty din?"
Matar Kawun ki ce wacce nake Baki labarin suna hanya" zata sake magana na kusa da ita ta
make bakina "Haba Hanisa meye haka.." wacce tacewa Hanisa na kalla a qalla zata Kai sha
shida , tace "Wallahi Halima kin fiya bin ƙoƙof" hararanta Halima tayi kafin tace min ."ya Sunan
ki"
"Jiddah"
"Suna me dad'i zamuyi Qawance?"
Murmushi nayi kawai tare da mayar da hankalina kan abinda nake ,
Wani i'rin kallo Hanisa take bin ta dashi ba tare da kowa ya lura da hakan ba, mikewa tayi ta nufi
Dakin su wayarta dake makale da Caji ya cire tare da Kiran mahaifiyarta tana d'auka tace "hello
umma Kinganta kuwa yarinyace fa wacce a yanzun take 14, akwai kyau duk da bak'ace Wallahi
umma tana da bala'in kyau sekin kalli hancinta da qwayar idonta dayake Nan kaman na mage
zaki tabbatar da hakan"
*D'aya B'angaren*
Mikewa Bashama tayi cikin bala'in tashi hankali "Hanisa wallahi tunda na rasa Arab to Wallahi
D'aya bayan d'aya dukk'an su sesun rasa shi abin takaici ya rasa wacce ma ze aura se yar
cikinsa a l'na ya auro ta ma" "Wallahi umma ban sani ba Amma karki damu a hankali dan
binciko Miki" Sallama sukayi tare da kashe wayar,
Rayuwata a kaduna wani i'rin rayuwana da zance Alhamdulillah domin Ummin halima tana
girmama lamarina uwace na gaban kwatance Wanda ta tsaya a gidanta makarantar su Halima
wacce ta nace da se munyi qwance aka sakani zamu tafi takwas Se karfe D'aya zamu dawo
muna yi sallah zamuyi wanka muyi shirin islamiya Wanda yake mallakin Ummi ne tsakanin
makarantar da Gidanta babu nisa sosai sannu a hankali lokaci ke tafiya har na shafe tsawon
shekara biyu a gidanta na mayar da hankali sosai a kan karatuna ban cika magana sosai da
mutane ba cikin Kankanin lokaci Allah ya d'aukaka al'amura na kowa son qwance yake dani
Sabida kokari na, Amma basa gabana domin Wallahi Halima kad'ai da Hanisa sun isheni
kokarina da qwanzo na yasa malaman makaranta ke bala'in Sona Aure kan na watsar dashi
domin Daman ban d'aukeshi da wani mahimmanci ba rayuwana nake cikin qwanciyar hankali
yau a matukar gajiye nake hakane yasa driver na sauke mu na shiga Gida da sauri na fad'a
d'akinmu kasancewar inna fashin sallah yasa nayi wanka tare da fad'awa saman gado Hanisa
da shigowarsu kenan tace "kai Jiddah yau Kuma barci ne" ya mutsa fiska nayi tare da juyawa
mata baya domin bana jin yin magana tsaki tayi domin wannan halin nawa na bala'in bata
haushi Sabida in na Mata i'rin Haka seta fita sabgata ni kuwa ban damuwa , l'nama nake sanin
na b'ata mata rai Halima ne de dake bata da hakuri Nan zata hauni da masifa takan ce.
"Gaskiya jiddo banson iskanci da shariya ya inna Miki magana zaki bawa iska ajiyata?"
"Kiyi hakuri" iya abinda nake ce Mata kenan, duk da haka be Mata se tayi kananun surutai i'ta
bata son wannan halin nawa na fiya miskilanci wani lokaci se Ummi ta daka mata tsawa take
hakura da mitan,
A hankali nake kirga kwanakina har na shiga kirga mako har na koma wata ayau nake lissafin
shekarata Hud'u a Gidan ya kasance inna da sha takwas kenan mun kammala sakandiri lafiya
sakamako yayi kyau Dan murna har azumi nayi domin duk nafisu Makin me kyau, a so biyu
Arab ya tab'a zuwa tsakanina dashi gaisuwa dan nama manta da matsayinsa gurina. Zaman
wata uku mukayi kafin Ummi ta samo Mana wani makaranta ban tab'a tsintar kaina cikin
damuwa da bak'in cikiba seda ta shilar shigata jami'a domin seda na gwammace da banyi
karatu ba a rayuwata nayi kuka Kuma har gobe inna kuka domin abinda nayi ban tab'a tunani
ze shafi ahalina ba, tunda na had'u da Arab nake kuka Kuma har yanzun kuka nake.
Cikin doki da murna muka fara zuwa makaranta a gida kuwa Ummi ta dage sosai gurin koya
Mana girke girke yau da huri muka muka fito inna zaune nida Halima Hanisa muke jira Halima
ce ta mike tare da fad'in "Kinga bari na duba abu a library inna zuwa" hankalina na kan karatun
da nake nace Mata "toh" batare da na d'ago ba, wata Yarinyar dake nesa dasu tana ganin tabar
gurin ta karaso muga desk din tayi "Hi Jidda Usama" d'agowa nayi domin sarai nasan muryanta
tun shigowata take bibiyata ta nace min yanda kuka San cingon, murmushi tamin Tami nima na
mayar Mata roban yogurt biyu ta ajiye tare da tura d'ayan gabana "bisimillah" Girgiza Mata Kai
nayi domin kawa kawai naji zuciyata ta kasa nutsuwa da i'ta marerece min tayi ni kuwa naki
karshe mikewa nayi tare da kashe littafaina nace "Aliya nagode azumi nake" juyawa nayi na bar
gurin tab'a Bluetooth din dake makale da kunninta tayi "kunde ji Wallahi taki Sha dan Allah zan
gwada in tasan wata bata San wata ba"
Cikin tsananin b'acin rai ta ture Yogurt din tare da barin gurin daman ba tafiya nayi ba duk
abinda ta fad'a inna jinta d'aura hannu nayi akai tare da sallati Nan da nan hawaye ya cika
idona wake bibiyar rayuwata ne? Banida me bani wannan amsar cikin tashin hankali na fara
kokarin tafiya ji nayi an dafa kafad'a na da sauri na juya Hanisa tace "Jiddah lafiya na ganki ke
d'aya me kike anan? Halima fa" cikin rawan murya nace "Taje duba abu ke muke jira tun d'azu"
Hanisa tace "Amma meke damunki naji muryanki haka?" Girgiza Mata Kai nayi, "bakomai"
Karasowan Halima yasa muka tafi Gida tun daga wannan lokacin na rasa walwalata Hanisa tayi
tambayar duniya naki fad'a mata Halima ma tayi mita har ta gaji tabari wasu i'rin mugayen
mafarkai nake sosai na dage da addu'a saraka da azumi duka inna yi domin sakada maganin
masifa, a hankali na fara wani i'rin rama , Daman nagi na gwanar Kib'a ba, Nan da Nan na
zabge .. Ummi de ta zuba min ido bata tambaye ni ba domin ta lura inna da mugum zurfin ciki..
_Banyi Alkawarin Typing kullun ba Amma isha Allahu na dawo zaku ringa jina inna samu lokaci
Nagode_
https://chat.whatsapp.com/HsMb0FG2FMMFCBLoDfHoyQ
Ga link Dan Allah idan kinsan ba karantawa zakiyi ba karki shiga, in kinsan bazakiyi comment
ba karki shiga!
*Maman Faruq*
12/26/23, 9:03 AM - UMMI JB: *♡SIRRIN ƊAUKAKA♡*
_Wattpad@ayshajb_
®️í ¼í¼�
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION..í ½í³ší ½í³š*
7..
Tunda nayi sallar subayi na koma azkhar dinma da kyar nayi domin wani i'rin mugum kasala
nake ji, kwanciya nayi Hanisa da Halima sun fita domin al'adace da zaran mun idar da sallah
zamu fita munyi shara mu gyara gidan duk da akwai masuyi Ummi bata sangartamu ba, aiki
muke sosai domin nike girki Sabida bala'in kaunar abinci na mayar da hankali sosai gurin
karance karance littafan girki ban b'ata lokaci gurin karatun novels, kamar yanda na maida
hankalina gurin, Girki Hanisa kuwa gwanace gurin had'a turaruka masu kyau da khamshi Tawa
Halimat an barta gurin zanen lalle da kitso,
"Masha Allah yan Mata na sannunku ubangiji ya baku mazajen Auren nagartattu Wanda zasu
rike mu ku, rabbi ya maku mazan da zasu d'aukaka daraja da martaban ku, inna Hauwa?" Ta
karashe maganar tana tambayar su, murmushi sukayi dukk'an su, cikin jin dad'in addu'ar ummi
Hanisa tace "Ameen Ummin mu, Jiddah bata jin dad'i tana kwance d'aki" Halima ta karb'i
zancen da fad'in "ummi bansan abinda ke damunta ba, ko magana bata son yi"
"Subhanalillahi bari na dubata"
Hanyar d'akinsu tayi,
"Wallahi duk se naji wani iri in-law, ba lafiya" cewar Hanisa kamar zata fashe da kuka Haka tayi
maganar..
Ajiye wukar da take yanka lawashin albasa Halima tayi "bari kawai nima karfin Hali nakeyi
Amma na damu