Showing 48001 words to 51000 words out of 82684 words

Chapter 17 - Sirrin Daukaka Book Complete by Aisha Jb Mrs Danshuwa

bud'e min Kofa Hauwa!" K'ememe taki bud'e Mata kofar Haka har ummi ta gaji ta koma falon
ta zauna.

Wayarta ta d'auka tare da Kiran Nafisat tana d'auka tasa mata kuka. "Lafiya?" Nafisat tace mata

"Maman Jamil wani nauyi zan d'aura miki Ga amanar Aakif dan girman Allah banida wadda zai
masa Kyakkyawan rik'o sai ke, Ki kula min da Yaro na dan Allah" kashe wayar tayi tare da
fashewa da sabon kuka. "Allah kana gani Allah in wani laifi na maka wadda kake Hukuntani
Ubangiji na tuba, Allah ka yafe min.."
Maman Faruq
12/26/23, 9:03 AM - UMMI JB: ♡SIRRIN ƊAUKAKA..!♡*

Farin Jini Writer's Association

Page23.


Haka ta wuni a d'aki tana kuka ko lek'owa waje batayi ba, rayuwar daki tacigaba dayi, Bata jin
dad'in komai  ko abinci ummi ta kawo mata sai tayi da gaske take cin kad'an , kukan d'anta take
yawanji yana cika kunnuwanta Ga zaurawa ta ko'ina zuwa sukeyi , bata san ya'akayi jama'a
suka san bazaurace i'ta ba, Yau da abin ya i'sheta ne ta fito d'akin ummi ta shiga tana sallan
walaha , zama tayi kusa da i'ta tana sallamewa ta kwanta jikinta tare da sakin kuka, addu'a
ummi tayi ta tofa a ruwa d'agota tayi tare da Sanya kofin a bakinta  Bisimillah tayi tare Da
shanyen ruwan tana sauke ajiyan numfashi. “Ummi.." kasa karasawa tayi sakamakon hawayen
dake zariya saman fiskanta share mata fuska ummi tayi “Allah ya sanya Dangana a zuciyarki
Ubangiji ya sassauta wannan zafin ran da kike fama dashi kiyi hakuri kiyi hakuri,  ki fauwala
Allah lamuranki ki cire damuwar Aakif wiya bata kisa..." Hannuwan ummi ta rik'e

“Wallahi bazan i'ya ba, 'Dana na cikin wani hali Yana bukatar kulawata Dan Allah ki rok'eshi
ummi ya bani Yarona!  'Dan uwanki ne ,Bakiji yadda kunnuwa suke jiyo kukansa ba, Kullun
mafarki nake dashi yana kuka Yana mik'omin hannu ummi.."

“A Gabanki so nawa inna kiransa ba ya d'aukan kirana so nawa inna tura masa saƙo baya bani
amsa laifi na kike ganin ko? Zakice nafiya son Kaina da ƙanina ko Hauwa'u?.." zataci gaba da
magana Jiddah tace. “Kiyi hakuri ummi" daga Haka ta mike ta fita, d'akinta ta koma.

  Bayan sati biyu.

Fitowarta kenan daga wanka taji yaro yayi Sallama Himar ta saka tare da Fitowa “wa kake
Nima?" Yaron yace. “wai ana Sallama da Jiddah.."

"Koma kace bata Nan" har zai fita ummi dake Fitowa tace “Je kace tana zuwa"

"Amma ummi.." katseta tayi “Kimanin wata takwas kenan duk wadda yazo sai ki Kore shi me
yayi zafi Jiddah?" Sunkuyar da kai tayi K'asa .

“Babu Aure cikin tsarina a Yanzun d'ana kawai nake bukata, ummi duk wadda ya aureni Yanzun
gangan jikina ya Aura zuciyata da tunani na yana ga Yarona, ki barni ummi bana bukatar wani
Namiji cikin Rayuwata!" Ummi tace. “Laifi wani baya shafan wani shalele Nah, in har na i'sa jeki
shirya ki fito.."  ‘Daki ta koma tare da saka doguwar rigan atamfa shigowa ummi tayi tare da
kallonta sama da K'asa “wani i'rin shigace wannan? Haka zaki fita Baki shafa mai bare Hoda,
Yanzun wannan katon Himar d'in zaki saka? Haba Jiddah ban hanaki suturta Jikinki ba, amma
ki cire wannan Himar d'in ki saka mayafi yaushen rabon da kiyi kwalliya ya kamata ki sanyawa
zuciyar ki nutsuwa"

“kwalliyar me Ummi? A Yanzun ban bukatar wani Namiji yaga kyawuna bare har na rud'ashi,
zamana a Haka yafi min wallahi in har kika ce na sake shiga na fasa fitan!" Murmushi ummi tayi
“Allah ya sauke wannan shed'anin dake kanki"
"Ameen" tace sannan ta fita.

Batayi Sallama ba ta bud'e gaban motar da yake “Kaine wadda ke niman iso dani ko ? da alama
an fara bud'e babinka na Karshe To bara na fad'a maka ban shirya Aure ba, Bak'in aljani gareni
abinda yasa Mijina ya sake ni kenan Wallahi kana Aurena Zaka mutu in kashirya ma yaranka su
zama marayu to.." da sauri Mutumin yace “a a Wallahi" murmushin jin dad'i tayi sannan tace
“Shi kenan zaka i'ya tafiya"

Tana tsaye Gurin ya tada motarshi sai da taga fitarshi sannan ta shigo Gida, Haka ta ringa
Koran duk wadda yazo Gurinta da Sunan Baƙin Aljani gareta. Wasa wasa aka shafe shekara da
watanni Abin na Bata mamaki ganin yadda take Wahal dasu Amma har yanzun Banzaye
wawaiyu basa ganewa Matsorata ne, ta kanyi dariya in ta tuna yadda suke rikicewa da zaran
tace Bak'in Aljani gareta. i'do kawai ummi ta zuba mata,  randa abin ya i'sheta ta isketa d'aki
lokacin tana duba sakonin ta Email d'inta “Hauwa'u" ummi ta kira sunanta. Kallo d'aya Tama
ummi sannan ta d'auke Kanta domin tasan abinda ya kawota “Na'am Ummina" janye laptop d'in
tayi daga Gareta. “Hankalin ki zaki bani magana zamuyi" tagumi tayi tare da zuba mata i'do
“Maiyasa duk wadda yazo niman Aurenki kike koransa? Ki fad'amin Auren ne baki so ko me?"

Hannunta ta matse har sai da yai Ƙara. “Ummi bawai Auren bane bana so ban shiryawa Auren
bane,  sabida har Yau, ban samu wadda zuciyata tayi na'am dashi bane, Nifa ba Budurwa bace
ya kamata in samu nutsattse wadda yasan mutumci da Kuma kimar d'iya mace , Namijin da zai
iya kula dani nake bukata inna son Namijin da ko yau na mutu zai ringa tunawa  dani Ummina
inna son Namiji Kamili mai Addini inna son Namijin da yasan  wacece mace , abin Nufi Namijin
da zaiyi Hakuri da Halayyar ta Akwai Mazan da Basu da Hakuri da zaran mace ta b'ata musu
zasu hauta da fad'a ta inda suke shiga ba ta Nan suke fita ba, inna son Nagartacce wadda zai
na min Uziri wadda da zaran nayi masa kuskure Zai rarrashi zuciyarsa wadda da zaran na ɓata
masa in na bashi Hakuri zai karb'i Uzirina Ya Hakura inna Son Namijin da zai tarairaye ni inna

son Namijin da zai shagwaɓa ni inna son namijin da zai mai dani tamkar yarinya inna son
Kimtsattse tunda Kinga ni watsattsiya ce ko Ummi? Banida Nutsuwa! Mazinaciya, inna son
Salihi wadda zai karb'e ni a ko ya-ya nake, inna son Namijin da zai Mutumta ahalina Ya
girmama min Ummina ,Yah Allah Babu wani sarki Bayan Kai, Allah Kai mai Kyauta ne, Ubangiji
kamin Kyautar Bazata! Allah kai mai azurtawa ne, Yah Rahimu ka azurtani da Kimtsattsen Miji.
Allah kai meji Ne, Ubangiji ka amshi rok'ona Albarkan Wannan rana ta Juma'a..."

Wani i'rin kuka take mai tab'a Zuciya, tana magana. i'ta kanta ummi jikinta yayi masifar sanyi a
duniya, Babu kalma mafi Muni da za'a jefeka dashi kaman ace maka mazinaci abun da ciwo
shiyasa har yau take jinshi a ranta i'ta a iya sanin da tayiwa Jiddah yarinyar Akwai yafiya Amma
da wuya ta manta abinda aka mata duk da tariga da ta yafe mishi tasha jin tana addu'ar Allah
yabi Mata Hakk'inta Akan K'azafin da aka mata, abin da ciwo sosai Amma ya za'ayi sai Hakuri.

“Ummi kina ganin kaman ban kyautawa ko? To kiyi hakuri tunda Aure kike so nayi zan tsayar da
Mutum nayi Amma nasan bani da nagartan da za'a Soni ko Ummi?" Ta karasa maganar tana
tsare Ummi da idanuwanta masu Kama da mage, mayar da kukan dake son kwace mata tayi.

“inji wa? duk mai niman mace ta gari yazo gareki, Wallahi kina da nagartan da za'aso had'a
zuri'a dake, matakin nasara shine hakuri, Kawaici d'auke Kai, ka mayar da komai ba komai ba,
ka d'auki rashin gaskiya a inda kasan kai mai gaskiya ne, ka rufawa d'an uwanka Asiri! Duk fa
kece mai wannan halin shiyasa kullun nake takaicin maiyasa Ibrahim ya barki? Wani lokacin
nakan masa uziri sanin baya cikin hayyacinsa, kiyi hakuri Hauwa'u insha Allahu Ubangiji maji
rok'o ne Allah zai baki Mafiyinsa"

Rumgumeta nayi inna kuka Wallahi inna Mata k'auna, na tsakani da Allah “Nagode Ummina
Allah yaja da ranki"

Shafa kaina tayi “Amin shalele Nah" Daga Nan ta shiga mata nasihohi har aka Kira azahar
sannan tabar d'akin kwanciya nayi kasancewar inna fashin sallah Nan na tunduma tunanin
Duniya, Kiran da sahiba ta ƙwala min ne yasa ni mikewa “Maman Aaleen" Murmushi tayi tare da
Zama gefenta "Na'am Maman Aakif Kinga tashi muje Kasuwa zaman gurin d'aya ya i'sa haka"
Yamutsa fuska nayi "Ke Bari ban son fitan ne kawai" da sauri tace "Haba Sahibata taso muje
muga Gari Allah da kaina zan tuka motar!" Ba yanda na i'ya ganin ta nace yasa ni miƙewa na
Shirya.

Mun tadda Ummi Zaune da Yan biyu tasowa sukayi tare da gaishe ni shafa kansu nayi inna jin
dama nawa ne haka “Ya karatu Yan biyu na" had'a baki sukayi Gurin fad'in “Alhamdulillah
Anti-meh" Halimatu tace “Hajiya Ummi ga angwayen ki zamuje Anguwa da sahibata” Ummi tace
“Hanisar fa wato Kuna ware min 'Ya a duk lokacin da kuka keb'ance Ku biyu Ko? bana son
Haka fa, banson wariya" Hararan Halimatu nayi “Nifa Ummi ba ruwana  i'tace dai da kini bibinta
gwara ki fad'a mata" Jan hannuna tayi muka fita tana mai cewa. “Naji Ummi ayi Hakuri za'a
Gyara" muna karasawa Gurin motana ta fasa dariya nace. “Yar Banza Dole kiyi dariya"

Bud'e motar tayi tashiga Nima na shiga d'ayan gefen “Allah sarki Sir Nabil Mutumin arziki..."

Buga sitiyarin motar nayi “Ke zanci abun kazanki Wallahi in baki rabani da maganar nan ba,
haba ke kiyi Hanisa tayi! Mutumin Nan Yanzun haka ya mance daku Kuna Nan Kuna damin
kanku Akan shi..." Da sauri Halima tace. “Wa? Wallahi haihuwar su Aaleen Setin Dirowa na
kayan Yara ya sai min ga Kyautar dubu talatin cab ai Sir Nabil ba k'ashin Yarwa bane.."
“Kinga dakata! daman maganarshi ne yasa kika fito dani koya?" tada motar Halima tayi.
Anguwar Kawo  sukaje Gidan wata k'awar su, sun Sha hirar yaushe Gamo kafin ta rako su “Sai
inna Kuma Yamma nayi fa?" Na fad'a inna kallonta “muje mu d'anyi siyayya mana"

“Toh muje"  muna isa ta faka motar Fitowa mukayi wayarta ne yayi Kara muna tafiya tana waya
inna gaba Bansan ya akayi ba na bige wata mata cikin masifa tace “Dalla can ke makauniyar
ina ce?" Kayanta na shiga kwashewa “Yi hakuri..." Ai kasa karasawa nayi wazan Gani.. ihu tayi
tare da kaimin Rumguma “Jiddah..!" Nima cikin jin dad'in nace “Fadila kece?" Jan hannuna tayi
muka koma Gefe “Nice ya kike ya Bayan rabuwa ya iyalai ? Kuma Dan nasan Yanzun kin Tara
sosai.." dariya nayi nace “Alhamdulillah ya naki iyalan?"

“Alhamdulillah Jiddah kai gaskiya naji dad'in Ganinki sosai Anan kike har yanzun?" Girgiza mata
kai nayi “a a nade Zo ne..." Horn din da aka mata ne yasa tace. “Oga na jirana bani Number ki
zamuyi magana" musayar Number juna mukayi tare da yin Sallama “Keda waye Haka?"
murmushi nayi “Wallahi nida Fadila ce Yar ajin mu" Halima tace “ayya" tafiya muka fara yi, nan
ta siya abinda zata siya muka fito Gurin Biyan kud'i ne naja birki, inna kallon matar dake Gaban
mu kasa hakuri nayi na tab'a ta. “Ke kaman Jummai?" Juyowa matar tayi tana kallona sama da
K'asa “Hauwa'u d'iyar Asma'u da Usama, tsohuwar matar d'an Kasuwannan Ibrahim Arab!" Ta
karasa tana murmushi “Makira banyi mamaki ba tunda nasan Halinki azzaluma butulu wacce
Bata San halacci ba, ina dukiyata da kika tattara , kece sanadiyar Mahaifana ni Kuma insha
Allahu nice ajalinki Makira makaryaciya insha Allahu Zaki ga karshen ki.." dariya tayi tare da fita
bin bayanta nayi ina zaginta tare da tsine mata “Ke Kuma fa da zaki biyo matata kina zaginta..."
Katseshi nayi. “Au Allah Nagode maka matarka ce ma? Ubangiji ka i'ya had'i me Gidan hayar
mu ko? Banyi mamaki ba, domin da had'in bakinka ta kwashe dukiyata wanda yayi sanadiyar
fad'uwar mahaifina ya samu ciwon shanyewan b'arin jiki, hakan bai maka ba ka tashe mu a
Gidanka wadda sanadiyar bakin cikin nan take mahaifina ya Had'iyi zuciya ya Mutum
mahaifiyata tabi  Bayan shi insha Allahu zaku ga karshen Kun Tsoffin Banza kawai..!” Halimatu
ce tazo taja hannunta Mota ta shiga da i'ta,

“A lna kika San mahaifiyar Aaliyah da har kuke sa'in-sa Jiddah?" Bud'e i'do nayi sosai  inna
kallonta tare da jin mamakin furucinta. “daman wannan tsohuwar Banzan ce uwar Aaliyah ahh
lallai biri yayi Kama da Mutum tunda har Hali yazo d'aya ba shakka wato i'ta ce Uwar Aaliyah..."
Na fad'a inna dariya mai had'e da hawayen bak'in ciki, domin ban Macen halin da matar Nan ta
jefamu ba. “Meke tsakanin ku?"

“i'tace tsohuwar matar babana, a gonarshi ya tsinceta tana kwana wai i'ta bakuwace ya kaita
Gidan maiGari shine maiGari yace tudda Gidanshi da D'aki Kuma Yana da Hali yaje ta zauna
Gurinshi Ashe mutumiyar Banza ce mahaifina ya mata komai mahaifiyata ma Haka, domin
ganin yadda Jummai ta nuna i'ta mutumiyar Kirkice yasa mahaifiyata da kanta tace ya Aureta,

Bayan ya Aureta Nan ta fara Fitowa da halinta inda a lokacin da wayo na, inna ganin komai
Kuma inna ji Haka aka wayi gari ta siyar da Gidan da muke ciki tare da Gonan mahaifina
tatattara komai tabar Gidan dalilin Haka yasa muka shiga matsin rayuwa Bayan mun koma
Gidan haya, mahaifina ya yanke jiki ya fad'i ganin bamuda komai na hatsi ga 'Yan uwanshi duk
sun gujeshi ke Sahiba munga rayuwa a gaban idona mahaifina Ya mutu... Naga tozarta da
wulak'anci, wasu mutanen basu da tunani basa tuna Goben su, masu tuna cewa Gaba tafi baya
yawa ƙalilan ne. Abinda matar Nan Tama mahaifiyata na musgunawa Allah kad'ai zai saka
mana..."

Shuru Halima tayi tana sauraronta kafin ta sauke numfashi. “taɓ lallai wannan Mata ta cika
butulu gaskiya taci amana Kuma insha Allahu Allah zai saka muku Yanzun inna dangin
mahaifiyarki?" Jiddah tace. “Ban sansu ba!" Halima tace. “Ya kamata ki laluɓosu gaskiya!"
Gyad'a kai tayi “insha Allahu zan duba kayan mahaifiyata domin Akwai wani kundin data tab'a
bani sai dai ban tab'a bud'ewa ba. ban tab'a bincika ba, domin bana duba abinda ba'a bani izini
ba" Jan motar tayi muka fara tafiya “Ya kamata ki bincika sannan ki dibo dangin mahaifin ki ,duk
da abinda suka Miki Bai kamata ki watsar dasu ba, naka naka, Ne, duk lalacewarsa" jingina
kaina nayi da jikin Kujerar. “inna Musu aike akai akai bana jin zanje garesu Nan kusa domin
zuciyata Bata bani hakan ba"

Halimatu tace. “Allah ya kyauta" Haka har muka karaso Gida.

***
Zama tayi kusa dashi tare da d'aura kanta saman kafad'arshi Tunda suka dawo k'asar su ,ta
rasa gane Kanshi da Gindin shi, ya mace akan wata daban wacce a yanzun take matar wani
bashi da kuzari kaman yadda yake Da, shafa K'asunbar sa tayi, duk da shi ba ma'abocin tarawa
bane domin bata K'aunar ganin Gashi ko sili d'aya a fukanshi  “ƙalbi  shekaru masu yawa har
Yau, ka kasa , cire wannan shegiyar yarinyar a ranka Bayan kasan matar wani ce Yanzun Haka
sun hayaiyafa , Jin maganar Haihuwa yasashi zabura ya mike Zaune “Nuwairah tashi muje a
binkici Lafiyar ki inna bukatar Haihuwa nasa Sunan Amma h na!" Wani i'rin kallo take masa
daga bisani ta fashe da kuka tare da shigewa cikin Gidan da gudu tayi shashin iyayen su!
“wayyo na mutu na lalace Nabil zaka kashe ni inna sonka kana Son wata macen da take tare da
mijinta wayyo Innarmu" (mahaifiyar Nabil kenan) Da sauri ta fito ta kamata “Me Kuma ya had'a
ku wai kukan  kullun baku rabuwa da rigima ne? Haba sai kace ƙananun Yara girmafa ake
kodan baku ganku da Yara bane!" Ta fad'a tana kallon Nabil dake shigowa “Innarmu ki tambaye
shi har Yau yarinyar Can yake so shekara kusan takwas ko Tara ne ya kasa cireta a ranshi bare
ya Rumgumi K'addara nifa na gaji da Halinsa baya bani Kulawa a matsayina na, matarsa bashi
da wani lokaci saina tunaninta" Da sauri ta mike tayi d'akin Mama-Sadin wacce ke kwance
tsawon shekaru tun tafiyar Autarta Asma'u har yau tana kwance komai mata ake Amma tana
i'ya magana tana motsa hannunta Zaune ne dai bata i'ya mikewa “Mama-Sadin kicewa Angonki
ya kulani Yana azabtar da Ruhi na. na gaji fa Aure ba riba ko daga gurin shi nema wa yasani..."

“Lokacine baiyi ba, in yayi zaku haihu tunda kullun in kuje asibiti lafiya lau ake baku sakamako
insha Allahu lokaci na zuwa kije zan masa magana" mikewa tayi "Toh Nagode mama!"

“Ance ana nimanka Gurin aiki Amma kaƙi komawa me kake Nufi?" Sosa kanshi yayi tare da
Sunkuyar da Kanshi ƙasa “Nabil.."

“Na'am Innarmu"

“Tashi ka fita min Anan" mikewa yayi “Toh kiyi hakuri zan duba Kuma zan tafi Amma inna
mafisar ƙaunar Jiddah Babu yadda za'ayi zuciyata ya rabu da i'ta!..."

“Kinji ko lnnarmu? Kina ji a Gabanki Yana fad'a Amma kin kasa hanashi fad'a! Yah Nabil so
kake ka tarwatsa zuciyata ne! Wallahi ni kad'ai na ,na i'sheka Rayuwa duniya da lahira! inka
Auri wata mace kasheta zanyi ko ka manta Jini shuwa ce! Babana Arab ne, ko 'Yar wa ka Aura
saina kashe! Kuma na kashe Banza Kasan inna da Gata, Yayyu na zasu Tsaya min ubana zai
tsaya min" Sanin halinta na kishin Banza ne yasa mahaifiyarshi barin Gurin.

Jikinshi ta fad'a tare da sakin malalacin Kuka tureta yayi tare da barin Gidan Gabad'aya Yana
sane da motar dake binshi har ya karaso wani gurin hutawa Fitowa tayi tana rangaji kaman
wata karaman yarinya “Shekara nawa kina bibiyata Aaliyah na fad'a miki bana sonki bana
K'aunar ki, Haba! Ki barni mana ki koma k'asarki. ki dena bibiyata Haka.." murmushi tayi tare da
Kama hannunshi tana murzawa cikin nata “Sir Nabil inna sonka Ko baka sona zan zauna da kai
a Haka, wannan de da kake Hauka akan ta, tana Gidan Mijinta, to menene dan munyi Aure kai
nake jira har ilah Yau, sai ka Aure ni Wallahi Kona addabi Rayuwarka!" Mikewa yayi tare da
Zame hannunshi d'akin da ya Kama ya nufa da Mugun gudu tabi bayanshi tare da tura kofar
Ganin Yana shirin Kullewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login