Showing 1 words to 3000 words out of 51592 words
Chapter 1 - Shaukin So Book Compelet Mrs Sadauki
[04/03 13:39] MRS SADAUKI: *SHAUƘIN SO*
```LoVe story```
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}
*FCWA*☀️
________________________
Ina yi wa ɗaukacin musulmi Barka da sallah, Allah ya karɓi ibadunmu ya kuma gafarta mana
kurakuranmu Amen !!!
Page 1-2
Sanyin la'asar ne ya sauka ya haɗe da sanyayyar iskar da ke kaɗawa, giza-gizai na gudu hadari
sai gangamuwa yake yayinda garin sai ƙara lumshewa yake yana ƙara duhu.
Mutane sai harhaɗa kaya suke suna guduwa,abubuwan hawa na ta wucewa kowa na ƙoƙarin
ƙarasawa gida kafin ruwa su sauko saɓanin malam Nur da ya ƙara gyara zama akan kujerarsa
sai ci gaba da koyar da karatu yake ba tare da yayi la'akari da yadda Ɗalibai sai leƙen waje
suke ta manyan tagogin ajin ba.
Cikin dadaɗar muryarsa yake rero ƙira'a mai shiga rai da ɓargon jiki amman sam Ɗaliban
hankalinsu bai wajensa.
Lura da hakan yasa shi rufe Qur'anin yana fuskantar su "ku nutsu in kuna nutsuwa don babu
wacce za ta fita sai ta biya min wannan shafin tom"ya faɗa yana tamke fuska tamau alamun
babu wasa a ciki,sanin halin malam Nur yasa duk suka shiga hankalin su duk da ya kasance
mai barkwanci amman wani sa'in ya kan rikiɗe ya koma miskilin malami ta yadda ko ƙwaƙwaran
motsi mutum bai yi in yana cikin aji musamman lokacin karatu.
Karatu suka ci gaba da yi cikin nutsuwa suna koyon yanayin yadda duk yake lanƙwasa ƙira'arsa
wanda hakan ba ƙaramin daɗi yake wa malam Nur ba.
Tun da aka fara karatun yana lura da ita yadda ta takure wuri guda sai ƙanƙame jikinta take
alamun jin sanyi duk da tana cikin ƙaton hijabi.Zuciyarsa ce ta fara rawa,tausayinta ya tsargu a
ransa cikin hikima ya sallami ɗalibai cike da murna suka fara fita aji duk yana kallonta har
lokacin da ƙawarta Samira ta kama hannunta suka fice.
Lumshe ido yayi yana sauraren bugun zuciyarsa,tunda ya sanyo ƙafa makarantar nan ƴan mata
suka fara rubibin shi daga masu nuna alamar suna son shi sai masu turo masa saƙo amman ita
ko kallon shi bai dame ta ba.
Buɗe ido yayi jin ƙarar saukar ruwan,miƙewa yayi ya buɗe window yana leƙawa yayafi ne ake
amman masu zowa da gudun nan.
Cikin zuciyar shi ya ke tambaya 'shin ko har ta kai gida?'dan ya ga alamu bata son sanyi
sosai,huci ya sauke kafin ya ɗauki makulin motarsa ya fito.
Filin makarantar tsit yake dan dama duk sauran malumai sun daɗe da tashi ajinsa ne wanda ya
kasance ajin ƙarshe(na manya ga ba ɗaya)kawai ya tsayar da su.
Ƴar ƙaramar ƙofa yabi ya fita inda yayi parking ya nufa ya shige tare da yi ma motar key bai
tsaya ko ina ba sai bakin tangamemen get ɗin gidansu ,horn yayi mai gadi ya buɗe ya shige.
Tun kafin ya shiga falon yake jin ƙarar sauti na tashi,cak ya tsaya yana kallon su yadda suke
rawa tamkar ƴaƴan makaɗa sam ba su lura da shi ba sai sauka wayar caza suka ji ,ihu suka
fara suna neman agaji amman ƙarar tv ta hana aji sai da yayi masu lilis sannan ya ƙyale su tare
da kashe tv.Sai kuma a lokacin Maman ta sauko tana hararen su kafin ta tsayar da malam Nur
da ke ƙoƙarin buɗe ɗakinsa"Ustaz sai yanzu ka dawo tun ɗazu nake ta tsimayen ganin
ka"tsayawa yayi jin muryar mahaifiyarsa,gaishe ta yayi sannan ya ƙara da "eh Maman
shigowata kenan kuma sai na tarar da waɗan can maras hankalin suna shaƙiyanci duk da sun
san sun yi laifi na ƙin zuwa makaranta shine suka ƙara da wani laifin"ya ƙarashe maganar yana
ƙyaci alamun jin zafi abun.
Inda suke a rakuɓe Maman ta kalla tace "ku tashi ku fice min da gani in ba shashanci ba ana
ruwa zaku saka kiɗa maimakon karatun Alkur'ani,ai Ustaz in ka biye ta waɗannan sai su hauda
maka hawan jini"tana gama rufe baki suka miƙe cikin azama suka shige ɗakinsu.
Ƙarasowa yayi kusa da mahaifiyar tasa yana kallon ƙullin maganin da ke hannunta,miƙa masa
ta yi ya karɓa tare da dubanta yace "na me ne kuma wannan?"
"Cikin ruwan wanka za ka zuba shi sannan ka kaɗa cikin madara ka sha,dan Allah kar ka ce
min a'a ko tambayata ba'asi"shiru yayi yana nazarin maganar kafin yace "toh maman in shaa
Allah zan yi yadda kika ce"da murmushi Maman ta dafa kansa tace "Allah yayi maka albarka ya
cika maka burinka na alkairi"da "Amen"ya amsa kafin ya wuce part ɗinsa ita kuma Maman ta
shiga kitchen.
Sanin darajar mahaifiya da girman alƙawari shi yasa Ustaz yin amfani da maganin ba tare da ya
san ko na mine ne ba,abinda ya sani dai uwa ba za ta taɓa cutar da Ɗanta ba.
Yana fitowa daga wanka ya saka doguwar jallabiya fara sol ya kunna ƙira'a a Sheikh Sudais
yayinda kuma yake yin tasbihi da hannunsa,idonsa a lumshe suke yana jin sautin ƙira'ar na
ratsa shi gefe guda kuma tunanin Nazifa ne maƙale a zuciyarsa sai dai da zarar ya fara sai ya
yakice ta a rai kasancewar yau Litinin yana ɗauke da azumi a bakinsa.
Kiran sallah da wayarsa ta ɗauka ne ya sa shi saurin miƙewa ya ɗauro alwala ya fito falo inda
kayan buɗa bakinsa ke jiran shi.Kamar kullum yau ma Maman ta ƙayata ɗan ƙaramin capet ɗin
da yake zama lokacin shan ruwa da kayan ciye-ciye.
Zaunawa yayi akai tare da tanƙwashe ƙafafunsa addu'o'in shi na yau da kullum ya fara kafin ya
gabatar da buɗe bakin.
Sanyayar ajiyar zuciya yayi lokacin da ya kwankwaɗi jus ɗinsa na zoɓo wanda ya sha kayan
haɗi,wani jus ɗin ya ƙara tsiyayawa a kofi ya ɗan saka maganin da maman ta basa ya motse
sannan ya shanye.
Ruwan saman da ake ne suka ɗan tsagaita wanda ya bai wa musulmai maza fitowa yin Sallah
magrib,duk da an yi ruwa masallacin cike yake da jama'a su Ustaz sune a sawun gaba kamar
kullum.
Sai bayan an gama sallah ne ya gaida mahaifin nasa wanda mafi akasari shi ke jan sallah
magrib, isha'i da asubah.Cike da kulawa Baba ya amsa yana tambayar shi wunin
ɗinsa"alhamdullah Baba ya gajiya ?"cewar malam Nur,a takaice Baba ya amsa mashi da
"alhamdullah"kafin suke rankayowa gida.
Ko da suka zo gida sun tarar da Maman da ƴan matanta suna cin abinci,hararar su Nur yayi
yana amsa barka da shan ruwan da Maman ke masa kafin ya wuce part ɗinsa.
Ƙaton hoton ya ƙura ma ido yadda take murmushi gwanin kyau sai ta banbanta da sauran
Ɗaliban da alamu ita bata ma san an ɗauki hoton ba,daidai fuskarta ya shafa ya na mai dafe
saitin zuciyasa.
★
A ɓangaren Nazifa kuwa tun zuwanta gida ta duƙunƙune cikin bargo tana hawayen azaba
yayinda ƴan gidansu suka yi cirko-cirko suna jajanta ma juna game da ciwon Nazifa wanda sai
gaba yake babu sauƙi.
Inna ce ta ƙarasa kusa da ita ta yaye bargon tana mai taɓa wuyanta,rau yake sai ɗan karen zafi
kamar garwashi haƙoranta kuwa sai karkar suke suna gamuwa.Cikin tausayi Inna ta dubi yaya
Ɗalhat tace "ko asibiti muke zuwa? Tunda maganin ya ƙi yi mata aiki" ajiyar zuciya ya sauke
yace "toh Inna mu je can ɗin amman ba zuwan ba kar mu je su tsula mana kuɗi"murya na rawa
Inna tace "a'a ai asibitin gwamnati za mu je tunda can kuɗin cirar takarda kawai za mu biya,je
ka taro mana ɗan sahu "da sauri Ɗalhat ya fita ba jimawa sai ga shi ya dawo duk ya jiƙe da
ruwa,kamar wata gawa haka ya naɗota cikin bargo tare da sungumarta ya shigar da ita
adaidaita.Gaba ya shiga ita kuma Inna ta zauna baya tare da Nazifa ,CSI Ali Shaibu ɗan sahun
ya kai su kamar yadda suka buƙata.
Adaidaitar na tsayawa Ɗalhat ya fito zai ɗaukar ta cikin murya maras lafiya tace "zan iya tafiya
da kaina"taimaka mata yayi yana tattare bargon suka nufi ciki,Inna na ƙoƙarin kwance kuɗi ta
sallami mai ɗan sahu yace ta bari godiya ta yi masa tana masu mara masu Ɗalhat baya.
Inna na shiga ta tarar da Ɗalhat sai faman faɗa yake da wata nurse akan tace doli sai ya tafi ya
karɓo takarda shi kuma yace ta dubata kafin ya dawo shine tace taƙi ta yi ɗin.
Cikin alamun a tausaya masu Inna tace "ƴata ki taimaka ki duba ta don haihuwar da iyayenki
suka yi maki,mai rubuta takardar kamar na ga ƙofar shi a rufe"a zafafe nurse ɗin tace "sai ku
jira har ya dawo ko kuma ku canza asibiti...."Bashir ne yayi saurin katse ta wanda shi ma likita
ne yace "haba Rakiya ba ki ganin halin da take ciki ne?Kuma dan tsufan wannan ai kin
taimaka"ya ƙarashe maganar yana mai juyawa inda Ɗalhat ke tsaye yace "me ke damun
ta?"cike da jin daɗin hallacin da yayi masu ya shiga yi masa bayani "eh to duk in an yi ruwa ne
ko kuma lokacin sanyi sai jikinta ya rinƙa ciwo tana jin sanyi"kai Bashir ke ɗagawa kafin ya ɗibi
jininta ya kai lab cikin ɗan lokaci ya dawo da fara takarda,sai da ya naɗe lemar (parapluie)
sannan yayi mata allura.
Inna da Ɗalhat na gefe sai godiya suke zuba masa, murmushi kawai Bashir yayi yace "ba komiy
ai yi wa kai ne".
Barci mai nauyi ta samu sai fitar da gumu take tana sauke ajiyar zuciya,gefen gado Inna ta
zauna yayinda Ɗalhat ya bi bayan Bashir dan karɓo magani.
Sai bayan sallah isha'i suka dawo gida,cike da mamaki Jamila ƙanwarta ke kallonta ganin ta
warke lokaci guda cikin kasa ɓoye mamakinta tace "anty kamar ba ke ce aka fita da ke a
duƙunƙune ba ya jikin naki ?"
"Da sauƙi na ma warke yunwa nake ji me kika dafa?"
"Dafa duka ta shinkafa"ta bata amsa ta na mai ɗaukar kwano ta zubo mata,ba wani ci ta yi sosai
ba ta tashi ta yi alwala da ruwan zafi ta gabatar da sallah da ake binta.
Lamo ta yi kan sallaya fuskar malam Nur na yi mata gizo, murmushi ta yi tuna lokacin da ya lura
da ba cikin hayyacinta take ba duk sai ya ruɗe "sai yaushe zaka furta ne?"ba ta san a bayyane
ta yi maganar ba sai jin Jamila tace "mi za'a furta?"yi ta yi kamar ba ta ji ta ba ta tashi ta haye
katifar da suke kwana ta cigaba da tunanin malam Nur har barci ya ɗauke ta.
Ƙarfe bakwai cicif a makaranta tayi ma malam Nur,tun kafin ya ƙaraso ajin yake jin sautin
muryarta sai karatu take cikin nutsuwa tare da ba ko wane harafi haƙinsa.
Bakin window ya tsaya yana ƙare mata kallo,sanye take da hijab da sket na uniforme ɗin
makaranta hannunta riƙe da al'ƙur'ani amman ta rufe shi alamu hadda ce take.Idonta a lumshe
suke yayinda ɗan ƙaramin bakinta wanda ya sha janbaki sai motsawa yake yana fitar da
dadaɗan amo na muryarta.
A hankali ta buɗe su kuma,ido biyu suka yi a tare zukatansu suka buga dam,cikin i'ina tace
"as..salamu aleyka yaa mu'alim"sai da ya ƙarasa shigowa cikin ajin sannan ya amsa sallama
yana mai tambayar ta "ba ki jin tsoro ne kullum ke kike fara zuwa makaranta ina ɗayar
take?"wani daɗi Nazifa ta ji kafin tace "ta na gida sai zuwa ƙarfe takwas take zuwa" "Ke kuma ba ki iya jiranta ko?"ɗan ɗagowa ta yi ta kalle shi tace "um..ai saboda na yi hadda ne
nake zuwa da wuri"jinjina kai yayi ya karɓu alƙur'anin hannunta ya fara yi mata tambayoyi,sai ya
jawo Aya yace ta ci gaba ko kuma ya tambaye ta cikin wace sura ce ita kuma ta na basa
amsa.Sosai duka zukatan biyu suke jin daɗin wannan kusancin a haka har mutane suka fara
taruwa sai dai babu wanda ya shigo aji sai leƙen su da ake wasu na gulmar dama soyayya
suke.
Lokacin shiga aji yayi kowa ya shiga,nan Nazifa ta ji ta a takure ganin rabin ɗalibain ajin sai
harararta ake yawancinsu duk masu son malam Nur ne.
"Ke miye haka?dan Allah ki saki jikinki duk kin wani takure kawai dan surutun mutane ba komai
ba ne ke cindu sai baƙin cikin ganin kin samu abinda suke so shekara da shekaru"cewar Samira
murmushi kawai Nazifa ta yi ba tare da tace komi ba domin tun ba yau ba ta fahimci ɗin suna
son junansu ba tare da su sun sani ba,tun ba ta yarda da zancen Samira har ta yarda da lalle
tana son Malam Nur.
Duk karatun da ake masu na yau sam ba ta fahimta don rabin hankalinta yana can duniyar
tunani,ƴar ƙarar rawar da aka kaɗa alamun lokacin shan iska yayi ne yasa ɗaliban fara fita dan
karyawa,"Malama ki tashi mu tafi ko yau ba ki cin komai ?"ta tsinkayo murya Samira cikin
masifa, murmushin da ya zame mata jiki ta yi tana mai miƙewa har sun kai bakin ƙofa suka ji
malam Nur yace "Naziiii"cak ta tsaya zuciyarta ta shiga lugude kallon Samira ta yi da ido ,ita
kuma ta yi mata alama da ta tafi tare da ɗaga mata gira kafin take ficewa.
A hankali ta dawo kamar wacce ƙwai ya fashe ma a ciki har ta zo gaban teburinsa inda yake
zaune a kujera ya ɗora hannuwansa akan table ɗin mai ɗauke da littafai.
"Ga ni mu'alim"ta faɗa kamar za ta yi kuka,bai ce mata komyi ba sai ma ƙoƙarin ciro wani littafi
yake.
Turo baki ta yi gaba tana jin haushin shanyata da yayi har ta fara tunanin ko dai ba kiranta ba
ne yayi sai kuma ta ji yana cewa "ya kamata ki ƙara da karatun wasu littattafai dln ilimi yawa ne
da shi ga waɗannan ki je da su gida ki yi nazari gobe za mu fara su"amsa ta yi ta juya za ta tafi
yace "am...ban gama ba"tsayawa ta yi, jin bai ce komai yasa ta ɗago kanta karaf suka haɗa ido
wani irin lantarki mai game da shock suka ji a tare da sauri ta mayar da kanta ƙasa.Murmushi
yayi yace "ki na iya tafiya"kamar mai jira ta juya da sauri ta fara tafiya kamar wadda aka yi ma
dabaibayi..........
[10/03 14:46] MRS SADAUKI: *SHAUƘIN SO*
```LoVe story```
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI✍️}
*FCWA*☀️
________________________
age 3-4
Tun daga nesa Samira ke ƙare mata kallo har ta ƙaraso,dungure mata kai ta yi tace "ƴar sa ido
kallo me ne kike yi min?"dariya ta yi tace "to Naziiii ni kam mi zan kalla a nan,kawai na ga yau
duk a takure kike kamar wata kaza da ƙwai ya fashewa a ciki haka kike tafiya tsaya ki ga na
gwada miki ma.Kin ga yadda kike tafiya"Samira ta faɗa tana kwaikwayon tafiyar Nazifa "ke dai
kika sani uwar sa ido"shine abin da ta ce.
"Babu wani sa ido sai gaskiya,wai me ne yace miki?"ajiyar zuciya ta sauke ta gwada mata
litattafan da ya bata "na mi ne ?"
"Karatu za mu rinƙa yi"jan baki Samira ta yi tace "sabon kiciyi..."wani dundu Nazifa ta kai mata a
baya cikin jin haushin furucin tace "Noori ɗin ne kike ce ma kiciyi?"amsa ta bata da "eh ɗin in ba
kiciyi ba me ne na wani kame-kame ai sai ya fito fili yace maki yana son ki ba ya fake da koyar
da ke ba"kamar daga sama suka tsinkayo murya malam Nur yana cewa "in kun gama gulmata
sai ku shiga aji"da mugun tsoro duk suka juyo sai dai tuni ya wuce sai bayansa suka hango.
Sai da Nazifa ta sayi taiba suka wuce aji,a gaggauce ta shanye taibar ta ɗauki ruwa tana sha
ita kuma Samira sai aukin kallonta take.
"Lafiya ko na sauya maki ne?"Nazifa ta tambaya "a'a ko ɗaya kawai na ga kina shirin zautar da
malaminmu ne,har fah zai shigo ko da ya ga ki na cin abinci ya koma na san jira yake har ki
gama"waro ido Nazifa ta yi sai kuma ta ƙyale ganin malam Jabeer ya shigo aji da alamu kuma
shi zai masu karatu.
Rubutu ya fara a allo sannan ya juyo ya fara tambayoyin akan karatun da ya gabata su kuma
ɗaliban na bashi amsa,cike da ƙwarewa ya shiga yi masu bayani muhimmancin amana da
gaskiya suna tsaka da karatu malam Nur ya shigo ya zauna shi ma ya na sauraren jawabin
malam Jabeer.
Ko da aka tashi tsayar da ita yayi ya ɗan mata tambayoyi bisa karatun da aka yi inda ba ta gane
ba ya sake yi mata bayani har ta fahimta daga nan ya fara jan ta da hira har yake tambayar
mene ne ya sameta jiya nan ta faɗa masa tana fama da sikila ne cikin tausayi yace "me yasa ba
ki je asibiti ba?"
"Mun je mana har suka bani magani"
"Wace asibiti kuka je?"ya tambaye ta "CSI Ali Shaibu"ta basa amsa "ki rasa asibitin da za ki je
sai wannan?"ɗan kallon shi ta yi a raunace sai kuma ta mayar da kanta ƙasa tana wasa da
yatsun hannunta,wani gwabron numfashi ya sauke da ya tuna ba kowa ne ke da halin zuwa
asibitin kuɗi ba.
"Ina ne gidanku?" ya tambaye ta yana mai tsare ta da idanu,ba ta yi zaton haka ba amma har
ƙasan ranta ta ji tambayar " nan ne kusa ba nisa wajen gidan Alhaji mai tumaki"ta basa amsa
"To daga nan ina za ayi aje?"
"Ai makwabtanmu ne daga gidansa sai namu"kai ya jinjina kafin yace "ok wuce ki tafi Samira na
jiran ki Allah kauwo afuwa"da "Amen "ta amsa kafin su fito tare.
Turus suka