Showing 1 words to 3000 words out of 33902 words
Chapter 1 - Mutum Da Rigar Aljan Book Compelet by Mrs Sadauki
[07/10 à 08:44] MRS SADAUKI : *MUTUM DA RIGAR ALJAN*
*Gajeren labari...*
Story
and
Written by
*MRS SADAUKI✍*
Dedicated to *PRINCESS AYSHATOU*
☀️ *FIRST CLASS WRITTERS ASSOCIATIONS*☀️
___________________
BISMILLAHI RAHMANI RAHIM.
*'Kir'kiraren labari ne ban yi shi dan cin zarafin wani ko wata ba*
```Wannan book tun daga farkon shi har izuwa 'karshe sada'karwa ne gare ki masoyiyya Indo
shalelen first class ina yin ki```
FREE BOOK
Page 1-2
Gudu take cikin daji ta na yi ta na faɗuwa sannan ta miƙe ta ci gaba,wani uban ihu ta ƙwala ta
na mai ja da baya tare da girgiza kai.
Yawun bakinta ne ya kafe ,idonta suka firfito lokacin da ta ji zara-zaran yatsun shi sun huda
cikinta sun lume can ciki , zaƙulo hajinta yayi ya fara ci kamar wani maye jini na bin hannunsa.
"MARYAM?MARYAM....?" firgigit ta tashi a tsorace ta na dafe cikinta saurin riƙeta momy tayi
"lafiyar ki kuwa kike fizge-fizge?"
"Momy *WILLIAM* wlh ba mutum ba ne,ha...han " sai kuma ta kasa furta komai sai wani '
ƙanƙame jikinta da ta fara yi sakamakon wani sanyi da ya mamaye duk wani ɓargonta.
Luuu ta yi baya ta faɗa bisa gado wani barci mai kama da mutuwa ya ɗauketa,buji-buji take gani
kamar ta na farke kamar ta na barci wani duhu ne ya gilma ta idonta nan wata baƙar tsohuwa ta
bayyana mai farin gashi.Bakinta buɗe yake mai d'auke da zaƙa-zaƙan haƙora uwanda suke
kamar na dalma.
A hankali tsohuwar ta fara shafa gefen fuskarta ta na tofa mata yawu a ƙarshe ta ƙyalƙyace da
dariya ta na kiran sunan WILLIAM a take wani kyakyawan saurayi ya bayyana fuskar shi ɗauke
da murmushi yayin da tsohuwa ta ɓace.
Kyawawar surar jikinta ya ƙura wa ido kafin ya kai hannun shi ya fara sarrafata,har ya zarce da
mu'amala da ita.
Sosai yake jin daɗin sabuwar rayuwar da ya fara a yau,a yadda yake yi mata ɗin yasa duk
jikinta karɓar saƙon,ya ɗauki lokaci mai tsayi kanta kafin ya samu nutsuwa wanda yayi daidai da
tashinta daga barcin.
Maryam ta buɗe ido a hankali kafin ta miƙe zaune,ji tayi duk jikinta ya saki ga wani uban ciwo
da gajiya da suk saukar mata. A haka ta lalaɓa ta shiga toilet dan ɗauro alwala domin yin sallah
la'asar da tun lokacin da zata soma barci aka yi ta,yanayin da ta samu kanta yasa ta fara
ƙoƙarin son tuno ko mafarki tayi amman ta kasa tuna ganin ta samu 'kwan'kwanto yasa tayi
wanka ta fito.
Tapis ta shimfid'a ta tada sallah a nutse,a sujada ƙarshe ne ta daɗe ba ta ɗago ba ,inda ta ke
kwaranyo addu'a kamar haka "ya Allah ka yaye min duhun da ni ke ciki ka hasko min larurar da
ke damuna,na sani ni ɗin mai rauni ce ba ni da iko ko isar da zan ɗauke wa kaina damuwar da
ni kaina ban santa ba amma ina jin zuciyata ta yi min nauyi" ta ƙarashe cikin kuka.
Ta na gama sallah ta cire hijab ta ɗaure kanta da towel domin tsanar da ruwan,kafin ta ƙarasa
gaban miroir ta na ƙare ma kanta kallo tun daga kyakyawar fuskara ta mai d'auke da siririn
hanci da jajayen laɓa har zuwa shanyayyen cikinta wanda ya ɗan yi tudu wajen marar ta hakan
ya fitar da shap ɗinta na coca cola.Ta ɗan ɗauki lokaci wajen kallon kanta kafin ta fara shafa
mai da turare ta cire towel ɗin kanta ta na mai harɗe gashin waje guda.
Ta na shirin fitowa suka yi kiciɓis da Khalil wanda dawowar shi kenan daga school,"bonsoir
Mr"ta ɗan faɗa can ƙasan maƙoshi sai da ya ƙare mata kallo sannan ya ɓata fuska yace"yanzu
har a gida da Mr za ki kira ni?"rausayar da kai ta yi ta ce "ka yi haƙuri Yaya ni mantawa nake"
murmushi yayi ya ce "yanzu kika tashi daga barci ko?Kin ci abinci?" yayi mata tambayar a jere.
"Eh yanzu zan ci" ta ba shi amsar ta na mai yin gaba don ita sam ba mai son yawan magana ba
ce, ta kula kuma in ta biye wa Khalil sun shekara nan ya na faman tambayar ta kamar wani ɗan
jarida.
Kai kawai ya girgiza ya shiga ciki yayin da ita kuma ta nufi madafa inda momy ke girkin dare
"sannu da aiki momy " ta faɗa lokacin da ta ƙarasa ciki gun mahaifiyarya wadda ke kwashe
tuwon laushi "yawwa sai yanzu kika tashi?To maza ɗauki abincinki ki ci ki zo na aikeki gun
hajiya Zahra" da "toh" ta amsa ta na ɗaukar kwanon abincinta,sai da ta ci ta ƙoshi ta yi nar
sannan ta wanko hannu da bakinta ta zura hijab tare da yi a momy sai ta dawo.
Tafe take ta na rangaji kamar wata bishiya ta na wani daf-daf kamar wadda ke tsoron 'kasa ko
tausayi har ta shigo layin gidan hajiyaZahra,da sallama ta shiga gidan amma tsit babu kowa sai
kukan tsuntsaye da talutalu.
Cikin bud'e murya ta 'kara rangad'a wata sallamar nan ma shiru hakan yasa ta juya da nufin
komawa don ba tabi'ar ta ba ce shiga d'akin mutane bayan ba a bata izini ba.
Murya hajiyar ta tsinkayo ta na cewa "ah! aha! Maryam ce?Shigo mana ina wanka ne " ta fad'a
daga can bakin 'kofa,wata sallamar Mayarm ta sake yi kafin ta shiga d'akin ta na mai gaishe ta.
Cikin d'aki hjy ta shiga sai ga ta ta fito da 'katuwar leda ta na mai cewa "ungo ki kai mata ki ce
zan yi mata bayanin kud'in kayan ta waya, in ta zab'a ki maido min sauran" karb'a Maryam ta yi
ta na mai cewa "to sai an jima".
Kasancewar ba wani nisa ba ne tsakanin su yasa ta saurin dawowa,cikin murna momy ke duba
kayan a take ta zab'a ta maida saura cikin leda ta ce wa Maryam " tashi ki mayar mata da
wannan"cikin murya da ke nuna gajiya mai game da 'kiwa Maryam tace "haba momy na gaji
yanzu fa na dawo daga can ki bari har zuwa an jima in zan je exercice sai na biya da su" cikin
d'aga murya momy tace "ban son sakarci ni sa'ar ki ce maza tashi ki kai mata ko na yi miki
dukan tsiya ina ce dai har da ke na d'aukar ma kayan".
Cikin jin haushi Maryam ta d'auki ledar kayan ta na jin zuciyar ta na tu'ki'kin ba'kin ciki da b'acin
rai,yadda take jin wani 'kunci ne ya sa har idonta ya ciko da hawaye har bata ganin gabanta
tafiya kawai take ba tare da tsammani ba sai ganin gilmawar wani abu ba'ki tayi gaban ta.....
***
MARYAM ABACHA shaharara établissement américaine da ke jahar maradi,duniyar gayu da
'kwazo sun tabbatar babu wata had'ad'iya école kamar ta duba ga yadda d'alibanta ke 'yan
gayu babu 'kabilar da babu na différents pays africains kama daga Ghana,Tchad,Mali, Nigeria
da dai sauransu.
Wani kyakkyawan matashin saurayi ne kwance kan bed,waya maƙale a kunnen shi.
Cikin cool voice ya ke fira sai wani lumshe ido yake da alamu ya na jin dad'in zancen,can 'kasan
ma'koshi yace " please baby yi min kiss kafin ki kashe"
"Muaaah! mn cœur je t'aime" d'ayan b'angaren aka fad'a
"Love you too" ya bata amsa kafin ya d'ora da "baby kar fah ki mance da hotunan da na ce ki
turo min fah"
"OK kar ka damu bb yanzu zan turo ma " cewar Laila ta na 'ko'karin kashe kiran don tun d'azu
ta ke son tashi ta d'ora girki, ya na shirin magana kittt ta yanke kiran 'karar texte taji ya shigo
```har da hotunan da kike da 'kananan kaya babyna``` shine abin da ta gani girgiza kai ta yi ta
na mamakin Nur.
A b'angaren Nur kuwa data ya kunna ya na jiran sa'kon masoyiyyar tashi,babu jimawa kam ta
turo hotunan sai dai babu na 'kananun kayan kamar yadda ya bu'kata amman dayawan pic d'in
sun d'auki hankalin shi don har tashi yayi zaune ya na ihu.
Rahul wanda su ke d'aki guda ne yayi saurin duban shi ya na cewa "ya dai friend ko ta samu
ne?" ya fad'a ya na mai d'aga masa gira dama tun farkon wayar su yake kallon Nur d'in.
"Kai dai bari aboki ina yarinyar da mu ka had'u facebook da ita last week?To ita ce ta turo min
hotunan ta ashe kyakyawa ce har haka" cewar Nur ya na lasar leb'en shi na 'kasa,girgiza kai
Rahul yayi yace "to uban son mata tashi mu je terrain na san yanzu har sun fara buga game".....
NO COMMENT NO TYPING♀️ in yayi maku na cigaba ko kuma na ajiye na maida shi gefe♀️
[07/10 à 09:24] MRS SADAUKI : *MUTUM DA RIGAR ALJAN*
*Gajeren labari...*
Story
and
Written by
MRS SADAUKI ✍
Dedicated to *PRINCESS AYSHATOU*
☀️ *FIRST CLASS WRITTERS ASSOCIATIONS*☀️
___________________
BISMILLAHI RAHMANI RAHIM.
FREE BOOK
Page 3-4
'Katon terrain d'in buga ball ne mai d'auke da korin shukar nan sai she'ki take,maza na buga ball
yayin da mata ke ihu da shewa sai 'kara tunzura uwanda su ke supporter suke.
Elli wacce ke masifar son Nur ce gefe sai faman d'aga 'kyalle fari take wanda yake kalar kayan
'yan équipe d'in su Nur,duk lokacin da Nur ya amshe 'kwallo sai ta yi ihu ta na mai fad'in sunan
shi wanda har ya sa na kusa da ita yin tsuki don duk ta cika masu kunya.
Cikin rub'ab'ar hausar ta tace "don wuba mutum ya tanka ni ya ga bala'i" dariya Ikilima ta she'ke
da ita su na mai tab'a hannu ita da abokiyarta kafin ta maida raddi "hohoho!Ke ni kam wasu
matan ba su son ciwon kan su ba ana gudun su amma su na li'ke wa mutum mtsw!" ta ja tsuki
'kawarta ce ta karb'e "pls Iki tunda dai shi bai ma san ta na son shi ba don Allah ki 'kyaleta".
Duk da Elli ba wani Hausa take ji sosai ba amma ta gane da wannan ce budurwa Nur da aka
sha faɗa mata ya na da wacce yake so,tsayawa ta yi ta na 'kare ma Ikilima kallo wacce ta ke
fara sol siriri mai d'auke da jajayen leɓa sab'anin ita da take ba'ka 'kirin ' doli ya 'ki kula ni ashe
baturiya ya gani amma in sun san wata ai ba su san wata ba,zan bi duk wata hanya da zai sa
ya soni' Elli ta fad'a a zuci.
Hutun da aka je ne ya basu damar tsayawa, wanda hakan yasa Nur zuwa wajen da Iki ke zaune
"bb c'est comment?Ka gaji ko?" ya tsinkayo murya Elli na fad'a ta na mai mi'ko masa exotic
,karb'a yayi yace "merci" tare da sakar mata murmushin da ya 'kona ran Iki.
"Mine ne kuma na yi mata murmushi sai ka ce wata abar 'kwarai?" Iki ta fad'a ta na mai b'ata
rai.
"Ba ki ga jus ta bani ba uwar kishi" ya fad'a ya na d'an hararenta wanda hakan yasa ta yi fushi
ta mi'ke, riƙo hannunta yayi ta fizge ta bar shi nan tsaye bin ta kawai yayi da kallo.
"Lambar ka please " Elli ta fad'a ta na mai mi'ko masa dan'kareriyar wayar ta,karb'a yayi ya
saka mata domin shi in dai mace ce babu kalar da bai so.
Cike da murna Elli ta nufi layin da room d'in mata yake,babu kowa d'akin hakan yasa ta tub'e
zigidir kamar yadda ta saba in za tayi wanka.
Ba ta jima ba ta fito daga wanka ta na mai d'aukar wayarta ta shiga wasap,number Nur ta duba
tare da ciro hoton dp ɗin shi.
Kamar ta mutu haka take jin son shi,kiss d'in wayar ta yi ta na mai tura video call ba tare da
b'ata lokaci ba ya d'aga.
'Kuri su ka yi wa juna shi ya na 'kare ma surar jikinta kallo yayin da ita kuma fuskar shi mai
d'auke da saje take ma kallon so.
"Hi baby" Nur ya fad'a ya na sauke ajiyar zuciya,murmushi kawai ta yi ta na sake ma shi kallon
'kurilla.Ganin ta'ki magana ya ce "mine ne kike yanzu?"
"Komai! Wanka ne na yi"
Murmushin yaudara yayi yace "ko na zo na shafa miki mai?"
"What is mai?" ta tambaye shi don ba sosai take jin hausa ba
"Pardon pommade" waro ido tayi cikin jin dad'i tace "da kuwa na ji daɗi sosai" cikin zumud'i Nur
yace "da gaske ki na so?" kai ta d'aga masa.
"OK turo min lambar d'akin ku gani nan zuwa"ya fad'a ya na mai katse appel d'in,a gagauce ya
fara kimtsawa Rahul dai kallon shi yake tare da mamakin yadda abokin nasa ke jarabar mata.
"Ka ji tsoron Allah! Ka tuna kai ma ka na da ƙannai mata,shin za ka ji daɗi in ka ga samari na
yaudarar su kamar yadda kai ka ke yi wa ƴaƴan wasu?" Cewar Rahul don bai jin daɗi sam.
Nur ya dube shi ya ce "ban fa son sa ido,wai ina ruwan ka da rayuwata? In zan yi sallah ko
azumi ba ka taɓa cewa mi yasa nake yin su ba duk da su na ayyukan alkhairi sai ƴar
shaƙatawar nan da nake ta tsone ma ido?"
"Ba haka ba ne abokina! Ina yi ma hannunka mai sanda ne saboda wajen kwaɗayi kuɗa ke
mutuwa"
"To na mutu ɗin! Ai dama duk mai rai mamaci ne!"
Rahul ya girgiza kai ya ce "akwai dai ranar ƙin dillanci!"
Nur bai tanka shi ba,sai ma wayarsa da ya ɗauka wacce ya ji ta yi ƙara alamun shigowar text.Ya
duba sai ya ga,lambar ɗakin ce Elli ta turo masa.A gurguje ya fita ya na ayyana abubuwa
dayawa a ransa har ya isa ɓangaren.
Bai wani sha wuya ba ya gane d'akin , yadda take tun farko ba ta canza ba daga ita sai towel
kamar lokacin da ya ganta a appel .
" Ki shigo mana"cewar Elli ta na mai d'auko mai cikin valise kamar yadda ya bu'kata.
'Ashe gaba ma da gaban ta duk iskancina ashe ga baki ne ga wata nan za ta fara koyar da ni
na ainahin' cewar Nur a zuci ya na mai 'kura mata ido kawai.
Duk da kasancewar shi musulmi bai sa ya ja da baya wurin aikata abin da ya san ba huruminsa
ba ne.Kamar ƴar tsanar roba ko kuma ƴarsa ya shafe Elli da mai ita kuma sai murmushin
yaudara take masa.
Shi kuwa Nur bai mata wani salo da zai nuna mata ya na son lalata da ita ba,sai dai shafin mai
da yayi mata.Towel d'in jikin ta ta cire ta zura doguwar riga irin ta su ta gwarawa kafin ta feshe
jikinta da turare,Nur kam na zaune bakin bed ya na kallonta har ta gama shiryawa tace "ko za
ka raka ni cin abinci in babu damuwa?".
****
Cikin 'kan'kanan lokaci wannan duhun ya rufe Maryam kan ta farga sai ganin ta tayi cikin dokar
daji ita da wata tsohuwar mata wadda gashi ya rufe wa fuska.Da zarazaran yatsunta ta kama
hannun Maryam suka soma tafiya kamar ba gobe sun dad'e sosai a haka kafin su 'karaso wani
tsibiri mai d'auke da manyan duwatsu wanda a nan suka yada zango .
'Karasowar su ke da wuya wani kyakyawan saurayi ya fito tsakanin wasu dutsina biyu wanda
aka yi masu ado da wani jan 'kyale,murmushi yayi lokacin da yayi tozali da fuskar Maryam
hannu ya tara mata alamun ta zo gare shi.
A hankali ta fara 'ko'karin cire hannun ta daga na tsohuwar nan ,amma ta ji shi gam hakan yasa
ta kai dubanta gare ta nan idonta yayi tozali da za'ko-za'kon akaifu,luuu tayi dan firgici da sauri
William ya tarota ta fad'a 'kirjin shi.Cak ya d'auketa ya shiga da ita daga ciki ya na mai jin wani
farin ciki na mamaye zuciyar shi. Bisa wani gado mai kama da na sulba ya shimfid'eta ya na mai hura mata iska a fuska.
Wani lummm ta yi da fuskarta tare da bud'e idonta tarau a kan ta shi,murmushi ya sakar mata
ita kuma ta tsare shi da ido ta na kallo kafin ta yun'kura ta na 'ko'karin tashi.Mayar da ita yayi ya
shafi gefen fuskarta,motsa baki ta yi ta na mai furta "who is you?" maimakon ya bata amsa sai
yayi murmushi tare da shafar idonta a take barci ya d'auke ta.......
[09/10 à 06:41] MRS SADAUKI : *MUTUM DA RIGAR ALJAN*
*Gajeren labari...*
Story
and
Written by
*MRS SADAUKI✍*
{Cham rose}
Dedicated to *PRINCESS AYSHATOU*
☀️ *FIRST CLASS WRITTERS ASSOCIATIONS*☀️
___________________
BISMILLAHI RAHMANI RAHIM.
Page 5-6
Tunda momy ta gama girki ta d'auro alwala domin sallah magrib ta gabato,har ta ida sallah
Maryam ba ta dawo ba hakan yasa ta kira number hjy Zahra dan tambayar ta ,nan fa ta shaida
mata ai ita sam bata ga Maryam ba.
Cikin zafin rai momy ta shiga 'kwala ma Khalil kira wanda shi ma bai dad'e da dawowa daga
masjid ba,"na'am momy ga ni"
"Dan