Showing 18001 words to 21000 words out of 33902 words

Chapter 7 - Mutum Da Rigar Aljan Book Compelet by Mrs Sadauki

da juna biyu saɓanin Talatu wacce ko ɓatan wata
bata taɓa yi ba.

Samun cikin Suweiba shine farkon abinda ya fara jefa gaba tsakanin ta da Talatu domin ba
ƙaramin ƙwallafa rai alhalin gidan suka yi ga Ɗan cikin ba,tun daga Alhaji ,Hajiya ,Salis uwa uba
Sani wanda tun farko Allah yayi shi da son yara.


Cike da zullumi Talatu ta shiga kewaye cikin ɗaki domin samo ma kanta mafita,can tayi
murmushi tare da cewa "yauwa doli na samu ciki ko kuma ke ma ki rasa naki iyee bari na
kirawo ƙawalliya"bugu biyu ta ɗauka cikin kirarin da Talatu ta saba yi mata tace "Zahra
tauraruwa mai haske duniya,um...wani taimako nike son ki min ki haɗa ni da malamin ki ko Allah
sa na dace wannan karin na samu ciki"
Wata shewa Zahra ta rangaɗa kafin tace "ai dama na san kwanan zance tunda naji an ce
Suweiba nada ciki na san da sai kin neme ni,amman fah magana ce babba kamar yadda na
gaya maki tun farko dan aikin malam sai an bayar da jini na mutum ba dabba ba"ajiyar zuciya
Talatu ta sauke kafin tace "yanzu dai sai gobe in mun haɗu".


Durƙushe suke gaban wani ƙaton arne ya na zayyano masu yadda abun zai kasance tare da
gindiya sharaɗa masu ƙarfi a inda yake cewa "doli ne wanda zaki bada jinin shi ya kasance
makusancin ki ne ma'ana kamar cikin familyn ku,sannan wacce zaki kawo takalmin nata tare da
zanen da ta ɗaura a jikinta ya zamana zufar jikinta ta buge shi zata haukace ne domin muddin
ta tsaya cikin hankalin ta asirin ki zai tonu"ko da boka ya zo da wannan batu sai Zahra tace "mi
zai hana ki kawo na Suweiba tunda ita ma ta nada ciki kin ga shikenan"murmushi Talatu tayi
"wlh kamar kin shiga zuciyata tunda takalmin mai ciki ake so ai shikenan ɗan cikin nata kuma
sai aba dodani jinin sa na harbi tsintsu biyu da dutse guda"cewar Talatu kafin ta maida dubanta
ga bokan ta sake jaddada ƙudirinta akan Suweiba.

Babu wani ɓata lokaci ya fara kiraye-kiraye ya na shafar wani faranti wanda ke ɗauke da ruwa a
take Suweiba ta bayyana,alamu yayi masu da su leƙo cike da al'ajabi da kuma yarda da aikin
bokan suke kaɗa kai ganin hatta jinjirin da ke cikin cikin Suweiba sun hango.Kuɗin gaske Talatu
ta baiwa boka tare da yi mashi alƙawarin tukuici mai tsoka in buƙata ta biya.


Bayan sati guda da faruwar haka Talatu ta kashe cibiyar pampon ɗakin Suweiba da kuma na
tsakar gida,babu a ko jima sai ga Suweiba ta fito da ɗaure gaba da kwandon wanka ta nufi toilet
ɗin tsakar gida wacce a ciki a ka tanadi ƙaton tano na ruwa.

Ko minti biyu bata fara ba da wanka Talatu ta ɗauke zanen Suweiba ta kai ɗaki inda tuni Zahra
ke jiranta.
Cikin dariya mugunta ta saka takalme guda na Suweiba a leda tare da zanen ta baiwa Zahra ita
kuma ta fice domin kaima boka.




Da dare an haɗu a dining kamar yadda suka saba dukan ƴan gidan ke haɗuwa a ci abinci,nan
ne fah Suweiba ke gayin an sace mata zane ɗazu Allah yasa ma ba'a gama da hijab ɗin
ba.Sosai aka shiga tattauna maganar inda Talatu take cewa "ƙila bararoji ne masu kawo tallar
maganin gashi ni sam hankalina sam bai kwanta da su"kamin wani ya tanka Suweiba tayi wata
irin ƙara ta dafe ciki, kasancewar cikinta ya shiga wata takwas da ƴan kwanaki sai aka ɗauka ko
naƙuda ce shiyasa aka kaita asibiti magani kawai aka basu suka dawo gida.



To tun daga wannan lokacin fah Suweiba bata ƙara samun lafiya ba,dama-dama ma Sani nayi
mata addu'ar da ya saba tun da samu cikin domin neman kariyar ɗan cikinta.



Cikin dare gari yayi tsit Talatu ta fito ta shiga barbaɗa magani tare da ambaton sunan Suweiba
sannan ta wurwurga wani dunƙulan abu ta jefa sama ta na mai cewa "kogon Kiresh wanda ke
can kusan bangon duniya can zaki je Suweiba"ta na gamawa ta shige ɗaki.




Tun asubar farin taji haniya tsakar gida,fitowa tayi kafin ta kai da tambaya taji Sani na sake
maimaitawa "wlh ko da na tashi ƙofar ɗaki a rufe take balle in ce fita tayi"
"Ka tabbatar kuma sai da ta shigo ɗaki sannan ka kulle ƙofa?"cewar Alhaji mahaifinsa"eh baba
ni na shimfiɗar da ita ma fa"Sani ya ƙarashe maganar cikin rawar murya.


Abun mamaki tun daga wannan ranar babu wanda ya sake tambayar Suweiba kaf gidan in ka
cire Sani wanda tun farko ya kasance mai riƙon addini shiyasa sihirin bai kama shi ba.
A duk lokacin da Sani yayi ma mutane maganar Suweiba sai suyi mashi ɗaukar mahaukaci
hatta iyayen da suka haifeta sun manta da ita, wannan dalilin yasa Sani ya dage da addu'ar
Allah ya bayyana mashi ita da nema mata kariya.
Addu'ar Sani ita ke neman kawo masu cikas wannan yasa Talatu ta biya ƴan daba suka kashe
shi,Salis yayi kukan rashin ɗan uwan shi sosai dan har sai da ya zauce.

SUWEIBA POV.

Bayan sun gama sunnah aure sai take jin kamar gabanta na faɗuwa hakan yasa ta shaida ma
mijinta Sani nan yace ta tashi suyi wankan tsarki sai suyi nafila budar bakinta sai cewa tayi "na
gaji ko gobe na yi"nan take wani duhu ya fara rufe mata ido sai barci,ganin haka yasa shi ma
Sani ya kwanta.


Kamar cikin mafarki taji ana kiran sunanta tare da yi mata raɗa a kunne,a tsorace ta tashi kawai
sai ji tayi an cillata wani wuri mai ƙololuwar nisa.



Halitta da ta gani ga banta ne yasa ta fara ja da baya duk da wurin duk ciyayi ne da ƙayoyi,ba
komai ba ne ta gani illa bayan wata tsohuwar aljana wadda gashin da ke jikinta ma kaɗai abun
tsoro ne.



Wata naƙuda ce ta sauko mata gadan-gadan a take ta haifu ba ta shirya ba,kukan jariri shi ya
katse ma mother bautar da take dan a duniya babu abinda ta ke so sama da ɗa.


Jin ƙamshin bil'adama yasa ta rikiɗa ta zama mutum kafin ta juyo inda Suweiba take cikin jini,da
sauri mother ta ɗauki jaririn ta na kallo kafin ta yanke mashi cibiya tace "mi ya kawo bil'adama a
kogon Kiresh wanda hatta aljanu ma suna shakkar shigowar sa saboda haɗarin da ke
ciki?"maimakon Suweiba ta bata amsa sai kawai ta kece da dariya tare da rugawa a guje
amman sai mother ta sa dogon hannunta ta maido da ita,kallon idon Suweiba kawai tayi ta
fahimci sihiri aka yi mata da kuma wanda yayi mata.


Duk da Suweiba na cikin halin hauka bata manta kalmar shahada ba,nan ta shiga jerota kafin
rai yayi halin sa sosai mother ta shiga damuwa dan lokaci guda taji ƙaunar su taimako guda tayi
mata shine ta maidota duniyar bil'adama nan aka tsinci gawarta aka suturtata a ka kaita gidanta
na gaskiya bayan anyi neman danginta ba a samu ba.

"William shine sunan ka ɗan mama ina sonka,zan reneka mu ɗauki fansa tare zan sa ka zama
*MUTUM DA RIGAR ALJAN*"cewar mother ta na mai baiwa William nono a nan take ya kama
ya fara sha.

TALATU POV.


Shiru-shiru tana jiran samun ciki amma har an kwashe 5ans(5years)ko dakwaye ba tayi ba,sai a
shekara ta bakwai ne ta samu ciki wanda ke da mugun laulayi da azaba gefe guda kuma cin
kuɗi dan kullum cikin ciwo take wannan yasa duk kuɗin familyn yayi ƙasa wanda har ya kai da
Salis fara neman aikin gwamnati yayi nasara samu kuwa domin yanzu tsufa ya zo ma Alhaji
kasuwanci ya aje sai ya zamana duk nauyin su ya koma kan Salis.

Shekarar da Talatu ta haifi ƴar ta Maryam a wannan shekarar aka saida rabin gidan da suke
zaune Salis ya sayi wani gida daban saboda tsangwamar da Hajiya ke nuna ma Talatu.


```Wannan ne ɗan ƙaramin tarihin```

CIGABAN LABARI....


Cikin tashin hankali daddy ya ƙaraso yana "subhanallahi kar dai a ce ciwon ne ya
dawo?"kasancewar momy sadda tana ƙarama tayi rashin lafiyar farfaɗiya.
Ruwa masu sanyi Maryam ta zuba mata aiko ta farka ta na mai ɓoye bayan daddy.....



*****

Cikin rashin madafa Laila tace "ok zan yi amman sai ka min alƙawali banda sex ɗin
dai"kwanciya Nur ya gyara ya fara kalalameta da daɗin baki tare da ƙara shimfiɗa mata gada
zare "ok naji amman doli sai ranar lundi tunda gobe weekend ne,amman kuma ka san ba a
school ɗin ku zan je ba ko?" "Eh akwai wani gida daban in baki ra'ayin nan ɗin"
"Ok sai da safe"cewar Laila ba tare da ta jira cewar shi ba ta kashe kiran jin motsin Abba.

Saurin liƙe ido tayi kamar mai barci sai abinda bata sani ba hasken wayar ta ya gama tona mata
asiri, girgiza kai Abba yayi tare da kashe masu hasken ɗakin.


Ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗaukar wayar ta tura ma Nur message na jaddada ƙauna da
soyayyar da take mashi.

A ɓangaren Nur kuwa ba su wani jima da gama waya ba kiran Iki ya shigo,cikin zumuɗi ya ɗaga
suka fara firar soyayya mai cike da baɗala wanda hakan yasa shi shaf ya manta da wasu wai
Esta da Rahul.




Ranar Lundi (Monday) ƴan magana kan ce ko mushe na tsoronta, wannan yasa duk ɗalibin
ƙwarai kan zuwa kan lokaci.
Shiri Laila take kamar ba gobe duk wani lungu da saƙo na jikinta ta feshe shi da wani arnen
turare.


Fitowar ta falo rataye da bag ɗin school yayi daidai da shigowar Abba domin har ya fita ya dawo
yayi mantuwa,cike da ɓacin rai da kuma mamakin halin da ta tsiro kwana biyu yace "duk turare
ne kika baɗa kamar ƴar bori kuma wai a haka zaki fita?"

Cikin i'ina ta sharo ƙarya "Abba kwalbar turaren ce ta fashe shine na goge da hijab ɗina amman
bari na canza wani,ƙila dan ina mura ne shiyasa ban ji hawan kan da yayi ba kuma Abba ai ka
san ban saka turare mai ƙamshi wannan...."ɗaga mata hannu yayi tare da mata nuni ta koma
ɗaki ta canza.



Nur kwance bisa ɗakin wani abokin shi yana jiran Laila sai duba lokaci ya ke ƙarfe tara suka yi
alƙawali yanzu kuma duka 7 na safe da ƴan mintina.
Tsuka ya ja kafin ya miƙe ya jawo plate ɗin indomi ya fara ci ya na korawa da jus,kamar daga
sama yaji ana bubuga gida lokaci guda kuma text ya shigo wayar shi " ```gani a ƙofar gida ka zo
ka buɗe min kar wani ya gan ni```" har da wani ihu Nur yayi kafin ya nufi hanyar waje........
[18/10 à 14:35] MRS SADAUKI : *MUTUM DA RIGAR ALJAN*


*Gajeren labari...*
Story
and
Written by
*MRS SADAUKI ✍️*
{Cham rose}
Dedicated to *PRINCESS AYSHATOU*

☀️ *FIRST CLASS WRITTERS ASSOCIATIONS*☀️
___________________
BISMILLAHI RAHMANI RAHIM.



Page 30-31


Murmushi Nur ya saki lokacin da idon shi suka yi tozali da Laila cikin doguwar riga ta
abaya,hannunta riƙe da bag.
"Na fah zata ba zaki zo ba"cewar Nur ya na mai matsawa dan ba Laila hanyar hucewa,shigowa
ta yi ta na mai cewa "sai gashi kuma na zo"ta faɗa cikin cool voice tare da nufar hanyar ɗakin.

Da ta shiga sai kuma ta ƙara da
"Waooo amman ɗakin nan ba ƙaramin haɗuwa yayi ba"rungumeta yayi ta baya yana mai cewa
"Allah baby?"kai ta ɗaga alamun eh,sunkuyo kanshi yayi gefen wuyanta yace "ai gidan mu sai
yayi wannan kyau "murmushi mai sauti Laila tayi tace "kaiii amman naji daɗi ko gidan ku na
Sonisi zamu zauna?"cike da mamaki Nur ya juyota da alamun tambaya fuskar shi yake kallon
ta,"eh mana ko ka manta kace min duk gidajen mahaifin ka na Sonisi yafi kyau?"murmushi yace
"na manta shaf na zata ba mu taɓa hirar ba ne,am....bari na kawo maki jus".



"Kar ka ɗauko min na mango nafi son goyave"cewar Laila ganin ya nufi frigo,waigowa yayi yace
"kamar kin san ko shi zan ɗauko maki,ni Mango ne favorite ɗina"ya faɗi haka yana mai tsiyaya
mata jus ɗin a kofi.


Kusa da ita ya zauna cikin salon su na ƴan duniya ya shiga ɓalle mata butanin riga yana mai
cewa "ya kamata ki cire wannan ki ɗan sha iska"sunne kai Laila ta yi ta na ɗan noƙewa shi
kuwa Nur har jikin shi ke rawa yana maganar zuci"yarinya kin shigo hannu tunda har tsotsayi
yasa kika kawo kan ki".

Cikin mintina da ba su fi talatin ba Nur ya karɓe budurcin Laila,cikin murya mai nuni da rarashi
ya fara mata magana "miye kuma baby?ina ce dai ko auren muka yi ni ne zan karɓi Virgin naki
ko?to miye abun damuwa a nan ki yi shiru please kukan tamkar narkarka dalma nake jin shi a
zuciya"wani murmushi ta saki wanda ba ta san lokacin da ta yi shi ba kafin ta shafi sajen fuskar
shi tace "Nur ina sonka so marar misaltuwa zan iya yin komai a kan ka ciki har da kisan kai,Nur
ban taɓa sanin haka rayuwa ke da daɗi ba sai yau da na kasance tare da kai kuma ina fatan ci
gaba da kasancewa da kai har ƙarshen rayuwata ko ta halin ƙaƙa ne"tana gama faɗin haka ta
shige cikin ƙirjin shi,wani abu Nur yaji yana shiga jikin shi wanda ya kasa tantance ko mine ne.

LAILA POV.


Cike da jin haushi ta koma ɗaki ta canza hijab kafin ta fito da sauri ta nufi ƙofar gida,cikin sa'a
kuwa ta samu abun hawa har bakin get ɗin makarantar su ya sauketa.


Tana fitowa ta tsinkayo Zee da sauri ta ƙarasa gunta tare da rungumeta cikin murna tace
"ƙawata yau akwai labari "ɗan tureta Zee tayi "ke ni sakar ni kin wani ruƙunƙume ni sai kace kin
samu Nur"cewar Zee tana ɗan ja da baya,"to ai akan shi ne nake son baki labari kin ga abaya
nan nazo da ita in an jima zuwa ƙarfe tara nake so ki raka ni wajen shi"cike da mamaki Zee tace
"mi kuma za ki yi wajen sa baki jin tsoro ne?"maimakon Laila ta bata amsa sai kuma ta ɗauko
mata wani zance "ke ni ba ma wannan ba wlh jiya nayi mafarkin Nur na biyata da gudu ga wani
ƙaton ƙadangare a hannun sa wai sai ya cilla min shi,sau wajen uku yana tullo min shi ina
kauce wa har sai ya kusa faɗowa jikina"waro ido Zee tana cewa "Allah kyauta ya kuma kare ki
daga sharrin shi,muje cikin aji please ki koya min math".


Cours ake amman hankalin Laila sam bai jikinta,tunani kawai take yadda moment ɗin su zai
kasance da Nur ana haka har lokacin fita shan iska yayi.


Hijab ɗinta ta cire ta ɗora doguwar rigar abayarta kafin ta fito bakin titi jiran abun hawa,sai da ta
sha tsayuwa sosai kafin wata farar mota ta tsaya kusa da ita.


"Ma chérie Laila ashe ki na nan?har na wuce na tsinkayo ki"cewar wata farar mace lokacin da
ta zuge gilashin mota,kallon inda ta santa Laila ta shiga yi amman sam ta kasa tunawa a haka
dai ta amsa mata ta ƙarashe da cewa "sai dai ban gane ki ba"murmushi tayi mata tace "ki shigo
na aje ki inda zaki"cikin zumuɗi Laila ta shige gidan gaba ita kuma ta ja mota suka tafi.

Sai da suka yi ɗan nisa ta samu wuri ta yi parking tana mai kamo hannun Laila tare da yin
magana cikin wani yare tun daga wannan lokacin Laila ba ta sake sanin inda take ba sai tashi
tayi ta ganta a gida.


Kai ta dafe ta na son tunawa da abin da ya faru amman ta kasa,abu guda kawai ta tuna shine ta
canza kaya izuwa abaya zata wajen Nur "to amman ya aka yi na kasa tuna ko na je ko ban je
ba wash "ta faɗa tare da ƙara dafe kanta.

Paracétamol ta ɓalla ta sha ko ta samu relief tare da ɗan kishingiɗawa. Wayarta ce ta bado
haske alamu kira na shigowa,lambar Nur ce ke yawo a jikin screen ɗin.Sai da ta kusa katsewa
sannan ta ɗauka,kamar kullum da sallama bakinta amsawa yayi kafin yace "na gajiyar da ke
sosai ko?kiyi haƙuri baby har magani na zuba maki a jus dan kar ki wahala sosai,am...ya
maman ta lura da canjin ki ko kuwa?"cewar Nur wanda ke ta zuba kamar kanya,shiru Laila ta yi
ta na jin zuciyarta na bugun tara-tara sam ta kasa tuna komai ,ga Nur na yi mata wani zance da
alamu ta je gidan na shi,cikin i'ina tace "canjin mi?"
"Tafiyar ki mana ko kin manta kince zafi kike ji ba zaki iya tafiya daidai ba?"jin Laila ba tace
komai ya ci gaba da cewa "humm! Amman fah baby kin haɗu sai dai raki ko dayake ba laifin ki
ba ne fitar virginité ne da wuya,ki kula da kan ki sosai ta yadda babu wanda zai gane zan tafi na
yi sallah"ƙit ya katse kiran.

Shaɓe-shaɓe haka fuskar Laila ta ɓace da hawaye, "shikenan na ci amanar iyayena kaicona ni
Laila mi yasa ka aikata haka gare ni Nur ?kenan ka san ba zan iya ba shine ka zuba min
magani wayyo na shiga uku"ta miƙe tsaye ta na yarfe hannu kafin ta shiga saffa da Marwa ta na
tunanin wanda zata gayawa,Zee ce ta faɗo ranta hakan yasa ta ɗauki waya ta kirata bugu ɗaya
aka ɗaga.


Ba tare da ko Laila ta yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login