Showing 15001 words to 18000 words out of 33902 words

Chapter 6 - Mutum Da Rigar Aljan Book Compelet by Mrs Sadauki

ta na yin baya-baya har ta kai jikin gado.

Tsalle ta yi ta bi ta jikin Maryam sai jin wata murwa wacce ba za ta tab'a mantawa ba ta na ce
mata " Talatu d'aga ni kar ki kashe ni"ihu momy ta runtuma tare da zubewa sumamiya.





Awa wajen uku kenan a na abu guda faman 'kara ma momy ruwa amman har yanzu ba ta
farfad'o ba,sai ma wani jijiga da take alamun furgici likitoci kuma sai faman scaning suke na
'kwa'kwalwa yayin da gefe guda kuma Maryam sai rizgar kuka take ta na faman kiran momy
abin da kuma suka kasa fahimta duk lokacin da Maryam ta ambaceta to murya Suweiba momy
ke ji wanda hakan ke sa ta jijiga.



Wani likita ne da ya lura da haka yace Khalil ya fitar da Maryam,hakan kuwa aka yi can wajen
asibitin suka fito ya na bata ha'kuri da rarrashinta.

Su na fita momy ta farka sai faman ajiyar zuciya take,"sannu madame "cewar nurse " yauwa
dan Allah kar ku bari wannan macen ta sake shigowa ban son ganinta"momy ta fad'a ta na
kuka.
Cike da mamaki nurse d'in tace "wace mace ko wannan yarinyar?" kai momy ta d'aga mata ta
na share zufar da ke keto mata.Kallon Dr nurse ta yi wanda yayi sa'ke ya na nazarin momy.

***


Jiki babu 'kwari Laila ta yi wanka tare da sallah kafin ta d'auki al'kur'ani ta karanta wanda sam
babu nutsuwa domin mafarkin da tayi sai yawo ya ke mata a cikin kwanya.
Zuciyarta a cunkushe ta fito dan d'ora girkin marice, ba ta tarar da kowa ba hakan yasa ta shige
madafa ta fara girka tuwon shinkafa da miyar kub'ewa d'anya.


Siraci ne ya bugi hannunta a take ta 'kwala 'kara sai kuma tayi sa'ke ta na maganar zuci "toh ina
ga hutar jahannama?wlh na tsani kaina ma tunda har na fara tunanin aikata sab'on Allah mafi
muni wai Zina kaiiii amman Laila kinji haushi" duk a zuci take maganar,hawayen da suka
kwaranyo mata ta goge kamin ta ci-gaba da aikin da take.



A b'angaren Nur kuwa wani irin tausayin Iki yaji na rabata da Virgin nata yayinda kuma b'angare
d'aya na zuciyar shi ya ke jin damshin sonta.Ita kuma baiwar Allah sai bayan sun tabka kuskure
ta shiga nadama tare da fargaba kar Nur yace bai auren ta.......
[18/10 à 11:08] MRS SADAUKI : *MUTUM DA RIGAR ALJAN*


*Gajeren labari...*
Story
and
Written by
*MRS SADAUKI✍*
{Cham rose}
Dedicated to *PRINCESS AYSHATOU*



☀️ *FIRST CLASS WRITTERS ASSOCIATIONS*☀️
___________________
BISMILLAHI RAHMANI RAHIM.


Page 28-29

Kwance take ta lumshe ido sai saƙa da warwara take,ta rasa abin da ke mata daɗi komai ya
jagule mata dan ko abinci ta kasa ci.Ba wani abu ba ne ke damunta face halin ko in kula da Nur
yake mata tun ranar da suka yi wayar ƙarshe inda har ta so tabi son zuciya ta faɗa kogin
nadama sai kuma mafarkin da tayi ya taka mata burki.

Ƙara jaraba kiran lambar Nur ta yi a karo na barkatai amman shiru har ta yanke bai ɗaga
ba,wasu siraren hawaye ne suka shiga kwaranyo mata ta gefen ido suna jiƙa pilown da ta ɗora
kanta.


Ba ta taɓa sanin ta na son Nur ba sai yanzu da ya ƙaurace mata wanda ba ta san dalilin yin
haka ba,hannu ta ji a fuskarta ana goge mata hawaye ba ta buɗe ido ba sai tsinkayo murya
Rahila ta yi tana cewa "kiyi haƙuri anty ki bar kuka ki maida lamarin ki da Allah,kar fah ki manta
a ko da yaushe umma na tunatar da mu da cewa duk wanda ya baiwa Allah ragamar rayuwar
shi to ba zai taɓa ƙasƙanta ba"Rahila ta ƙarashe maganar cikin raunananiyar murya.


Murmushi mai ɗauke da hawaye Laila ta yi tana mai tashi zaune ta rungume ƙanwarta,cikin
murya kuka tace "na gode sosai da tunatarwa my ƙanwa haƙiƙa na kasance mai sa'ar
kasancewar samun ki a matsayin ƴar uwa"ta faɗi hakan tana mai jan ajiyar zuciya tare da huci
mai ƙarfi kafin ta kuma cewa "ya kin ci abinci?"kai Rahila ta girgiza "ke na ke jira ai tun ɗazu
nake jiran fitowar ki amman ba ki fito ba shine na zo kiran ki kar tuwon ya huce"cewar Rahila
tana mai miƙewa tsaye "ok tafi ki jira ni".



Sai da ta goge fuskarta da kyau ta yadda umma ba za ta gane tayi kuka ba kafin ta fita,bisa
tabarma ta zauna kusa da Rahila wacce tun tuni ta sa kwanon tuwo gaba tana jiranta.


Abincin suka fara ci wanda rabin hankalin su ya na kan tv inda ake haska wani série
TÉRÉSA,cak Laila ta tsaya da barin cin tuwon lokacin da aka buɗo jarumin film ɗin yana kissing
budurwa shi tare da jifarta da kalaman soyayya.


Rumtse ido ta yi tana ji tsikar jikinta na tashi yayin da kwanyarta ke hasaso mata yadda abun
zai kasance ita da Nur.

Tsawar da Abba ya daka mata ne yayi sanadiyar ɗaukewar uban murmushin da take zubawa
tare da maidota daga duniyar tunanin da ta lula.

"Sannu da zuwa Abba "ta faɗa cikin rawar murya,bai amsa ba sai wani kallon tsaf da ya ke bin
ta shi kafin ya wuce inda umma ke zaune wadda gama sallah ta kenan.Ledar hannun shi ya
ajiye kafin yace "uwar yara yanzu ban hana ki saka tashar turawa a gidan nan ba?shine kika
wani zo ki na jan cazbaha su kuma suna kallon tv duk abin da za su kalla ke ba ruwan
ki"sunkuyar da kai umma ta yi kafin ta shiga bashi haƙuri maimakon ya sauka sai kuma ya sake
hawa "wane haƙuri zaki bani bayan ki na son gurɓata tarbiyyar yarana?yanzu sabida Allah
hakan ya dace ke kina aikin Allah su kuma ko sallah ba su yi ba amman ke hankalin ki kwance?
Abba ya tambaya cikin ɗaga murya wanda yasa ran umma ɓaci "haba mai gida su wasu
ƙananun yara ne da basu san daidai ba da kullum sai nace suyi sallah?"cewar umma ta na mai
ninke tapis.

Sasauta murya Abba yayi yace "amman kin san saboda su muna iya shiga wuta ko?domin
Allah yace mu kula da kan mu da ƴaƴan mu daga shiga huta,yanzu za ki ji daɗi ki na aljanna
yaran ki na wuta?"cikin rashin jin daɗin yadda umma ta mayar mashi da magana tace "kayi
haƙuri tabbas ba zan ji daɗi ba kuma na sani ƴaƴanmu kiyo ne a gare mu kuma ranar lahira sai
Allah yayi mana bincike akan irin yadda muka kiyaya su"murmushi Abba yayi najin daɗin
kallamanta dan tabbas shi da kan shi yasan umma ta na cikin nagartatun mata domin tun can
saboda addinin ta ya aure ta.


"Alhamdullah tunda kin fahimta yanzu sai a kiyaye bance kar a kalli tv amman a san abin da za
ayi kallo,ku kuma maza ku tashi ku yi sallah"cewar Abba ya na mai shiga ɗakin shi.





NUR POV.

Tun lokacin da ya ɓare Ikilima cikin ledarta ya rasa sukuni,sam bai ji ya na maradin komai
kamar ya kasance da ita sosai Elli ta ga canji ta yadda ya ke wani shareta dakyal take samun
shi shi ma ba wani jamawa yake ba gidanta in ma yaje bai wuce romance.



Tun Elli ba ta damuwa har takai ta kasa ɓoyewa ta sanar da Esta nan ne Esta take ce mata "ai
kin makkaro domin yanzu ya samu sabuwa a leda ya bar yayin ki"kallon ban gane ba Elli tayi
mata ita kuma ta cigaba da cewa "eh mana ko baki san sun jone shi da Iki ba?ai tuni ya
garwaya da ita kuma shine first da ya fara saninta a ƴa mace" ƙwallo ido Elli tayi tace "na shiga
uku wai da gaske kike ko wasa?ita Ikin ta faɗa maki haka?"dariya Esta tayi tace "babu wanda
ya gaya mani ni na sani da kaina kuma na gaya maki ne dan ki fidda rai"rufe bakin Esta ke da
wuya Elli ta fara kuka tana suratai tare da zayyano irin moments ɗin da suka yi masu daɗi

wanda har ya kai yasa zuciyar Esta ayyana wani ƙudiri.



Tun bayan magrib gaban Nur ke faɗuwa haka kawai ya ji ra'ayin karanta alƙur'ani mai
girma,cike da nutsuwa yake karatun cikin sauti mai daɗi ya ɗauki lokaci kafin ya tashi ya tafi
masallaci yana dawowa kuma ya ci gaba.
Sosai ya ji zuciyar shi ta yi sanyi tare da samun nutsuwa,rabon da yayi karatun al'ƙur'ani har ya
manta sai yau kuma ba dan bai iya ba.



Sai da yayi addu'a sosai kafin ya maida ƙur'anin,sai a lokacin Rahul ya shigo ɗakin ya na
ƙanƙame jiki kamar mai jin sanyi.


Ɗan buɗe ido Nur yayi ya kalle shi kafin ya taɓe baki yace "an dawo daga yawon
shaƙatawar?"ya faɗi hakan yana mai yi wa Rahul kallon tsaf,harara ya zabga mashi ce "dalla
can malam wane yawon shaƙatawa bayan duk ka wani takura ni da karatun ka"cewar Rahul ya
na mai hayewa kan bed,tashi zaune Nur yayi cike da mamaki yace "yanzu ƙiyayar musulunci
har ta kai haka ga zuciyar ka ta yadda har karatun al'ƙur'ani zai takura ka?shi fah waraka ne ga
al'umma"martanin hararar Rahul ya mayar mashi kafin yace "eh ga ku Musulmi ba mu ai takura
ne a gun mu ko kaɗan ban son jin karatu"Rahul ya faɗa ganin irin kallon da Nur ke mashi yasa
shi saurin sauya fira da cewa "wai nace ina budurwar ka malamar nan kwana biyu na ji shiru
kabar ƙorafi a kanta"ɗan sosai ƙeya yayi kafin yace "wai Laila ?tana nan amman na jima ban
kirata ba ko ta kira ni ban ɗauka"


Cike da mamaki ya tambaya "dan mi?"direct ya bashi amsa da "in ba haka nayi mata ba to lalle
bazata taɓa bari na moreta ba "

Cikin nuna ƙin jin daɗin haka Rahul yace "Please Nur ka ƙyaleta tunda ka nada su Elli da Iki su
kaɗai sun isheka kar ka ɓata yarinya mutane"saurin katse shi yayi da "no kar kayi ɓarnar bakin
ka ai yanzu Nur bai sake alaƙa da wacce ba Virgin ba,tuni Iki ta buɗe min ido ashe suma mata
kamar sabuwar mota ce wadda take dal a leda ba ɗaya take da wadda aka riga aka buɗe
ba"galala Rahul yayi da baki yana kallon shi gira Nur ya ɗaga yace "Yes ko baka ga yanzu Elli
bata gabana ba sai Iki?"kafin kace wani abu suka ji an banko ƙofa ,Esta ce cikin sleepinc dress
sai wani karkaɗa jiki take kamar zata ƙalle.


Da sauri Rahul ya taso yayi huging nata yana mai jawota suka faɗa bisa godo,kamar yadda
suka ba yau ma luluɓewa suka yi cikin bargo suna aikata masha'ar su sai nishi suke da fitar da
numfashi tamkar su ɗaya ne cikin ɗakin.

Duk da ba yau ba ne farau ba amman bai hana Nur jin haushi ba,nan ya lalubi wayar shi ya
shiga kiran Iki shiru bata ɗaga ba a na cikin haka kiran Laila ya shigo wacce kewa da gubar
soyayya ta hanata barci.


Ɗagawa yayi ba tare da yace komi ba,ajiyar zuciya ta sauke tare da fara gaida shi da kyal ya
amsa wanda sam yadda yake mata magana bai mata daɗi "dan Allah bbna kayi haƙuri kar ka
sake yi min irin wannan hukunci kaji?"a yadda take magana kawai ya tabbatar mashi da cewa
Laila ba ƙaramin so take mashi ba hakan ya sa yace "a'a miye na bani haƙuri kawai haka ne
daidai kowa ya kama gaban shi tunda baki iya yi min ɗan ƙaramin abinda na saki Allah gama
kowa da rabon shi"cike da tashin hankali Laila ta tari numfashin shi da cewa "ba fa haka ba ne
bb abinda ka tambaya ne baida kyau"


"Mine ne baida kyau ?romance ne fah kawai kin fi kowa sanin yadda nake sonki ba zan iya
cutar da ke ba,kuma Virgin naki nayi tanadin shi ne sai ranar tarihi ta first night ɗin mu"ko da
Nur ya zo nan da zancen shi sai tunanin Laila ya kasu gida biyu ta yarda da shi ko kuwa a'a ....





****


Jikin momy ba a cewa komai sai hamdallah ga Allah dan yanzu tabar firgita sai mugayen
mafarkai wanda sai tsakiyar dare aji ta ƙwala uban ihu in kuma an tambayeta sai ta fara
kame-kame a ƙarshe tace babu komi.


Ɓangare guda kuma har an tsaida maganar auren Khalil da Maryam wanda jiran daddy kawai
ake a saka ranar biki.Sosai Khalil ke murna da auren yayinda kuma gefe guda yake cikin ruɗani
game da lamarin Maryam wani sa'in ta kan nuna mashi soyayya wanibi kuma tsana da hantara
dan har ikirari take in ya bari aka ɗaura auren su sai ta zama ajalinsa a ƙarshe ta fashe da kuka.



William POV.

Tun lokacin da mother ta ɗaure shi da bai sake ganin ta ba,sai dai a mafarki inda duk abinda ke
wakana a duniyar bil'adama yake zo mashi tiryan-tiryan.
Babu abin da yake ɗaga ma shi hankali sai auren da za ayi ma masoyiyyar shi.



Cike da firgici ya farka daga barcin da ya ke,karo na farko da yaji haushin mother domin ya san
duk wannan tuggun ita ta ƙulla shi.



Lumshe ido yayi yana mai yin tunani akan wata formule ta tsafi da mother ta koyar da shi,a
hanki ya fara motsa bakin shi tare da karanto ɗalasiman tsafi a take Maryam ta bayyana a jikin
bango tamkar a tv.



Zaune take a cikin toilet ta haɗa kai da gwiwa sai gwanjin kuka take,kamar daga bisa yaji ta fara
magana "Please mahaɗin rayuwata ka zo gare ni yanzu ka bar sona abaya a duk sadda na
shiga toilet nakan ji kamar ina tare da kai yanzu kuma ka bar zuwar min gashi har ana son min
aure da wanda ban so"ta ƙarashe maganar cikin kuka kafin kuma daga bisani ta miƙe ta nufi
bakin mirror tayi tsaye tana kallon surar jikinta.


Hankalin William ne yayi mugun tashi ganin kyakkyawar surarta ta bayyana tarau ta yadda ya
ke ganin komi na jikinta,so ya ke ya miƙe amman ya kasa a na haka ya tsinkayo Khalil yana
bubuga ƙofar toilet ɗin.



Cike da so da ƙauna Khalil ya shiga bubuga ƙofar yana cewa "sweety kiyi sauri ki fito har mai
kwalliyar da mai ɗaukar hoto sun zo"can cikin toilet ta ja wani uban tsuki kafin tace "na ƙi na
fiton kum...."cak maganar ta tsaya sakamakon kanta da taji ya sara sai kuma ta ci gaba da
cewa "ka jira ni honey yanzu zan fito da fatan dai har ka shirya?"cike da mamakin al'amari'
Maryam ya amsa mata da "eh"kafin ya fice daga ɗakin.


A ɓangaren William kuwa wani tuƙuƙin baƙin ciki mai game da ɓacin rai ne ya rufe
shi,sakamakon ganin mother ta shige cikin jikin Maryam dan canza mata aƙida na yi ma Khalil
biyayya .


A gagauce Maryam ta yi wanka ta fito sai wani rawar kai take irin na amare,mai kwalliyar ce ta

shigo nan ta tsantsara mata kwalliya kafin ta tayata zaɓen kayan da za ta fara sakawa.


Wata rantsatsar shadda bleu ciel Khalil ya shigo da ita wacce ta kasance iri ɗaya da ta jikin
shi,miƙa ma Maryam yayi yana murmushi"ki saka wannan kin ga mun yi anko"maimakon ta
karɓa sai wani shagala da ta yi da kallon shi,gira ya ɗaga mata yace "ya ko shirin bai yi ba?"dan
sunkuyar da kai tayi tace "na ga kamin kyau ne ba kamar kullum ba" "To in ba abun ki ba ko kin manta na kusa zama ango?"
"Haka ne"ta faɗa tare da karɓar kayan.



A babban falo aka shiga ɗaukar su hoto ,da ka gan su ka ga masoya irin yadda suke aika ma
juna da kallon soyayya.
Cike da farin ciki momy ke kallon yaran nata sai murna take,a ƙasan zuciyarta kuma addu'a
take "Allah kasa har a gama bikin nan fatalwar Suweiba ba zata zo min ba,ta yadda zan
gwangwaje sosai"ba ta ita tunanin ta ba ta tsinkayo Suweiba a fuskar Maryam tamkar da ita ce
ake ɗaukar hoto,har zata kawar da kai taga tana hararar ta .Bugun zuciyar momy ne ya ƙaru
nan ta fara karanta duk addu'ar da ta zo bakin ta.


"Momy ki shigo ayi mana na family"cewar Maryam ta na mai sakar mata murmushi wanda
momy ta gan shi kamar bakin tsoho babu haƙora,cike da tsoro ta girgiza kai alamun ba za ta je
ɗin ba.
Fuska Maryam ta kwaɓe cikin sakuwa tana bubuga ƙafa tana mai cewa "ni dai ban yarda ba ki
zo kawai ayi mamu"tashin hankali wanda ba'a sa mashi rana domin idon momy wata halitta
daban ta hango a matsayin Maryam a take ta zube ƙasa a sume wanda yayi daidai da shigowar
daddy.


*WAIWAYE....*


Alhaji Hamidine shahararren ɗan kasuwa ne wanda duk illahirin nahiyar Nijer ta san da shi,a
maraɗi yake a zaune a wata unguwa ta masu hannu da shuni Ali Dan Sofo.
Matar shi guda tal Hajiya Turai,ƴaƴan su biyu maza Salis shine babba sai Sani wanda ya
kasance ƙarami kuma Auta.

Lele da gata tare da sangarta su suka yi ma uwannan yaran ƙawa domin basu san wata wahala
ba tun suna ƙanana har suka mallaki hankalin kansu suka yi aure.

Talatu ita ce ta kasance matar Salis shekarar su biyu da aure kamin Sani ya auro Suweiba

wadda tun watan auren su Allah ya azurtata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login