Showing 24001 words to 27000 words out of 33902 words
Chapter 9 - Mutum Da Rigar Aljan Book Compelet by Mrs Sadauki
ta dawo ta zauna a wurin da yayi mata nuni.
Malam Rabi'u ne ya shigo, kasancewar an yi mashi bayan tun kafin ya zo yasa shi fara karatu.
Wani irin gurnani momy ta fara yi tana cewa "malam kar ka ƙona ni domin wannan matar babu
abin da ya dace da ita sai azaba"nan mother ta shiga fallasa asirin momy kafin daga ƙarshe
tace "ko kashe ni zaka yi ba zan fita daga jikin ta ba "karatu malam ya shiga yi wanda ya
galabaitar da mother cikin ƙaraji da azaba take magana "zan fita amman dan Allah kar ku raba
ni da William ina son shi ni na raine shi"
"A'a wlh ba zan bar maki jikana ba Malam ka taimaka kace ta fito min da jika"cewar Hajiya tana
kuka,riƙeta daddy yayi yana kwantar mata da hankali.
Sai da aka sha daga sosai kafin mother ta haƙura ta bayyanar da William,ashe dama ko da ya
ɗauki Maryam bai tai ko ina ba suna cikin gidan.
Duk mutanen wurin kallon ikon Allah suke ganin William gefe guda kuma Maryam ce sai riƙe
mashi hannu take.
Hajiya Turai kuwa kasa motsawa tayi dan ganin tsantsar kamar da yayi da Sani.
Hannu malam ya aza bisa kan William ya shiga karatu ,wani baƙin abu ne ya shiga amayarwa
kamar ran shi zai fita shi kuma malam sai ƙara ƙaimi yake.
Ba ƙaramar galabaita William yayi ba dan sai da ya amayar da nonon da mother ta bashi tun
yana jariri wanda shine silar kasancewr shi *MUTUM DA RIGAR ALJAN*
Kamar ɗokewa ruwa haka momy ta dawo daidai bayan tayi atishawa uku,kallon mutane ta shiga
yi bisanin ta ƙura ma William ido wanda ke kwance yana fitar da numfashi.
Motar ƴan sanda ce ta tsaya,tisa ƙeyar momy aka yi ita da Hajiya Zahra.So take tayi magana
domin yafiyar daddy amman bakinta yayi mata nauyi,idonta na zubar da hawaye aka tura su
cikin mota.
Da taimakon Khalil William yayi wanka,ya shirya tsaf cikin wata dakakiyar gizna fara sol wadda
ta kasance ta Khalil ɗin ce.
Dama tun can ya karɓi kalmar shahada,jaddada masa ita kawai aka yi tare da sauya masa
suna.
Mutanen da suka yi saura aka zazauna aka ɗaura auren Mohammed Sani tare da Maryam Salis
akan sadaki ƙanƙane.
Sosai Khalil yayi jarumta wajen kwantar da hankalin shi,amma duk da haka a ƙarshe sai da ƴar
ƙwalla ta zubo ma shi jin an ɗaura aure amma ba da shi ba.
Wani irin sanyi mai game da daɗi ne ya luluɓe William wanda yanzu aka maida mashi suna
Mohammed,hannun Khalil ya kama cikin cool voice yace "ka sanyawa ranka dama ba matar ka
ba ce,ina mai baka haƙuri duk da wannan shine zaman lafiyar ka dan mother tana iya haukata
ka ko kashewa in ka auri Queen "Khalil na jin haka ya ƙyarƙyaro murmushin doli.
Mutane sai barka biyu ake yiwa Mohammed ta aure da musulunta,shi kuma sai wani jin shi
yake sama a doli shi ga ango.
***
Zaune take a ɗaki Zee na faman shafa mata dilka a jiki,yayin da ita kuma ta maƙala écouteur da
kunne sai waya suke suna hira soyayya ita da Dr.
Cikin shagwaɓa tace "Please ka kashe har mu gama,dilka fah ake shafa min a jiki"Laila ta faɗa
kamar zata yi kuka don tunda bikin su ya rage sati biyu Dr ya sha mata kai da kiraye-kirayen
waya,zaro ido yayi yace "ga jikiii?ga jiki fa kika ce?wane dan karanbani ne yake aikata wannan
kuskuren?"turo baki gaba tayi tace "Zee fah ce kuma ai na ga ba wani abu ba ne tunda mace ce
ƴar uwata"numfashi ya sauke cike da tsantsar kishi yace "Please kice mata ta rufe idonta kar ta
kalle min ke tunda ba ita ta biya min kuɗin sadakin ba"dariya Laila ta yi kafin ta tsinke kiran.
Yadda suka yi da Dr Laila ta gayawa Zee,dariya tayi tace "eh lalle samun wuri ai sai kice
taimaka mashi ne nayi dan fatar jikin ki tayi laushi"cewar Zee tana mai wanke hannunta a roba
dan har ta gama shafa mata.
"Rabu da shi ni wlh har mamakin shi nake sam yanzu bai jin kunyata ba kamar da ba"jan baki
Zee tayi tace "ai gwara hakan domin kun kusa zama ɗaya"
NUR POV.
Sosai jikin shi ya fara yin dama tun ranar farko ɗin da aka kai shi asibiti.
Maman ce ta shigo hannunta riƙe da ɗan ƙaramin kwandon abinci,sallama tayi Nuratu wadda ta
kasance ƙanwar Nur ta amsa tana mai cewa "maman albishirin ki?"da fara'a tace "goro mi ya
faru?"rungume uwar tayi tace "Nur yayi magana kuma har tashi yayi ya shiga douche dan
karambani sai da ya so yin wanka nace ya bari har a tambayi likita".
"Da gaske Nuratu?ko dai dan ki kwantar min da hankali ne?"maman ta faɗa tana ƙarasawa
bakin gadon da Nur ke kwance ta tsura mashi ido.
"Allah da gaske nake maman bari Dr ya shigo ki ji da bakin shi,dan da kanshi ya ce ya bari har
a gama sa mashi allura ruwa tunda lokacin sakata yayi allaso daga baya yayi wankan"cewar
Nuratu tana mai son tabbatarwa maman gaskiya ta faɗa mata.
Hamdallah maman tayi kafin ta shiga shafa fuskar tilon yaron nata,Nuratu ma ƙarasowa tayi ta
kafe Nur da ido tana jin hutar son shi na ƙara ruruwa a zuciyarta.
Bayan sallah Zuhur Nur ya farka tare da salati bakin shi, ƙoƙarin miƙewa zaune yake nan daddy
ya taimaka mashi ya jinginar da shi a pilow.
Kallon su ya tsaya yi ɗaya bayan ɗaya kafin ya rufe ido yana sauke ajiyar zuciya,yanzu ne ya
tabbatarwa kanshi tabbas babu abin da ya kai dangi daɗi.
Buɗe ido yayi jin hannun mahaifiyar shi kan fuskar shi tana goge mashi hawayen da ke zuba,
"miye kuma na kuka bayan sauƙi ya fara samuwa?ai godiya za ka yiwa Ubangiji"faɗawa yayi
jikin maman tare da fashewa da kuka mai ƙarfi "maman sam ban kyauta maku ba kun bani
tarbiyya amman na yi fatali da ita,baku rage ni da komi ba am...."kukan da yaci ƙarfin shi ne ya
hana shi ƙarasawa,iyayen shi na rarrashinsa yayin da Nuratu ke kuka biyu na murna da na
baƙin cikin ganin abun ƙaunarta cikin damuwa.
Da kyar Nur ya yi shiru sannan ya shiga toilet yayi bruch da wanka,sabbin kaya ya saka.
Nuratu da kanta ta shiga bashi salade na fruits a baki,sai da ya ci sosai wanda rabin hankalin
shi na kanta sai kallonta yake yana mamakin yadda ta girma cikin lokaci ƙanƙane .........
[20/10 à 19:53] MRS SADAUKI : *MUTUM DA RIGAR ALJAN*
*Gajeren labari...*
Story
and
Written by
*MRS SADAUKI*
{Cham rose}
Dedicated to *PRINCESS AYSHATOU*
☀️ *FIRST CLASS WRITTERS ASSOCIATIONS*☀️
___________________
BISMILLAHI RAHMANI RAHIM.
34-35
Tun lokacin da William ya dawo duniyar bil'adama komi na shi ya canza,a baya ya kasance
shiru-shiru saboda mother kawai ya sani saɓanin yanzu da ya kasance mai surutu.
Cikin hanzari ya fito daga ɗakin da ya kasance an bashi,hannun shi riƙe da tapis zai je
masallacin juma'a.
Tun da ya fito take satar kallon shi ganin yau kyawun da yayi na daban ne duk da cewa dama
shi ɗin kyakyawa ne.Caraf idon su ya harɗe cikin na juna,sadda kai ƙasa Maryam ta yi ta na mai
jin kunya kamata da yayi tana kallon shi.
Rumtse ido ta yi numfashinta na fita ɗaya-ɗaya yayin da gudun zuciyarta ya ƙaru a sa'ilin da ya
zo daf da ita, murmushi yayi yace "Assalamu alaiki amaryar Md da fatan kin wayi garin yau
lafiya?"saurin ɗagowa ta yi jin kalaman shi sam ba ta zaci zai yi mata magana ba kasancewar
yadda auren su ya zo da sarƙaƙiya bai sa sun keɓe ba ko yin wata hira.
Duƙawa yayi ya hura mata iskan bakin shi kan fuskarta,firgigit ta dawo daidai tare ɗan turo baki
gaba shi kuma yayi saurin caɓe laɓanta duk biyun ya shiga kissing.
Sakinta yayi ya na maida numfashi kafin ya zuba mata idanun shi uwanda suka canza kala,kai
ƙasa Maryam ta fara wasa da zoben hannunta tana mai jin wani farin ciki.
"Amarya Md kiyi min magana ko na kai ki ɗaki" cewar William dan ya ga a ɗaɗare take,jin haka
yasa Maryam ta yunƙura da ƙarfi zata guduwa ɗaki sai aka yi rashin sa'a tayi tuntuɓe ta faɗa
jikin shi.
Wata sanyayar ajiyar zuciya suka sauke a tare,luf ta lafe a jikin shi tana jin wata natsuwa na
shigar ta.Ƙugunta ya zagaye da hannuwan shi,kafin ya sauko da kanshi wajen wuyanta daidai
saitin kunnenta yayi mata raɗa.Da sauri ta jimƙe ido tana mai ɓoye fuskarta cikin ƙirjin
shi,"Please baby ki sake ni kar na rasa jam'i,am...kin ga sai na sake alwala"maƙe kafaɗa tayi
alamar ta ƙiya hakan yasa William ciciɓarta ya nufi ɗakinta da ita,kan bed ya direta tare da
kwantowa yayi mata rumfa.
Tsura mata ido yayi ganin yadda ƙirjinta ke yin ƙasa da bisa wanda hakan ya kasance na
fargaba ne,ta ƙasa t-shirt ɗin ta ya zura hannu ya fara yi mata tafiyar tsutsa har ya kai sama.
Hannun shi ta riƙe tana mai jan numfashi gabanin ta girgiza mashi,cikin rarabewa tace "lok..acin
sallah y..ayiii"jin haka William ya mirgina gefe yana mai jin wani abu na tsarga ma shi tun daga
kwanya har tafin ƙafa.
Yana fita Maryam ta miƙe zaune tare da dafe zuciya kafin ta saki wani ƙayatacen murmushi
lokaci guda kuma ya ɗauke tuna irin halin da ta tarar da momy jiya da suka kai mata ziyara,duk
ta jeme tayi baƙi.
Ganin tunanin momy babu abin da zai haifar mata sai tarin damuwa yasa ta shige toilet ta ɗauro
alwala tare da gabatar da sallah.
★Bayan sallah isha'i,duka famyling sun haɗu a falo Hajiya Turai (kakar su Maryam)tayi gyaran
murya kafin tace "salihu ya kamata fah a fara shirye-shiryen tarewa ƴaƴan nan,tunda komi ya
riga da ya lafa ko ya ka gani?"gyara zama dady yayi yace "dama tuni na sa a gyara gidan da na
siya kwanaki yanzu haka an gama komi har penti,gobe in Allah ya kai mu sai ayi jere" "A toh gwara dai haka,ni ma gobe zan koma gidana"Hajiya ta faɗa tana mai tashi tayi masu sai
da safe kasancewar tun wuri take kwantawa.
Mohammed dady ya kalla wanda kan shi ke duƙe tunda Hajiya ta fara magana,"Md in akwai
abin da kake da buƙata ka sanar da ni kaji ko?"kai William ya daga shi kuma dady ya tashi ya
bar wajen sai ya rage daga shi sai Maryam.
Turo baki gaba tayi tace "Ni abar kallona tunda ba tv ba ce"dariya Md yayi wadda ta fito da
tsantsar kyawun shi kafin yace "ya aka yi kika san ina kallon ki in ba dai kema kallon nawa kike
ba?"
"A'a ni ban kalle ka ba,jikina dai ya bani"Maryam ta faɗa tana mai kallon shi cikin ido.
Sun daɗe suna kallon juna kafin ya sauke ajiyar zuciya yace "mi kika yi min tanadi gobe?"kawar
da kai tayi sannan ta amsa da "mi za ayi goben?"waro ido yayi yace "au!baki sani ba?gobe
daren farkonmu mana"murmushin gefen baki tayi tace "to miye na sauri ka jira har goben
mana,ai surprise ne"da sauri ya taso daga inda ya ke ya zauna kusa da ita yana mai tambayar
ta "haba?ki bari Dan Manzo,ashe akwai didima"ɗagowa tayi tana kallon shi cike da mamaki
yadda ya iya Hausa har haka.
Gira ya ɗaga mata "yaa miye na kallona?"
"Barci nake ji"ta bashi amsa "ok muje na raka ki"Md ya faɗa yana mai jan hannunta izuwa room
ɗin ta.
Washe gari
Tun safe aka shiga gyaran ɗakin amarya,dangin uwa da na uba duk an taru sai hira ake wacce
rabinta duk jajen abin da momy ta aikata ne.
Nasiha mai ratsa jiki iyaye suka yi ma ango da amarya kafin a kaita ɗakinta, Mohammed ya
samu rakiya Khalil wanda ya koma tun falo yayi masu fatan alkairi.
Hamdallah yayi ga Ubangiji ganin irin ni'imar da yayi mashi lokaci guda,sallama yayi amman
bata amsa ba sai gwanjin kuka da take.Bed ɗin ya hau ya jawo ta jikin shi ya shiga aikin rarrashi
daƙyar ya shawo kanta har suka yi alwala suka yi sallah suka ci abinci da jus.
Daren farko mai cike da ni'ima hakan ya kasance ga wannan masoyan biyu,sun nuna ma junan
su soyayyar zahiri saɓanin wacce suke yi ta mafarki.
Wani irin kuka ne ya zo ma Maryam lokaci guda sa'ilin da taji Md na raɗa mata addu'a
kasancewa da iyali,murya na rawa tace "a'a ban so Please ka bari ina jin tsoro ne"
"Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un, Please William kar kayi wlh ban so tsoro nake ji"muryar Maryam
ke faɗa cikin kuka,ɗago jajayen idanun shi yayi yana kallonta cikin murya ta irin ki tausaya min
yace "ayya babyna ki haƙuri mu raya daren nan kin kau san lokacin da na ɗauka ina jiran
wannan ranar?miyasa baki so alhalin burin masoya shine wannan?"kai kawai ta iya girgiza
mashi tana son ya ɗagata sai yunƙurin tashi take,cak ta tsaya jin William na kuka kamar wani
ƙaramin yaro yana mata magiya zuciyar ta ce ta tsinke da lamarin shi hakan yasa ta ƙanƙame
shi gam,shi kuma ya kwararo addu'a yana mai zuwa wajen cikar burin shi duk yadda ya so ya
bita a sannu gagara yayi jin shi wani fagen rayuwa inda bai taɓa zuwa ba.
Bayan komi ya lafa ya jawo ta jikin shi suna sauke ajiyar zuciya,kamin ya shiga sa mata albarka
da dadaɗen kalamai masu tsayawa a rai.....
***
Baka jin komi sai kukan Laila gefe guda kuma mata sai rangaɗa buɗa suke,cikin kuka take riƙe
ƙafafun umma tana jin kamar kar su rabu yayin da kuma wasu mata biyu ke ƙoƙarin miƙar da ita
tsaye dan tuni ƴan daukar amarya suke jira.
Har aka shiga mota Laila bata bar kuka ba kamar wacce ake zuba ma ruwan zafi a jiki sai gumi
take haɗawa,tsayuwar motar shi ya tabbatar mata da an iso gidan.
Magajiya umma ke jaye da ita,bata ajeta ko ina ba sai tsakiyar gadonta.Bayan an yi addu'o'in da
aka saba kowa ya watse ya rage daga ita sai Zee wacce ita ma jiran zuwan ango ne take domin
Laila ta riƙe ta gam taƙi saki.
Tun suna sa ran zuwan Dr Dee har suka fidda domin ƙarfe ɗayan dare ta gota abin da basu
sani ba Dr yana can falo ya kasa shigowa ɗakin ƴar abokin shi.
Kamar daga sama yaji murya Zee na cewa ita ɗayan ɗakin zata ta kwanta ƙila sai dare ya ƙara
tsanantawa Dr zai shigo.
Ƙarfin hali yayi ya nufi ɗakin tare da yin sallama,Zee ta amsa tana mai cewa "yauwa ga angon
ki nan ni bari na koma falo"da sauri Dr yace "No kiyi zaman ki mana ai yanzu zan koma"Zee
kam ficewa tayi ba tare da ta saurare shi ba, yayin da Laila ta tafo zata bin bayanta,hannunta Dr
ya riƙe yace "ina kuma za ki?"taurau ta fara yi da ido alamun tsoro kuma sun bayyana kan
fuskarta.
"Koma ki zauna bakin gado ki jira ni"yana gama faɗin haka ya fita waje sai gashi ya dawo da
plate biyu ƙarami da babba,Zee ya bata ta kaima tare da jus.
Har yayi wanka da alwala Laila bata dawo ba,leƙawa yayi falo Zee kawai ya gani har ta gama ci
sai sharɓar kwana take.Cike da mamakin inda Laila ta shiga ya maido ƙofa kawai sai yaji motsi
a drower ya na buɗewa yayi tozali da Laila ta takure wuri guda duk ta haɗa uban gumi.
Ƙuri yayi mata da ido yana kallonta ita kuma sai ƙara lunƙumewa take tana ririƙe jikinta shi abun
dariya ma ya bashi.
Baki Laila ta turo ganin ya kasa cewa komi sai kallonta kawai da ya ke,fuskar tausayi tayi cikin
alamun tsoro take magana "Please uncle ka ƙyale ni wlh tsoro nake ji,kuma fah Zee tana nan
falo"ta ƙare maganar hawaye na zubo mata sharrr a fuska.
Lumshe ido Dr yayi yana jin yadda zuciyar shi ke motsawa tana bugawa da ƙarfi kamar zata
faso ƙirji,bai bata amsa ba sai tunanin zuci da ya fara "ta yaya ma zan far maki alhalin banda
wannan ƙarfin zuciya,ni ina jin kunyar ki ke kuma tsorona"volume ɗin kukanta da yaji yasa shi
saurin buɗe ido tare da furta "ya Salam!oyaaa!fito muje muyi sallah ba zan maki komi
ba"tsagaita kukan ta yi tana kallon shi dan gano ainahin gaskiyar,kai ya jinjina mata yana mai
miƙa hannu ya taimaka mata ta fito.
Wanka tayi da alwala ta fito sai wani raba ido take kamar munafuka, murmushi ya sakar mata
yana mai shiga gaba ya ja su sallah.Bayan ya sallamce sosai ya kwararo masu addu'a kafin su
fara ciye-ciye wanda Dr ne jigon cin nata abincin.A tare suka yi bruch inda Laila tayi tsaye cikin
toilet tana jiran ya fita ta sake yin wani wankan,kallonta yayi ya ɗaga mata gira alamar su fita mi
take jira.
Ɗan turo baki tayi ta nuna mashi shower hakan yasa ya fita dan bata damar yin wankan cike da
mamakinta kamar wata agwagwa.
Sosai Laila ta tsala wanka ta wanke duk wani lungu da saƙo na jikinta duk dama jikinta bai da
datti,towel ta ɗaura wanda ya kawo mata har ga ƙwabri kafin take fitowa.
A zaune ta tarar da shi gaban troly sai faman duba kayan da zai bata ta saka yake,duk wadda
ya ɗauko sai ya hangi wadda tafita kyau hakan yasa duk ya fitar da