Showing 27001 words to 30000 words out of 33902 words

Chapter 10 - Mutum Da Rigar Aljan Book Compelet by Mrs Sadauki

rabin kayan.


Sadaf-sadaf ta wuce ta ɗauki hijabin da ta cire ta saka kafin ta tsaya bakin coiffeuse ta shiga
shafa mai da turaruruka masu ƙamshi,ta madubi ta hango ya na nufota hannun shi riƙe da wata
ficiciyar rigar barci.

Ido ta waro jin yayi sama da hijabin jikinta yana dariya kafin ya ɗauke cak ya ajiye bakin
bed,towel ɗin yake ƙoƙarin janyewa ita kuma ta riƙe shi gam.

Kan bed ɗin ya haye ta baya ya kwantar da haɓar shi kan wuyanta kafin ya fara sunsunar
ƙamshin jikinta tare da sauke laɓan shi,a tare suka sauke ajiyar zuciya lokacin da yayi mata
ƙawanya da hannuwan shi.Lumshe ido yayi yana jin zuciyar shi na bugawa a lokaci ɗaya da

tata,cikin dabara ya zame towel ɗin ya saka mata rigar da ita da babu duk ɗaya.

Rumtse ido Laila tayi jin ya saketa yana mata dariya ƙasa-ƙasa,alamu sun nuna ba ta san
lokacin da ya saka mata rigar ba ma.

Cikin jin kunya take jan rigar dan rufe mata cinyoyi amma bakin tsawon ta bai wuce
mazaunanta ba,tsaye yayi yana kallonta tare ƙare ma surar ta kallo,ƙwal-ƙwal tayi da ido cikin
shagwaɓar da ba ta san yaushe ta koyeta ba tace "pant..."waro ido yayi ya na kallonta,dariya
yayi ya miƙo mata pant ɗin rigar wanda ya kasance string baki ta saki tana kallon shi ganin abu
kamar igiya tace "Ni dai bani son shi abani na ƙwarai na saka,yo wannan miye zai tare"a yadda
take magana yasa bugun zuciyar shi bugawa da ƙarfi dan zai iya cewa point faible/rauninsa ɗin
shi ce,a take wata kasala ta sabkar mashi cikin jarumta yace "Please ki saka haka nan dare
yayi muje mu kwanta"ya faɗi hakan ne yana mai rage hasken ɗakin tare da neman gefen bed
ya kwanta a sanyaye.


Kallon shi tayi kafin ta cillar da pant ɗin ta miƙe ta fara tafiya sai tsinkayo muryar shi tayi "zo ki
kwanta"a dake yayi maganar cikin bada umarni,dawowa tayi tana waige-waige inda zata ga
pant ɗin da ta jefar.

Ganin ya tashi zaune yasa ta turo baki tana mai hawan bed,hannuwan shi ya buɗe mata
alamun ta zo sai da tayi ɗan jim sannan ta faɗa jikin shi.Wata sanyayar ajiyar zuciya ya sauke
yayin da ita kuma ƙwallar tausayin kanta ta fara taruwa cikin idonta.

Ƙyam ya ƙara matseta a ƙirjin shi yana mai tunanin wace shawara zai ɗauka cikin uwanda
zuciyar shi ke bashi,shashekar kukanta ne ya fargar da shi.Haɓarta ya ɗago yana mai kai
halshen shi kan fuskarta ya na lashe hawayen,wani irin yammm-yammm ta fara ji a jikinta ɗif
hawayen ya tsaya sai ajiyar zuciya jin ta bar kukan ya sasauta dishashiyar murya shi yace
"miye?tsorona kike ji ko?"kai ta ɗaga mashi alamun eh ɗin,duk da halin da ya ke ciki bai hana
shi murmusawa ba kafin yayi baya ya kwanta sai ya zamana tana bisa fafaɗen ƙirjin shi,kamar
wata jaririya haka ya fara dadaɓata har sai da tayi barci.......
[20/10 à 20:17] MRS SADAUKI : *MUTUM DA RIGAR ALJAN*

*Gajeren labari...*
Story
and
Written by
*MRS SADAUKI*
{Cham rose}
Dedicated to *PRINCESS AYSHATOU*

☀️ *FIRST CLASS WRITTERS ASSOCIATIONS*☀️
___________________
BISMILLAHI RAHMANI RAHIM.


Page 36-37


Zaune suke suna hira yayin da Nuratu ke faman ba Nur yaourt,ba zato ba tsammani sai ganin
wata matashiyar yarinya suka yi ta shigo tana kuka.
Duka kowa hankalin shi ya maido yana kallon ta,kafin akai da tambaya wacece sai suka ki tace
"Nur haka zaka yi mani?na cancanci haka dama gun ka duk irin zallar ƙaunar da muke ma
juna?"

Kallon shi suke yi suna son jin ƙarin bayani,kallon ƙasa da sama yayi mata kafin yace "wacece
ke?ina kika san ni ?"

Baki sake tare da firgicin jin furucin shi tace "Nur Iki ce fah,Ikilimar ba ka gane ni ba?"tsuki Nur
ya ja yace "ke Malama kar kiyi min hauka fice ki ba mutane wuri,ni ina na san wata ikil"wani irin
ihu Ikilima ta ƙurma tana kiran sunan Allah.


Cike da kulawa maman tace "zo nan ƴata"ta faɗa tana yi ma Ikilima nuni da hannu,zuwa tayi
gaban maman ta tsugunna "gayamin miye alaƙar Ku da shi?"

"Saurayina ne kuma har da alƙawarin aure yayi min hakan ne yasa na biye mashi muka ta
aikata masha'ar mu har yayi min ciki"



Jin maganar babba ce yasa maman ta nuna mata wurin zama.Ƙarasowa Ikilima tayi kusan mar
tana goge ƴar ƙwallar da ta zubo mata,"gaya min abin da ke tsakanin ki da Nur sabida Allah kar
ki min ƙarya"cewar maman tana zaunar da Iki bisa capet tare da kamo hannayenta.


Labarin rayuwar Nur Iki ta shiga zayyanowa tiryan-tiryan babu abin da ta ɓoye,jikin su ne duk
yayi sanyi yayin da Nur ya sunne kai cike da kunyar iyayen shi.


"Ka wani sunne kai miye gaskiyar lamarin?"cewar dad sai da ya ɗago ya saci kallon Iki game da
harararta kamin ya mayar da kai yace "gaskiya ta faɗa"dukan su salalami suka shiga yi duk da
dama zuciyoyin su sunyi amana da maganar Ikilima.

"To shi cikin wata nawa ne?"maman ta tambaya cike da kunya ta amsa da "wata biyu"ajiyar
zuciya maman ta shiga saukewa dan takaici kafin ta umarci Nuratu tayi ma Ikilima masauki a
part ɗin ta.

Cikin jin haushin haka Nuratu ta ɗauko trollyn kiiiiii ta nufi ɗakinta,bin bayanta Ikilima tayi a zuci
kuma tana tsine ma Nuratu ganin cin fuskar da tayi mata.

"Keee! yarinya ki tsaya kiji Nur nawa ne ni ɗaya dan haka ki shiga taitayin ki,kin wani zo da
ƙaddararen ciki kin yaɓa mashi to koma dai mahaifa ce kina haife shi zaki tafiya ki bar mamu
gida"Nuratu ta faɗa lokacin da Ikilima ta shigo ,ɗan kasaƙe Iki tayi kafin ta sakar mata
murmushin mugunta tace "ƙaddararen ciki ya bani damar zuwa nan haka kuma shi zai sa a
aure ni dan doli,kuma ki tsaya kiji babu rabon kura a ciyawa duk ƙarfin zaki yayi kaɗan ya
tunkari Giwa ni nan nafi ki iya tashanci da duniyanci bari ganin nazo gidan ku zan iya sa ayi
waje da ke mtwsss"Iki ta ƙare maganar tare da bangazar Nuratu ta wuce ƙofar da take tunanin
toilet ce.


Galala Nuratu tayi da baki tana kallon ikon mai sama tare ganin ƙoƙarin Iki ta yadda ta datsa
mata maganganu ba tare da wani ɗarrr ba,bakin gado ta zauna tana jiran fitowar ta dan ta ɗauki
alwashin sai ta rama kafin ta fita.


Firgigit ta dawo daga duniyar saƙe-saƙen da take sakamakon jin saukar ruwa bisa fuskarta, Iki
ta gani gabanta ɗaure da towel iya cinya tana sakar mata murmushi.


Ruwan yatsunta ta ƙara yarfa mata a fuska tana mai cewa "ki sake shawara in tunanin ki zaki
iya karawa da Iki to kwanyar ki ta gaya maki ba daidai ba,dan ni walki ce daidai ƙugun kowa get
out Malama kin wani tsare ni da wasu shagun idanu naki"jiki babu ƙwari Nuratu ta miƙe ta fita
tana waiwayen Iki.

A gagauce Ikilima ta shafa mai ta shirya cikin riga da sket na kanti,kayan sun ɗame ta sosai
wanda ya ba ɗan tudun cikinta damar fitowa.Murmushi tayi ganin yadda kayan suka yi mata
mugun kyau,turare ta saka ta zauna bakin bed tana tunanin rayuwa bisanin ta miƙe ta fita zuwa
falo.

Da murmushi maman ta tarbeta tana cewa "ma fille yanzu nake cewa a kai maki abinci sai
gashi kuma kin fito,zauna a nan na haɗo maki abun taɓawa"murmushi kawai tayi ta zauna da
inda aka yi mata nuni,cikin ƙananan lokaci maman ta dire ƙaton farenti gabanta wanda duk
fruits ne yankaku sai jus.

"Na gode"ta faɗa can ƙasan maƙoshi,kanta maman ta shafa tana hararan Nur da ke ta kallon Iki
tun fitowar ta kawar kai yayi gefe zuciyar shi na ɗan dokawa da ƙarfi.


Ayaba ta ɗauko ta kai baki tana ɗan taunawa a hankali,duk jinta take a takure sakamakon ido
da ta ji na biyarta.
Gefen da yake ta waiga ƙurrr ta kama shi yana kallonta,gira ta ɗaga mashi ta ɗan motsa baki
tace "ya aka yi?"waro ido yayi a zuci kuma faɗi ya ke "samun wuri,ji yadda take wani yauƙi sai
kace ta saba shan ayabar"kamar ta san abin da yake cewa ta murguɗa mashi baki,alama yayi
mata da kin shigo hannu yarinya .
Ganin in ta biye mashi ba zata ci abun kirki ba yasa ta juya mashi baya ta ci-gaba da ci hankali
kwance har sai da ta ji cikinta ya cika ta sha jus tare da kwanciyarta bisa salon,dandanan barci
ya ɗauke ta.

Tun daga dogayen farcen ƙafafunta ya fara kallonta har izuwa ƙirjinta wanda yake cike dam
,sosai ya ji ra'ayin ta sai dai babu dama sata lahira.
Zaman shi ya gyara ya ƙura mata ido irin yana son ya ciyar da idanun shi abinci,bai taɓa sanin
Iki na da kyau na halitta ba sai yau cikin zuciyar "Allah ya kai damo da harawa"da ya faɗi yafi a
ƙirga.


Lumshe ido yayi yana jin duk wani sashen gangar jikin shi na neman taimakon gaggawa,duk
hidimar da suke na cin abinci bai dame shi ba duk da an ce ya zo yaci yi yayi tamkar wani mai
barci.


Nuratu kuwa da an jima-an jima sai ta saci kallon Iki tana haɗiyar yawu kamar wata mayya,tsan
dai ta miƙe ta nufi ɗaki kan bed ta kwanta rub da ciki tana hasaso surar Iki tun daga lokacin da
ta ganta da towel har izuwa yanzu da ta ganta cikin wanna kayan wanda suka sa ta ida zautar
da ita.

A hankali ta jawo ƴar ƙaramar wayata ƙirarar tecno,wani blue Film na mata ƴan lesbian ta buɗe
ta shiga kallo sai wani ƙura ido take ta yadda screen ɗin ke ƙarami amman tafi gane ma haka
tunda babbar wayarta kullum sai maman ta amsheta.

Cikin ɗan lokaci ƙalilan Nuratu ta fita da cikin natsuwar ta,hankalinta ya tashi ta rasa mi ke mata
daɗi.
Har zuciyarta take jin wani mugun son Ikilima ya shigeta tare da wata muguwar sha'awarta duk
da dai bata taɓa yin lesbian ba sai dai ta kalla amman yanzu karon farko tana son ta fara yi.

***


Tun bayan auren su suka shimfiɗa wata kyakyawar rayuwa mai cike da so da ƙauna,kullum
suna manne da juna tun Maryam tana kukan abun har ta kai ta saba ya zame mata jiki in ma
William bai nemeta ba ita takan ja ra'ayin shi.


Cikin ɗan jin haushi ta ƙara leƙowa ɗakin ta ga har yanzu bai gama shiryawa ba tace "Dear
yanzu sabida Allah har yanzu baka gama ba?sai wani yanga kake kamar mace"dariya yayi yace
"wa ya sani ko macen ce ni amman bari mu gwada mu gani"ya faɗa yana mai riƙe ƙugunta ya
ɗaga mata gira,buge mashi hannu tayi tana aika mashi hararar wasa tace "dan banda aikin yi
sai kace wata injin"dariya ya kuma yi yaja hannunta yace "raguwa ai ko injin ɗin ma yana
hutawa balle mutum,zo mu tafi kar ki sa nayi latti"
"To in ma mun yi laifin waye ba naka ba"cewar Maryam da tana mai kulle ɗakin kafin ta nufi
mota inda William ke jiranta tun tuni.


Key yayi ma motar suka ɗau hanya tunda suka fara tafiyar babu wanda yace ma ɗan uwan shi
kanzil,kowa da abin da yake saƙawa a ran shi ba kamar Maryam wacce duk ta shagwaɓe fuska
abun tausayi tana tunanin ko wane hali zata tarar da mahaifiyarta ta.


Ba suyi tsinke ko ina ba sai gidan kaso wanda ranar asabar an keɓeta ne dama dan ziyara
masu mugayen ayyuka kama da kisan kai,oder ƙwaya da dai sauran su.


Bisa kujeru suka zauna zaman jiran a fito masu da momy,can kamar minti goma sai ga ta biye
da wani ɗan sanda biyu da kuma soji guda.
Tun kafin ta ƙaraso Maryam ta fashe da kuka tana nunata da hannu tana cewa "yanzu nan
momy ce?Momyna fa"babu zato ba tsammani taji muryata mai cike da rauni tana cewa "Ni ce
my Mery,ni ce ɓaƙin halina ya ja min ba komi ba,dan Allah ki yafe min ban cancanci na zama
mahaifiya ba duk da son gani na haifi ɗan cikina ya rufe min ido na manta Allah shine ```Yuhuyi
wa Yumit``` shi ke da rayuwa da mutuwa na salwantar da jinin wata akan biyan buƙatata"momy
ke wannan maganar idonta na zubar da hawaye,ba tare da ƙyanƙyami ko ƙyama ba Maryam ta
faɗa jikin mahaifiyarta wace ke warin dauɗa da ɗoyin ciwuwurkan da aka ji mata wasu bugun
ƴan sanda ne wasu kuma wajen faɗa ne tsakanin su ƴan gidan yari.


Wata ƙwalla ce ta zubo ma William yana jin son mahaifiyar shi duk da bai taɓa ganinta ba tare
da kewar mother wacce ta kasance uwar shi ta biyu.Jami'an tsaron su kan su sai da suka ji

jijiyoyin jikin su sun tsinke tabbas Uwa UWA ce babu tamkar ta a duniya.


Kai momy ta shiga girgizawa da ƙoƙarin cire Maryam daga jikinta dan kar ta ɓata farar shaddar
jikinta amman sam Maryam sai ƙara ruƙunƙumeta take tana kuka mai cin rai........
[20/10 à 20:32] MRS SADAUKI : *MUTUM DA RIGAR ALJAN*

*Gajeren labari...*
Story
and
Written by
*MRS SADAUKI*
{Cham rose}
Dedicated to *PRINCESS AYSHATOU*



☀️ *FIRST CLASS WRITTERS ASSOCIATIONS*☀️
___________________
BISMILLAHI RAHMANI RAHIM.


Page 38-39


A hanyar su ta dawowa tsit kake jin motar babu mai magana,ganin har yanzu Maryam na cikin
zullumi yasa William nufar gidan dady da ita.
Tun daga ƙofar gida suka ga canji,gidan ya sha sabon penti da ƙofar mota sabuwa.Wuri ya
samu yayi parking ƙarƙashin inuwar icce,fitowa suka yi William na amsa gaisuwar da ƴan
majalisa masu zama suke mashi yayin da Maryam ta shiga gidan tana rangaɗa sallama.
Wata ƴar matashiyar mata ta fito wacce ba zata wuce 34yeas ba ta amsa mata tare da cewa
"ah!ah amare ne tafe lale da zuwa Maryama"turus Maryam ta yi ganin matar ba ƙaramin tada
mata hankali yayi ba domin irin shigar ta kawai ya tabbatar mata da matar uban ce ,a inda take
tsaye take sakarwa Maryam murmushi mai nuni da ta ji daɗin ganinta.

"Wuce mana kika wani tsaya a nan "cewar William wanda shigowar shi kenan,ganin bata da
niyyar motsawa yaj a hannunta suka ƙarasa.
"Marâtre ina kwana da fatan kun tashi lafiya?"WILLIAM ya gaisheta,ƙayatacen murmushi tayi
tace "lafiya lau Son ya gida ya aiki?"
"Alhamdullah"ya amsa mata a takaice yana kallon Maryam kafin yace "ki gaisheta"kamar wadda
aka yi ma doli tace "ina kwana!"hannunta Falila ta riƙo ta ja ta zuwa ɗaki tana mai amsa
gaisuwar kafin ta ƙara da "na daɗe ina jiran zuwan ki dauther sai yau Allah yayi nufi,da fatan dai

ki na lafiya ko?"kai kawai ta ɗaga alamar "eh"wajen WILLIAM ta waiga tace "my Son lafiya na
ga amarya taka silencieuse?"dariya yayi yace "barta marâtre ai zata wargatse zuwa an jima ƙila
dan bata san ki ba ne"ya faɗi haka yana mai tasowa ya zauna kusan Maryam ɗin yayin da
Fadila ta miƙe ta nufi kitchen da kawo masu abun taɓawa.
Tafukan hannunta ya riƙe ya soma magana cikin taushi "baby ki saki jikin ki wannan ita ce
marâtre (wato matar mahaifi da French)ya kamata ki ɗauketa tamkar uwa domin ita ɗin ƙanwar
ummata ce wadda ta kawo ni duniya,na ɓoye maki ne dan gudun kar ki shiga damuwa amman
an daɗe da ɗaura auren su tun lokacin da gaskiya ta bayyana shine dady ya nemi alfarmar
aurenta dan sake ƙulla wani zumuncin"shiru yayi ganin Maryam ta yi mashi ƙuri gabanin
hawaye su fara silalowa kan fuskarta,jikin shi ya jata yana goge mata hawayen tare da rarashi.


Aje tray ɗin marâtre tayi bisa table tace "kiyi haƙuri Maryam na san zaki ji abun wani iri amman
tabbas na daɗe ina son mahaifin ki tun can dama shi ma haka,sai dai lokacin da muka so ƙulla
soyayya sai ɓacewar anty Suweiba (mamar WILLIAM)ya dagular da komi dan sosai ahalin mu
suka manta da naku ahalin inda a ɓangare guda nake ji na rasa wani jigo na rayuwata wanda
ya haifar min korar duk wani saurayi mai niyya aurena har kawo wannan lokacin da gaskiya ta
bayyana"ɗan tsagaitawa marâtre tayi tare da yin murmushin da yafi kuka ciwo tace "Maryam
zaki iya ɗaukata duk yadda kike so amman ki sani ni na yafe ma mahaifiyar ki tun tuni haka ma
iyayena yanzu haka rarashin Hajiya Turai (kakar su Maryam)muke tayi ni da dadyn ki dan a
samu a fitar da momyn ki sann...."rungumar da Maryam tayi mata ne ya hanata
ƙarasawa,rarashinta take tana bubuga bayanta Ita kuwa Maryam sai ƙara volume take tana
cewa "ina sonki marâtre ko ba komi ke ƴar uwar umma ce naji ina ƙaunar ki har ƙasan raina".


Ƴar ƙwalla dady ya goge wanda duk abin da ake ya na ji daga can ɗakin da yake,kukan su da
yaji ya tsananta ne ya fito sai kuma ya ci karo da abun farin ciki jin ƴar shi wacce yafi so duk
duniya ta aminta da matar shi.


Ƙarasawa yayi yace "to koke-koken ya ya isa haka ku zo mu ci abinci,uwar yara mi kika dafa
mana ne?"cewar dady.
Murmushi ɗauke da fuskar su suke kallon shi kafin marâtre tayi ƙarfin halin cewa "ai ban dafa
da kai ba ƴaƴana kawai na girka ma"dariya duka su kayi har Maryam mai kuka.

"Au!abun son kai ne?to babu matsala bari naje restaurant na ci"dady ya faɗa cikin gyatse,haƙuri
ta bayar kafin ta gabatar masu da abun karyawa.Cike

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login