Showing 66001 words to 69000 words out of 73876 words
yana kan kofar shigowa "_
_" Ta matsu Bata sa uban ya'yan ta a idoba" wata irin San yanyar a jiyar zuciya ta sauke
lokacinda ya yi sallama da muryar shi mai tafiya da hankalin y'an mata "_
_" Tunda ya sawo kanshi cikin falon ya zuba mata idanu yana aika mata da sakonni masu
wuyar fassara ta kalle shi cikin tsananin shaukin ganin shi sannan ta dukar da kanta ta cigaba
dabawa yaranta nono"_
_"Karasowa yayi ya zauna a kujerar dake Gefen ta " yafara gaishe su cikin tsananin girma
mawa "_
_" Gwaggo Rabi tace " aa mai gida dama kana hanya? Yace eh Wallahi mun gama da jaji yanzu
sai komawa legos kuma"_
_"Toh ubangiji Allah ya kiyaye ku d'an nan yasa kugama lafiya, yace 'Ameen Gwaggo,_
_"Ya maida Hankalin shi wurin yaranshi dake hannun ta " tareda sauke idanun shi a kan jajayen
na shanunta da suka ciko bulbul da ruwa "_
_" Tuni idanunshi yafara canja kala " cikin rage muryar shi yace " Madam Am Hungry " Ya mike
tsaye " kikawo min yaran kafin Abinci "_
_" Tace mai toh ta mike tareda bin bayanshi daukeda Abulkhairi tana shiga ya karbeshi " ki
kawomin Momy na da kuma ummul khairi"_
_"Ta juya zuwa falon ta kwaso su duka ta zube mai su akan gadon shi " idanu ya zuba musu
yana kara godewa Allah " domin bai gajiya da kallon su "_
_" Tafara jeramai kayan Abin cin shi a kasan Capet din dake tsakiyar dakin domin tasan Al adar
shi bayason cin Abinci a sama"_
_"Saida ta gama ta dawo kusa dashi " Baban yara ga Abincin kazo kaci"_
_"OK maman yara " yafada cikin zolaya ya mike tareda tube rigar jikin shi har ma da wandon
yarage dagashi sai short nicker da singlet "_
_" Kallon kirar jikinshi kawai takeyi kamar kullum kara murdewa yakeyi " ta juya domin zubamai
Abincin batayi Auneba taji ya fisgota zuwa kirjinshi "_
_" Haba madam wannan irin Jan Aji haka " ai sai in rude ko dan sannu da zuwa ban samu ba fa'
" tafara mutsu mutsu domin kwacewa yariketa ta mau a jikinshi "_
_" Saifa kinyi min magana zan kyaleki " Ta bude baki cikeda yanga irin na matar so " Sannu da
Zuwa' " nop ba irin wannan nakesoba"_
_"Kafin tayi yunkurin cewa komai ya hade bakinsu wuri daya" yafara aika mata da lafiyayyan
kiss kamar zai tsinke mata halshe"_
_"Tafara tayashi domin rage mai zafin duk da tana dar dar dashi "_
_" Kukan Abulkhairi yadawo dashi a gigice ya nufi yaron jikinshi narawa " oh baba na Meya faru
kake kuka bakaso Dady ya More ne?_
_"Saida ya dan lallashe shi sannan yace " kizo kibashi yasha" " ta dan Bata fuska' yanzufa ya
gama shan nono Allah ya faya tsotso shi kam su ba ruwan su"_
_"Yace " sory please akara mai kadan ' ta matso gefen gadon ta zauna tareda zage zip din rigar
ta taciro nonon yamika matashi tafara bashi nonon"_
_"Gaba daya ya zubawa nonon idanu yana kallon su kamar ya karbe abakin yaron ya maye
gurbin shi"_
_"kasa daurewa yayi ya matso jikinta ya sanyata a tsakiyar shi ya dora hannun shi akan dayan
yafara shafawa yana lumshe idanun shi "_
_" Ruhi" stop mana ga yaronka gaka kuma? Ya manna bakinshi daidai kunnen ta " ai namafi
yarona rigima a halin yanzu " don haka kisan y'anda zakiyi dani nima ina layi"_
_"Dariya yabata tace " haba dai ai nafada maka sainan da wata biyu"_
_"Kinaso inje Asibiti kenan " kinsan y'an da nakeji kuwa? Gaba daya naji banajin yunwar ma ke
kawai nake bukata yanzu' "_
_" Ta kalle shi cikeda tsoro " Ruhi" wasa kakeyi ko? Allah Husnah ki San nayi dani kawai yanzu"
ganin da gaske yakeyi tace bari taje takai ma su Gwaggo yaran"_
_"Yace kibar min yarana anan ban gaji da ganin su ba " tashi kawai yayi ya shiga dakin yaran
cikin kayan da suka samu ya kwaso wasu gadajen su ya jera a cikin dakin shi "_
_" Kallon shi takeyi har ya gama shirya gadon ya sanya su ciki " Dawowa yayi kan gadon ya
janyota jikinshi tafara tureshi " haba Ruhi" meye haka?_
_"Wait and see" romancing dinta yafara yi tareda zame rigar jikinta jikinshi narawa yafara
sarrafata tun tana nokewa har tafara tayashi "_
_" Hau kace mata yayi gaba daya " oh my Angel yanzu Bakida tsarki? Don Allah yana daukewa
ki fadamin kafin in mutu da bukatar ki please "_
_" Gabadaya yafita hayya cinshi ita kanta ta tausaya mishi sosai a dole tafara yimai dabarun da
zata dan kwantar mai da hankali "_
_"Yaji dadin hakan sosai sai godiya yake mata " dama kin iya irin haka bakya yimin ? Tayi dariya
" yace daga yau dole arika yimin idan zamuyi......._
_"Tayi saurin mirginawa gefen shi ta janyo rigar ta zata saka " yace ina zakije? " zanje dakina
inyi wanka" nan ba bathroom ne ? Ko so kike su Gwaggo su gane na matse ki"_
_"Saida tamike sannan tace" to sai me mutum da mijin shi " ya waro idanu "cikeda jin dadi "
Allah matana? Oya zo inkara yi tunda kin sallama "_
_" Ai da gudu ta fita yafara dariya " tayi sa'a sun shiga daga ciki domin anfara kiran Salla
"wanka tayi ta gyara jikinta sannan tayi shiga mai sauki cikin wata irin doguwar Riga mai guntun
hannu tareda dan karamin mayafin ta"_
_"ta leka su Gwaggo ta gaishe su " sukace " ina yaran? Suna wurin baban su suna bacci bari
inkawo muku su"_
_"Aa kyale su yagana da Abinshi shida zai tafi yabar su "_
_ta samu ta sulale ta koma wurin mijinta" Tasame shi akan dadduma yana lazimi" saida ya idar
ta gai sheshi"_
_"Yace inajin yunwa madam kinki bani Abinci " ta jefeshi da wani irin kallo " da shi kadai yasan
ma'anar shi "_
_" Ta riko hannunshi yamike ta taimaka mai ya cire jallabiyar jikinshi ta nade Salla yar Sannan
tajashi har zuwa wajen data jeramai kayan Abincin "_
_" Ta bude kulolin tafara zubamai white rice data dafata da kayan lanbu tayi wani irin kyau
saboda su green Bean's din data zuba akai" ta bude Kumar stew dinda taji namomin kaji ta
zubamai akai"_
_"Ai tuni miyan shi ya tsinke" wannan girkin matana ne wow? This is delicious ""_
_" yadauki spoon domin yanzu ne yunwa ta dawo sabuwa yafara aika girki yana Bata labarin
aikinshi dakuma zancen komawar shi legos "_
_"gaba daya jikinta yayi sanyi" domin jitake kamar su dawwama a haka kullum suna tare gashi
yanzu yara har uku Bata ba zancen bin miji ta ina zata fara"?_
_"Saida yadafa ta " me kike tunani haka?"batareda tunanin komai ba ta ce" banaso kana tafiya
ko ina " takarasa tareda zurarowar hawaye "_
_" Ya Ajiye spoon dinda ke hannunshi yajanyota zuwa jikinshi" haba matar soja yakamata ace
yanzu' kin zama jaruma kin saba da yanayin aikin mijinki "_
_"Ta share hawayenta tareda cewa" zaka rika zuwa koda yaushe? Tafada cikin sigar shagwaba
"_
_" Wani irin murmushi yayi mai dan sauti" Husnah " kina tunanin Kinfi ni son mu kasan ce a
tare? Ko y'an zu nasan idan ma nace zamu tafi tare gida baza a bariba da kafata kafar iyalina "_
_" Ya kalli yaranshi dake ta faman bacci a cikin gadon su " inason kasan cewa daku Husnah
akoda yaushe nima bada son raina nake tafiyar ba_
[4/20, 9:29 AM] Feenat Marubuciya: í ¼í¼¼
*AURAN SOJA*í ½í±¨â€�✈
_patients love & sacrifice_
*~Story written by~*
*Fenerh*
https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATIONí ½í²«í ½í²«í ½í²«~*
*~�We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our
creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u
np pain~*
62&63
_"Ya dauki lokaci yana lallashin ta tare da kwantar mata da hankali'_
_"Saida ya tafi sallar isha ta samu ta sulale ta koma dakinta bayan ta kwashe yaranta "_
_" Ya dawo yaga wayam shida yasa ran zai kwana ajikinta " har ya kwanta yaji Sam bazai iya
kwanciya shi kadai ba bayan yasan yana kusa da matar shi"_
_"Dakinta ya nufa shanye da jallabiyar shi yayi sa a dakin na bude ya tura a hankali " ya shiga
tsaya yawa kawai yayi yana kallon su "_
_" Gashi tana bacci ga yaran nata cilla kafa sama Alamar sun tashi Abulkhairi ne ke baccin
shi"_
_"Karasowa yayi dauke da kyakkyawan murmushi a fuskar shi" ya samu gefen su ya daukesu
duka biyun a cinyar shi yafara yimusu wasa saida dayar tafara tura hannu a baki alamar yunwa
takeji ya kalli Husnah daketa baccinta hankali kwance "_
_" Ya janye Abulkhairi a kusa da ita ya kwantar da ita da kanshi ya Ciro mata nonon ya saka
mata abaki Saida ta koshi ya saka ma dayar Sannan ta fara motsawa"_
_"Kamar a mafarki takejin ana tsotsar ta tareda kuma shafata da Sauri ya janye y'ar shi tareda
riketa ganin tana juyi zata danne mai yarinya "_
_" Ta bude idanunta ta zuba a kan fuskar shi ya sakar mata murmushi " sory muntashe ki ko "
yunwa mukeji shiyasa"_
_"Amma meyasa kike kwanciya tareda su? " yanzu da kin danne min yarinya da bana kusa'
tunda suna da gadon su ki rika kwantar dasu idan sun farka ki basu nono"_
_"Tace" OK sir Amma mekazo yi a nan ? Bai Bata Amsa ba saida ya kwashe yaran ya mayar a
kan gadon su Sannan ya dawo kusa da ita ya zame jallabiyar shi yarage dagashi sai short
nicker kawai ya raba gefen ta ya kwanta"_
_"Tareda rungumota zuwa kirjinshi " ta zaro ido " Abban yara me zakayi? Umman yara bacci
zamuyi kawai ba abinda zanyi miki "_
_" Ya zan kwana nikadai kamar wani gouro " ya cumuimuyeta a kirjinshi tun tana tsoro harta
saki jikinta ta koma baccin ta"_
_"A ranar shi yayita jigilar yaran idan sun farka batareda ya damu Maman su ba haka ya kwana
sintirin kula da y'an uku n shi har zuwa Asuba lokacin da suka koma baccin su shi kuma ya
mike ya dauro Alwala yafara tayarda Salla "_
_" Yana kan sallaya har saida gari yafara haske Sannan ya koma dakinshi "_
_" A haka Kamal yayi kusan sati daya a Zaria kullum yana kula da iyalin shi kamar kar yatafi "
Amma ya zatayi AUREN SOJA N kenan"_
_"yafara shirin komawa legos gaba daya hankalin ta ya tashi " ita gaskiya Bata tunanin zata iya
sabawa "_
_" Yana kula da y'anda take ta faman daure fuska tana shirya mai kayan shi " matsawa yayi gaf
da ita batareda ya cemata komai ba ya rungumota "_
_" A kunne yake rada mata " Madam karki damu na samo miki Abinda zai rika debe miki kewa
ta" da kinyi Arba' in zaki fara zuwa A.b.u "_
_" Wani uban tsalle ta buga tareda rungumo shi sosai tafara manna mai kiss ta ko ina tana
godiya domin babban burinta zai cika na ganin ta zurfafa iliminta"_
_"Nagode Ruhina Allah ya barmin kai yakareka daga dukkan nin sharri ka gama min komai
yayana kuma mijina uban yarana"_
_"Aa duk ni kadai madam wannan irin matsayi? Kamafi haka a wurina my Ruhi "_
_" Sun rabu cikin farin ciki batareda yabarta cikin fushi ba " saida ya biya gida duk da kusan
kullum sai yaje unguwar su kuma sun San da tafiyar shi "_
_" Saida yaje ya musu Alkhairi kamar ko wane lokaci idan zai tafi Sannan ya wuce "_
_" A sannu komai ketafiya Husnah tayi Ar'ba in ga yaranta sunyi wayon su sun ciko bul bul
kamar ba y'an uku ba saboda suna samun Abinci mai kyau da kuma lafiyayyan ruwan nono"_
_"Cikin ikon Allah Kamal ya cika mata Alkawari n ta tafara zuwa makarantar ta cikin kwanciyar
hankali yaran kullum a gida take barin su wurin masu kula da su "_
_" Gwaggo Rabi ta koma gidanta sunayin Arba in yarage sai tsofaffin nan guda biyu wurin su
take barinsu har ta dawo daga school "_
_"Kamal kuwa tunda yaji tayi Ar'bain yake so yazo Zaria Amma aiki ya rikeshi kusan kullum sai
ya mata zancen shifa yafara gajiya Allah zai gudo ko kwana daya ne yayi ya koma"_
_" Ta kan kwantar mai da hankali " Tace yayi hakuri har yasamu isasshen lokaci domin ita
bataso yazo yayi kwana daya yatafi"_
_" kusan kullum zancen kenan kuma shi gaskiya yana Azabtuwa gashi yanzu girkima dole
yakeyi da kanshi domin Maman sudais suma sunyi posting zuwa makurdi"_
_"Yauma yadawo aikinshi yana kokarin neman Abinda zaici yaji an bude kofar an shigo " yasan
bamai shigomai gida sai yaranshi kuma sai yakira su ,ya fito domin ganin waye"_
_"Tsaya wa kawai yayi ya matse fuska " ganin wadda ke tsaye cikin matsattstsun kaya tana
wani kara'i raya da jikinta"_
_"Lateefa what are you doing in my house? A hankali take takowa cikeda yanga tana karkada
jiki" oh my Kamal I have came to visit you bcos I missed you so much "_
_" tafara kokarin rungume shi yayi saurin tureta gefe" " stop it OK and get the hell out of my
house "_
_" Impact who let you in? I thought I have warned you to stay away from my life_
_"Know am married with three children and I love my wife so much " so am warning you to stay
away from me and my family "_
_" Cikeda kissa da kisisina tafara cewa" Kamal what A about me? " saboda kai nakasa yin Aure
naki kula kowane namiji nafada maka zan iya zama dakai a haka"_
_"Ni ko baka Aureni ba inaso mu kasance tare tafara matsawa kusa dashi tana mai zubawa
faffadan kirjinshi idanu tareda muscles dinshi"_
_"Kafin yayi wani yunkuri harta fada kirjinshi saida yakusa zubewa saboda wani irin shocked da
yaji " Yama kasa tureta saboda a hannu yake dama "_
_" tafara shafarshi tareda kokarin hada bakinta da nashi " sai A lokacin ku zari nshi yadawo ya
hankadeta gefe tareda zabga mata lafiyayyan mari"_
_"Have you lust your mind? Kin taba ganin na hada jikina da kazamin jikinki da kowane namiji
ke runguma? Am warning you for the last time lateefa stayed away from me idan ba hakaba
zakiyi regretting sanina a rayuwar ki"_
_"Ya bude kofar ya hankadata waje Sannan yakira sojan dake kula da gidan yamai warning'_
_"Samuel what is your work hare' ? I don't want to see are in my house "_do you understand?
Ya yi saurin sarawa " yes sir"_
_"Yana shigewa tayi saurin karbar wayarta a hannun Samuel " ta bude pictures din tayi wata irin
shewa " tank you Samuel you are good to go"_
_"Tajuya zata tafi yayi saurin shan gabanta "ware is my promise? " oh don't worry am free for
you today ta kashe mai ido daya Sannan ta juya tana kada duwai wuka"_
_"Shi kuwa sai kallo yake yana lashe baki ' ta tafi da burin saita nunamai illar kiranta da yayi da
Ashawo"_
_"Kamal kuwa yana shigowa ya dafe kanshi Gabadaya ji yake yau idan baije ga Husnah ba
Akwai matsala "_
_" Duba lokaci yayi yaga karfe hudu da kusan rabi a gurguje yake shirya kayan shi tareda kiran
odilin shi yamai bucking plight zuwa Kaduna "_
_" Yau Husnah ta samu kanta da gyara jikinta har zuwa tayi saloon tayi gyaran gashi tareda
tsantsara lalle tafito kamar wata sabuwar Amarya "_
_"su Inna dake gidan sai tsiya suke mata " tace " gida takeson zuwa ta kwana tanason ganin
su Inna r ta rabonta dasu ta kwana biyu "_
_" Ta shirya yaranta tashinfide biyu a bayan motar ta Sannan ta sanya daya a gaba ta dauki
kayan su da suke bukata ta saka a boot saida ta sanya musu belts Sannan tafada mota ta tayar
"_
_" Tafiya takeyi cikeda natsuwa saboda yaranta har Allah yakaita lafiya lokacin karfe biyar na
yamma tasamu su bilal a kofar gidan yana hango motar ta yataso"_
_"Aunty sannu da zuwa " kece da yamman nan? tace " eh bilal kashiga da ummulkhair kadawo
ka daukar min kaya na zuwa cikin gidan"_
_"Ita tasaba guda biyun ta nufi cikin gidan sukayi karoda shi zai fito" ka kulle min motar key na
jikinta idan ka Ciro kayan"_
_"Cikeda zumudi ta nufi dakin Inna Habi tana kwala mata kira " gani nan y'ar gidan Inna r ta "
Sannu kinji da fama da wa innan buhun fulawar "_
_" Tasa hannu takarbi daya " muje wurin Gwaggo ta ga yayanta Inna Amarya na zaune tace " ai
inajin ihun