Showing 1 words to 3000 words out of 38755 words
Chapter 1 - Mummunan Zato Book 3 Complete Halina Mashi
MUMMUNAN ZATO BOOK 3
*í ½í³”í ½í³”í ½í³” Page 1*
Da gudu ya fito yana kiran "Jabir! Jabir!!" Dai dai lokacin da Jabir ke fitowa daga garejin motoci, inda ya
ajiye motar da suka shigo yanzun nan,ya ji muryar Ogan nashi cikin wani firgici, da gudu ya nufo ƙofar
falon inda suka yi kiciɓis da maigidan nashi ɗauke da A'isha ga jini na zuba. A guje ya koma ya fito da
mota ya shiga suka fizgi motar a guje, duk da haka Uncle gani yake tamkar Jabir ba gudu ya ke ba, ya ce
"Jabiru mu yi sauri fa,ƙila ma ta cika."
Suna isa da gudu ya É—auke ta bai damu da jinin da yake zuba jikinshi ba, ya shiga asibitin yana kiran
"Doctor! Doctor!?" Nurses É—in da suka ganshi tuni suka nufi gurin da ake aje gadon da ake tura marasa
lafiya, kafin su iso ai shi tuni ya kai Office ɗin Doctor. Bakin ƙofa suka ci karo da Likitan, shima ya firgita da
ganin jinin. Nurse's suka iso tuni ya zube ta kan gadon, suka tura da gudu sai Emergency,shima ya bi su
amma kafin ya shiga tuni an turo ƙofa, sauran Nurse's ɗin suka ce "Yallaɓai kayi haƙuri ka jira Doctor za
ya yi aikinshi, lokacinne ya kalli jikinshi tun daga rigarshi har wandonshi jini ne. Nan take zuciyarshi ya
yanke cewa cikinshi ya zube, ya dunƙule hannunshi ya kai ma bango duka ya kifa kai jikin bangon yana
mai jin wani irin raÉ—aÉ—i a zuciyarshi.
"Oh Allah! Dama ba zan ga ɗan kaina ba?" Wata zuciyar ta ce "kada ka yi saɓo." Nan take ya ce,
"Allahumma ajirni fi musibati." Sai ya saka dangana cikin zuciyarshi,ya yarda Allah da ya bashi wannan shi
ne zai bashi wani,ya saka hannu cikin aljihun wandonshi ya ciro wayarshi,layin Alhajinmu ya kira, lokacin
da yaji muryarshi yana cewa, "Abubakar ya ya?" Zuciyarshi ta karye ko yaushe in yana gaban mahaifanshi
ko yana waya da su ya kan ji shi tamkar yaro ƙarami. Cikin rawar murya tamkar Zai fashe da kuka, ya ce
"Alhaji A'isha tayi ɓari muna nan asibiti." Tamkar ya soka mishi ƙaho a cikin zuciyarshi, ya ce,me ka ce
Abubakar? Kana nufin meɗakin ka ce ta yi ɓari?" Ya amsa da cewa "Eh muna asibiti." Jabiru yana ta
kallon maigidan nashi cikin tausayawa. Bayan ya gama wayar da Alhajinmu ya kira Nafisa ya sanar da ita,
Jabiru ya ce maigida ko zamu je ka canza kayan nan? Cikin ko in kula ya ce kada ka damu Jabir, bari mu ga
yanda jikin A'ishan yake."
Sai ga Hajiya Jummai da Hadiza sun shigo da sauri, Jummai ta soma kuka tana kallon kayan jikinshi.
"Alhaji me zan gani haka? Alhaji ba dai ɓari tayi ba?" Hadiza ma cikin matsananciyar damuwa ta ce "Mun
shiga uku ni Dija, yanzun ina A'ishan ta ke?" Yanda suka nuna damuwarsu sai shi ne ya koma yana
lallashinsu. A haka Alhajinmu ya same su can sai ga Nafisa, duk da kukan da Jummai ke yi da tagumin da
Hadiza ta yi bai sa zuciyar Nafisa yarda da su ba, shiru-shiru Likita sai dai Nurse ta fito da gudu ta É—auko
wancan ta zo da gudu ta koma ciki, don haka sai ya soma fitar da rai da rayuwar A'isha. Nafisa ta zo ta
dafashi, "Kayi haƙuri Bros, Allah yana tare damu, insha Allahu Allah zai isar mana komai." Ya saka hannun
shi a kafaÉ—arta, amma bai iya cewa komai ba, sai dai girgiza kai kaÉ—an yake yi,jim kaÉ—an Likitan ya fito,
Nurse's na biye dashi sun turo ta a kan gado Uncle ya nufo shi yana cewa, "Ya ya Doctor?" Likitan ya ce
"jira ni" cikin Office ya shiga,ɗakin da za'a ƙwantar da ita, Nurse's suka turo ta ciki,sai da suka sa ta a gado
tare da ruwa sannan Likitan ya ce, "Nurse ɗin su gyara ta da ƙyau, sannan kada su bari kowa ya shigo in
da take. Ya fito ya nufi office É—in shi inda ya samu su Uncle cirko-cirko a tsaye, ya shiga ya zauna yana
cewa "Ranka ya daÉ—e bismilla,ku zauna." Ya É—auki wani handkachief ya share zufar da ta zubo mishi a
fuska, ya ajiye ya dube su. "Ranka ya daɗe yanzun dai muna buƙatar jini ne
" Alhajinmu ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce, "To sai a gwada mu,in bai yi ba sai a nemo." Likitan ya ce
"Ranka ya daɗe ai kai ko ya yi ba zamu ɗibi naka ba saboda girma, sai dai na "Yallaɓai." Uncle wanda
tunani da damuwa ta hana shi magana,ya sauke wata nannauyar ajiyar zuciya, ya ce dama kai ba za'a
taɓa jininka ba, sai dai nawa" ya ci gaba" Likita cikin ya fita ko?" Cikin ƙarfin hali Likitan ya ce, "Ba zan
tantance ba yanzun,da so ma muke musha kan jinin da ke zuba." Uncle ya miƙe "muje gurin ɗiban jinin."
Likita ma ya miƙe yana cewa, "Sai mun je an gwada." Ya ce jinina zan iya ba kowa, Likita ya ce "to
shikenan,sai mu É—iba mu gwada lafiyar shi, sannan mu tace."
Cikin ƙanƙanin lokaci suka ɗaurawa A'isha jini, duk mai imani in ya ga A'isha sai ya tausaya mata, don
haka suka hana kowa zuwa gurinta.
Ƙwance take tamkar gawa, sannan jini ana sa wani, wani na fita. Alhajinmu da ya je ma da Hajiyarmu da
labarin halin da ake ciki, bayan sallar isha'i ta ce da Alhajinmu su je ta duba ta.
Ta tsura mata idanu tana kallonta lokacin da Likitan suka shigo da Uncle, Alhajinmu ya dubi Likitan ya ce
"Doctor wane ci gaba aka samu zuwa yanzu?" Likitan cikin karaya ya ce, "Sai dai godiyar Allah, amma
lamarin ya ruɗani, don muna toshe nanne can na ɓallewa." Hajiyarmu ta matsa kusa da ita, ta kama
hannunta ta dubi Likitan ta ce "Kai É—annan gaya min gaskiya,ko dai yarinyar nan bata ne?" Likita ya ce
tana da rai Hajiya bata rasu ba." Ta ce Innalillahi wa'inna ilaihir'raji'un, wannan kuma wanne irin ciwo ne
haka?" Alhajinmu ya ce "Likita yanzun menene shawarar ka?" Likita ya ce "Addu'a kawai ce mafita,don ni
ban taɓa karo da irin wannan matsalar ba."
Uncle ya jingina da bango don ya kula zaya iya faÉ—uwa. Duk da (AC) É—in dake É—akin bai hana shi zufa ta yi
mishi wanka ba, Alhajinmu ya ce, "wannan sai dai mu ƙara,don kullum cikinta muke." Ya dubi Hajiyarmu
"Ina ganin ko zan samu su Malam Yakubu ne?" Ta ce, "Za'a iya samun su É—in, tunda suma waÉ—annan
mutanan babu abinda ba sa saka É—an Adam a ciki." Su Alhaji Bello sune suka yi ta ba Uncle magana,
lokacin da yake cewa, shi dama tuni yasan A'isha ba zata tashi ba, saboda shi duk matar da ya aura
mutuwa take. Yanzun me zai ce da Mustapha? Alhaji Bello da Alhaji Salisu suka ce, "ka daina wannan
maganar, kada ka manta cewa, kai Musulmi ne."
Nafisa da Uncle suka ƙwanta gurinta,don anyi-anyi ya je gida ya ƙi, Hajiya Jummai ma da ƙyar su
Hajiyarmu suka iya lallashinta, irin kukan da take yi ta so ta ƙwana aka lallaɓata suka tafi (kun ji makirci).
Tun shida na safe Alhajinmu suka iso da su Malam Yakubu, lokacin sun samu Nurse's suna gyarata, suna
cire kayan shinfiÉ—ar da na jikinta don haka dole suka jira, Nafisa ta fito ta sanar da su an gama, suka shiga
addu'a suka soma yi suna tofa mata, cikin ikon Allah sai ta soma motsi,tana motsa ƙafa, ganin haka sai
suka soma karatu,nan ta soma mutsu-mutsu, suka umarci Uncle ya riƙe ta kada ta faɗo. Suna ta karatu
can ta soma gunji,suka yi, suka yi ko wanene ya yi magana, amma shiru. Sai dai can suka ga ta miƙe tana
hamma, suka yi addu'o'i suka tofa mata, sannan suka ce ya fita ya dai ƙi yin magana ne. Sannan suka tafi
da ƙudurin cewa zasu aiko mata magani, suka kuma sake bada shawara game da yawan karatu, sannan ta
daina ƙwanciyar la'asar,in zata ƙwanta. To ta ƙwanta kamar da azahar zuwa la'asar, zatayi baccinta
hankali ƙwance ga kuma lada.
Bayan tafiyarsu, Likitan ya iso,nan ya duba ta,ya cika da mamakin ganin ta tana numfashi, kuma
numfashin ma irin na masu lafiya, Nan suka sanar da shi komai, ya ce "To mun gode ma Allah da yasa aka
gano bakin zaren, yanzun in ta É—an huta sai mu duba lafiyarta." Uncle ya yi hanzarin cewa, "Likita kana
ganin za'a samu cikin nan?" Doctor ya dubeta cikin karaya, sannan ya kalleshi "Yallaɓai ba zan iya
tabbatar wa ba, saboda ta zubar da jini har da guda-guda,ban sani ba ko har da É—an tunda yanzun bai
wuce É—an guda É—in ba."
Uncle ya yi ajiyar zuciya,dama shi tuni ya cire rai sai dai yana roƙo Allah ya bashi wani mai amfani.
Su Hajiya Jummai kowacce tana cike da murna, saboda murna kowace tana maƙale da waya tana sanar
da duk wanda ta san zai taya ta murna. Jummai dai suna waya da Aminiyarta ta ce, "Ai ciki tuni ya jima da
bin ƙwararon asibiti,kin ga yanda jini ke malala kuwa?" Kari ta ce, "Dama ba na gaya miki ba? Wani sa'in
in kana son biyan buƙata sai ka bi ta irin waɗannan hanyoyin." Hajiya Jummai ta ce "Don wannan me
sauƙi ne,ni da na kashe rayuka ma wannan har ya dame ni? Kedai Allah ya shige mana gaba." Karima ta
ce, "Sai na zo jaje,ƴar iska ki ka ƙuƙe kina kuka,kai! Su Jummai makiran duniya." Jummai ta sheƙe da
dariya ta ce, "Kin san Allah,kukan da nake yi a zuciyata ina yin sa ne saboda shegiyar ta ƙi mutuwa, amma
ba don tausayi ba." Karima ta ce,"aini na sani,ke ce fa!" Ita ko Hadiza ko da ta sanar da Hajiya Lanti, sai ta
ce "Dama ai boka ya gayamin hakan ce zata kasance, yanzu sai ki dage kafin ta dawo ta kuma É—auka,
kema ki dage ki ɗauka. Sannan yanzu wani farraƙu za'a haɗa min, ya ce aikin dai da tsada, amma ko
sarƙarki ne za'a saida in yazo hannu sai ya maida miki." Ta ce, "To Hajiya zan yi duk yanda ki ka ce." Ta ce
gobe zan zo jaje,in nazo sai mu yi magana in taho da sarƙar ko? Ta ce, "To."
Ƙarfe ɗaya saura, A'isha ta farka, miƙa ta yi gami da salati, sai ta ji hannunta da igiya. Cikin sauri ta kalli
hannun nata,jini! Ta furta da ƙarfi Nafisa da ke zaune can gefe ta taso da sauri ta riƙe ta tana faɗin,
"Sannu A'isha." Cikin tsananin tsoro ta ce, "Anty Nafisa me ya sameni?" Nafisa ta ce ba komai ki ƙwanta."
Ta ce "Ina uncly?" Nafisa ta ce "Ya tafi masallaci." Ta koma ta ƙwanta shiru, sai ta soma tuno abinda ya
faru da ita, ta tuna hayaƙinnan mara daɗi da ta shaƙa, ta tuna cewa ta ji wani abu yana bin ƙafafunta a
lokacin ne ta kai hannunta sai ta ji an sa mata (always) a firgice ta tashi zaune tana cewa, "Anty Nafisa na
yi ɓari ko?" Nafisa ta dafa kafaɗunta ,"kada ki damu A'isha, Allah da ya baki wannan shi ne zai ba ki wani
." A hankali ta koma ta ƙwanta, sannan ta runtse ido da ƙarfi gami da girgiza kai,a fili ta furta "Allahumma
a jirni fi musibati,wakalifini kairan minha." Ta tausaya ma Uncle. Ta lumshe idanu, tana tariyo yanda aka
yi cikin ya samu lokacin da zai fitar zuwa jikinta har tsoro ya bata, ta zata numfashinshi ne zaya fita,
ma'ana ranshi ni zaya fita. Ita kanta ta ci baƙar wahala kafin ya samu hanya ma tukunna, hawaye ne suke
sauka akan gefen fuskarta,sai ta ji saukar lallausan hannu a fuskarta,ko bata buÉ—e idanu ba ta sani Uncle
ne. Ya saka Æ´an yatsunshi yana share mata hawaye,ta buÉ—e idanu a hankali ya yi É—an murmushi. "Beby
kin tashi?" Wasu sababbin hawayenne suka sake zubo mata, ya ce "ki daina kuka Beby, insha Allah very
soon za mu samu wani." A cikin zuciyarta ta ce, "Babu kamar É—an fari."
########
[12/18, 08:23] Ummi Tandamaí ½í¸‡: *í ½í³”í ½í³”í ½í³” Page 2*
Likita ya turo ƙofa ya shigo tare da sallama, Uncle ya amsa tare da miƙa mishi hannu. Bayan sun gaisa ya
isa gaban A'isha yana tambayar ko ta farka ne? Uncle ya ce "Ta farka yanzunnan." Bayan Æ´an dube-duben
da likita ya yi mata, sannan ya bata magani. Ta yunƙura ta amsa tana sha, bayan ya gama ya ce da Uncle
yana Ofis. Tare ma suka jera bayan sun zauna, Doctor ya dubi Uncle ya ce, "Yallaɓai har yanzun ban gano
cikin nan ba,zai iya kasancewa yana nan haka nan zaya iya kasancewa babu shi, saboda wannan ruÉ—anin
ne ma na yanke shawarar ba zan mata wankin mara ba,in nufin wankin mahaifa,zamu bar ta ta ɗan ƙara
samun lafiya a gama mata ƙarin jinin, sannan in an ƙwana biyu sai ta zo mu duba." Uncle cikin sadaƙarwa
ya ce, "Babu wani abu, Allah ya shige mana gaba." Daga nan A'isha ta ci gaba da amsar magani, sannan
jinin dake zuba ya tsaya ƴan jaje kam ga sunan, Hajiya Jummai ta kawo wannan ƙawa ta kawo wannan
ƙawa, ana musu jaje tana hawaye sai sun fita ta yi ta dariya.
Satin A'isha É—aya aka sallame ta, Likitan ya ce nan da sati biyu ta dawo, kafin ta koma É—akin sai da Uncle
yasa aka yi karatun Ruƙiyya,a cikin shi, bayan ƴan ƙwanaki A'isha ta gyare tamkar ba ta yi jinya ba,ranar
da ta cika sati biyu, Uncle ya ce su koma asibiti ta ce ba ma sai taje ba, domin yau ta tashi da al'ada,
wannan ko yana nufin ba ta tare da ciki. Cikin tausayawa kan shi ya ce "To Allah ya bamu mai amfani."
Haka dai zaman gidan ya koma mata babu daɗi,gurin Uncle kawai take samun sauƙi. Hatta da ƴan aikinsu
ta kula da zata sauraresu, rashin mutunci za su mata. Uche ne kurum babu ruwanshi,sai ko sauran
direbobin gidan,don haka ba ta saka kowa aiki ita take kayanta, duk ranar girkinta zata zage ta yi wa
Uncle ɗinta duk kalar girkin da ranshi zaya ƙwanta ga kalolin abin sha. In ko suka zo ƙwanciya sai ya
kusanceta sau biyu, wani sa'in har da safe yana mai fatan Allah yasa ya samu rabo. Cikin haka sai
ƙwatsam! Aka wayi gari Hadiza ta ƙwanta riris,wai tana da ciki. Shi kanshi Uncle ba ya ce ga dalilinsa da
yasa bai yi murna ba,watan bai ji abin a ranshi ba, sai dai duk da haka ya nuna kulawa gareta,sam bata
yarda ya kaita asibiti ba, sai dai suje da Hajiya Lanti, kuma wai Likitanta daban bata son asibitin da suke
zuwa,bai yi mamakin yanda suke amsar kuÉ—i daga hannunshi ba, domin Hadiza in yana É—akinta kafin ya
ƙwanta da ita sai ta sara mishi kuɗi ya biya, to ballantana tana da ciki. Jin wannan labarin ya saka Hajiya
Jummai cikin ruÉ—u in da ta kuma bazama don zubar da cikin Hadiza kamar yanda take zaton ta fitar da na
A'isha.
Ita ko A'isha ta yi wa Uncle murna har ranta, sannan ta samu damar zana jamb É—inta,fatanta bai wuce ta
haye ba. A'isha tana mamakin yanda har yanzun take jin wasu abubuwa irin na da watan kamar tana son
kaza bata son kaza,sai kuma tashin zuciya wani lokacin wannan lamarin kan É—an É—aure mata kai, amma ta
danganta hakan da cewa me yiwuwa saboda can da tana jin haka ne shi yasa ya zamar mata jiki, don
haka sai kurum ta share. Hadiza dai ana nan anata langaɓe-langaɓe shin cikinne?.
Ranar Litinin da safe A'isha ta gama shiri kenan saboda tana so Uncle ya sauketa gidansu Nafisa, har sun
fito sai taga sabuwar mai aikin da Hajiya Lanti ta kawo,ta shiga É—akin Hadiza da gudu. Tana zuwa ta cewa
Hadiza "Ga maigidanku nan za su fita da Æ´ar gwal" (Sunan da suke kiran A'isha dashi kenan). Nan ko ta ce
"Tabawa bani wayar can in kira shi." Dama Tun da A'isha taga matar ta kallesu ta juya tasan cewa wani
abu zai biyo baya. Har ya taka mota zai shiga sai wayarshi ta soma ruri, ya koma da baya ya É—aga wayar
tare da cewa "Ya ya dai Hadiza?" Cikin kuka ta ce, "Cikina na ciwo." Da sauri ya nufi cikin gidan,tana jin
takunshi sai ta soma birgima. Nan duk ya ruÉ—e ya ce, "Ko muje asibiti ne?" Ta ce, "a'a Hajiyata ta mance
ta wuce da magunguna na gida,ka amso min." Ya fita da sauri. A hannun Jabir ya amshi makullin ya ce
yana zuwa. A'isha tana cikin mota ya ce ta koma gida yaje ya dawo, yaje ne ya amso ma Hadiza magani a
gidansu. Ranta ya É—an sosu, ta sani Hadiza ta yi haka ne don kada su fita da maigidan, ta daure ta ce to ko
Jabiru ya kai ni da wata motar? Ga mamakinta sai ya É—aure fuska,na ce ki koma ki jira ni ko?" Bata kuma
cewa komai ba, ta fito da ƙudurin cewa ta fasa fitar in dai ta koma ciki to ba za ta fita ba.
Tabawa na tsaye tana gadi ta koma ciki tana dariya tana cewa, "wallahi gata nan ta dawo." Dariya Hadiza
ta shiga yi sannan ta É—auki wayarta da sauri ta kira Hajiya Lanti, ta zayyane mata komai, Hajiya Lanti ta
ce"Haba yanzun ki ka soma ta ɓukawa,dama gurin mutumin nan da naje ya bani wani abu wai in bashi ya
sha, to Allah yasa ya sha ɗin yanzun da ya zo zan bashi." Hadiza ta ce "To kawai sai dai in zaki sa a zoɓo."
Ta ce, "To bari a nemo kafin ya zo. Sannan bana son kiyi saken da za'a gane ba cikin nan ba ne,kin ga ta
haka ne zamu samu mu gama dashi." Hadiza ta ce, "kiyi sauri ki nemo zoɓon kafin ya iso, sannan ki nemi
maganin da zaki bashi." Hajiya Lanti ta